Sashe 21
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ga kuma abun da take tsoro! Wato duk yanda zata kai ga faɗa musu cewa ba laifi tayi mishi ya saketa ba ba zasu yarda ba. Idan kuma ta fito fili ta faɗi gaskiyan al'amarin ta tona mishi asiri ne sannan wasu ba zasu yarda ba zasu ce ƙarya take mishi tana son wulaƙantashi ne a cikin mutane. Ta sani kuma zata iya rantsuwa Mama ma ba zata yarda da ita ba, to me amfanin bayyanawan? A zaman da tayi dashi ya kyautata mata don haka ba zata so ta kwaye mishi zani a kasuwa ba, ta wani gurin kuma Daddy uba yake a gurin Halima ƙawarta. Idan ta fito ta faɗi matsalarshi da wani ido zata ƙara kallon Halima? Zata rufa mishi asiri ko don waɗannan dalilai biyun amma ba zata taɓa daina jin haushin yanda ya saketa ba. Me yasa ba zai iya bata takardarta a hannunta ba sai dai ya ajiye ta je ta ɗauka? Ashe tun kafin ya tafi sunanta sakakka ce a gurinshi bata sani ba! Wannan sakin da yayi mata da kuma salon da yayi amfani dashi wajen sakin zai kasance a cikin zuciyarta har ƙarshen rayuwarta, ba zata taba mantawa dashi ba har abada.
"Wallahi, wallahi babu laifin da nayi mishi."
Shiru Mama tayi tana zaune a gurin har na tsawon minti biyu tana kallon Juwairiyya sannan ta ce,
"Idan zaman hakan kika zaɓa gaki ga ita Juwairiyya, amma sai dai zan faɗa miki ba lallai bane ta miki daɗi ba. Sannan ba a kanki aka fara yiwa mutuwa ba, hakan da kika yi kin nunawa Allah kenan baki da tawakkali baki san ƙaddara ba. Ga ki ga gidan Juwairiyya, in kuma kina da wayo sai ki san yanda zaki yi mijinki ya mayar da ke gidanshi." Tana faɗin hakan ta tashi ta koma ɗakinta, abincin ranar yau kuma bai samu ya shiga cikinta ba.
Fitan Mama daga ɗakin yasa Juwairiyya ta ƙara fashewa da kuka domin gashi nan hatta uwar da ta haifeta bata yarda da ita ba, haka kuma duk duniya ita za'a bawa laifi babu wanda zai yi tunanin laifinshi ne. Wannan shine ƙalubalen da Juwairiyya ta fara fuskanta bayan aurenta da Daddy ya ƙare.
****
"Gata can zata tafi makaranta, ka ganta sulum-sulum kamar in ka saka mata yatsa a baki ba zata iya ciza ba amma nan jarababbiya ce." Faɗin Garbati mai shago da yake can ƙasan layinsu Juwairiyya.
"Cewa aka yi Jarababbiya ce?" Wani baƙon mutumi ya tambaya yana mai kallon lokacin da ta tari mai napep akan titi ta shiga suka tafi.
"Haka dai ake faɗa, wai tsohon tafi ƙarfinshi saboda jarabarta shine da ya ga ba zai iya ba ya sallameta." Garbati ya amsa mishi yana bawa wani saurayi sigari.
Saurayin yayi caraf ya karɓi zancen yace,
"Ba haka aka faÉ—a ba fa, cewa aka yi yana zarginta da É—an cikinshi ne amma bashi da shaida shine ya saketa."
"To in dai hakane ai abubuwan da aka faɗa da yawa, ni wannan na ɗauka don shi zai fi zama gaskiya. Gaskiya ana mata kyakkyawar shaida zai yi wuya a ce fasiƙanci take yi da ɗanshi, sai dai baka san halin mutum na ɓoye ba amma gaskiya zai yi wuya."
"Wai menene sauran abun da ake faÉ—in?" Mutumin ya sake tambaya amma Garbati yayi shiru kamar bai ji ba don ya lura kamar takanas mutumin ya zo domin binciken halin Juwairiyya.
"Ai ka san baban ƙawarta ta aura, to an ce wai ƙawar tata ce bata son auren shine tayi yanda ta rabasu. Wasu sun ce ta rainashi ne, wasu kuma suka ce sata take mishi tana kawowa gidansu...." Saurayi mai sigarin ya fara zayyanowa Garbati yayi saurin katseshi da cewa,
"Wannan kam duk wani mai hankali ma ba zai É—auka ba, da tana da waÉ—annan halayen da mutanen unguwan nan ne zasu fara sani. Lukman don Allah kayi tafiyarka kar da sassafen Allah ka É—auki alhakin Æ´ar mutane." Ya bugi tsuntsu biyu da dutse É—aya.
Wannan magana ta sa Lukman ya tafi yana busa sigarinshi shi kuma mutumin yayi jimm kamar ba zai tafi ba, can kuma ya miƙe ya karkaɗe rigarshi ya shiga mota ya tafi.
"Mutane sai shegen gulma da bin diddigi." FaÉ—in Garbati bayan ya ga tafiyar mutumin ya manta cewa da shi aka fara kafa chaptern Juwairiyyan.
Juwairiyya ce zaune a class tana jiran lokaci yayi Lecturer ɗin ya fita don ta samu ta koma gida da wuri. Yana fita ta bi bayanshi ta fita daga makarantar ta tari napep sai gida, a can ta tarar da aikin da yake jiranta na girkin rana da kuma gyaran ɗakin Mama kafin ta dawo daga aiki, domin kuwa Mama ta kori mai aikinsu tace bata ga amfanin zamanta a gidan bata aikin komai ba, duk kuwa da cewa Juwairiyyan tana zuwa makaranta watarana ma a can take wuni amma a haka zata dawo ta samu wasu aikin suna jiranta. Wani abun da ta lura dashi shine ko Surayya ƙanwarta da yanzu take SSS 3 bata kaita tiƙan aiki a gidan ba, kamar Mama tana mata kora da hali ne. Amma wannan bai dameta ba kamar maganar aure da Mama ta fara matsa mata a kai.
