← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyarta 'Mama' Nurse ce wanda kullum tana fita aiki da safe zuwa ƙarfe ɗayan rana, duk nauyin gidan na ci, sha, sutura, rashin lafiya da kuma abun da ya shafi makarantar ƙannenta a kanta yake babu mai taimaka mata. A hakan kuma ga kakarsu wato mahaifiyar Mama da kullum ake kashe kuɗi a kanta dalilin rashin lafiyan da tsufa ke kawoshi. Don haka wannan ɗawainiyan da Muhammad yake musu ba ƙaramin taimakon Mama yayi wajen samun sauƙin hidimar gidan ba. Kullum tana faɗawa Juwairiyya ta miƙa godiyarta amma bata da masaniyar ko sau ɗaya ita Juwairiyyan bata taɓa isarwa ba.

Dalili kuwa shine, meyasa tun lokacin da Hafiz yake da rai baya mata magana ko amsa gaisuwarta sai da ya rasu zai nuna ya fi kowa tausayinta? Kuma bata nemi taimakonshi ba, jira take yi ta dawo hayyacinta ta fara sana'a don ta taya Mama kula da gidan. Aure kuma babu shi a babinta domin karatu take so ta fara a Gombe State University tun da daga unguwarsu Arawa sai makarantar ko da ƙafa zata dinga zuwa tana dawowa.

Da wannan tunanin ta shige cikin gida ta samu Sumayya na tattara kayan tana kaiwa falon Mama wanda a da shine na Babansu.

"Wannan bawan Allah bai manta da zaman amanan da yayi da abokinshi ba, Allah Ya biyashi da mafificin alkhairi." FaÉ—in Sumayya a lokacin da Juwairiyya ta tsuguna zata ware kayan shayin ta kai É—akinsu domin Mama tace ta dinga É—auka.

Shiru ta yi amma a zuciyarta ta amsa, har ta miƙe da niyyar tafiya sai ta samu kanta da tsayawa ta dubi Sumayya da murmushi a fuskarta ta ce,

"Hafiz É—ina dai ya yiwa takwara Sumayya, wallahi ko yanzu ban gama gaskatawa, ji nake yi kamar wasa yake mini."

"Allahu Akbar!" Sumayya ta kama bakinta har tana jin hawaye na taruwa a idanunta.

Itama Juwairiyya hawayen ne ya taru a nata idaniyar har suka kwaranyo kan ƙuncinta, saurin sharesu ta yi kana ta nufi ɗakin nasu don adana abubuwan hannunta.

Minti goma da haka Sumayya ta gama girkin rana, hakan kuma yayi daidai da dawowar Mama daga aiki wacce ta kwaso gajiya ta nemi guri ta zauna a falonta aka kawo mata abinci.

Tana cin abinci Juwairiyya ta shigo mata sannu da dawowa Mama ta amsa tana tambayarta ko ta ci nata.

"Mama sai anjima zan ci bana jin yunwa yanzu."

"Adda Juwai ki bata labarin abun alkhairin da ya faru." Faɗin Sumayya da take kwance akan kujera hannunta riƙe da wayarta tana chat da saurayinta da aka musu baiko.

"Me za'a faɗa mini?" Mama ta kasa haƙura ta tambaya tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

"Muhammad ne ya sakawa É—anshi sunan marigayi Hafiz."

"Allahu Akbar. Allah Sarki, mutumin nan ba ƙaramin so yake yiwa abokinshi ba. Allah Ya rayashi Ya sa ya ɗauko halin takwaranshi kyawawa, shi kuma Allah Ya gafarta mishi."

"Ameen." Duk suka amsa cikin sanyin jiki.

"Sai ki shirya ki je ki dubota da jaririn ki samu abun da zaki kai musu. Ƴan'uwan marigayin sun sani kuwa?"

"Bana tunanin sun sani don da ƙannenshi sun kirani sun faɗa mini ko Ummarshi."

"To ki kirasu ki sanar dasu, zai yi wuya su ji basu faÉ—a miki ba kam." FaÉ—in Mama domin ta san an yi zaman lafiya da mutunta juna tsakanin dangin Hafiz da É—iyarta, wanda har yanzu suna zuwa dubata in an kwana biyu.

