Sashe 18
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daddy da bai yi expecting ganinta haka ba sai ya tsaya yana kallonta da alama tafiyar zata yi kyau. Bai amsa ba hakan yasa ta yi gyaran murya ta matso kusa dashi tana kallonshi innocently tace,
"Daddy baka da lafiya ne?"
Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya shiga sannan ya juyar da kanshi kan dinning table inda ta jera mishi abincin ya ce,
"No, lafiyata kalau. Kina lafiya?"
"Lafiya kalau, sai zaman kaÉ—aici. Gidan shiru babu kowa watarana har tsoro nake ji."
"Uhm, zaki saba a hankali Juwairiyya. And ki daina jin tsoro babu abun da zai sameki."
"To Daddy." Ta faɗa tana murmushi sai can kuma murmushin nata ya faɗaɗa tayi wani guntun tsalle ta riƙo hannunshi tana cewa, "Daddy albishir!"
Ƙaramin ruɗewa yayi ko kasa numfashi yayi ne bata gane ba amma bai amsa wannan albishir ɗin da wuri ba sai da ta ƙara maimaitawa. Hannunshi kuwa da ta maƙale a ƙirjinta tana bouncing shi Daddy yake kallo sai kuma ya dawo ya kalli fuskarta.
"Goro." Yayi gyaran murya yana ƙoƙarin zame hannun nashi amma ta ƙi sakinshi.
"Na duba internet na samu dishes irin naku masu diabetes da yawa shine yau na maka kunun acca da cookies sugar free."
"Sounds amazing, to nagode bari in ci abinci da cookies É—in sai anjima da dare in sha kunun. Kin ga yau babu shan fruits."
"To Daddy, bari in ɗauko maka Cookies ɗin." Da haka ta fita daga falon cikin walwala har ta ɓace masa da gani.
"Ya Allah." FaÉ—in Daddy yana takawa zuwa dinning table.
Yana fara zuba abinci a plate Juwairiyya ta dawo hannunta ɗauke da wani kyakkyawan ƙaramin tray da cookies ɗin a ciki, a gefen Daddy ta ajiye sannan ta matso kusa dashi har jikinsu na gogan na juna ta ce,
"Bari in saka maka." Da haka ta karɓe serving spoon ɗin ta ƙarisa saka mishi ya fara cin abincin jiki a sanyaye.
Abun da ta lura dashi shine kamar ya rage walwala, ko dai da gaske baya son mu'amala da ita. Ji tayi gwiwanta yayi sanyi ta fara waswasi a ranta ko dai bata burgeshi bane? Ko dai tayi zumuɗin yayi yawa ne? No! Bata fara don ta bari ba! Dama ba lokaci ɗaya zata karkato da hankalinshi gareta ba, dole sai ta ɗauki lokaci kuma sai ta jajirce. A ƙarshe tana fatan Allah Ya sa wanka ya biya kuɗin sabulu.
"Abincin yayi daÉ—i?" Ta tambayeshi bayan ta dawo da walwalar fuskarta sannan ta zauna a gefenshi.
"As always Juwairiyya. Na faÉ—a miki girkinki yana mini daÉ—i, nagode."
Murmushi ta yi wannan karon har cikin ranta wanda yasa kumatunta suka lotsa ciki kana ta miƙe tsaye tana duban agogon hannunta ta ce,
"Bari in barka ka huta, sai anjima Daddy." Ta haka ta fita daga cikin falon bayan ta ɗauki Cookie ɗaya tana humming waƙa a hankali.
Tana shiga ɗakinta ta rufe ƙofar kana ta jinginu da gini tana gwalalo idanunta waje, lallai ta cancanci a jinjina mata. Daddy da take jin kunyarshi yau shi take ƙoƙarin seducing? But amma bature yace desperate times call for desperate measures, Daddy mijinta ne halalinta ba wani random mutum a waje ba don haka zata iya yin komai don ganin ta inganta wannan zama nasu da bata san yaushe ne ƙarshenshi ba.
A ƙa'idan Daddy idan ya dawo daga office zai zauna a gida har sai an kira maghrib, daga nan kuma in ya fita ba zai dawo ba sai an yi isha. Don haka Juwairiyya tana ganin an yi isha ta yi wanka tare da canja kaya wannan karon zuwa wata doguwar riga ɗinkin bubu da aka yiwa aiki da stones. Sosai take walwali sannan ta yiwa kanta simple kwalliya wanda ba zai sa ace she is trying so hard ba. Da haka ta kallaba ɗauri mai ƙayatarwa kana ta nufi sashen Daddy bayan ta ɗauka mishi kununshi.
Da sallama ta shiga ta samu yana zaune a ƙasan carpet yana karatun Jarida da gilashi a idanunshi, sanye yake cikin jallabiya fara tass wacce ta mishi kyau ba kaɗan ba a fuskar juwairiyya. Ta lura in dai ya dawo gida kayan sakawanshi kenan don yana dasu design kala daban-daban kusan ashirin a wardrobe ɗinshi wanda take gani in ta je mishi gyara.
"Daddy sannu da dawowa. Ga kununka." Ta faÉ—a tana ajiye flask É—in a kan dinning table.
"Sannunki da É—awainiya, ki sako mini a kofi."
Da haka ya koma karatun jaridarshi Juwairiyya kuma ta zuba mishi kunun tare da saka mishi irin sugarn su sannan ta gauraya ta tako zata kawo mishi. Da gangan tayi ɗan tuntuɓe kaɗan wanda tayi kamar zata faɗi amma ta tare kanta, Daddy cikin azama ya miƙe yana tambayarta lafiya kana ya yiwo kanta ya kamo hannunta tare da karɓan kofin yana mata sannu.
