Sashe 23
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juwairiyya tana gama karantawa ta É—auko wayarta don ta kira Salima amma ta samu wayarta is switch off, hakan yasa tashi ta je ta tafasa maganin tayi wankan dashi sannan ta karanto Du'a'ul Kanzul Arsh tare da wasu addu'o'i na karya sihiri ta sha ruwan, bata jima da gamawa ba bacci mai nauyi ya É—auketa.
Da ta tashi da asuba da ciwon kai ta tashi wanda ta alaƙantashi da kwanciyar da tayi wuyanta ya lankwashe. Tana idar da sallah ta ƙara ɗaukan addu'o'in kamar yanda Salima ta umurceta ta karantasu ta sha a ruwa wani kuma tayi ta shafa a jikinta. Gari na gama wayewa ta gama aikinta ta tafi makaranta akan idan ta dawo tayi abincin rana zata je ta dubo Hafiz Junior, ta ma manta da cewa wani mai suna Salisu ya ce kar ta je.
Bayan ta dawo gida ta É—aura girki tana yi tana duba wayarta wacce Salisu yake kira akai akai. Tsaki ta ja da taga kiranshi na ashirin da uku tun safiyar yau, ita sai yanzu ma take mamakin yaya aka yi ta iya cigaba da fita tana hira dashi alhali tun farkon zuwanshi bai burgeta ba! Tana gama abinci Mama ta dawo daga aiki take tambayarta me ya samu wayarta Salisu yana ta kiranta bata É—auka?
"Wallahi haushinshi nake ji Mama, kawai ki bashi haƙuri ba zan aureshi ba. Zan jira har Allah Ya kawo mini wani." Ta faɗa tana ajiyewa Mama abinci a gabanta.
"Me kika ce? Sai da auren naku ya matso sannan zaki ce ba zaki aureshi ba?" Faɗin Mama tana dafa ƙirjinta kamar wani babban laifi Juwairiyya ta yi.
"Mama ni yaushe nace zan aureshi? Sai dai in da ke yayi maganar amma ni ban taɓa cewa zan aureshi ba wallahi. Shi ya faɗa miki haka?"
"Kar ki yarda ki fara wallahi domin dukkaninmu ranmu zai ɓaci. Ni zaki watsawa ƙasa a ido Juwairiyya? Ni ce nan na tambayeki ko kina sonshi kika amsa mini ehh zaki aureshi shine yanzu zaki ce kin manta?"
Shiru Juwairiyya tayi tana tunani sannan ta tuna lallai an yi hakan. To amma ina hankalinta yake da zata auri mutum irinshi kamar É—an daudu?
"Sai yanzu na tuna wallahi, amma ni gaskiya na fasa. Ba zan iya auren irinshi ba."
Shiru Mama tayi tana kallonta kamar mai kallon wata baƙuwar halitta, rainin wayon Juwairiyyan har ya kai haka ko dai barinta da tayi tana karatun ne yasa ta fara haɗuwa da ƙawaye masu hure mata kunne? Me yake damun Juwairiyya?
Abun da Mama bata sani ba shine Juwairiyya na fama da sihirin da Salisu ya mata a zuwanshi na biyu. Malaminshi ya bashi kwalli da zai zizara a idanunshi wanda da zarar ta kalli cikin idon nashi shikenan zata faɗa sonshi sannan zata dinga bin maganarshi kamar raƙumi da akala. Haɗuwan Muhammad da Salisu yasa Muhammad ya gane ba haka banza ya barta ba domin kuwa babu abun da bai sani ba game da rayuwar Juwairiyya. Labarin da ake bashi mara kyau akan Salisu yasa ya yanke hukuncin zuwa ya gani da idanunshi. A nan ya gane lalle Salisu yayi halin nashi don dama an ce yana biye-biyen malamai wasu kuma sun ce yana bin ƴan'uwanshi maza, shi Muhammad wannan ba damuwarshi bane, damuwarshi ita ce rayuwar Juwairiyya yanda zai kareta daga sharrinshi domin ya ɗauki alƙawari mai wuya, alƙawarin da yake wahalar dashi har ya jefashi a wani halin da bai shirya masa ba.