Juwairiyya bata jima a gurin Mama ba ta koma ɗaki dama can ne gurin zamanta kamar matar Liman. Tana zaune tana tunanin me ya kamata ta yiwa Salima na fitan biƙi Sumayya ta shigo ta sameta.

"Yanzu ke kina ganin me zan saya mata? Na san kaya kam iyayenta sun loda mata don masu kuÉ—i ne, haka sauran Æ´an'uwa da abokan arziki. Ina son in yimata kyautan da zata yi amfani dashi kuma zata ji daÉ—inshi."

Shiru Sumayya ta yi, can kuma fuskarta ta yalwatu da murmushi ta ce,

"Babu kyautan da zaki mata yanzu ta ji daÉ—in shi irin Turaren wuta da kuma Humrah. Kuma shine zata yi amfani dashi ba zata kyautar ko ta sayar ba, kin san shi baya yiwa mace yawa sai dai ya mata kaÉ—an."

"Amma kin kawo shawara wallahi. Yanzu ni da nake tunanin zuwa gobe ta yaya zan samu turaren wutan a ƙanƙanin lokaci haka?"

"Ga Dukhan By Ain a Instagram 08088929221. A Abuja take kuma ana yabon turarenta sosai, don ina ganin yanda ake bada positive reviews a Highlights ɗinta. Kwanaki da aka yi auren ƙawata Salma a gurinta duk aka sayi su Turaren wutan, su Kulacca da Humrah. Bari in binciko miki page ɗin don ina following ɗinta, kuma na faɗawa Mama a gurinta za'a haɗa mini turarukana."

Juwairiyya ta harari Sumayya cikin wasa tana cewa,

"Yaran zamani baku da kunya wallahi. Yanzu baki ji kunyata ba?"

"Ki ji Adda Juwai da wata magana, akan turaren wuta fa muka yi magana ba maganin mata ba." Sumayya ta amsa tana danna wayarta tana dariya.

"Shi É—in ma ai zaki iya, yaran yanzu menene baku sani ba."

"Ni kam mu bar maganan nan kina sakani kunya, yauwa gata nan, ki duba daga ganin turarukan an san na Æ´an gayu ne sannan na amare don kowanne ta bashi sunan da ya dace dashi."

"Su kuma uwaren gidan fa?"

"Suma zasu iya saya su saje cikin amaren."

Murmushi kawai Juwairiyya ta yi kana ta karɓi wayar daga hannun Sumayya ta fara ganin pictures ɗin da sunansu da kuma yanda za'ayi amfani dasu. Nan Sumayya ta dawo ta bayanta ta fara mata bayani dalla-dalla.

"Akwai 'Irresistible' wanda Sandal flakes ne ita mai sayarwan ta canja mishi suna. Ga kuma 'Coated Kajiji' wanda ta haÉ—a da secret ingredients É—inta. Ga kuma 'Blissful' gab-gab, wanda ta ce it's best used on clothes, home & body because it's very strong & last long. Wa zata bari wannan ya wuceta? Not me!"

"Ga kuma 'Soothing sandal' shi kuma Sandal Coconut ne, ta ce it has a very soothing scent, best use in ana neman sudden ƙamshi. Musamman in maigida ya kiraki a waya wai gashi yana zuwa da baƙi."

"Wai dama haka kike da surutu Sumayya?" Faɗin Juwairiyya tana duban ƙanwar tata.

"Adda Juwai ke kam ki saurara mana. Yauwa, sannan akwai 'Down to Earth' wato Halut kenan, sai 'Malaak' Halut-hawi mix ne, can be used for clothes, body and home. 'Field of dreams' daga jin sunan kin san yafi daɗi a saka in ana ruwan sama, wai niƙeƙƙen kajiji ne mai sa nishaɗi.
'Habiby mix' kuma signature ɗinta kenan, 3 sticks ta haɗa for clothes, body and home. Gasu nan dai birjik sai wanda kika zaɓa."

