Sashe 3
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Oh mutum sai sakalci. Tsakaninki da Allah aikin me kika yi yau da har kike cewa kin gaji?" FaÉ—in Salima tana ciro kayan cikin ledan tana ware wanda zata shigar kitchen da kuma wanda zata kai É—akinsu a gefe.
 Dariya Juwairiyya ta yi. "Baza ki gane ba. Amma in kina da miji kamar Hafiz kullum a gajiye zaki dinga jinki."
 Shewa Salima tayi har da tafa cinya tana dariya. "Da alama ku bakwa gajiya da wannan harkan. Mu sai mu yi sati biyu ma wallahi wani abun bai shiga tsakaninmu ba musamman in ya kwanta rashin lafiyar nan. Wani lokaci ina so amma sai inyi shiru gudun kar in 6ata mishi rai idan na nema."
 Fara'ar da ke fuskar Juwairiyya ce ta ɗauke domin ta tsani ta ga ana kwara ko cutar mutum alhali babu yanda ta iya. Ta lura duk hiran da zasu yi da Salima matuƙar maganan Muhammad ta shigo ciki sai ranta ya ɓaci saboda halinsa kaff da yake gwadawa matarsa babu na ɗauka. Tana kuma jin tausayin Saliman domin ta lura har da sonshi yake ɗawainiya da ita, wanda har ta kai bata iya ganin laifinsa.
"Kin san kowa da halittarsa, wataƙila shi ba mai son yawan sex bane." Cewar Juwairiyyah wanda zata iya rantsewa wannan shine karo na farko data taɓa kare Muhammad bata kusheshi ba idan an gwada mata halinsa.
To yaya zata yi? Yawan kusheshi a gaban matarsa zai iya jawo wani matsala tsakaninsu don haka tun suna asibiti ta yiwa kanta alƙawarin daina hakan tunda ita wacce take cikin rayuwar bai dameta ba, kuma a hakan suke zaman auren ba tare data nuna mishi bata son hakan ba.
Murmushi Salima tayi tana cigaba da ware kayan. "Shima haka ya faɗa, yace inyi haƙuri da yanda na sameshi ba yin kanshi bane."
"Ohh dama har wani haƙuri yake baki? Wallahi na ɗauka bai taɓa furta kalmar haƙuri ga kowa ba tun da yake. Ikon Allah, ashe idan kuka keɓance soyayya yake nuna miki mu kuma kin bar mu da jin tausayin ana takura miki." Juwairiyya ta ƙarisa maganan cikin mamaki tana murmusawa don har wani relief ta ji a zuciyarta.
"Shiyasa kika ga ba komai ya mini nake ɓata rai ba, sometimes ya kan nuna mini kulawa sannan babu abun dana nema na rasa a gidan nan, shi dai ki barshi da saurin hawa idan aka yi abunda baya so."
"Dama tsakanin mata da miji sai Allah, wanda kuma ya shiga tsakaninsu shi zai ji kunya." Juwairiyya ta furta ba tare data daina murmushin ba.
Suna hiransu har Salima ta gama aikin nata ta sunkuci trolley É—in tare da sauran tarkacen ta nufi É—akin Muhammad sannan ta fito suka kwashi na kaiwa kitchen suka yada zango a can suna hira Juwairiyya na tayata girkin. Sune basu gama tuwon ba sai da aka kira sallan isha suka yi sallah sannan suka ci tuwon, bayan sun gama suka fara kallo Juwairiyya na recommending wa Salima wasu zafafan Korean series akan ta nema zata ji daÉ—in su.
 Takwas da rabi suka ji ƙarar buɗe gate ɗin gidan mota ta shigo wanda suka ayyana a ransu mazajensu ne suka dawo, tun kafin a kashe motar wayar Salima tayi ƙara tayi saurin ɗauka tare da yin ƙasa da murya ta fara gaishe da wanda yayi kiran nata.
"Ya jikin naka? Da fatan baka jin komai?"
"Ki zo ki haÉ—a mini ruwan wanka." Ya faÉ—a ba tare da ya amsa gaisuwar tata ba, kafin ta amsa ma ya kashe wayar.
