Sashe 25
Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har maghrib tana nemanta amma bata sameta ba, gashi Mama har ta kafa mata doka kamar kwanakin can wai ba zata fita ba sai da izinin Muhammad mijinta. Abun dariya ya so ya bata, wato shi Muhammad É—an lukutin zata tambaya idan zata fita?
Ganin babu sarki sai Allah yasa Juwairiyya ta danna kiran Muhammad wanda bata ma san ya aka yi ta samu numbernshi ba.
"Don Allah ka zo ina son ganinka." Shine abun da ta faÉ—a da ya É—auki wayan.
"Ba zaki iya jira har ki tare ba kenan?" Ya bata amsa daga cikin wayar.
Sai da tayi jimm sannan ta gane inda maganarshi ta dosa. Kunya da kuma takaici ne ya zo ya rufeta wai yau ita Muhammad yake faÉ—awa maganar banza? Ko da yake laifinta ne da ta faÉ—i wannan sentence É—in don koma waye ne ya ji zai É—auka wani abun take nufi.
"Dalla ni ba abun da nake nufi ba kenan. Allah Ya sauwaƙe God forbid bad thing. Magana nake son mu yi." Ta faɗa a hasale tana ɗaga murya.
"Idan kin koyi magana da miji ki kirani sai mu yi maganar a natse." Da haka ya kashe wayarshi ya bar Juwairiyya da É—an banzan mamaki a fuskarta. Wai da gaske kashe wayar yayi? Lallai bai san wacece ita ba.
Shiru tana zaune tana tunanin zai kirata amma har aka shafe minti ashirin bai kirata ba, kuka ne kaÉ—ai bata yi amma haushi kam ya kusa kasheta. Ashe dama bai daina wannan halin nashi ba?
Ganin babu Sarki sai Allah yasa ta kirashi ta fara magana a hankali.
"Don Allah magana nake son yi da kai in zaka iya zuwa."
"Na ji." Kawai ya faɗa ya ƙara kashe wayarshi.
Wannan karon hanjin cikin Juwairiyya ne ya kaÉ—a domin da alama ta manta waye Muhammad, ta manta É—an banzan halinshi da take kushewa kullum a gaban kowa. Ashe bai daina ba? Yanzu ta yaya zata iya zaman auren dashi na shekara huÉ—un yana gwada mata wannan halin? Lallai watarana zasu yi kokawa, amma da ta tuno siffarshi sai ta girgiza kanta, ba zata fara ba! To yanzu kam yana zuwa ne ko dai?
Bayan wani minti ashirin É—in ya kira wayarta, tana É—auka ya faÉ—a mata yana waje.
Sai da ta faÉ—awa Mama kafin ta fita ta sameshi a cikin mota yana zaune, ganin ta fito yasa shima ya fito suka tsaya gefe da gefen juna.
"Ina ta neman Salima amma har yau wayarta a kashe. Lafiyanta kam?"
"Shine maganar?" Ya tambayeta da É—an mamaki a fuskarshi.
"Akwai wasu amma wannan ne farko."
"Wayarta ce ta fashe."
"Don Allah yaya ta É—auki zancen auren nan? Ta yi fushi ko?" Ta tambayeshi cikin zullumi.
"Ba zan iya faÉ—a miki ba amma dama ta san hakan zai iya faruwa."
"Ban gane ba." Ta faÉ—a cikin ruÉ—u.
"Sai wanne?"
"Ba zaka fahimtar da ni ba kenan?"
"Eh."
"Sai kuma batun tarewa ta ina so sai bayan na gama exams kafin nan mutanen da suke cikin gidana sun fita."
"Me kike nufi kenan?" Ya tambayeta yana É—aga girarshi É—aya wanda bata gani ba dalilin duhun dare.
"A can zan zauna." Ta bashi amsa zuciyarta na bugawa. Dama ta san sai sun kai ruwa rana kafin ya yarda.
"Kina nufin ba zaki zauna a gidana ba kenan ni zan dinga binki gidanki?"
"Ni ban ce ka dinga bina ba, ba lalle sai ka zo inda nake ba."
"Juwairiyya me kika É—auki aure ne? Wasan yara ko shiririta?"
"Yau karo na uku kenan kana kiran sunana a rayuwarka." Ta faÉ—a duk kuwa da irin taraddadin da take ciki.
"Kar ki canja mana magana. A gidana zaki zauna har lokacin da Allah zai buÉ—a mini in canja muhalli, but for now a can zamu zauna."
"Don Allah Muhammad ka rufa mini asiri kar ka kafe akan wannan maganar, aurenka da nayi ma na san Salima zata ji zafinshi shiyasa nake son yin nesa da ita ta yanda ba zata dinga kallona ba balle ranta ya dinga ɓaci. Ka ga kuma gidan ka na zaman mace ɗaya ce ba zai ishemu mu biyu ba. Don Allah ka yi haƙuri."
"Yanzu bari in tambayeki. Wancan mutumin da kika aura kin faÉ—a mishi cewa a gidanki zaki zauna?"
Girgiza kanta ta yi don bata san ina maganarshi ta dosa ba.
"Sai nine da kika rainawa arziki zaki nemi tarewa a gidanki? No. Sai kuma wani magana?"
Wani mololon baƙin ciki ne ya zo ya tokarewa Juwairiyya wuya, ji take yi kamar ta ɗauki sanda ta yita zabga mishi tsabar haushin shi da take ji. Zai ɓata mata tsari, ba haka ta tsara ba. Ta so ta tare a can gidanta da marigayi Hafiz ta yanda zata yi nesa da Salima haka kuma Muhammad ba zai dinga damunta ba saboda zata san yanda zata dinga ɓata mishi rai yana nisantarta, a haka tayi ta cin karenta babu babbaka ita ɗaya har ta gama makaranta ta samu aiki ta kashe auren. Duk wannan tsarin da tayi Muhammad na neman wargaza mata shi.