Tun bayan mutuwar aurenta Daddy bai nemeta ba haka itama bata sake nemanshi ba sai Halima ce da take yawan kiranta wanda Juwairiyya ta yi blocking ɗinta don bata ga me zata faɗa mata ba. A yanda ta lura Daddy bai faɗawa Halima dalilin rabuwarsu ba sai cewa yayi wai a tambayeta, to kenan ita ce mara rufin asiri mara kunya da zata buɗi baki tace ga matsalar da suka fuskanta har ya kai ga datsewar zaman nasu? Duk irin tambayar duniyar da Mama tayi mata akan dalilin sakinta da aka yi kuwa ta ƙi faɗa mata domin tayi alƙawarin rufawa Daddy asiri har ƙarshen rayuwarta, na biyu kuma ta sani ko ta faɗa Mama ba zata yarda ba zata ce karya take mishi don bata son komawa. To wa ya fita son komawa gidan Daddy? Ita ta ji ta gani zata iya zama dashi duk da lalurar da yake fama da ita amma bai nemi shawararta ba ya saketa, duk hakan bai isheshi ba sai da ya ƙara da kin kiranta har sai da ta gama iddah sannan ya nemeta a waya yana tambayar wai ya take. Kalma ɗaya ta 'Coward' ta furta mishi daga nan shima tayi blocking ɗinshi. Ana haka kuma sai gashi wai ya zo ƙofar gidansu, babu yanda ta iya haka ta fita don a gaban Mama aka yi kiran nata.
"Juwairiyya kina lafiya?" Ya tambayeta yana mai mata kallon tausayi domin har ta canja ta ƙara ramewa.
"Kalau. Me ya kawoka ƙofar gidanmu?" Ta tambayeshi kai tsaye domin ta so ta tsigeshi tass amma kwarjininshi da girmanshi sun haɗu sun danne wannan tsiwar tata.
"Na zo ne na dubaki, sai na lura kuma bakya murna da ganina."
Wannan magana da yayi shi jawo hawayen da Juwairiyya take ta dannewa suka zubo kan fuskarta ta dubeshi duk jikinta a sanyaye ta ce,
"Daddy sakina dai kayi, sakina kayi ka ajiye mini takardar sai da naje na ɗauka na gani sannan na gane ni sakekkiya ce. Bamu yi haka da kai ba sannan ba haka muka yi alƙawari ba, ka mini gaggawa ka datse mini farin cikina ka dawo dani rayuwar da nake gudu. Wallahi baka kyauta mini ba, zuwanka kuma ya ƙara fame mini wani ciwo a zuciyata don Allah kar ka sake zuwa inda nake, zaman da muka yi a baya ma ya isa. Don Allah ka tafi." Da haka ta juya ta shige cikin gidansu ta barshi tsaye a gurin shima yana jin kamar yayi kukan.
Bata jima da shiga ba yara suka yi sallama suka fara shigowa da kayan masarufi mai yawan gaske, hakan yasa Mama da ta tareta a tsakar gida tana tambayarta dalilin zuwan nashi ta dakata har aka gama shigo da kayan sannan yaro na ƙarshe ya shigo da envelope mai kauri ya miƙa mata wai in ji Alhajin waje.
Tana buɗewa ta ga kuɗine a ciki wanda a baya ya ɗaura mata a kan takardan sakinta wanda zai yi kimanin dubu ɗari biyu, sai kuma wata wasiƙa wacce kamar yanzu ya rubutata. Saboda rashin sanin me ya rubuta a ciki yasa Juwairiyya ta miƙawa Mama kuɗin ita kuma ta shiga da wasiƙar ɗaki ta fara karantawa kamar haka....
'Zan fara da ƙara baki haƙuri Juwairiyya duk da nasan yayi kaɗan ya goge laifin da na miki, amma kiyi haƙuri ki kuma yafe mini domin rabuwarmu shine mafi alkhairi kuma ba zan iya cigaba da zama dake ina cutar da ke ba, wallahi ba zan iya ba. Sannan ina sonki ina ƙaunarki zaman da nayi da ke kin shiga zuciyata ba zan taɓa mantawa da ke ba har ƙarshen rayuwata. Kafin ki aureni I'm a broken man, bayan haka kuma ya ƙaru da cewa ba zan iya biya miki buƙatunki ba, you deserve someone better someone who can take care of you. A ƙarshe ina miki fatan alkhairi, Allah Ya miki albarka Ya kuma baki miji nagari wanda zai riƙeki amana don you are a rare gem Juwairiyya, da ina da lafiya wallahi babu abun da zai sa in rabu da ke. Allah Ya miki albarka.
Daddy.'
 Tun daga ranar bata sake jin ɗuriyar Daddy ba haka kuma Halima ma ta daina nemanta don da alama tayi fushi ne, sai dai bata sani ba cewa ba laifinta bane kuma ba zata iya faɗa mata gaskiyan abun da ya faru ba. Mama kuma ta mata faɗa ta mata nasiha amma kullum maganarta shine 'ba laifina bane ya sakeni'. Labaran da ake faɗa a kanta kuwa duk yana dawowan kunnensu wanda Mama tafi kowa shiga ɓacin rai don ta san ɗiyarta ba zata taɓa neman ɗan mijinta ba ko kuma tayi sata ba. Ire-iren waɗannan ƙalubalen yasa Mama ta fara mata kora da hali wai duk don ta gaji tayi aure. Wannan kenan.