 Juwairiyya ma wayarta ce tayi ƙara ta ɗauka cikin ɗoki da kuma murmushi a fuskarta tace,
"Bee."
"Awanni kaÉ—an da rabuwa da ke amma nayi kewarki. Gani a waje ki fito mu tafi gida."
Lumshe idanunta tayi cike da annushuwan yanda yake nuna mata ƙauna a fili babu 6oye-6oye.
"I missed you too. Bari in fito yanzu." Da haka ta kashe wayar ta dubi Salima dake jiranta ta gama wayar don ta mata magana.
"Ba dai tafiya zaku yi ba?" Ta tambaya tana riƙe ƙugunta wanda yin hakan ya fallasa tumbi da kuma manyan hips ɗinta, da yake Salima irin matan nan ne chubby, farare kuma kyawawa masu jikin hutu don iyayenta suna da wadata, sai gashi kuma data tashi aure Allah Ya haɗata da ɗan lukuti irinta duk da cewa bata kaishi ƙiba da tumbi ba.
"Wallahi tafiyan ne. Allah ya bashi lafiya sai kuma gani na gaba." FaÉ—in Juwairiyya tana yafa gyalenta kana ta É—auki wayarta.
"Ina son miki rakiya har waje amma Muhammad ya sakani aiki kar yayi ta jirana ban mishi ba. Kiyi haƙuri don Allah." Ta ƙarisa maganar tana marairaice fuska.
"Wallahi kar ki damu babu komai I understand. Sai anjima kar shima ya gaji da jirana."
Da haka suka yi sallama Juwairiyya ta fita daga gidan ta samu Hafiz a waje a cikin motarshi. Tana shiga ya jawota jikinshi ya fara kissing É—inta tana dariya tana kaucewa.
"Laaa me haka? Irin wannan ambush kamar kayi shekara baka ganni ba." Ta sa hannu ta riƙe kanshi da yake kwantarwa kan ƙirjinta.
"Ina gwada miki irin kalar kewarki da nayi ne. Ya kike?" Ya zuba mata mayun idanunshi da suka canja kala dalilin abun da ya faru tsakanin su, duk da cewa cikin motar akwai duhu kaÉ—an bai hana Juwairiyya gano fitina a kwayar idanunshi ba.
"Lafiya kalau." Kawai ta iya cewa dashi domin itama tuni ya canja mata yanayi saboda ta zama rainon Hafiz don ya mayar da ita kalarsa tuntuni.
"Mu tafi?" Ya tambayeta cikin sarƙewar murya.
"Yes Bee."
Nan take ya tayar da motar suka fita daga unguwar suka fara tafiya akan babban titi zuwa unguwarsu.
"Zan mana take away me zaki ci?" Ya faɗa yana ƙoƙarin karya kwana zai shiga wani restaurant da ke nan bakin hanya.
"A koshe nake domin naci tuwo a can, da yake miyar karkashi suka yi shiyasa ban É—auko maka ba saboda baka ci."
GyaÉ—a kai Hafiz yayi kana yayi parking ya fita zuwa cikin restaurant É—in Juwairiyya ta bishi da ido cike da wani zazzafan sonshi dake fisgarta. Tafiyarshi ma kaÉ—ai abun kallo ne domin bayan kyan sura da yake dashi, Hafiz ya san wankan da ya dace da shi.
 Tana zaune a cikin motar tana kwatanta irin son da take mishi ya dawo ya miƙa mata ledojin hannunsa ta kar6a ta ajiyesu a seat ɗin baya.
"Na saya miki ice cream ki sha yanzu kar ya narke." Ya tayar da motar ya fita daga harabar restaurant É—in, ita kuma cikin murna ta É—auko ice cream É—in tare da mishi godiya ta fara sha suna hira har suka iso gida.
Yana gama cin abincin ya jawota jikinshi suka fara hira har lokacin baccinsu yayi suka kwanta. Kanta dake kan damatsanshi ta É—aga kaÉ—an tana duban fuskarshi tace,
"Bee menene ya faru da kai É—azu? Kace idan ka dawo zamu yi magana."
