← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 26

Sashe 4

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Babu wanda zan je in tambaya wani abu, kuma gidan da kaga na shiga gidan wani distant relative É—in Babanmu ne ya aikeni gurinsa nima ban ta6a zuwa ba sai yau."

"Don Allah kar mu yi haka da kai mana." Hafiz yayi saurin faÉ—a cikin kwayewar fuska yana kallon Muhammad.

"Mallam ka kalli gabanka kar ka juyemu a cikin kwalbati. Zan yi tunani a kai."

Washe gari da yamma sakaliya Hafiz da abokin nashi suka isa ƙofar gidan su Juwairiyya suka aika yaro yayi kiranta bayan Muhammad ya faɗa mishi sunanta a binciken da yayi na dole.

Tana fitowa ta samu Hafiz a tsaye suka gaisa ya gabatar da kanshi tare da faɗa mata dalilin zuwanshi babu ɓata lokaci domin shi aurenta yake son yi. Bayan ta ja mishi aji akan cewa bata tsayawa da samari sannan ya roƙeta da girman Allah kan ta bashi number wayarta kafin ya gabatar da kanshi gurin iyayenta. Kamar bata so ta bashi numbern, a nan yake faɗa mata tare da abokinshi yake wanda suna hangoshi a cikin mota a gaba dasu amma ko sau ɗaya bai waiwaya ba. Hafiz ne ya kwala mishi kira Muhammad ya juyo rai a 6ace kamar an mishi dole.

"Ka zo ku gaisa mana." Hafiz ya faɗa yana roƙanshi ta cikin ido don kar ya kwafsa mishi.

"No I'm good." FaÉ—in Muhammad flatly kana ya juyar da kanshi.

  Hafiz haushi da kuma kunya ce ta cikasa wanda bai ƙara minti biyu ba Juwairiyya ta mishi sallama ta shige gida akan cewa mamanta zata mata faɗa idan ta ga ta jima.

  A mota Hafiz yayiwa abokin nashi tatas kan cewa ya wulaƙantashi shi dai Muhammad yana shiru bai ce komai ba, ƙarshe da yaga Hafiz ya fusata da gaske sai ya bashi haƙuri yace zai gaisheta idan suka sake haɗuwa.

Abun da basu sani ba shine ita Juwairiyya tun a lokacin ta ji ta tsani Muhammad domin bata son duk wani abu da ya danganci wulaƙanta mutum. Daga ganin suturun jikinsu da kuma motar da suka zo dashi ta gane suna da wadata in dai ba arowa suka yi ba, amma hakan bashi zai sa abokinsa ya wulaƙantata ba don bata kai su kuɗi ba. Duk da cewa Hafiz ya burgeta amma halin abokinsa yasa ta ji baza ta iya kulashi ba, hakan yasa da dare da yayi ta kiranta ta ƙi ɗauka har ya gaji ya daina.

  Washe gari da safe ta fito daga gidansu zata tafi islamiyya, da yake ta gama secondary school wata uku da suka wuce kuma mamanta ta hanata cigaba da karatu wai aure zata mata ta samu Hafiz rakuɓe a katangar gidansu da alama ita yake jira da fito. Yana ganinta ya sha gabanta fuskarshi abun tausayi da alama ko wanka bai yi ba ya fito.

"Laifi ne na miki kika ƙi ɗaukan wayata?"

  Tsabar mamaki kasa magana ta yi domin wannan abun da yayi a littafin Hausa ne kaɗai ta ji ana yi wato saurayi ya kasa runtsawa har sai ya shawo hankalin buduwarsa.

"Ko dai ban miki bane tun farko sai ki faɗa mini ba wai ki bani numbernki sannan ki ƙi kulani ba."

  Ganin ana wucewa ana kallonsu ga kuma uwa uba hakan da yayi na nuna damuwarsa a kanta yayi matuƙar burgeta, domin ita tana son a nuna mata kulawa da soyayya don haka ta buɗi baki ta ce,

"Na yi bacci da wuri ne. Sorry."

  Ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya dafa ƙirjinshi saitin zuciyarshi ya ce,

"Har na ji sanyi a zuciyata, we cool?"

Murmushi ta yi don ta lura yana yawan saka turanci a maganarsa wanda ba forcing É—inshi yake yi ba irin ta gane ya iya turanci, a'a ta tabbatar haka ya saba domin ko sau É—aya bata ta6a kamashi da murÉ—ewar harshe grammatical error ba.

"Yeah, we are cool. Bye." Ta faÉ—a tana ratsewa ta gefeshi don kar ya sakata latti a sakata wanke banÉ—aki.

  Bata yi taku biyar ba ta ji wayarta na ƙara ta zaro daga cikin jakarta domin tasan babu mai kiranta a wannan lokacin sai mahaifiyarta hala tayi mantuwa ne a gida zata kai mata asibiti inda take aiki, amma ganin numbern Hafiz wanda bata yi saving ba yasa ta juyo ta dubeshi yana tsaye a inda ta barshi da waya a kunnenshi alamar shi ɗin ne dai ya kirata.

  Murmushi yayi ganin ta tsaya tana kallonshi kana ya mata nuni da wayar hannunta wanda hakan yasa ta farfaɗo ta amsa wayar gami da karawa a kunnenta, muryarshi ta fara ji yana cewa,

"I know ko nace ki zo ki shiga mota in kaiki school É—in baza ki yarda ba saboda it seems your parents raised you right, so Allah ya kiyaye hanya Ya kuma baki ilimi mai albarka. Take care."

Yana gama faɗin hakan ya kashe wayarsa kana ya shige motarsa ya tafi ya barta a gurin zuciyarta na bugawa da ƙarfi ba don tsoronshi ba sai don a take a wannan lokacin ya sace zuciyarta ya tafi da ita.

A ranar Hafiz ya zo da yamma bayan ta amince mishi amma bai zo tare da Muhammad ba, gefe guda kuma yasa an mishi binciken halayenta aka kuma sanar mishi cewa tana da hankali da nitsuwa kamar yanda yayi tsammani. Bai yi wasa ba ya turo iyayensa gurin dangin Babanta aka bashi izinin hira har aka musu baiko.

  Tun rana ta farko da Hafiz yazo da Muhammad bai ƙara zuwa dashi ba har aka saka ranar aurensa da Juwairiyya wacce ta kaucewa duk samarinta tace shi zata aura. Sai ana ribibin auren nasu ne suka haɗu wanda shi Muhammad ɗin ne ya ɗaga mata gaisuwa amma tayi kamar bata ji shi ba.

  Da yake tana yawan jin labarin shi gurin Hafiz yasa ta gane shi ɗin abokinshi ne na ƙut da ƙut, sannan ta fahimci yana da girman kai amma ita neman abu ta yi a gurinshi da zai wulaƙantata? Har aka yi bikin tsakaninta da Muhammad babu jituwa, sannan ko bayan auren bai je gidansu ba sai da suka yi wata biyu wanda ta lura Hafiz ne ya matsa mishi suka zo nan ma bai ci komai a gidan ba ya tafi.

Juwairiyya Ahmad ita kuma ƴa ce ta farko a gurin mahaifiyarta sai sauran kannenta mata biyu da namiji ɗaya. Babansu ya rasu tun suna yara hakan yasa mahaifiyarsu ta zauna a cikin gidan mijin nata tare da ƴaƴanta ba tare da ta sake aure ba, kuma ta ɗauko mahaifiyarta tsohuwa da take ƙauye suna zama tare da yake ita ma mijin nata ya rasu. Cin su da shan su duk a kan mahaifiyarsu yake wacce take Nurse a wani Maternity wanda jajircewarta da kuma jimawanta tana aiki yasa aka bata matsayin Matron na asibitin gaba ɗaya. Hakan yasa ta samu ƙarin albashi ta kuma cigaba da kula da ƴayanta har ta aurar da Juwairiyya.

