Sashe 12
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga ranar bai sake waiwayarta ba, sai dai kuma bai fasa aiko mata shopping kowanne month ba.
Ko da ta dawo cikin gida Mama ta tambayeta me ya faru cewa ta yi ya nemi aurenta tayi declining domin ba zata munafurci Salima ba, Juwairiyya bata ga amfanin yiwa Mama ƙarya ba domin shi da bakinshi ya faɗa mata sun yi maganar da ita.
"Allah Ya kyauta." Kawai Mama tace, daga nan kuma bata ƙara ɗago mata zancen Muhammad ɗin ba.
A nan Juwairiyya ta dawo daga dogon tunanin da take yi ta dubi Mama da tayi kasaƙe tana kallonta tace,
"Ki bani wata uku zan nemi É—aya daga cikin zawarawan nawa in aura sai a haÉ—a aurena da na Sumayya."
"Ke kika yankewa kanki lokaci ba ni ba, don haka idan lokacin nan ya cika baki fito da mutum ɗaya ba wallahi, wallahi Juwairiyya kin ji na rantse? Ni da kaina zan zaɓi ɗaya daga cikinsu a ɗaura muku aure! In kin ga dama ki bijire a nan ne kuma zaki gane duniya budurwar wawa ce."
Mum Fateey 👌
TAFIYAR MU
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064
(7)
Yau Ilyas ya zo gurin Juwairiyya, abun mamaki yana aikawa kiranta bata ɓata lokaci ba ta fito, sannan ta ƙara bashi mamaki ta hanyar yi mishi sallama tare da ɗaga mishi gaisuwa. Tunani ta yi mai zurfi, duk maneman nata da suka rage Ilyas ne kaɗai ta ga zata iya rayuwa dashi in har ta faɗa son shi. Sauran kam ko tunaninsu bata so kwakwalwarta ta kawo mata.
Shi kuma Ilyas tsabar murna kasa rufe bakinshi yayi, a jikin motarshi ta jingina yayin da shima ya fito ya tsaya a gefenta. Bayan Æ´an gaishe-gaishe su ka É—an yi shiru na wasu Æ´an seconds kafin ya buÉ—i baki ya fara magana.
"Alamu sun nuna addu'ata ta karɓu, na ɗauka akwai sauran aiki a gabana Hajiya Juwairiyya."
"Hmm." Kawai tace don bata san me zata faÉ—a ba.
Basu jima ba ta koma cikin gida domin tuni hirar ya gundureta ba don kuma Ilyas bai burgeta ba, a'a haka kawai ta ji bata son su tsawaita hiran. Tun daga ranar suka fara soyayya a hankali har ta kai Juwairiyya na iya hira da shi cikin walwala a nan kuma ta gane ta kamu da son Ilyas. Ita a rayuwarta idan namiji ya iya soyayya nan da nan zai sace zuciyarta, sannan ya dinga martaba mace ya ɗauketa a matsayin abu mai tsada abar tattalawa kamar yanda Hafiz yake cewa. Ta ɗauka ba zata taɓa samun namiji irinshi ba amma sai gashi Allah Ya kawo mata Ilyas duk da cewa bai kai Hafiz ɗinta ba. A hakan ma ta godewa Allah sannan tana ji a jikinta in dai ta aureshi zasu zauna lafiya domin tana da labarin matarshi tana da hankali bata da fitina ko kaɗan, to me ya fi ranta?
Wata ɗaya har da sati biyu da fara soyayyarsu ta ji shiru bai mata maganar aure ba, hakan yasa da aka ƙara sati biyu ya zama saura mata wata ɗaya wa'adinta ya cika ta yanke shawarar mishi magana.
Yau ma ya zo hira kamar kullum tana jingine a jikin motarshi wacce ya mata nacin su dinga shiga ciki suna hira amma ta ƙi. Saboda ko a lokacin da take budurwa bata shiga mota ta yi hira da saurayi, saboda bayan Mama ta haneta ita kanta ta san abun da zai iya faruwa a ciki ba mai kyau bane.