"Ni babu abun da yafi burgeni irin 'Earthly wonders' saboda sau nawa ina ɗaukan kaya amma sai in ji yana warin damshi? Shi kuma wardrobe ball ne da zaki jefa a cikin wardrobe yana saka ƙamshi sannan yana ɗauke warin damshin." (Mum Fateey ma tayi order)

"Gurin Khumrah kuma akwai Khalty (normal Black Khumrah), Fatum (normal White Khumrah),
Liquid Gold (oudbased white khumrah). Sai Maya (Oudbased black Khumrah),
Royalty in a bottle (musk based Khumrah), sai uwarsu ubansu wato 'Ain's Signature' Bodymilk ne na jiki, ana iya sawa a ruwan wanka, da ke da bathroom ɗinki duk ku ɗau Ƙamshi. Yana hana warin zufa. Kuma both maza da mata can use it. It has the nicest scent."

"Tana da Kulaccam, 'Malika' (Lotion Kulaccam) 'Ahlaam' (Vaseline kulaccam)."

"Yanda kika zauna kina zayyane turarukan nan kamar haɗin gwiwa aka yi ke da ita. Yanzu dai zan saya mata kala huɗu ki tayani zaɓe."

Da haka suka darje suka zaɓi turaren wuta kala huɗu, khumrah kala biyu da kuma Kulaccam kala biyu. Sai da suka zaba suka kira numbernta 08088929221, daga nan ta basu account number Juwairiyya ta tura kuɗi, kana ta musu alƙawarin gobe da hantsi kayansu zai iso su karɓa a tasha.

"Ya kika ji muryarta?" FaÉ—in Sumayya tana murmshi.

"Me muryan ya yi?"

"Wallahi kalan Æ´an gayu."

Dariya Juwairiyya ta yi kana ta gyaÉ—a kanta ta ce,

"Ba laifi tana da zaƙin murya."

Kuma zaku iya kawo tallenku a muku cikin hikima da jan hankalin mai karatu a cikin farashi mai sauƙi daga 5k zuwa kasa.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

(6)
Washe gari asabar aikan Juwairiyya ya iso ta aika ƙaninta Walid tashan mota ya je ya karɓo mata. Da yamma ta shirya tare da Sumayya suna jiran ƙannen Hafiz biyu mata da zasu biyo su tafi tare. Ana idar da sallah la'asar suka shigo gidan da sallamarsu, gaishe da Mama kawai suka yi suka fita ƙofar gida inda motar ɗaya daga cikinsu mai suna Hafsat yake fake, dashi kuma zasu je gidan mai jegon.

Suna tafiya suna hira tsakaninsu har suka iso gidan Salima, Hafsat ta buɗe booth suka fara ciro kaya ita da ƙanwarta Zainab suna ajiyewa a ƙasa. Daɗi ne ya ziyarci zuciyar Juwairiyya ganin irin hidiman da dangin Hafiz suka yiwa mai jego da jaririn, ta sani Hafiz ɗan'uwansu ne amma ita a gurinta sun mata kara ba kaɗan ba.

A jiya da ta samu labarin ta kira ta faɗa musu, Umma mahaifiyar Hafiz har da kukanta, yau gashi sun aiko mata da kaya niƙi-niƙi tare da alƙawarin Umma da sauran family zasu zo ganin jariri daga baya.

Almajirai suka samu a waje suka tayasu shigar da kayan, Salima da wacce take tayata zaman biƙi suka karɓesu hannu bibbiyu, aka kawo musu juice tare da soyayyen naman rago. Su Juwairiyya suka yi godiya sosai akan karamcin da aka musu na sanya sunan marigayi Hafiz da aka yi. Suma su Salima suka yi godiya bisa hidiman da aka musu.

"Tun jiya nake ta zuba ido na ɗauka zaki zo, da naga baki zo ba shine na kira Muhammad nace ya miki albishir da kanshi. Da dai sunan Babana za'a saka amma nace ya mayar da sunan marigayi zaki ji daɗi ba kaɗan ba." Salima ta ƙarisa maganan hawaye na taruwa a idanunta.

Juwairiyya share fuskarta ta yi dalilin hawayen da ya zubo mata, kana ta dubi jaririn da yake hannunta yaro fari kyakkyawa wai mai sunan Hafiz É—inta.
Chapter 10 · 0% Book details