Sashe 11
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nagode da wannan karamcin Salima, Allah ne kaÉ—ai ya san daÉ—in da naji a cikin zuciyata. Kin kyauta mana ba kaÉ—an ba, Allah Ya bar zumunci Ya kuma raya mana Muhammad Hafiz."
Dukkan Æ´an É—akin suka amsa da 'Ameen'. Basu jima sosai ba suka tashi tafiya aka basu cincin É—in suna.
"Ni wallahi ku bari zamu hau napep ni da Sumayya, ke kuma Hafsat sai ki sauƙe Zainab a gidanta kar zagayen ya miki yawa." Faɗin Juwairiyya a lokacin da suka fito waje.
"Ai yanda na ɗaukoki haka zan mayar dake har ƙofar gidan Mama, babu abun da zaki faɗa da zai hanani kai ku."
"Ke dai kina son wahalar da kanki wallahi, mu je to kar maghriba ya sameku a hanya."
Bayan sun sauƙesu suka shigo gida, a nan Juwairiyya take labartawa Mama irin karamcin da Salima ta mata, yanda ta sa aka fasa saka sunan Babanta aka saka na Hafiz."
"Kai Masha Allah ta yi ƙoƙari sosai Allah Ya bar zumuncin da ke tsakaninku."
"Da bata yi casting mijinta out irin haka ba, yanzu mu mun É—auka shi yayi niyyar yiwa abokinshi takwara alhali ashe ita ce."
"Koma yaya ne duk sun yi ƙoƙari amma ba zan taɓa mantawa da Salima ba, ta cika ƙawar amana."
Mama kallonsu kawai take yi bata sake cewa komai ba, har suka gama hiransu suka watse.
*****
Bayan shekara É—aya.
Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata faÉ—a kamar yanda ta saba kullum idan bazawari yayi sallama a waje tace ba zata fita ba.
"Na san kina son mijinki kika rabu dashi amma kin ga rayuwar nan bata da tabbas, yanzu gashi nan rubibinki ake yi amma gaba kaɗan zaki ga yayinki ya wuce an rasa mijin auren. Ki yi amfani da opportunity ɗin da kike dashi a cikin maneman naki ki darje ki zaɓi wanda zuciyarki ta aminta dashi, kiyi aurenki ki rufawa kanki asiri. Juwairiyya baki da ɗa baki da jika aure ba zai baki wahala ba kuma ba zaki rasa kalan mijin da kike so ba, kar kiyi wasa da damanki har ya kuɓuce miki. Zawarawa masu ƴaƴa suke wahala wajen samun mazajen aure domin mazan yanzu basa son ɗawainiyar kowa, wani idan zai samu a riƙe mishi ƴaƴanshi ma zai yarda. Kuma na faɗa miki ba zaki koma makaranta ba muddin kina zaune a cikin gidan nan, wallahi ba zaki janyo mini bakin jama'a ba ana shigowa gidan nan ana ƙirga zawarawan ciki ba."
Surayya har ta buɗi baki zata yi magana sai kuma ta rufe, da cewa zata yi a littafin Ruwan Zuma haka Ummii wato uwar Laila ta faɗa mata, sai dai da ta tuno irin ɓacin rai da zai biyo baya sai ta gimtse bakinta. Yaushe ma aka bata wayar? Kwata-kwata yau wata biyar ne shine zata ƙara yin wani wawancin? Ba dai ita ba!
"Ina miki magana kin yi shiru." Mama ta faÉ—a a hasale.
"Kiyi haƙuri Mama."
"Ni ba haƙuri zaki bani ba, cewa na yi ki zaɓi miji kiyi aure."
Shiru Juwairiyya ta yi kanta a ƙasa tana tunanin rayuwarta a gidan mahaifiyarta ya fara zama takura a dalilin maganar aure da ake mata kullum sai dai in ba'a yi sallama a waje ba. Karatun da take son farawa an hanata, sana'ar girke-girken ma Mama ta hanata a cewarta in Juwairiyya ta saba da riƙe ƙuɗi da zaman kanta zata ƙi auren. Yau shekara ɗaya kenan har da wata shida da rasuwar Hafiz, maza kala-kala sun kawo mata cafka, wasu da kyakkyawar niyya wasu kuma da neman banza babu ko kunya a tattare da su.