"Ni fa sanyi nake ji a wajen nan, nayi da ke mu shiga mota mu yi hiranmu a ciki amma kin fi son sanyi yayi ta shiga jikinmu."
Murmusawa kawai Juwairiyya ta yi kana ta fara tunanin ta yaya zata É—auko mishi zancen tunda in a al'adance ne namiji ne yake fara kawo maganar aure ita kuma ta amsa.
"Bikin Sumayya yanzu saura wata É—aya."
"Haka dai muke ta lissafi tare. Allah Ya nuna mana da rai."
"Ameen Ameen." Ta amsa sannan ta yi shiru.
"Ya dai naga kamar kina cikin damuwa?" FaÉ—in Ilyas yana matsowa kusa da ita.
Idan za'a tambayi Juwairiyya aibun Ilyas abu guda zata furta shine bai ɗauki taɓa macen da ba nashi ba a matsayin zunubi. A farkon zuwanshi yana respecting space ɗinta, amma suna fara sabawa ya nemi ya riƙe hannunta tare da son su shiga cikin mota su yi hira, babu ɓata lokaci ta nuna mishi bata son hakan don bata manta da cewa laifi ne mai girma aikata hakan ba.
"Wallahi Mama ce ta damu wai sai a haÉ—a aurena da na Sumayya. Na ce mata ni dai har yanzu baka mini maganan ba."
Shiru Ilyas ya yi, can kuma yace,
"Dama tuntuni ina son mu yi wata magana da ke amma na rasa ta yaya can É—auko miki ita."
Jin furucinshi yasa cikin Juwairiyya ya kaɗa, nan da nan kuma ta fara addu'an Allah Ya sa ba cewa zai yi ba zai aureta ba, domin in har ya mata haka ya kassarata. Duk manemanta dama ƙalilan ne suka rage, a hakan ma tana fara soyayya da Ilyas ta koresu don ita tace ba zata yaudaresu ba, ba zata haɗa manema da yawa a lokaci ɗaya ba. Ilyas kuma da niyyar aure ya zo mata domin har bincike ta sa anyi mata a kanshi aka ce bashi da aibu. To me zai faɗa mata?
"Ina jinka." Kawai ta iya cewa dashi tana sauraronshi.
Gyaran murya ya fara kana ya gyara tsayuwarshi ya fuskanceta tarr yace,
"Juwairiyya ina sonki ina kuma da niyyar aurenki, sai dai a yanzu matata ta samu labarin ina nemanki muna ta fitina a gida. Yanzu abun da nake so dake shine ki yarda mu yi auren sirri tsakaninmu, zan baki sadakinki ba tare da kowa ya sani ba sai mu biyu, da zarar nayi settling É—in matata sai mu bayyana auren ki zo ki tare."
Shiru ta yi har na tsawon minti ɗaya kanta a ƙasa tana tunani, shi kuma Ilyas ido ya zuba mata yana ta gyara tsayuwarshi kamar mara gaskiya. Can Juwairiyya ta ɗago kanta da ɗan guntun murmushi a fuskarta tace,
"Shikenan zan yi tunani a kai. Amma yaya batun....?" Ta nuna kanta sannan shima ta nuna shi.
Ƙura mata ido yayi yana son fahimtar me take nufi, kashe mishi ido ɗaya ta yi wanda hakan yasa fuskarshi ta washe hakwaranshi suka bayyana cikin farin ciki.
"Yauwa Æ´ar gari, wannan ba matsala bace. Nuhu abokina da name baki labarinshi yana da gida a nan cikin New GRA, unguwar ma ba'a gama cika ba kuma gida ne mai kyau. A can zamu dinga zuwa muna rage zafi har lokacin da zamu bayyana auren."
"To idan nayi ciki kafin nan fa?"