"Subhanallahi, Juwairiyya garin yaya haka? Ina baki ji ciwo ba kuma kunun bai zuba a jikinki ba?" Ya faÉ—i hakan yana duba dukkan jikinta har lokacin bai saketa ba.
Marairaice fuska ta yi kamar zata yi kuka cikin shagwaɓa tace,
"Ina tahowa zan kawo maka kunun shine na ji nayi tuntuɓe, amma bai zuba a jikina ba."
"To Masha Allah, amma ki dinga kula next time Allah Ya tsare na gaba. Ki zo ki zauna na ga kamar kina karkarwa."
Juwairiyya tana son cewa shine yake karkarwan amma ta kunshe bakinta tayi shiru tana dariya a ranta. Halima ta faÉ—a mata weakness É—inshi shine Cuta. Da zarar ya ji ahalinshi basu da lafiya to fa duk wata kulawa ta duniya zai nuna musu, yana tausayawa mai cuta sannan baya raina cuta ko da ciwon kai ne dalilin abun da ya faru da tsohuwar matarshi shiyasa a daren da aka kawo Juwairiyya yace ko ciwon kai ta ji ta faÉ—a mishi su tafi asibiti.
A kan kujera ya zaunar da ita kana ya ajiye kofin akan center table sannan ya dawo gefenta ya zauna yana kallon yanda take numfashi É—ai-É—ai alamar dai ta tsorita.
"Daddy ka ji har yanzu zuciyata bata daina bugawa ba wallahi." Da haka ta ɗauki hannunshi ta manna a ƙirjinta saitin zuciyarta.
Daddy dai bai ji bugun zuciyar ba amma ya ji wani abun na daban, cikin dabara ya sauƙe hannun nashi ya ce,
"Na ji, sosai take bugawa. Sannu, ko zaki sha ruwa?"
"A'a, sai dai chocolate."
Hararanta yayi cikin wasa ita kuma ta mishi gwalo wanda hakan yasa yayi dariya yana karkaÉ—a kai.
"Ku yaran nan na rasa gane meyasa kuke da son zaƙi. Ban taɓa jin mutumin da aka yiwa offering ruwa don ya kwantar mishi da hankali ba yace shi sai chocolate sai ke Juwairiyya sweet tooth."
"Daddy ni ba sweet tooth ba ce." Ta faɗa a shagwaɓance.
Bai ce komai ba amma kuma murmushin bai bar fuskarshi ba ya jawo kofin kunun ya kurɓa sannan ya ƙara na biyu.
"Marigayiya tana mini kunun nan kusan kullum, watarana kuma tayi mini na Tamba. Yayi daÉ—i sosai nagode."
A gurin wata hakan zai zama kamar ya ɓata musu yanayinsu ne amma a gurin Juwairiyya ta ga hakan ne a matsayin wani babban cigaba domin bai taɓa mata maganar tsohuwar matarshi ba, kenan a hankali ya fara sabawa da ita har yau ya kawo musu hiranta.
"Nima akwai ranar da na zo gidan nan Halima ta kawo mini na sha amma dai da sugarn mu, Mummy bata gane an taɓa mata kununta ba sai daga baya." Ta ƙarisa maganan tana dariya domin da gaske hakan ya faru, a lokacin suna secondary school aka tashi daga makaranta suka biyo gidansu Halima akan zata ƙarbi wani style ɗin ɗinki amma suka samu ba'a gama abincin rana ba sai kunun Daddy da ya rage, Halima ta sato musu suka sha.
Daddy murmusawa yayi kana ya kaÉ—a kanshi ya ce,
"Ta faɗa mini hakan ya faru, Halima akwai rigima. Tun tana ƙaramarta tafi Abdul jalil kiriniya, there was a time da ta mari wasu yara a waje....."
Da haka hiran ya canja salo ya dawo kan Halima, Juwairiyya tayi dariya domin labaran rigiman Halima da Daddy yake bata, ta wani guri kuwa daɗi take ji sosai domin zata iya rantsewa wannan shine karon farko da ya zauna suna hira. Kullum maganarsu bata tsayi amma yau ta ga improvements, kenan nisanta kanta daga gareshi da take yi a da shi yasa shima ya ja baya ko dai menene? Sai da goma ta wuce sannan suka farga dare yayi, Daddy kuwa ya sha kunu har kofi biyu sannan yace a ajiye mishi sauran zai sha da safe. Sallama ta mishi ta tattari kwanukan da zata kai kitchen ta nufi ƙofar fita amma ta ji Daddy ya kira sunanta.
"Juwairiyya."
Juyowa tayi fuskarta É—auke da murmushi ta amsa.
"Cookies É—in sun yi daÉ—i na cinye su duka. Thank you."
"Aikina nake yi Daddy, in kana buƙatar wani abun ma ka faɗa mini. Good night."
Murmushi kawai yayi kana ya juya ya fara kashe tv itama ta juya ta tafi sashenta tana jin farin ciki a ranta.
Sati biyu da haka zamansu ya ƙara daɗi domin zasu zauna su yi hira, wani lokaci kuma zasu zauna a falonshi yana karatun jarida ko yana aiki ita kuma tana kallon Korean series ɗinta da ya zame mata jiki. Duk abun da yace ta dafa mishi tana yi hakan yasa yanzu ta san menene favorites ɗinshi da kuma waɗanda baya so. Sai dai abun da ta kasa canjawa shine Daddy baya son taɓa jikinta, sannan ko ita ce ta taɓashi zai yi dabarar da zasu rabu ba tare da yayi hurting feeling ɗinta ba. Ita kuma a yanzu da suke zama su yi hira sai buƙatarta ya fi na da, domin ganinshi kaɗai kan sa ta jita a wani yanayi. Tana buƙatar mijinta amma bata san meyasa har yanzu bai gane ba balle ya bata abunda take so ba.