← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 26

Sashe 15

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai ana kiran Juwairiyya a waje." Faɗin wani yaro a can bakin ƙofar gidansu.

Tsaki Juwairiyya ta ja kana tace a ranta an kusa daina mata wannan kiran domin haushi take ji ba kaɗan ba. Amma tunawa da ta yi cewa wataƙila Daddy ne sai ta yi saurin ɗauko hijabinta ta fita domin yau saura kwana huɗu a ɗaura musu aure wanda har gidansu ya fara tara baƙi na nesa amma ita ko ganin idon mijin bata yi ba. Sadakinta kawai aka aiko mata har dubu sittin, sannan Halima tare da wasu ƴan uwan mahaifin nata suka kawo mata ƙuɗi dubu ɗari uku da hamsin na wanda zata sayi sutura da kayan kwalliya.

Tana fita ta ja tunga ta tsaya dalilin ganin motar Muhammad da ta yi, kamar ba zata je ba amma ta ga yanzu ne ya kamata ta mayar mishi da martanin kan addu'a mai  kama da gatse da yayi mata a ranar da zasu rabu. Tana isa bakin motarshi ya fitar da ƙafarshi ɗaya waje ya daidaita zamanshi kana ya ce,

"Na ji labarin zaki yi aure, Allah Ya bada zaman lafiya. Sannan ina tunanin a nan zan dakata da turo miki aika da nake yi tunda zaki koma ƙarƙashin wani."

"Dama ba ni na sakaka ba."

"Nima ban ce ke kika sakani ba, kuma ba don ke name yi ba, ina yi ne don abokina."

"Gori ka zo ka mini kenan?"

Kallon ta yayi wanda in zai iya ƙirgawa yau na goma da tara kenan, murmusawa yayi wanda shi kanshi sai da yayi mamakin hakan. Kuɗi ya ciro a cikin aljuhunshi ya miƙa mata yana cewa,

"Ga gudumawata dubu hamsin, ni ba mai kuÉ—i bane."

"Bana buƙata, tukunna me ya kawoka ne?" Faɗin Juwairiyya cikin gajiyawa, domin ƴar tsiwar da take son ta mishi ma ta kasa.

"Na zo miki bankwana ne, sannan in baki gudumawata. Ko kina tunanin akwai abun da zai kawoni?"

Bata amsa ba kuma bata karɓi kuɗin da yake miƙa mata ba har hannunshi ya gaji ya mayar ya ajiye a gefenshi.

"Ki matsa zan tafi." Yana faÉ—in hakan ya ja murfin motarshi ya rufe.

Bai ƙara seconds uku ba ya bar ƙofar gidan. Ita kuma Juwairiyya jiki ba kuzari ta koma cikin gida, domin wanda take zato ba shi ne yazo ba, shi kuma Muhammad ta so faɗa mishi magana mai zafi amma bata samu damar yin hakan ba, dalilin yayi sanyi sosai ba kamar yanda ta sanshi ba. A da ko gaisuwarta ba ya amsawa amma yanzu har shi yake mata fatan alkhairi a aurenta? Ta wani gurin tana ganin laifinta domin riƙon nata yayi yawa.

Kwanci tashi asarar mai rai. Biki ya zo domin har an yi walima ranar Jumma'a akan washe gari asabar za'a ɗaura auren. Ƙiri-ƙiri Juwairiyya ta ƙi yin kwalliya balle ta yi shiga na alfarma don waliman, a cewarta ba zata ci zamaninta sannan ta ci ta Sumayya ba. Don ita har yanzu bata gaskata cewa aurenta za'a yi ba dalilin har yau bata ga fuskar mijin ba, hakan ya sa a matsayinta na yayar amarya take shige da fice yanda ya kamata. Mama ta so hanata akan cewa ai itama amarya ce amma Juwairiyya ta kafe dole aka zuba mata ido aka barta.

Washe gari aka ɗaura aurensu wanda Halima ce ta kira Juwairiyya cikin tsantsan farin ciki tana cewa cikin waƙa.

"An É—aura, an É—aura. Kin zama matar Daddy Allah na gode ma."

