Sashe 13
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mama don Allah ki yi haƙuri kar ki mini haka, ki ƙara mini wasu wata ukun wallahi zan zo miki da mijin aure. Duk waɗanda na koresu bani da masaniyar daga ina suke balle kuma in karɓi number wayarsu."
"Ni dai na faÉ—a miki kuma na yi rantsuwa ba zaki sakani kaffara ba." Mama ta mayar mata da amsa kana tayi shigewarta É—akinta.
Cikin tashin hankali Juwairiyya ta fice daga falon Mama ta koma nata ɗakin, ta ɗauka idan ta bawa Mama labarin abun da ya faru zata barta tunda ba laifinta bane kuma ba ita ta ƙi auren ba. Ta yarda zata auri Ilyas shiyasa take soyayya dashi wanda ita kanta Maman ta sani tunda tana ganin fitanta in ya zo hira. To me yasa ba za'a mata uzuri ba? Me yasa Mama take son takurawa rayuwarta haka? Me yasa ba zata bari ta nemi mijin cikin kwanciyar hankali ba? Wa ya faɗawa Mama cewa har yanzu ana irin haka? Sai yanzu ta yarda mazan kirki na aure suna wahala.
Tunanin duniyan nan ta yi don neman mafita amma babu solution, don bata da inda zata je ta kai Mama ƙara a bata haƙuri. Ƴan'uwan babanta da basu san cinsu da shansu ba ta sani sun fi kowa ma son tayi aure, domin da yanzu zata je musu da zancen haɗuwa zasu yi da Mama su uzzurata. Dangin Mama kuma babu mai sakata dole saboda duk wani da zata ganshi a matsayin uba ko uwa basa raye, shaƙiƙanta kuma ita ce babbarsu. Kakarsu kuwa wacce suke zaune gida ɗaya da ita da babu duk ɗaya, bata cewa kas balle as. Mace ce mai sanyin hali sosai wanda Juwairiyya take cewa sanyin halinta da haƙurinta ne suka sa tayi tsawon rai. To gurin wa zata je? Bata da kowa sai Allah, domin shi kaɗai ne zai sassauto da zuciyar Mama ko kuma ya sama mata mafita a cikin ƙanƙanin lokacin nan.
A kwana a tashi yau ya rage saura sati ɗaya auren Sumayya da Juwairiyya wacce bata da mijin aure, abun duniya duk ya bi ya dameta domin har tunanin guduwa ta yi amma ina zata je? Bata da kowa sannan ta kasa faɗawa kowa damuwarta balle a bata shawara, Juwairiyya tana da ƙawaye amma ita a gurinta su yi zumunci ne kaɗai ba wai su yi sharing sirrukan juna ba. Wannan dalili ya sa babu wanda ya san halin da take ciki sai ƴan gidansu.
Abun da Juwairiyya bata sani ba shine tuni Mama ta janye maganarta don har tayi azuminta uku na kaffara saboda ta sani mijin aure ba kamar zani bane da zaka je kasuwa ka siyo ka dawo dashi gida ba. Ta san ta uzzurawa Juwairiyya amma hakan da ta mata shine daidai. Kwata kwata a yanzu shekarun Juwairiyya ashirin da uku ne (23), yarinya ƙarama da ita bai kamata a barta tana zawarci har yayi tsawo ba. Tana da sauran ƙuruciyarta sannan zata samu mijin aure ba tare da an sha wahala ba, shiyasa tun lokacin da maza suka mata rufdugu ta so ta sauraresu har a samu wanda ya burgeta, ta matsa mata ta fita waje amma ta kasa hanata yi musu baƙin halin da suke tafiya basa ƙara waiwayarta. Wannan babban kuskure ne da Juwairiyya ta yi da zai sa gaba ta yi hankalin ba'a korar mai tayin soyayya, a duba a gani kafin a sallami mai tayin. Zata bar Juwairiyya a yanzu, amma ana gama bikin Sumayya zata tayar da zancen kuma ba zata zo mata cikin lallami ba.
Ana saura sati ɗaya biki ɗaya wata ƙawar Juwairiyya mai suna Halima ta kawo mata ziyara. Tare suka yi secondary school kuma sun yi zumunci sosai har aka yi auren Juwairiyya basu rabu ba, hakan yasa da aka tashi auren Halima itama Juwairiyya ta halarci kowanne event har aka gama Hafiz ne mai kaita yana dawo da ita. Bayan auren mijin Halima ya samu aiki a ƙasar waje inda yayi karatunshi, hakan ya sa ya tattari matarshi suka koma can da zama. Sai dai bayan shekara mahaifiyarta ta rasu wanda hakan yasa suka dawo gida Nigeria, mijin nata sati ɗaya kawai yayi ya koma ita kuma ta zauna kula da Babanta don bayan an watse gida ya rage daga shi sai ita. Matarshi ɗaya ce sannan su biyu ne kaɗai ƴaƴanshi, daga ita sai yayanta namiji wanda yake karatu a ATBU. Wannan kenan.
"I'm sorry to say, amma Juwairiyya kin ƙara ramewa. Ke da Daddy kuna fama wallahi, ban san raɗaɗin rashin masoyi ba amma na san rashin uwa, kuma a hakan naci gaba da rayuwa ban fasa ba. Kun fi kowa sanin ba zasu dawo ba, haka kuma yawan damuwarku ba zai amfanesu da komai ba, zasu so ku nitsu kuma ku cigaba da rayuwa sai ku aika musu da addu'a. Don Allah ki rage yawan damuwa, mutuwa kowa tana jiranshi babu mai zama a doron ƙasa."