Duk cikin maneman nata babu wanda ya mata, to ma yaushe ta yarda suka saba har soyayya ta samu shigowa? In Mama ta matsa mata fita waje bata wuce minti biyar da duk wanda ya ziyarcetan zata dawo gida, irin tarɓan da take musu kuma ya jawo da yawa basa dawowa sai ƙalilan masu naci, ciki kuwa har da Ilyas magidanci ɗan unguwarsu. Matarshi ɗaya da ƴaƴansu biyu, ba wani babba bane don ta tabbata zai yi sa'an Hafiz. Sosai yake mata naci har Mama ta san da zamanshi domin ya shigo sau biyu ya gaisheta.
Sannan ga Hussani da yake damunta wanda har tana tunanin kanshi ba ɗaya ba, tun tana lallaminshi su rabu lafiya har ta dawo tana ɗaga mishi murya tare da faɗa mishi baƙaƙen maganganu, sai dai duk da wannan wulaƙancin da take mishi bai sa Hussaini ya nuna ko sau ɗaya ranshi ya ɓaci ba, naci kuwa sai abun da ya karu. (Da alama dai ya karanta Ruwan Zuma kuma yana son ya kwaikwaya).
Sannan ga Muhammad, zuwanshi ya fi na kowa ɓata mata rai. Tana tunawa bayan haihuwar Salima da wata ɗaya ya zo kawo mata shopping ɗin monthly da ya saba ya nemi zai gaisa da Mamanta. Bata kawo komai a cikin ranta ba don haka ta mishi iso kana ta fita a falon ta barsu. Abun da ya bata mamaki shine tsawon lokacin da ya ɗauka yana magana da Mama, me suke cewa? Ta je bakin ƙofar da niyyar gulma suka ci karo a yayin da yake fitowa.
"Sorry." Ta bashi haƙuri tana jin takaici a ranta domin bata samu ta ji komai ba.
"Ki rakani mota akwai saƙon da zan baki." Ya ce da ita bayan ya sanya takalmanshi.
"Ka bawa yara su kawo mana." Ta faÉ—a tana shiga falon. Sai dai irin muguwar kallon da Mama ta mata yasa ta dawo waje ba shiri ta bi bayanshi.
"Lukuti kawai." Ta furta a hankali tana ganin yanda ƙeyarshi ta tara tsoka yana kuma tafiya ɗai-ɗai tsabar ƙiba.
A bakin motarshi Juwairiyya ta tsaya wacce tun zamanin samartaka da ita yake yawo wanda a yanzu har ta fara gajiya dashi ta kuma tsufa.
Zama yayi a cikin motar bayan ya É—an wahala sannan ya dubeta fuskar nan babu annuri ya ce,
"Tun ba yau ba naga kin fara tsayuwa da masu neman aurenki, hakan yasa nima yau na nemi izinin Mamanki don ina son fara neman yardarta kafin in zo gareki. Idan kin amince bana son dogon nema a É—aura auren ki tare."
Sai da ta ɗauki seconds goma maganarshi na yawo a brain ɗinta sannan ta kwashe da dariya. Sosai take yi har masu wucewa suna dubanta, hakan yasa ta tsuguna tare da ɓoye fuskarta a cinyarta taci gaba da yi jikinta na girgiza.
Sai da tayi dariyar mai isarta sannan ta miƙe tsaye tana share hawayen idanunta lokaci ɗaya kuma tana danne wata dariyar da ke son kwace mata. Bai ce mata komai ba amma ya haɗe rai sosai har sai da fuskarshi ta ɗan yi ja.
"Wai idan kin amince...Mwhahahaha....bana son dogon nema.... a ɗaura auren ki tare....Mwhahahaha" Ta ƙara kwashewa da dariya wannan karon har da riƙe ciki.