"Zamu yi amfani da protection ko kuma ki sha maganin hana É—aukan ciki." Ya faÉ—a hankali kwance kamar dama ya jima da wannan nazarin.
"Da alama ka jima kana tunanin nan, amma kuma meyasa tun zuwan ka baka faɗa mini hakan ba ai da yanzu an wuce gurin, nima da na samu sauƙi."
Wata dariya Ilyas ya saka Juwairiyya kuma ta murmusa tana kallonshi.
"Ke É—in ce an bani labarin kina da zafi, gashi kuma in bakya son abu babu mai sakaki dole. Amma dai nace musu sai dai in ba'a bi dake yanda kike so ba. Kin ganni nan? Bana son na ga ana takurawa mace ko kaÉ—an, ku mata sai da lallami."
"Hakane kam. Kuma idan mutum yana son yin zina da mace zai iya shafe har wata biyu yana bibiyarta don buƙatarshi ta biya. Su waɗanda suka faɗa maka ina da zafin sun manta basu faɗa maka cewa ina da ilimin addini ba, sannan ni ba shashasha ba ce."
Nan take annurin fuskarsa ta É—auke, domin sai a yanzu ya gane cewa shigo-shigo-ba zurfi ta mishi. Fuskarshi ya tamke don ya san daga yanzu duk wata kalma da zata fito daga bakinta ba lallai bane ta mishi daÉ—i ba.
"Ilyas ka bani mamaki ka kuma saka na ƙara tsorita da mazan yanzu. Masu hali irin naka sun zo amma da buƙatarsu suke zuwa a tafin hannunsu babu ɓoye-ɓoye, kai kuma sai da ka yaudareni da kyawawan hali har na faɗa sonka. Wallahi ni ba mazinaciya bace Ilyas, sannan na ɗauka zuwa kayi ka rufa mini asiri ashe kai tona mini asiri ka zo yi. Ka yaudareni ka kuma cuceni, Allah Ya saka mini." Sai a lokacin muryarta ta fara rawa ta nufi cikin gidan su cikin sauri tana share hawayen da ya zubo daga fuskarta.
Bata kai ga shiga É—aki ba ta ji ya kunna motarshi ya tafi, ta yi tsammanin zai kirata ya ce gwadata yake yi, amma shirunshi har ta shigo ya nuna cewa da gaske yake. Kuma tunda bai samu abun da ya zo nema ba ya tafi.
Baby wanda ya ga shigowar Juwairiyya balle ya ga halin da take ciki, tayi kuka sosai domin ta san in ba mutuwa ba bazata samu kanta a cikin wannan halin ba, da Hafiz ɗinta yana raye da babu wani ɗan iskan garin da zai zo ya nemeta da lalata, ashe an yi gaskiya da aka ce 'Mutuncin mace ɗakin mijinta' ashe aurenta ba ƙaramin rufa mata asiri yake yi ba. Yanzu ina zata saka kanta? Ga wa'adin Mama saura wata ɗaya ya cika! Da waye zata haɗata in bata nemo mijin auren ba? Da wannan tunanin Sumayya ta shigo ta sameta, amma ko da ta tambayeta me ya sameta bata iya faɗa mata ba, da haka ta lalatar da zancen.
Sati É—aya da haka Mama ta lura babu mai zuwa gurin Juwairiyya, hakan yasa ta kirata don a yanzu da biki ya saura sati uku tana son sanin halin da take ciki.
"Mama shima Ilyas yaudarata ya zo yi ba aurena zai yi ba."
"Ina jinki." FaÉ—in Mama tana tsareta da ido.
A nan Juwairiyya ta faɗa mata yanda suka yi wanda ya bawa Mama mamaki kwarai da gaske domin itama ta sa an mata binciken halayenshi da ta lura hankalin ƴar tata ya fi karkata kanshi. Ashe a ɓoye yake iskancinshi shiyasa ba'a gane ba.
"Kina da sauran sati uku, a cikin waÉ—anda kika koran sai ki kira wani ya dawo ku daidaita."