Jin haka ya sa zuciyar Juwairiyya ya buga da ƙarfi, kenan yau ta zama matar wani ba Hafiz ba? Bata iya cewa komai ba ta kashe wayar hawaye na zuba a idanunta. Ita kuma Halima tsabar murna bata ma gane ba domin tana cikin ƴan'uwansu da suka taru don yin ƙaramin wunin taya Daddy aure.

Da rana aka zo É—aukan amarya inda a nan ne Juwairiyya ta ga tijarar Mama.

"Don baki da hankali sai ki fita ba tare da izinin mijinki ba?" FaÉ—in Mama kenan tana hararar Juwairiyya.

Ihu ne kaÉ—ai Juwairiyya bata kurma ba amma sai da hawaye ya É—igo mata, juyawa ta yi ta shige banÉ—aki ta kira Halima don ta tambaya mata Daddy.

"Wannan ba hurumina bane Aunty Juwai, zan turo miki numbernshi ki kirashi ki tambaya da kanki."

"Halima kar mu yi haka da ke don Allah. Wallahi ba zan iya ba, ban san ta yaya zan fara mishi magana ba." Faɗin Juwairiyya tana jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaƙe wuyan Halima.

"A haka zaki koya matar Daddy, zan tura miki yanzun nan." Da haka Halima ta kashe wayarta, itama ta rama.

Juwairiyya tsabar haushi sai da ta naushi gini da ƙafarta, zafin da ta ji yasa ta yi hankali ta sunkuya tana sosa gurin tana wash wash.

Ƙarar shigowar saƙo ta ji a wayarta wanda tana dubawa ta ga numbern Daddy ne kamar yanda Halima ta mata alƙawari. Kamar ba zata kirashi ba amma ta ga in bata kira ba ita ce da asara, ta jima tana burin Allah Ya kawota ranar auren Sumayya ta yi ruwa ta yi tsaki, don haka ta yanke shawarar kiranshi.

Ringing biyu ya É—auka Juwairiyya ta É—aga mishi gaisuwa cikin ladabi kamar yanda take gaisheshi idan ta je gidansu Halima a da.

"Daddy dama ina son zuwa kai Amarya É—akinta ne."

"Babu komai zaki iya zuwa."

"Ai idan na faÉ—awa Mama ka barni ba zata yarda ba, Daddy ko zaka mata magana?"

Sai da yayi É—an jimm wanda har ta fara tausayin kanta sannan ya ce,

"Ki jirani zan zo na kaiki."

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

Marubuciyar Matar Kabila
Fatu A Birni
Ruwan Zuma
Canjin Muhalli

(9)
Zuciya na lugude Juwairiyya ta koma ɗaki inda ta bar ƙawayenta da suka zo tayata murnar aure ciki kuwa har da Salima. Wasu a cikinsu gulma ce ta kawo su domin basu yarda da cewa wai Daddyn Halima ƙawar tasu ta aura ba, wasu kuma suna ganin hakan haɗine daga Allah kuma sun dace da juna, domin kuwa dukkaninsu sun rasa abokanen rayuwarsu zasu tausayawa juna, kuma zasu fi fahimtar juna.

A gefen Salima ta zauna wacce take hira da sauran ƙawayen nata cikin sabo domin suna ɗan haɗuwa a gidan Juwairiyya lokacin da Hafiz yake da rai. Taɓa Salima ta yi wacce take bawa Hafiz Junior kunu a feeder ta rankwafo tana tambayarta menene.

"Wai Daddy shi zai zo ya kaini gidan amaryar."

Wata shewa Salima tayi wacce ta sa idon sauran Æ´an É—akin ya dawo kansu amma Juwairiyya ta yi saurin raba hankalinsu don kar su tambayi menene ya faru. Cikin dabara kuma tasa suka tafi don ta nuna musu itama zata bi tawagar Amarya Sumayya da za'a kai gidan iyayen mijinta da ke nan bayan gidan Sarki.

