← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 26

Sashe 2

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kuwa tana juyowa ta haɗa idanu dashi ta bar gefen Juwairiyya ta koma bakin aikinta ba tare da ta ƙara cewa komai ba. A hankali Hafiz ya take ƙafar Juwairiyya wacce tun shigowarsu ta samu plastic chair ta zauna bata ko kalli in da Muhammad ɗin yake ba, ɗago kanta tayi suka haɗa ido yayi mata nuni da mara lafiyan da bakinshi. Ɓata fuska tayi sannan ta dubi sashen da mara lafiyan yake tace,

"Ya jikin?"

Bai amsa ba illa kawar da kanshi da yayi bayan itama ya aika mata mummunan kallon irin wanda ya yiwa matarsa É—azu. Kwafa Juwairiyya tayi a ranta tana jin haushin wulakantata da yake yi tun ba yau ba, a ranta kuma zaginshi take yi tare da Hafiz É—in da ya matsa mata tilas sai ta zo nan.

"Ana gaisheka." FaÉ—in Hafiz ga Muhammad ganin bashi da niyyar amsa gaisuwar tata.

"A ina?" Yayi tambayar kamar da gaske bai ji ba.

Hafiz yayi ajiyar zuciya cikin gajiyawa da halinsu kana ya miƙawa Salima fruits ɗin yana cewa,

"You know what? Ya wuce. Salima ga fruits and idan kin gama tattaren ku samemu a waje mu mayar da ku gida. Kai kuma ka tashi mu fita kasha iska kafin su fito."

"Hafiz na kira Abbati zai taho da motata nasan yana hanya ko ma ya iso." Muhammad ya bashi amsa yana sauƙowa daga kan gadon sai ƙara take yi dalilin nauyin shi.

Juwairiyya ce tayi siririyar tsaki tana ayyanawa a ranta cewa lukutancinshi kaÉ—ai ma ta isa tasa cututtuka su dameshi tun da ba'a iya wata biyu sai ya kwanta rashin lafiya. Suna fita Salima ta dakata da abun da take yi tana murmushi tace,

"Sorry fa ƙawata, yau laifina ya shafeki gashi ko gaisuwarki ba'a amsa ba."

Tsaki Juwairiyya ta ja wannan karon ba tare da ta ɓoye sautinsa ba ta dubi Salima tace,

"Kina haƙuri da wannan mutumin, amma gaskiya ko sau ɗaya ne ya kamata ki nuna mishi bakya tsoronshi kuma ke mutum ce. He should stop ordering you around da kakkausar murya cikin bainar jama'a saboda hakan bashi da daɗi kuma girmanki yake zubarwa."

  Salima tana jin Juwairiyya ta fara faɗan data saba muddin tayi witnessing Muhammad yana treating ɗinta irin haka sai kawai taci gaba da aikinta wanda dama ta kusa gamawa.

"Hmm, ba zaki gane bane. Mu tafi kar suyi ta jiran mu bamu fito ba mu ƙara yin wani laifin." Ta faɗi hakan tana ɗaukar ƙatuwar ledan tare da wani mini trolley wanda Juwairiyya ta tabbatar suturun Muhammad ne a ciki.

"Ai komin rashin lafiyarsa bai kamata ya bar miki duk wannan kayan ki É—auka ba, he had to atleast take the mini trolley tunda janshi zai yi yana da taya, ke kuma sai ki É—auki ledan." FaÉ—in Juwairiyya tana tuna yanda Hafiz baya barin ta É—auki komai idan sun je shopping ko kuma zasu fito daga gida. Cewa yake yi zai yi spoiling É—inta saboda ita É—in abar tattalawarshi ce.