"Hmm, Halima ina cikin wani hali ne mai wuya." FaÉ—in Juwairiyya domin yanzu tana son ta buÉ—e cikinta ko zata samu a bata shawara.
"To Allah Ya yaye miki amma na menene?"
A man Juwairiyya ta zayyanewa Halima kaff halin da take ciki sannan ta ƙarishe da cewa,
“Wallahi Halima bani da maneman ma yanzu, in kika cire Hussaini babu kowa. To yanzu in ba Hussaini ba wa zata aura mini, wallahi in har aka aura mini Hussaini sai na gudu an rasani.â€
“Ya Salam! Juwairiyya kar ki sake faɗin haka, abun bai kai ga haka ba. Shi kuma Hussaini in banda rigima ina shi ina ke? Ya fi kowa daƙiƙanci a aji gashi har yau shi bai ƙaro ilimi ba kuma bai kama sana'ar komai ba."
"Kuma ni Allah Ya sani ba zan auri sa’ana ba.â€
“To ga wani dalilin ma.â€
Shiru suka yi na Æ´an wasu seconds sannan fuskar Halima ta washe da annuri tace,
“What if na kawo miki miji na gani na faÉ—a har gida? Mijin da bashi da aibu sannan zai riÆ™eki amana tamkar Æ´ar cikinshi? Mijin da zaki zauna a gidanshi daga ke sai shi babu mai takura muku? Mijin da yake da rufin asirin da ba zaki nemi komai ki rasa a gidanshi ba? Kina so!?â€
“Halima ina zaki samo mini mijin aure mai duka waɗannan qualities ɗin a ƙanƙanin lokaci haka? Sannan in ma an samu shi zai yarda ya aureni ne daga haɗuwa da ni?"
"Ina ji a jikina za'a yi auren nan shiyasa ƙaddara ta hankaɗoni gidan nan. Wallahi tun last month
mijina yake ta damuna akan in koma Turkey amma hankalina ya ƙi kwanciya da in bar Daddy shi kaɗai a cikin gidan nan, ina nan ma kullum cikin damuwa yake ina ga kuma babu ni? To kwana biyu da suka wuce ya daina ɗaukan wayata Juwairiyya, na san ina cikin fushin Allah kuma ina ɗaukan alhakinshi amma Daddy fa? Ni kaɗai yake gani ya ji sanyi a ranshi saboda Abduljalil tuni ya koma school baya dawowa gida sai ƙarshen semester. Juwairiyya......." Bata kai ga ƙarisa maganarta ba Juwairiyya ta katseta da hanyar ɗaga mata hannu.
"No, ba zan auri Daddy ba Halima! Wallahi ba zan auri Daddy ba.â€
“Juwairiyya….â€
“Kai ina! Mu bar maganan nan bana son jin komai.â€
“Don Allah ki saurareni in ya so zaki iya yanke duk hukuncin da kika ga dama. Ki saurareni please.â€
“Duk abun da zaki faÉ—a ba zai canja mini ra'ayi ba amma ki faÉ—a tunda kin kira sunan Allah. Haba Halima Daddy ne fa, Daddyn mu. A Æ´a ya É—aukeni fa.â€
“Ki dai saurareni.â€
“Ina jinki ai.â€
“Juwairiyya wannan aure da nake son haɗawa rufin asirinmu ne. Na farko ni zan samu in koma gurin mijina wanda yake fushi dani, na biyu Daddy zai samu mata wacce zata kula dashi sannan ta taimakeshi wajen ɗauke hankalinshi daga kan Mummy, he is lonely he really need a companion. Sannan na uku Juwairiyya ina zaki samu miji mai kyakkyawan hali kuma mai shirin aurenki a kwana bakwai? Kin san waye Mama zata haɗaki dashi? Bakya son kiyi zaɓinki kafin a haɗaki da wanda bakya so? Ki zauna ki yi tunani wallahi wannan shine kaɗai mafitan da in kin amince kin ceci mutane huɗu ne lokaci ɗaya sannan kema zaki samu kwanciyar hankali domin kin san waye Daddy halinshi na gari duk kin sani. Kiyi haƙuri Juwairiyya ki taimakeni, wallahi hankalina zai fi kwanciya idan na san a hannunki na bar Daddy."
"Wayyo Allah na! Halima idan na auri Daddy me duniya zata ce da ni? Zasu kirani butulu na auri Baban ƙawata."
"Da Mummy tana raye ne za’a faÉ—i haka, amma bata doron Æ™asa. Sannan duk wani da zai kawo suka akan auren man ina nan ba zan bari ba wallahi. Ke dai amincewarki kawai nake nema.â€
Shiru Juwairiyya tayi tana aikin tunani, wannan shi ake kira ‘Ga samu ga rashi’. Idan ta ƙi wannan haɗin ita ce a cikin tashin hankali, in kuma ta yarda mutanen duniya ba zasu barta ba. To yaya zata yi?
“Halima ki bani lokaci zan yi tunani amma wallahi ina tsoron bakin mutane, sannan shi Daddy zai amince ya auri ɗiyar cikinshi?"
"Wannan duk ba matsala bace, zan kiraki anjima da dare in ji hukuncin da kika yanke Juwairiyya. Don Allah kar ki manta taimakonmu kike yi dukkaninmu sannan hakan shine kaÉ—ai rufin asirinki."
"To shikenan Halima."
Mum Fateey 👌
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > [email protected]
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
TAFIYAR MU
Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064