Sashe 17
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Farko zan fara baki haƙuri akan yanda zaki samu gidana, I'm not trying to belittle or humiliate you amma wannan auren bana sonshi Juwairiyya. Kema kuma na san kin yi auren ne don kaucewa wata matsala da ke shirin faruwa dake to kin ga babu batun ɓoye-ɓoye tsakaninmu. Kin samu abun da kike so, ƙawarki ma ta samu abun da take so sannan nima ta wani gurin na samu relief domin babu wanda zai ƙara mini maganan aure da illolin zama ni kaɗai a gida. Zan ƙara baki haƙuri Juwairiyya don ba zan taɓa zama mijin da kika rasa ba haka nima ba zaki iya maye gurbin matata da na rasa ba. Zan yi ƙoƙarin sauƙe duk wani nauyinki da ke kaina na ci, sha da sutura, in kuma kina buƙatar wani abu kar kiyi ƙasa a gwiwa ki sameni ki faɗa mini, I promise in dai bai fi ƙarfina ba zan saya miki ko in mallaka miki. You are free ki je duk inda kike so amma sai kin faɗa mini, sannan Halima ta faɗa mini kina son komawa Jami'a, zan nema miki addmission da zarar shekara ta zagayo kici gaba da karatunki. Sannan abu na ƙarshe ki kiyaye lafiyarki please, ko ciwon kai kike ji ki faɗa mini mu je asibiti. Kin ji?
"Na ji Daddy." Faɗin Juwairiyya cikin sarƙewar murya kanta a ƙasa.
"Allah Ya bamu haƙurin zama da juna, sai da safe." Da haka ya sa kai ya fice daga cikin ɗakin ya bar Juwairiyya cikin tausayin kanta da kuma sabon gurin da ta tsinci kanta a ciki.
Itama ta sani babu soyayya a tsakaninsu amma yanda ya nuna mata da ita da babu duk É—aya sai ta ji kuka ya kwace mata, minti kaÉ—an da haka ta share hawayen fuskarta don bata ga dalilin zubarsu ba, ko itama ma bata shiryawa zaman aure ba sai da Mama ta matsa mata sannan ta saduda, to tunda ta samu mai irin tunaninta ai faÉ—uwa ce ta zo daidai da zama. Zata rayu dashi duk da cewa babu É—igon sonshi a zuciyarta amma zamansu shine rufin asirinta kuma rufin asirinshi, they are the perfect couple yet far away from perfect.
You should read "TAFIYAR MU" on #wattpad #romance
https://www.wattpad.com/1383895442?utm_source=ios&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_writing&wp_page=create_writer&wp_uname=suwaibamuhammad36&wp_originator=htUPDrz2G495Ia5Bld7VFwthiy1sT1wSebwHtQS7HISK4qDx1GxoviT1wc%2BKX%2BSPJgQAPULmkO3t2ba363Vlw2gx%2FskopTrLIAQf1Tu6FO6pDjACQv3dsR46vyTupZVi
Mum Fateey 👌
TAFIYAR MU
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
Wannan littafin na kuɗi ne a naira ₦500. Masu buƙata zasu biya ta wannan account ɗin 5139579011 FCMB Suwaiba babagana. Ga waɗanda basa son hayaniyar group zasu biya ₦650 a dinga tura musu kullum ta Private.
Free page
(10)
Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah. Yau wata É—aya har da sati uku da auren Juwairiyya da Daddy, sosai ta dawo da jikinta ta murje tayi kyau. Hutu ta samu a gidan Daddy wanda take samun irinshi a gidan Hafiz, bata aikin komai sai girki domin kuwa tana da mai wanke-wanke da shara da take zuwa kullum tana tayata aiki domin har falon Daddy ita take sharewa ta goge, ita kuma sai ta gyara mishi É—akinshi idan ya fita Office.
