← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kin taɓa ganin an yi maganin mallakar mutum Du'a'ul Kanzul Arsh? Addu'an da yake karya sihirin ne zai zama na sihiri?"

"To na uban me ka bani?"

"Da alama kin samu kanki, da kuma a nan kika tsaya kina kuka wancan wawan ya tasaki a gaba yana miki ihu kina bin umurninshi blindly." FaÉ—in Muhammad yana hararta don ya lura she is ungrateful duk da cewa bata san ceton da ya mata ba.

"Wallahi nima sai yanzu abubuwan suke ta dawo mini, na rasa gane meyasa nake bin duk maganarshi kamar wacce ya yiwa asiri." Ta faɗa tana murza goshinta a hankali tana tunani kanta a ƙasa.

Jin shiru Muhammad bai yi magana ba yasa ta É—ago kanta tana kallonshi. GyaÉ—a mata kai yayi wanda nan da nan kwakwalwarta ta fara haÉ—a mata nan da can!

"No!" Ta faÉ—a a hankali hawaye na taruwa a idanunta.

"Yes."

"No!" Hawayen suka zubo ta rufe bakinta da hannunta jikinta ya fara ɓari tana kuka.

"Look at me! Ki daina kukan nan kar ki jawo mana hankalin mutane kanmu." FaÉ—in Muhammad yana mata katanga da jikinshi kar masu wucewa su ga halin da take ciki.

Sai da ta É—an nitsu sannan ta dubeshi tace,

"Ya aka yi ka gane? Sannan kai ka kawo mini maganin da ya karya sihirin?"

"Baki da kunya, kina da raini sannan ba'a sakaki kiyi, da haka na gane."

In a wani lokaci ne ya faÉ—a mata haka zata ce zaginta yake yi amma wannan karon godewa Allah ta yi da ya har yasa ya gane cewa wai ba'a hayyacinta take ba.

Godiya ta shiga yi mishi babu ƙaƙƙautawa domin wa zai so akalar rayuwarshi ta zame daga hannunshi ta sauƙa kan hannun wani? Shikenan mutum ya zama kamar mutum mutumi bashi da tunanin kanshi sai abun da wani yace yayi! Akwai baƙar ƙaddarar da ta wuce wannan? Ai sai ta ji ashe a da hankalinta ma a kwance yake, yanzu kuma da ta san me ya faru da ita sai tsoro ya shiga ranta.

"To yanzu ya zan yi? Kar fa ya ƙara mini wani. Wayyo Allah na." Nan kuma ta sake birkicewa sai da kyar Muhammad ya saitata nan ma sai da ya ɓata rai ya mata tsawa.

"Idan ba zaki nitsu ba sai in yi tafiyata, ina da ayyuka da yawa na bari na zo ina babysitting É—inki."

"Why are you helping me? Na É—auka ka tsaneni."

Kamar ba zai amsa ba sai can kuma ya tsura mata ido ya ce,

"Saboda abokina Hafiz! Na mishi alƙawari kuma ba zan taɓa karyawa ba duk da cewa you are insufferable. And I don't hate you, halayenki ne bana so."

Harara ta watsa mishi kana tace,

"To yanzu ya zan yi kar mutumin nan ya samu galaba a kaina again? Gashi yau É—in nan Mama ta datse mini farin cikina wai ba zan sake zuwa school ba sai dai in bari ko kuma in yi aure in ci gaba da yi." Ta nemi shawaran Muhammad wanda a da in aka ce mata zata zo ta kalleshi a matsayin mai bata shawara zata zagi duk wanda ya faÉ—i hakan.

KaÉ—a kafaÉ—a yayi sannan ya gyara tsayuwarshi domin ya fara gajiya ya ce,

"Ki yawaita addu'a ko kuma kiyi auren, auren kuma shine rufin asirinki domin idan ya ji kin yi zai haƙura sannan zaki samu kici gaba da karatunki, nima kuma na huta da bibiyar rayuwarki don na fara gajiya."