 "Juwairiyya akwai maganar da nake so mu yi da ke amma bana son ki d'aukeshi da zafi ko kuma ki mini mummunan fassara don girman Allah. Kina ji na?"
https://www.wattpad.com/story/286189663?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=library&wp_uname=amerrly&wp_originator=22UCP3G1XlTWnQof8RLLhEnGEraPiUaFHVmje7x6ztppyuMxuAbQeX%2B5E8vWHz3xuLa5QFovcwjtYpH2f1CVPBuVKyNHvB62dyAtnx8cYRlSnEVu27donXzr4lRYGR5P
Mum Fateey 👌
TAFIYAR MU
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey)
Marubuciyar Matar Ƙabila
Ruwan Zuma da
Fatu A Birni
(2)
Hafiz Isma'il shine ɗa na huɗu a cikin mahaifiyarsa wacce ta kasance mace tilo wajen babanshi, sai ƙannenshi uku mata da duk sun yi aure suna ɗakin mazajensu, yayunshi uku kuma duk maza ne kowanne da iyalinsa.
Hafiz mutum ne mai ilimin addini da kuma boko sannan yana da kyawawan halayen da yasa mutane su ke son hulÉ—a dashi. Yana gama NYSC ya samu aikin gwamnati inda ake biyanshi salary mai tsoka wanda cikin ikon Allah ya tara ya sayi fili yayunshi suka dafa mishi yayi gini mai kyau na gani na faÉ—a.
Hafiz ya haɗu da Juwairiyya Ahmad ne wata rana da ya raka childhood friend ɗinshi Muhammad wani unguwa. Yana zaune shi kaɗai a cikin mota yana jin waƙa yana kuma danna wayarsa ya ɗago fuskarsa don ya gani ko Muhammad ya fito daga gidan da ya shiga amma bai ganshi ba, juya kanshi da zai yi gefen hagu ya hango wasu ƴan mata huɗu sun fito daga wani gida suna hira suna dariya, hankalinsa ne ya koma kan wata budurwa chocolate colored wacce ita ce ta ƙarshen fitowa daga gidan tana gyara hijabinta tana cewa ƙawayen nata su jirata ta musu rakiya zuwa bakin titi. Hakan ya tabbatar mishi cewa nan ne gidansu, kenan ziyara suka kawo mata.
 Har suka zo suka wuceshi idanunshi na kan oval face ɗinta wanda yake cike da annuri ta kasa daina murmushi. Sai da suka ɓace mishi da gani ya rufe idanunshi yana hasko fuskarta mai ɗauke da manyan idanu irin nashi da kuma hanci daidai fuskarta, abun da ya fi ɗauke mishi hankali shi ne lips ɗinta da suke full ta shafa musu lip gloss sai sheƙi suke yi har yana jin ina ma ita ɗin tashi ce.
Yana zaune a cikin motar ta dawo ita ɗaya ta shige cikin gidan tare da kulle ƙofar ba tare da ta gane cewa ana kallonta ba.
Shiganta ke da wuya Muhammad ya fito ya shiga motar suka kama hanyar gida yana yiwa Hafiz hira wanda shi hankalinshi na kan yarinyar daya gani wanda zai iya rantsewa ya kamu da sonta ne at first sight.
"Lafiyanka kam? Ina ta magana ka yi shiru ka shareni." FaÉ—in Muhammad cikin hasala.
"Wata yarinya na gani ta burgeni matuƙa kuma wallahi in har na bincika na ji tana da hali mai kyau zan aureta."
"Su kuma Æ´an matan da kake waya kana chat dasu fa?" Ya harareshi ta gefen ido.
Dariya Hafiz yayi ya sosa kai ya ce,
"Duk cikin su babu matar aure sai budurwar soyayya. Zamu yi soyayya kam tsantsa amma ni nasan ba aurensu zan yi ba saboda bana son mace mara kamun kai da rashin aji. Amma ka ga yarinyar nan dana gani? Ina kallon fuskarta na gane ba shashasha bace she is a wife material. Yanzu dai kai zaka shige mini gaba tun da naga alamar ka san makwabtan gidansu yarinyar ka tambaya mini halinta."