Juwairiyya bata da damuwan komai sai ta maigidanta da yake treating ɗinta kamar ƴar cikinshi, kullum da safe kafin ya fita aiki zai shigo har sashenta ya dubata ta bashi breakfast ɗinshi a cikin basket ya tafi dashi bayan ya tambayeta ko tana da buƙatar wani abu. Idan tana son fita zai barta baya hanata amma da sharaɗin ta dawo kafin maghrib. Yana dawowa daga aiki da yamma kuwa zai yi wanka ya ci abinci wanda shine na rana kuma na darenshi sannan ya zo ya ƙara dubata ya ji yaya ta wuni sannan ko tana da matsala.
A yanzu da ta fara sabawa dashi ta sake sosai har tana iya kallonshi cikin ido idan tana mishi magana wani lokaci akan abun da yake son a dafa mishi da yake yana da ciwon Diabetes ko kuma wata magana ta daban. Rayuwarsu ta zama kamar na Boss da employee wanda gaskiya ita Juwairiyya ta fara gajiya.
Zamanta da Hafiz ya koya mata juriya a fagen auratayya wanda har daga baya itama ta kama hannu ta zama daidai shi, matsalar da take fuskanta a yanzu shine Daddy ko hannunta bai taɓa riƙewa ba balle ya kirata shimfiɗarshi. Gashi ita ba itace bace domin kuwa tana buƙatar ɗa namiji a rayuwarta musamman yanzu da ta samu hutu, cima mai kyau ga kuma kwanciyar hankali. Sai yanzu ta fara gane dalilin da yasa Mama ta matsa mata tayi aure don ita kanta ta fara gajiya da wannan zaman.
Yau ma video call take da Halima mutanen Turkey wacce tun bayan aurensu da kwana biyu ta koma gurin mijinta.
"Ya zaman naku dai? Da fatan babu wata matsala?" Faɗin Halima tana kwaɓa batter ɗin cake a kitchen ɗinta yayin da laptop ɗin ke gabanta tana kallon Juwairiyya ta ciki wacce take shan Mango a wani ƙaramin bowl.
"Kullum maganarki kenan, ke bakya gajiya ne ko ke uwamu ce?" Juwairiyya ta bata amsa tana cakan guda É—aya da fork kana ta kai bakinta tayi rolling É—in idanunta ga Halima.
"You know you two are my responsibilities, dole ne in dinga bibiyarku don na ga alama kuna da taurin head."
"Halima baki da kunya, Daddyn ne mai taurin kai?" Ta yi dariya.
"Ni kin ji na kira sunan Daddy?" Itama ta yi dariya ta fara juye batter É—in cikin baking pan.
"Ohh da ni kike kenan?"
"Ni na isa Aunty Juwai matar Daddy? Amma seriously ya kuke?"
"Wallahi muna zaman lafiya bamu da matsala, bai taɓa ɓata mini rai ba sai dai ban sani ba ko ni na taɓa ɓata mishi." Ta faɗi iyakar gaskiyanta.
"I'm sorry to ask and I know it's not my place amma ya batun 'the do'?"
"Ya Salam Halima! Zan yi kamar ban ji me kika ce ba." Juwairiyya ta faÉ—a cike da kunya tana hararan Halima.
"Mu bar maganar wasa Aunty Juwai, da ni da ke duk ba yara bane, kuma mun san yaya aka yi auren nan sannan ciwon Æ´a mace na Æ´a mace ce. Wallahi burina yanzu bai fi in ga kuna walwala tare ba kamar kowanne normal mata da miji, I'll love to see that day."
Shiru Juwairiyya tayi tana tunani domin itama tana son ta samu wani su yi maganan ko za'a bata shawara, har yau kuma har gobe babu wanda ya san yaya aka yi aurenta da Daddy bayan Halima. To wa zata je gurinshi ta buÉ—e mishi cikinta in ba Haliman ba? Hakan ya sa ta kaÉ—a baki tace,
"Halima babu wannan batun domin ko yatsata bai taɓa kamawa ba."
Runtse ido Halima tayi sannan ta buÉ—e ta isa gaban oven ta saka cake É—in sannan ta dawo ta zauna kan dogon stool É—in da ke kusa da kitchen island É—in. Sai a lokacin dukkan hankalinta ya dawo kan Juwairiyya wacce ta ajiye bowl É—in Mangon a gefe kamar ya fita a kanta.