"Na yarda zan aureka Muhammad. Ka aiko sadakinka gobe a ɗaura mana aure." Ta faɗa da murmushi a fuskarta domin sai yanzu ta gane ɓullowar Muhammad a rayuwarta kullum ba haka banza bane, they were meant to be together ne. Salima zata fahimceta tana da tabbacin hakan. (Ohh, you don't!).

"No!" Muhammad ya faɗa da sauri yana ɓata fuskarshi.

"Yes." Ta ƙara faɗaɗa murmushinta.

Juyawa yayi ya nufi motarshi yana karkaÉ—a kanshi ta bishi tana cewa,

"Ka turo gobe a É—aura auren."

"Ke ki barni fa."

"But you promised him cewa zaka aureni idan na yarda. You promised Muhammad!"

Wannan magana yasa ya carke ya tsaya kana ya juyo ya dubeta bata daina murmushi ba ya ce,

"You will be the death of me. Ki faÉ—a musu gobe zan taho da magabatana a É—aura auren da safe."

"To maigida."

Rayuwar auren masoya biyun na tafiya daidai yanda suka tsara tun farkon fari, kwanciyar hankali da son juna ya kafu a cikin gidansu wanda hakan yasa suka zama abun burgewa ga jama'a da dama har wasu suna fatan ina ma su ne!

Suna tsaka da wannan jindaɗin ne rayuwarsu ta canja salo wanda hakan yayi sanadiyyar bankaɗuwar wani tsohon alƙawari mai wuyar cikawa. To yaya rayuwar tasu zata ƙaya? Ku biyo Mum Fateey domin yanzu zamu shiga gundarin labarin.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

(14)
“Cewa aka yi da ta ji labarin auren suma ta yi."

"Nima na ji wannan, to amma kuma wasu sun ce ita ce tace ya auri ƙawar tata."

"Ɗazu kuma na ji wai asiri ta yiwa ƙawar da mijin suke bibiyanta a gindi sun kasa rabuwa da ita, to in ba asiri ba don tana matar aboki kuma abokin ya mutu shekara uku da suka wuce babu ɗa tsakaninsu sai kuma su ci gaba da zumunci da ita? Ni dai wannan cin amanan da tayi yasa na daina kallonta a mutumiyar kirki, dama an ce ba'a shaidan ɗan kuturu sai ya mutu da yatsa."

"Ku naku duk mai sauƙi ne, ni abun da na ji sai da yasa na ja baya. Wai ashe bibiyar mijin ƙawar take yi har ya mata ciki shine ƙawar ta fahimta tace zata tona musu asiri suka yi gaggawan yin aure don su rufe."

"Ni dai koma menene gaskiyar ban ji daɗin auren mijin ƙawar tata da tayi ba. Haba ai da kunya da kuma nauyi, suna zumunci sosai har mijinta da ya mutu sai da ƙawar ta sa maigidanta ya mishi takwara. Yanzu duk wannan bai isa ya haneta aurenshi ba?"

"Kuna ta wani cece kuce, kuma duk maganar akan ita macen ce! Shi mijin ba zaku ga laifinshi bane da yake bibiyar ƙawar matarshi? An ce maza sun fi mata hankali to me yasa ba za'a ɗauki laifin kacokam a ɗaurawa namijin ba tun da ya fi hankali? Sai a mata uzuri tunda dama bata da hankali, ba haka mazan suke cewa ba?"

"Ku dai mu bar maganan nan haka, Allah Ya basu zaman lafiya kawai."

*****

Juwairiyya ce zaune a gaban Mama tana mata nasiha sannan ta ɗauki dubu hamsin ta miƙa mata tana cewa,

"Ga sadakinki nan, Allah Ya baku zaman lafiya Ya kuma sa gidanki ne na har abada Juwairiyya. Allah Ya kaÉ—e hau Ya kuma haÉ—a kanku kuyi zaman lafiya."

