Sashe 14
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
(8)
Juwairiyya ta kasa yanke hukunci, tun tafiyar Halima da yamma take kai kawo a ɗaki ta kasa samun nitsuwa, ana ƙoƙarin kiran maghrib yara suka yi sallama sun kawo shopping ɗin month. A tsakiyar gida suka jibge suka tafi Surayya da Walid suka fara ɗauka zuwa ɗakin Mama, daidai nan kuma Juwairiyya ta fito ta nufi gurin Mama da ke can cikin ɗakinta don ta bata shawara kan wannan gagarumin matakin rayuwar tata.
Tana shiga ta samu Mama tana waya don haka ta samu guri ta zauna har sai da ta gama,
"Kika ce duk waÉ—anda suka nemi aurenki kika koresu baki da number su, shi kuma Muhammad fa? Gashi yau ma an ce mini ya yo aika."
"Mama don Allah mu daina ma ɗauko maganan Muhammad, fisabilillahi ina ni ina auren mijin Salima? Wallahi idan ita ce ba zata taɓa auren nawa mijin ba, sannan in dai na auri mutumin nan ko awa biyu ba zan yi ba zamu rabu. Ya tsaneni, nima kuma na tsaneshi."
"Kar ki sake cewa kin tsani mutum, akul in sake jin kin furta haka ga É—an'uwanki musulmi. Kuma don baki da mutunci duk É—awainiyar da mutumin nan yake yi a kanki bakya gani shine zaki jefeshi da kalmar tsana? Uban me ya miki Juwairiyya? Kasheki ya yi ko bunneki ya yi da ranki? A zamanin nan mutum yana iya mutuwa ya bar Æ´aÆ´a amma kaff cikin abokanshi ba za'a samu mai yiwa yaran nan hidima kamar yanda mutumin nan yake miki ba. Baki haihu da abokinshi ba amma a hakan ya nuna har yanzu ba'a rabu ba. Juwairiyya ki kiyayeni, tukunna ma wa kika fitar don ina son sanar da Æ´an'uwan babanku da wuri ba sai an je gurin É—aurin aure ba."
"Na samu Mama. Daddyn Halima ne." Juwairiyya ta faÉ—a hawaye na taruwa a idanunta.
*****
A can gidan su Halima rigima ce ta kacame tsakaninta da mahaifinta wanda ya É—auki zancen a matsayin wasan yara da kuma rashin hankali.
"Daddy don Allah ka amince ka aureta, wallahi tana cikin damuwa domin Maman rantsewa tayi akan in har bata fito da miji ba zata aura mata duk wanda ta ga dama. Gashi a cikin waɗanda ta ƙi har da ƴaƴan baffanunta da suke ƙauye, duk da cewa bamu da tabbacin a cikinsu Maman zata zaɓa mata miji."
"Sau nawa zan faɗa miki bana son ƙara jin zancen nan Halima? In ba zamani da kawomu irin wannan lokacin ba yaushe ɗiya zata nemawa ubanta matar aure har ta dinga tura mishi ra'ayin da baya so?"
"Daddy ka tsaya ka ji mana."
"A zaune ma nake Halima, a zaune nake." Ya faÉ—a yana murmushi yana ganin wautarta a fili.
"Daddy na san idan har na tafi baka yi aure ba wallahi zai yi wuya kayi ɗin, shiyasa na zaɓo maka matar da na san zaka ji daɗin zama da ita sannan zata kula da kai."
"Gashi dama nace miki ina neman baby sitter ko?"
"Daddy please mana."
Shiru yayi yana ganin yanda ta dage ita da gasken-gaske so take yi ya auri ƙawarta. In banda shirme irin na Halima ta yaya zai auri ƴar cikinshi kuma ƙawar ƴarshi?
"To na ji. Ita ta yarda ne zata auri tsohon ƙawarta?"
"A'a tace mini zata yi tunani." Faɗin Halima tana jin tsoro a ranta kar Juwairiyya ta ƙi yin na'am da zancen.