"To wallahi baki isa ba. Ba zaki mayar dani mutumiyar banza ba mai baki biyu. Wato karatun da na barki kici gaba da yi yasa kike son ki gagareni ko? To wallahi ba'a gidan nan ba. Sai ki zaɓa karatunki ko aure! In ba zaki yi auren ba ki zauna a gida kin daina fita zuwa makarantan kenan, don haka daga yau na soke zuwa makarantar."
A bazata Juwairiyya ta ji furucin Mama wanda ya saka ta zaro idanunta tana kallonta cike da mamaki da kuma tsoro.
"Mama don Allah kar ki ce haka, nan da sati ɗaya fa zamu fara exams na second semester sannan kice ba zan ƙara fita ba? Ya zan yi da exams ɗin?"
"Sai ki bari wata shekara mai zagayowa ki yita idan kin yi aure kenan, in kuma wata shekarar ma ta zagayo baki yi auren ba sai ki bari sai wata. Batun makaranta kam na sokeshi dama mutane sun fara saka miki ido a kanshi."
Kuka Juwairiyya ta fara wiwi da idanunta don ta lura da gaske Mama ta hanata cigaba da karatun akan wani banza Salisu. To wai ita ina hankalinta yake da ta amince zata auri sakarai irinshi har kuma take fita su yi hira? Tana cikin wannan kukan ne tana bawa Mama haƙuri aka aiko wani yaro wai Salisu yana kiranta a waje, tsabar haushi bata san lokacin da ta fita ta ɗauki takalmi a bakin ƙofa ta jefi yaron dashi ba, Allah Ya taimakeshi ya gani yayi saurin duƙawa takalmin ya wuce ta saman kanshi kana ya fita da gudu bayan ya ɗura mata ashar.
Mama da ta ga komai sai abun ya ƙara ɗaure mata kai game da Juwairiyya, lallai da alama ta fara kufce mata, yaushe ta bari rashin hankalin nata ya kai haka?
"Sannu isheshshiya, nace sannu! Yanzu in takalmin ya bugeshi ya ji ciwo me zaki cewa uwarshi? To wallahi Juwairiyya ki fita a idona in rufe. Karatun na sokeshi sannan idan ba zaki yi auren ba ki fita ki faɗa mishi da bakinki ya daina damuna a office a kan zancenki, wallahi na gaji da fitinarki Juwairiyya. Kullum idan na doso gidan nan na tuna cewa kina ciki kina zawarci sai na ji gabana ya faɗi, na samu kin amince zaki aureshi shine yanzu zaki toɓare? Haba, yarinya ke kaɗai kin hanani kwanciyar hankali? Ke ce wannan gobe ke ce wannan? Kullum maganar da za'a kawo mini a kanki daban nan ma na yarda da tarbiyyar da na baki ne amma ko faɗin bana son in ji ana yi. Da kina gidan mijinki babu wanda zai dinga bin diddiginki shiyasa na gwammace kiyi auren ki huta nima in huta. Haba!" Tana gama faɗin haka ta shige ɗakinta ta bar Juwairiyya na kuka wanda tsananin mamakin kalaman Mama take yi.
Wato ashe ta gaji da kallonta a gidan? Wato gulmarta ake kai mata duk dama bata aikata komai na alfasha ba, in banda riƙe hannunta da Salisu yayi jiya nan ma bata san dalilin da yasa ta yarda har ya shammaceta haka ba. Ai kuwa baƙin cikinta ya ninku ya zo mata har wuyanta ya toshe mata maƙoshi, duk sai ta sauƙesu yau a kan Salisu tunda dama a kanshi ake mata wannan faɗan har aka hanata cigaba da karatunta alhali yanzu shine kaɗai yake ɗebe mata kewa da kuma ɗauke mata hankali kan damuwarta.