"To na ji ba zaka bini gidana ba amma ai zaka iya kama mini haya a wani guri kafin Allah Ya buÉ—a maka É—in."
"Bani da kuɗin karɓan hayan wani gida alhali ga nawa."
"Muhammad ka yi haƙuri don Allah, wallahi ko tsugunawa kace in yi zan yi don kar ka haɗamu gida ɗaya." Ta faɗa da bakinta amma zuciyarta na jin takaicin furucin.
"Ke ma ki yi haƙuri amma ba zan raba muku gida ba, tun farko haka ne tsarina kuma ba zan canja ba."
Tsabar baƙin ciki komawa ta yi cikin gida ba tare da ta mishi sallama ba. Tana shiga ɗaki kuwa ta ji wayarta na ringing wanda tana dubawa ta ga sunan Salima ce a jiki wanda ta sanya mata 'Maman Masoyi'. Tsoro ne ko fargaba ya hanata ɗauka sai Allah! A haka ya tsinke can kuma aka sake kira ta ɗauka hannunta na rawa bakinta kuma ya fara rasa yawu.
"Hello." Ta furta muryarta na rawa kaÉ—an.
"Amaryar mu! Baban Hafiz yace kina ta nemana a waya baki sameni ba, wallahi jiya ne yace in kashe wayar ban san dalili ba, daga nan kuma na ajiyeta a kan kujera Masoyinki ya jawo ya dokata a ƙasa sai da taci screen. Yanzu aka dawo mini ita daga gurin gyara shine nace bari in kiraki. Kar in cikaki da surutu, Congratulations! Allah Ya bamu zaman lafiya da fahimtar juna." Faɗin Salima ta cikin wayar da alama bata da damuwar komai a ranta.
"Ranki bai ɓaci ba da na aure miki miji?" Juwairiyya ta tambayeta tana jin hawaye na taruwa a idanunta.
"Ko bai aureki ba zai auri wata, to na gwammace a kawo mini ke domin na sanki kema kin sanni kuma zamu fi fahimtar juna mu lallaɓa rayuwar mu. Kin san yanda mijin namu yake, yanzu idan nace ma zan ɗaga hankalina sai na gwammace kiɗa da karatu."
Hawaye ne ya zubowa Juwairiyya domin da alama ta manta halayen Muhammad, da gaske ta manta. To in ba haka ba sau nawa Salima tana faɗa mata abubuwan da yake mata tana jin haushi a ranta har take jin da tana da iko dashi da sai ta hukuntashi! Yau gashi itama tun kafin aurensu ya kwana ya shirga mata baƙin ciki, kuma babu yanda ta iya dole ta bishi saboda babu yanda zata yi. Duk masifanta ta sani cewa ba zai yi amfani akan Muhammad ba.
"Da gaske baki yi fushi ba?" Ta ƙara tambayarta don sanin zuciyar Salima.
"Na faÉ—a miki ban ji komai ba, fatana Allah Ya bamu zaman lafiya. Maganganun da yawa amma sai gobe zan kiraki zan je in yiwa Muhammad aiki kar ya dawo ya samu ban yi ba."
Da haka suka yi sallama Juwairiyya na jinjina haƙuri irin na Salima, ta wani gurin kuma tana tausaya musu dukkansu domin Muhammad ya cika mugun mutum kuma mara tausayi.
Sati ɗaya da haka Juwairiyya ta fara exams wanda Muhammad ya nema mata mai napep da zai dinga kaita yana dawo da ita domin ya ce baya son tana zuwa bakin titi taran abun hawa, sannan shi kuma ba zai iya kaita ba domin yana da ayyuka. A haka taci gaba da rubuta exams ɗinta cikin nitsuwa domin bata da damuwar komai yanzu in ba ta Muhammad ba, yana zuwa dubata kullum sannan ya tambayeta ko tana da wata buƙatar da zai iya biya mata? Idan tana dashi sai ta faɗa ya saya mata, wani lokaci kuma sai ta ƙureshi ta tambayeshi abun da ta san ya fi ƙarfinshi, to a nan ne zasu yi dramansu su rabu. Sai kuma Mama ta daina tsangwamarta, Salima kuma da take tunanin za'a samu matsala da ita sai ta bata mamaki domin kuwa sai ta ga kamar ma sun ƙara shaƙuwa akan yanda suke a da, domin duk gyaran gidanta da ake yi na toshe-toshe tana faɗawa Juwairiyya watarana har ta mata video.
Dama gidan Muhammad ba wani babba bane, da ka buɗe gate ka shigo zaka samu farfajiyar gidan mai ɗan faɗi amma mota ɗaya zata iya ɗauka, ƙofofi biyu zaka gani a jikin ginin gidan wanda na gefen dama ƙofa falon Muhammad ne da kuma ɗakinsa da banɗaki a ciki, a cikin falon kuma akwai wata kofa wacce ita ta raba tsakaninshi da falon Salima, wanda ita nata gefen ɗaki take dashi da kuma kitchen ɗinta wanda yake da ƙofa ta bayan ɗakunan nasu. To wannan ƙofar tsakanin falon Salima da Muhammad ɗin aka toshe, sannan aka yanki wani guri kaɗan a cikin tsakar gidan nasu aka yiwa Juwairiyya ƙaramin kitchen kamar ɗakin maigadi.
Duk lokacin da Salima ta nuna mata progress É—in aikin sai tayi tsaki tana jin haushi a ranta sannan sai ta fara kushewa, tana faÉ—a mata cewa ita ba haka ta so tun farko ba, sannan ga plan É—inta na zama a gidanta amma Muhammad ya hanata. Wannan kenan.