Salima ta kalli kayan hannunta cikin confusion don ita bata ga laifin hakan ba, ai shine mara lafiya bai kamata ma tun farko ta barshi ya É—auki kaya ba, da haka suka fita daga É—akin tana cewa,

"Ni kuma dai bana ganin laifinshu, don sau da dama in ya mini faÉ—a to laifi nayi, kawai don Hafiz ya sakaltaki ne yana miki duk abun da kike so shiyasa kike ganin kamar ni a takure nake. But rayuwarku tana burgeni saboda yana nuna miki so da kulawa a duk inda kuke baya gajiyawa, ni kuma gogan nawa soyayyar ce bai iya ba kuma na kasa koya mishi."

"Alhamdulillah Hafiz is good to me, but I really hope one day kema a nuna miki so kamar yanda yake nuna mini, wallahi daga ranar zaki gane zaman da kike yi da Muhammad akwai takura da kwara a ciki. Allah kuma ya ƙara miki haƙuri akan wanda kike yi shi kuma ya shiryeshi. Ni na manta ne ma nayi magana, don na lura daga ke har Hafiz bakwa son laifinsa ko kaɗan sannan kullum cikin karesa kuke kamar wanda ya muku asiri." Ta ƙarisa maganan cikin raha ganin Salima ta fara shiga damuwa akan maganar da take yi wanda har ga Allah ba wai kusheshi take yi don ta ji zafi ba, a'a ita ta ƙi jinin ta ga ana cin zarafin mutum ne kuma yana shiru ya kasa taɓuka komai. Halinta na rashin ɗaukan wulaƙancin mutane yasa wasu suke cewa tana da rashin kunya da kuma masifa.

  Da haka ta canja musu hirar sannan ta karɓi ledan hannun Saliman suka fita daga building ɗin zuwa waje inda Hafiz yayi parking. Wayam babu su babu alamarsu sai wasu tsiraran motoci da kuma Keke Napeps da suke ficewa da mutane daga asibitin tunda lokacin visiting patients ɗin ya wuce. Juwairiyya ce ta ɗauko wayarta ta danna kiran Hafiz tana cewa,

"To ina suka yi?"

Hafiz yana É—aukan wayar ya fara magana,"Riya dama yanzu nake da niyyar kiranki wani abu ne ya taso mana cikin gaggawa muka tafi amma ga Abbati yana zuwa zai mayar da ku gida. Ina fatan hakan ya miki?" Yayi maganan cikin sanyin murya kamar yaron da yayi laifi yana neman tuba.

Wani sanyi ne ya ratsa zuciyar Juwairiyya tana tunanin ta yaya zata iya fushi mai tsawo da mutum kamar Hafiz? Mutumin da yake treating É—inta kamar ita ce kaÉ—ai mace a duniya kuma baya son fushinta?

"Babu komai Bee, zamu ƙarisa gidan Saliman idan ka gama abun da kake yi sai ka biyo ka ɗaukeni mu koma gida."

"Good girl. Sai na dawo."

Kafin ya kashe wayar tayi saurin dakatar dashi da cewa,"Bee, ya naji muryarka wani iri, lafiya kam?"

Tana saurara yayi ajiyar zuciya kana yayi murmushi mai sauti ya ce,

"Har na daina mamakin yanda kike gane canji a tattare dani daga sauraran muryata kaÉ—ai. I'm fine sai na dawo zamu yi magana."

Bata musa mishi lallai sai ta ji me yake damunshi ba saboda ta lura kamar ma driving yake yi, sannan ta san ba zai ta6a ɓoye mata damuwarshi ba kuma kamar yanda yayi alƙawari, yana dawowa gida zai faɗa mata kuma da shi da ita zasu zauna su magance matsalarsu ba tare da kowa ya sani ba. Sallama suka yi ta juyo tana kallon Salima wacce ke waya har tana rage tsayinta idan tana magana, hakan yasa Juwairiyya ta gane cewa da Muhammad ne domin shi kaɗai take bawa wannan girman kamar zata nitse cikin ƙasa.

Salima tana gama wayar ta mayar da ita cikin jakarta ta dubi Juwairiyya da ke waige-waigen ta ina zata hango mai É—aukan nasu domin zaman asibitin har ya fara gundararta.