"Aunty Juwai wallahi ban yi tsammanin Daddy zai ɗauki wannan lokacin ba tare da ya saisaita tsakaninku ba. Wallahi shi mutum ne mai fara'a da kuma sauƙin kai, tun bayan rasuwan Mummy na lura ya canja sosai but I thought daga baya zai dawo yanda yake ashe I was wrong. Lokaci yayi da zai cire komai a ranshi domin mutuwa tana kan kowa."
Juwairiyya bata ce komai ba illa kaÉ—a kanta da tayi tana aikin tunani, itama tana son Hafiz ya tafi ya barta sannan har yanzu bata mantashi ba balle ta daina sonshi, amma a hakan take son ci gaba da rayuwa kamar kowa tunda mutuwa bata hana walwala.
"Ko kuma ina zaton bai yi tsammanin zaki so ku zauna a matsayin ma'aurata bane domin sai da na mishi barazanar kashe aurena sannan ya yarda."
"Me kika ce?" Juwairiyya ta faɗa da ƙarfi tana zaro idanunta waje cikin mamaki.
"I'm sorry ban faɗa miki ainihin abun da ya faru ba amma hakan ba hujja bace da zai sa ya ƙi ƙarfafa auratayyanku ba. Ke mace ce Aunty Juwai, kiyi amfani da iliminki da wayonki da kuma young jikinki ki jawo hankalinshi kanki ki nuna mishi kina son a gyara wannan auren. Please try."
"Mu bar maganan nan kawai Halima. Ya batun cooking classes É—inki?" Da haka Juwairiyya ta shashantar da zancen ba don ba zata gwada abun da Halima ta faÉ—a ba sai don tana jin nauyinta domin Daddy da yake uba a gareta.
Bayan sun gama hiran Juwariyya ta zauna ta fara tsara yanda zata canja musu Tafiyar tasu, bata ce tana mishi so irin na soyayya ba amma kyautatawan da yake mata yasa ta ji tana ƙaunarshi domin kuwa ai zuciya ma tana son mai kyautata mata. To ko a haka aka tafi ta sani zata ji daɗin zama dashi sannan itama zata yi ƙoƙari wajen kyautata mishi da kuma bashi girmanshi.
Sai da aka yi sallan azahar sannan ta tashi ta ɗaura musu abincin rana wanda zai zarce ya zama na dare kamar yanda suka saba kullum. Kafin la'asar ta gama komai ta sallami mai aikinta kana ta faɗa wanka, cikin lokaci ƙanƙani ta gama shiryawa cikin farar riga mai V neck da baƙin wando wanda yake da adon lace a can ƙafan wandon. Sosai tayi kyau kamar wata ƴar tsana hakan yasa ta dinga juyawa a gaban madubi tana kallon kanta, in ba wanda ya sani ba babu wanda zai ce ta taɓa aure domin jikinta yana nan da ƙuruciyarsa. Ajiyar zuciya ta sauƙe bayan ta nitsu tana ganin suturan da ta saka, yau ne karon farko da zata taɓa saka English wears a gidan Daddy domin kuwa kullum a cikin atampa take watarana har da gyale ko Hijab.
Tana jin ƙarar shigowar motarshi zuciyarta ta buga da ƙarfi amma ta danne kana ta shiga kitchen don kai mishi abinci sashenshi. A da tun kafin ya dawo zata kai ta ajiye shi kuma idan ya ci zai zo ya duba lafiyarta to shikenan sai wata safiyar ko kuma in ya kawo mata abun kwalama da dare.
Sai da ta bari ya shiga É—akinshi ya gama abun da zai yi yana fitowa ita kuma ta shigo hannunta É—auke da tray mai É—auke da warmers É—in abincin.
"Daddy sannu da dawowa." Ta faÉ—a cikin ladabi har tana russunawa kamar yanda ta saba.