Kamar iska ta figi hijabinta dake bakin ƙofar kitchen ta fita waje ta samu Salisu a cikin motarshi ya harɗe hannunshi ɗaya, ɗayan kuma yana riƙe da waya ya kara a kunnenshi da alama ita yake kira domin yana ganinta ya ajiye wayar yana mai tamke fuskarshi. Tana isa gaban motar ta ja tunga ta tsaya tana huci kamar zata ci babu, tsabar masifar da yake nuƙurƙusarta har ta rasa ta ina ma zata fara azalzalarshi.
"Menene ya faru tun da safe ina kiranki kin ƙi ɗauka? Kin san bana son irin haka, in ma wata damuwa ce nace ki kirani ki faɗa mini ba wai ki barni ina ta wahala ba."
"Sannu ubana! Na ce sannu ubana Salisu. Kai ka ganka? Wallahi ka kiyayeni don in ba haka ba sai na maka rashin mutuncin da kullum ka tuna da ni sai ka koka. Mugun mutum mai shiga tsakanin uwa da ɗanta kawai. Auren da nace zan yi kuma na fasa, dama ni ban san ina hankalina yake da har na yarda zans aureka ba. Macuci azzalumi ɗan iska mai riƙe matar da ba tashi ba, ashe dama kai ma ɗan iskan ne ban sani ba? Ashe kaima zuwa kayi ka cuceni ka watsar ko? To wallahi ka ganni nan? Na fi ƙarfinka! Na fi ƙarfi mutum irinka, kuma in kana da zuciya a ƙirjinka kar ka sake tako ƙofar gidan nan da sunan ka zo gurina."
"Yauwa, ga Juwairiyyan da na sani." Faɗin Muhammad yana takowa a hankali yana murmushi mai ƙayatarwa.
Ta juya shima zata masifeshi ya É—aga hannunshi sama alamar surrender ya ce,
"Na zo tambayar meyasa baki zo kin duba Muhammad Hafiz bane."
Ai kuwa nan da nan ta sassauto ta matso gurin Muhammad tana cewa,
"Ya jikin nashi? Jiya nayi ta kiran mamanshi wayarta a kashe, dama akan idan na gama aiki zan je na dubasu ne. Kai kuma me kake jira? Ta juyo ga Salisu ta zare mishi ido wanda sai da ya ji É—arr a ranshi.
Mamaki kuwa yana cikinta tsulum domin har yanzu ya kasa gaskatawa wai Juwairiyya ce take mishi masifa ba! Juwairiyyan da bata mishi musu tana bin umurninshi kamar shi ya haifeta yau shi take yiwa masifa tana zaginshi? Ba dai aikin da Mallam ya mishi ya karye ba? Dama ba wani mai ƙarfi aka yi ba saboda baya son mutane su ankara don a yanzu ma an fara ganoshi. Dubanta yayi a karo na biyu ya ga tana watso mishi harara da alama ba zata daina ba har sai ya bar ƙofar gidan, hakan yasa ya rufe marfin motarshi ya tafi ba tare da ya ce musu komai ba, amma kuwa fuskarshi ta fallasa zuciyarshi wato bai haƙura ba kuma sai ya rama cin mutuncin da Juwairiyya ta mishi.
Dandandandandandan!
"Juwairiyya ina so mu yi magana da ke amma kafin nan ina so ki nitsu ki bani hankalinki."
Confused take kallonshi don bata san me zai faÉ—a mata ba.
"Lafiya kam?" Ta tambayeshi tana mishi iso zuwa inuwar katangar gidansu.
"Ba lafiya ba. Aikan da jiya aka ce miki Salima ce ta aiko miki ba ita ba ce, ni ne! Sannan na saka ta kashe wayarta ne don kar ki kira ta faɗa miki ba ita ba ce ki ƙi amfani da maganin."
"Innalillahi wa inna ilaaihir raji'un! Maganin mallaka ka bani?"
Kallonta yayi kamar wata wawuya yace,