"Zamu ƙara minti kaɗan domin Muhammad ya aikeshi kasuwa zai sayo karkashi zan mishi tuwo." Faɗin Salima tana gyara tsayuwarta.

Wani takaici Juwairiyya ta ji domin ta lura Muhammad sam baya tausayin Salima, tunda ya kwanta rashin lafiya tare dashi take kwana kuma a hakan da safe zata koma gida ta mishi karyawa ta bayar a aiko mishi kafin nan ƙaninshi zai zauna dashi, da azahar zata dawo da abincin rana har dana dare wanda wai shi gogan baya cin abinci iri ɗaya sau biyu a rana. To idan ta zo tun azahar ɗin shine baza ta koma ba sai washe gari da safe, kuma ko ta koma gidan ba hutawa zata yi ba abinci zata dafa ta ƙara dawowa dashi.

  To duk wannan ɗawainiyar da tayi mishi meyasa yau ba zai iya mata haƙuri ya barta ta huta ba? Anya mutumin nan yana da tausayi kuwa? Har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta rufe domin yawan maganar ma bashi da daɗi, domin ita Saliman zata ga kamar faɗa take son haɗasu, sannan ita ta ganshi tace tana so kuma take son zama dashi a haka ba tare da ta yi ƙoƙarin canja musu Tafiyar tasu ba. Sannan Juwairiyyan ta sani idan ta yawaita magana da kusheshi wataƙila Saliman zata ji haushinta saboda har ga Allah ita ma baza ta so taji wani yana aibata Hafiz ɗinta ba.

Wannan karon Salima ce ta canja musu hiran ta kawo musu hiran cikinta da ya shiga wata na uku amma tana nan garau babu rashin lafiya babu laulayi kamar ba ciki ne da ita ba. Ai kuwa ta taɓowa Juwairiyya gurin da yake mata ƙaiƙayi domin tana son duk wata hira da za'a sako maganar yara a ciki saboda tana son haihuwa, gashi yanzu shekarar aurensu ɗaya kenan da Hafiz amma ko ɓatan wata bata taɓa yi ba. Salima kuma sun shiga wata na shida kenan amma gata da ciki har na wata uku, ko dai ita juya ce bata haihuwa? Tana yawan yiwa kanta wannan tambayar wanda har ta kai bata ɓoyewa Hafiz damuwarta ba, shi kuma as usual kwantar mata da hankali yayi har yana tsokanarta da cewa dama bai gama moreta ba ta ƙara wasu watannin kafin ta ɗauki ciki. Ire-Iren wannan barkwancin Hafiz ɗin yasa ta rage nuna mishi damuwarta tana kuma addu'ar Allah yasa ta samu ciki ta riƙe ƴaƴanta a hannunta itama.

  Minti goma da haka Abbati ƙanin Muhammad yayi parking a gefensu ya fito ya ƙarɓi abun hannunsu ya shigar cikin booth kana ya shiga motar suka wuce gidan Saliman kamar yanda suka tsara.

  Wani gida madaidaici da ke unguwar Jekadafari  suka shiga wanda nan ne gidan Salima da Muhammad, Abbati ne ya fita ya buɗe musu gate kana ya dawo cikin motar ya shigar da su harabar gidan mai ɗaukan mota ɗaya. Suna tsayawa wata budurwa mai taya Salima aiki mai suna Nanayo ta fito daga cikin gidan ta musu sannu da zuwa tare da karɓan kayan abincin daga hannun Abbati ta shige dasu ciki bayan Salima ta umurceta da ta yanka karkashin ta kuma ɗaura mata ruwan tuwo. Sallama tare da godiya suka yiwa Abbati wanda ya ƙara fita da motar domin kaiwa mai ita.

A falon Salima daya gaji da haɗuwa suka sauƙa wanda yake cikin tsafta ga ƙamshi sai tashi yake yi a ciki, tuni Juwairiyya ta cire gyalenta ta ajiye a gefe tana sauƙe ajiyar zuciya irin ta gajiya.

"Wash Allah na."
Chapter 2 · 0% Book details