Daddy buɗe jaridarshi ya yi kana ya ɗaura ƙafarshi ɗaya kan ɗaya ya ce,
"Idan ta amince sai ki mini magana in tura gidansu." Ya yiwa Halima je-ki-ƙarata.
Cikin murna Halima ta miƙe tsaye tana cewa,
"I promise you Daddy ba zaka yi dana sanin wannan haÉ—in ba." Da haka ta saka kai ta fita daga falon shi kuma ya bita da ido yana karkaÉ—a kai.
"Yaran yanzu akwai shirme."
Juwairiyya bata sha wahalan samun yardar Mama ba akan aurenta da Daddy, a farko ta nuna hakan ba zai yiwu ba, amma bayan Juwairiyya ta faɗi positive dalilanta na wannan aure sai Mama ta fara sauƙowa.
"Yanzu Juwairiyya tsoho zaki aura kuma baban Halima?"
"Mama ni tsufarshi bata dameni ba, kuma ke ce kika sa na kawo miki shi, kuma gaskiya Mama da in auri wani gwara na auri Daddy."
"Na janye wancan maganan, zan ƙara miki wasu watannin Juwairiyya." Faɗin Mama ganin da gaske ƴar tata ta kafe akan zaɓinta.
Shiru juwairiyya tayi tana tunani, ta sani Mama ba zata ƙara mata lokaci mai yawa ba, to don haka ba taga dalilin da zai sa tayi sake reshe kama ganye ba. Ta sani rayuwarta ta lalace tun ranar da Hafiz ya daina numfashi, jindaɗin da ta samu a baya ba zata taɓa samun irinshi ba a gaba in ba wani ikon Allah ba. Daddy bashi da aibu, yana da kyansa daidai gwargwado ga kuma iya gayu fiye da wasu matasan yanzun. Ɗan boko ne sosai sannan yana da sanin addini ga uwa uba sanyin hali. Sau da dama in ta je gidan su Halima ta ga yanda suke wasa da Daddy sai itama ta ji kewar nata uban, sakin fuskarshi ga ƴaƴanshi bai sa suka ɓaci ba, sai ma kyakkyawar alaƙa da ke tsakaninshi da su.
 Tunda Allah ne Ya kawo mata shi zata aureshi don ta huta da matsalar Mamanta. Ta sani a yanzu ba'a yiwa yara auren dole ko kuma a matsa musu sai sun kawo mijin aure, zata iya yiwa Mama musu amma zuciyarta ba zata barta ta aikata hakan ba. Mama tana sonsu, son da a yanzu duk duniya babu wanda zai musu irinshi, Mama ta musu ƙoƙari tun bayan rasuwar mahaifinsu ita take kula dasu babu mai taimaka mata, a haka har ta aurar da ita ba tare da ta rasa wani necessitys na rayuwa ba. Don yanzu Mama ta matsa mata ta fitar da mijin aure sai ta zama maƙiyyarta? Sai ta bijire mata ta watsa mata ƙasa a ido yanda dangin babanta da ma wasu masu son ganin lalacewarsu su mata dariya? Idan ta bijire mata ta san wani irin bala'i zata tarar a gaba? No! Ta gwammace matsalarta ta tsaya a nan kar ta ƙara yawa. Rasuwar Hafiz kuwa ya sa ta gane duniya ba matabbata bace sannan komai mai wucewa ne. Itama bata da tabbacin ƙara wasu shekaru masu yawa. Wannan kenan.
"Mama idan dai ba wani mugun hali yake dashi ba ki barni in aureshi, da yanzu da nan gaban duk É—aya ne, duk ni É—in ce."
Shiru Mama tayi tana jin tausayin ƴar tata a ranta, ta san ta matsa mata amma hakan shine daidai in ba haka ba zama zata yi ba zata yi auren ba, yarinya ce mai jini a jika, in bata nemi namiji don zama a ƙarƙashinshi ba zata nemeshi don biyan wani buƙata.