Ɗaki ya rage daga Juwairiyya sai Salima da Hafsat (Ƙanwar Hafiz) waɗanda suma zasu je gidan amaryar. Suna zaune har ƴan tafiya da amarya suka tafi sannan Daddy ya mata text a waya. 'Ki fito ina waje.' Shine abun da ya rubuta ta ɗauki mayafinta zuciyarta na bugu wanda bata san dalilinshi ba.

Kafin ta fita sai da ta faɗawa Mama wacce ta ƙaryatata sai da ta aika aka dubo mata eh lalle shine sannan ta bari suka fita. Ita ta fara isa bakin window ta russuna ta gaisheshi sannan su Salima ma suka rufa mata baya tare da miƙa gaisuwarsu cikin girmamawa domin ya musu kwarjini ba kaɗan ba, dukkansu kuwa sun san ya haifesu. Sanye yake cikin plain white yadi mai tsada da aka yiwa ɗinkin jumfa da gare sai kuma hularshi ita kuma dark blue, sosai yayi kyau kamar ba ɗan shekara hamsin da ɗori ba.

Daddy cikin sakewar fuska ya amsa musu kana ya dubi Juwairiyya wacce tun fitowarta har lokacin bata kalli fuskarshi ba ya ce,

"Mu tafi ko?"

"Umm Daddy dama Hafsat tana da mota zamu tafi tare kar mu wahalar da kai."

"Ba damuwa amma tunda na zo ku shigo in kaiku."

Juwairiyya bata son musu dashi don dalilin da yasa kenan ɗazu bata ƙara kiranshi ta faɗa mishi cewa akwai mota a hannunsu ba, ita dama buƙatarta ya yiwa Mama magana ne amma kuma sai ya ce zai zo ya kaita.

Juyawa tayi tana kyafta idanu ta kalli su Salima da suke mata dariya ƙasa-ƙasa ta ce,

"Hafsat ki biyomu a motarki, ke kuma Salima ki shigo mu tafi." Ta faɗi hakan tana karɓan Hafiz Junior daga gurin Mamanshi.

Da haka ta zagaya ta shiga gidan gaba tare da yaron sannan ta rufe marfin motar, tana jiran Salima ta shigo amma sai ta hangota ta mirror ta shiga ta Hafsat. Basu kyauta mata ba da suka barta daga ita sai shi, nan da nan kuma ta ƙara nitsuwa domin numfashin kirki wannan bata yi. Shi kuma Hafiz Junior wasanshi yake yi da agogon hannunta bai damu da cewa mamanshi bata kusa ba, ya saba da Juwairiyya domin tunda ya fara gane mutane Salima take turoshi gurin Juwairiyya tare da mai aikinta yayi awa ɗaya zuwa biyu sai a mayar dashi, sannan ita kanta Saliman tana zuwa gidansu Juwairiyya sa'i da lokaci.

"Da alama ƙawarki ta fi son shiga can. Mu tafi ko?" Juwairiyya ta tsinkayi muryar Daddy wanda yake ƙoƙarin kunna mota.

Gyaɗa kai tayi tamkar yana ganinta kana suka fara tafiya su Hafsat na bin su a baya. Hannun Hafiz Junior ta kama tana wasa dashi don ta rasa me zata yi ɗaya taƙamaimai, duk kuwa da sanyin A.C da yake cikin motar wanda ya haɗu da daddaɗan turaren Daddy bai hanata haɗa zufa kaɗan a goshinta ba. She is nervous, she really is.

Sai da suka daidaita akan titi sannan ya tambayeta ina zasu yi, a hankali ta dinga mishi kwatance har suka iso wata magana bayan nan bata haÉ—asu ba. Yana yin parking ta mishi godiya tare da buÉ—e marfin motar zata fita ya dakatar da ita ta hanyar kama hannun Hafiz Junior.

"Dama kina da ƙaramin yaro ne?" Ya tambayeta wanda sarai ya sani bata taɓa haihuwa ba.

"ÆŠan abokin marigayi ne, takwaranshi."

"Allah Ya mishi rahama. Ga wannan ku yiwa amarya liƙi." Da haka ya damƙawa Hafiz Junior bundle ƴan naira ɗari yaron ya karɓe da sauri zai tura a bakinshi.
Chapter 15 · 0% Book details