Wata shida da aurensu suna zaman lafiya da nunawa juna so Muhammad ya tayar da maganar auren da zai yi. Ko da Hafiz ya nunawa Juwairiyya hoton matar da Muhammad É—in zai aura sai ta buÉ—i baki ta ce,

"Dama shi lukuti ai sai lukuta ce zata iya dashi. Wannan idan aka aura mishi yarinya ƙarama rana ɗaya zai karya musu ƴa da nauyinsa."

"Riya baki da kunya fa, me ya kai tunaninki har can daga nuna hoto kawai?" FaÉ—in Hafiz yana harararta da gaske.

"Sorry na taɓo rabin ranka." Ta mishi gwalo kana ta tashi ta shige kitchen don ɗaura musu abincin dare.

Bayan auren Muhammad da matarshi Salima su Hafiz suka je gidan amaren a satin farko bayan Hafiz ya tilastawa Juwairiyya zuwa. Tar6an da Salima ta musu yasa Juwairiyya ta sassauto domin ta yi zaton itama Saliman zata yi girman kai ne irin mijinta, ai kuwa kafin su tafi hira suke yi sosai har suka yi musayar number a kan zasu dinga ziyartar juna akai-akai.

Hafiz ya ji daɗin wannan ƙawancen nasu yayin da Muhammad kuma ya nunawa matarsa baya son hulɗarta da Juwairiyya yayi yawa, bisa la'akari da ya yi na cewa tana da raina mutane da kuma rashin da'a. Sai dai duk da cewa Salima na bin umurninshi amma wannan karon bai samu damar rabata da Juwairiyya ba, ƙarshe haƙuri yayi ya barsu sai dai Cold War da ke tsakaninshi da ita bai ragu ba sai ma gaba da yake yi.

Tun bayan aurensu Muhammad ya fara kwanciya rashin lafiya domin Ulcer da Typhoid da suka mishi rufdugu, Hafiz na yawan bashi shawarar ya rage cin junk foods da suke sakashi ƙiba suke kuma ƙara mishi cuta amma baya ji, da yake haka ya taso a gidansu suna cin duk abun da suke so babu mai hana su. Wannan kenan.

Present

Juwairiyya ce ta gyara kanta data kwantar a kan damtsen Hafiz ta ce,

"Ina jinka."

Shiru yayi kamar ba zai ce komai ba sannan ya fara magana a hankali kamar mai raÉ—a.

"Kin tuna É—azu na faÉ—a miki abun gaggawa ya taso shiyasa muka tafi bamu jiraku ba?"

GyaÉ—a kai ta yi tana haÉ—iye wani yawu mai kauri don zuciyarta bugawa ta fara yi haka kurum ta kasa nitsuwa dalilin Hafiz bai ta6a cewa zasu yi magana sannan yayi using wannan tone É—in ba.

"Bayan mun fito ne na ga jikin Muhammad a sanyaye na tambayeshi me yake damunshi tun da na lura ba rashin lafiyar ce matsalar shi ba a lokacin. Riya ashe muna tafiya da mutumin nan ne amma shi har ya cire rai da tsawon kwana yana ganin lokacinshi ya kusa, hawayen da naga yana yi ne yasa nace mu shiga mota kar mutane su yi ta kallonshi babu daÉ—i ana magana. A nan ya nemi mu bar asibitin mu je wani guri zai yi magana da ni, bayan mun fita muka samu wani guri muka tsaya. A nan yake faÉ—a mini wata magana wacce har yanzu na rasa yaya zan É—auketa."

  Shiru ta yi tana jiransa ya ƙarisa maganan lokaci ɗaya kuma zuciyarta ta sassauto ganin akan Muhammad za'a yi maganar ba wai a kan Hafiz ba.
Chapter 4 · 0% Book details