"Bashi da mummunan hali, Allah Ya sa hakan shi ya fi miki alkhairi. Amma ban taɓa jin ko sau ɗaya kin ce ya zo gurinki ba." Faɗin Mama cikin damuwa.
"Sau ɗaya ya zo shine na nuna mishi bana ra'ayi, bai sake zuwa ba sai yau ya aiko Halima." Juwairiyya ta yi ƙarya.
*****
"Daddy albishirinka?" Faɗin Halima cikin tsantsan farin ciki ga mahaifinta da ke shirin shiga bacci don lokacin har ƙarfe tara ta gota.
"Gobe zaki tafi?" Ya tambayeta yana dakatawa.
"Haha funny you. Ta amince Daddy, gobe ka shirya ka je ka samu baffanunta ku yi magana."
"Halima wai dama da gaske kike yi?"
Abun da ya faru a gaba ya jawo ɓacin rai tsakanin Halima da mahaifinta har ta kai tana kuka da idanunta, shi tun farkon zancen bai ɗaukeshi a matsayin maganar hankali ba, shiyasa da ta dameshi ya mata kora da hali. Saboda ya san ƙawar tata ba zata yarda ta auri tsoho mai shekara hamsin da biyu ba (52). Yana son ƴaƴanshi ya kuma sabar musu da su zauna su yi wasa da dariya dashi don haka da ta kawo wannan zancen sai ya ɗaukeshi a matsayin raha, ashe da gaske take yi.
"Daddy kar ka mini haka, wallahi na kwaÉ—aita mata wannan auren har ta sanar da mahaifiyarta duk sun yarda kai kawai ake jira ka gabatar da kanka. Ka rufa mini asiri kar kasa in ji kunya." FaÉ—in Halima tana share hawayen fuskarta.
"Ni da nake matsayin uba a gareki Halima ban miki auren dole ba saboda na san illanshi, amma yau ke kike neman tursasani in yi auren da ban shirya mishi ba? Babu batun aure a gabana Halima, rayuwar auren da nayi da mahaifiyarku ya isa sai kuma Allah ya haɗamu a Aljannah. Ki bata haƙuri, sannan ita ma mahaifiyar tata ki bata haƙuri."
Kuka cur-cur Halima take yi da idanunta, Daddy na neman wargaza mata plan. Sannan ba zata iya tafiya ta barshi shi kaɗai ba sai dai ta kashe aurenta ta dawo su zauna. Zata iya haƙuri da auren nata don shi ya rayu, ta rasa Mummy ba zata so shima su rasashi ba. Shine kaɗai katangar su and she can do anything don ganin bai tafi ya barsu ba.
"Shikenan Daddy, na san ban isa in maka dole ba amma wallahi ba zan barka kai kaÉ—ai a cikin gidan nan ba. Zan kirashi ya sakeni sai in dawo mu zauna, wallahi na gwammace in kashe aurena da in rasaka ko in barka cikin halin maraici."
"Kar ki kashe aurenki Halima, ki faÉ—a mata gobe zan je mu gana da iyayenta." Shine abun da Daddy ya faÉ—a kana ya tashi ya shige É—akinshi zuciyarshi na mishi zafi.
Yasan halin Halima, sosai zata iya kashe aurenta ta dawo su zauna, shi kanshi ya san zamanshi shi kaɗai bashi da amfani, saboda disadvantages ɗinshi ya fi yawa akan advantages ɗin. Amma me yasa ba zasu gane cewa Sadiya ita ce rayuwarshi ba? Sannan tafiyarta ya tafi da duk wani sha'awarshi na aure? Tsabar son da yake mata ya kasa yi mata kishiya, sannan tana haihuwar ƴa mace ya mayar da sunanta don ya nuna mata ta fi kowa a gurinshi. Ba haka ya so ba, amma tunda Halima ta kafe sai yayi auren, da ita da ƙawar tata duk zasu yi regretting daga baya, sannan ita Amaryar da kanta zata nemi saki ba sai ya miƙa mata ba.