"Me amsarki?" Kawai ya tambaya yana nazarinta.
Sai da ta saita kanta sannan tace,
"Maza baku da ta ido wallahi. Yanzu ni da nake ƙawar matarka kuma matar abokinka...."
"Late, you should add late."
Nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke ta dubeshi sama sa ƙasa sannan ta ce,
"Ba sai ka tuna mini cewa baya doron ƙasa ba, tsayawarka a nan tare da ni kaɗai ya isa ya tuna mini cewa mijina ya mutu. Kar ka ƙara zuwa ƙofar gidan nan da wannan zancen domin na farko, ni ba butulu ba ce, ina zumunci da matarka ba zan taɓa cin amanarta ba. Na biyu kuma har abada ba zan taɓa auren ɗaya daga cikin abokan Hafiz ba, domin hakan zai zama tamkar cin fuska ne a gareshi, ba zan wulaƙantashi ba. Sannan na uku, Muhammad, wallahi ko na rasa mijin aure ne ba zan aureka ba. Da mutum irina da mutum irinka ba zasu taɓa zama a ƙarƙashin rufi ɗaya ba, in kuma aka kuskura aka haɗasu to sai dai gobara. You hate me, nima kuma na mayar maka da daidai naka. Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shine kar ka kuskura ka nunawa Salima cewa mun yi wannan maganan saboda bana son alaƙar mu ya samu matsala."
"What if shi ya nemi hakan?" Muhammad ya tambayeta yana kafeta da ido.
"Shi waye ya nemi me?" Ta mayar mishi da tambaya don yayi confusing É—inta.
"What if Late mijin naki ne yace in nemi aurenki idan ya bar doron ƙasa?"
"Stop saying 'Late' i know he is late." Ta faɗa a harzuƙe.
"Hmm."
"And you are lying, kai ne ka sakashi ya maka alƙawarin idan ka mutu ya auri matarka Salima kuma ya faɗa mini tun a ranar saboda tsakanina dashi akwai kyakkyawar alaƙa bama ɓoyewa juna komai."
"To bai faÉ—a miki duka ba, he asked me to marry you too."
"Ƙarya ne."
"Ba zan taɓa yiwa mai rai ƙarya ba balle mamaci, ƙarya bata cikin halayena." Ya faɗa a hankali kamar ba shi ake yiwa ihu a kansa ba.
Shiru Juwairiyya ta yi domin ba haka ta so ba, ta so ne yayi losing mind ɗinshi ta cire filtern bakinta ta zageshi tatas, amma calm demeanor ɗinshi ya hanata hakan. He is too calm for her liking, kuma hakan na sakata jin baƙin ciki kamar ta kurma ihu.
Ganin ta yi shiru tana cika tana batsewa yasa ya kunna motarshi kana ya ja ƙofar ya rufe ya dubeta ya ce,
"Me kika ce? Zaki aureni?"
"Ko sunana baka taɓa ambato a bakinka ba, ko sunana baka taɓa sauraron harshenka ya furta ba, balle a kai ga so har aure."
"Ba wannan na tambayeki ba."
"Ba zan taɓa aurenka ba ko mazan duniya sun ƙare." Ta bashi amsa a numfashi ɗaya tana hararanshi.
"Shine final say É—inki ko zaki yi tunani?"
Wani malolon baƙin ciki ne ya zo ya tokare a maƙoshin Juwairiyya ta ji kamar ta fara kuka, wai bai ji abun da ta faɗa bane, meyasa ba zai yi fushi su yi uwaka ubanka ba?
Bakinta har rawa yake yi tsabar ɓacin rai ta ce,
"Har abada."
"Dama mun yi dashi akan sai kin ƙi amincewa kafin in barki. Allah Ya gani na cika alƙawari, ke kuma kar ki ce ban taya ba. Allah Ya bada sa'an neman mijin aure." Da haka ya yiwa motarshi giya ya tafi.