"Amin." Juwairiyya ta amsa kamar ma hankalinta baya gurin.

Da haka Mama ta sallameta ta koma ɗakinta ta samu guri ta zauna tana tunani. Wai shikenan da gaske ta zama matar Muhammad? Mutumin da ta tsana a da har take zaginshi tana kusheshi yau shine mijinta? Bayan wannan yaya zata yi da Salima wacce aka ce suma tayi da ta ji labarin mijin nata yayi aure kuma wai ita Juwairiyya ya aura? Anya bata tafka babban kuskure ba wajen auren Muhammad? Anya kuwa shima ba asirin ya mata ta nemi ya aureta ba? Kai da hankalinta! Don tana tunawa ta gwammace ta zauna da Muhammad akan ta rasa karatunta ko kuma worse Salisu ya mata wani asirin ya ɓatar mata da hankali har ya aureta. Sai dai da akwai wani option da zata samu a wannan lokacin ba Muhammad ba to da shi zata zaɓa. Lallai ta ƙaryata zancenta da take cewa ko mazan duniya sun ƙare ba zata aureshi ba. Gashi yanzu akan gujewa wani namijin ta zaɓi zama dashi don tsoro.

Fatanta Salima ta fahimceta domin ba son mijinta take yi ta aureshi ba, tayi hakan ne don shine only hope ɗinta don gujewa mummunar ƙaddara. Sannan da zarar ta samu ta gama makarantarta ta kama aiki zata nemi ya saketa a lokacin kuma ta san tayi girman da Mama zata barta taci gashin kanta. Da wannan tunanin ta ɗauki waya ta kira Salima amma ta ji wayarta a kashe, ko dai har yanzu bata farfaɗo bane? Tun jiya ta so kiranta fa faɗa mata amma sai ta ji ta gagara, don haka ta barwa Muhammad wannan aikin. Shi kuwa tunda suka gama magana jiya bata sake jin ɗuriyarshi ba sai sadakinshi da aka damƙa mata bayan an ɗaura aurensu da misalin ƙarfe tara na safe. Kwata-kwata mutanen da suka halarci wannan ɗaurin auren mutum goma ne, biyar daga gareshi haka biyar daga fanninta. Wani ƙanin babanta da bai san cinta ko shan ta ba ya buɗi baki yake faɗawa mamanta wai shi fa ya gaji da zuwa ɗaurin aurenta! Wannan magana ya yiwa Juwairiyya zafi da take sauraronsu daga can ɗakinta yayin da su kuma suke tsakar gida. Ta so ta fita ta faɗa mishi baƙar magana amma da ta tuna cewa Mama ba zata goya mata baya ba, kai karshe ma hakan zai jawo musu matsala yasa ta kame kanta amma ta mishi addu'a shima ya ji yanda ta ji. Ai ba yin kanta bane aure-auren, mijinta na farko mutuwa yayi wanda in ba don mutuwa ba babu abun da zai rabasu, na biyu kuma lalura yake dashi ya saketa ba da son ranta ba. Sai kuma wannan na ukun zata yi shi ne na wasu shekaru uku zuwa huɗu tsanani kafin ta samu ƴancin kanta ta kasheshi. Wannan kenan.

Duk ƙoƙarin da Juwairiyya ta kai ga neman Salima bata sameta ba, hakan yasa ta ji shakka ya shiga zuciyarta ba dai tayi fushi da ita bane? Ta ɗauka Saliman zata nemeta saboda tafi kowa sanin yanda ta tsani mijinta, zata tambayeta ba'asin yaya aka yi har hakan ya faru? A nan ita kuma zata mata bayani sannan ta ƙara da bata haƙuri don zata shigo gidanta ne ba da niyyar zama ba sai don ta yada zango kaɗan ta wuce.
Chapter 24 · 0% Book details