← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 26

Sashe 22

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A yanzu itama Juwairiyya tana son yin auren domin ta huta da faɗan Mama sannan ta huta da tsegumin mutane, hakan yasa wannan karon duk wanda yayi sallama da ita zata fita ba tare da an mata dole ba. Ita kanta mamaki take yi wato idan duniya ta bugeka zaka yi hankali babu wanda ya sani. Sai dai matsalar da aka samu shine duk cikin masu zuwa gurin nata a yanzu ƴan iskan sun fi yawa musamman da suka samu labarin cewa wai ita jarababbiya ce, waɗanda suka zo da niyyar aure kuma tayi rantsuwa da Allah su ba ajin aurenta bane. Duk da cewa tana son auren tayi alƙawarin ba zata auri wanda zata dawo tana dana sanin aurenshi daga baya ba.

Ana cikin haka Hussaini ya dawo da jarabarshi tare da wani magidanci mai suna Salisu wanda gurin aikinsu ɗaya da Mama sannan Maman ne da kanta ta bashi izinin neman Juwairiyyan. Ranar farko da ya fara zuwa ta nuna bai mata ba don haka kawai ta ji tana jin haushinshi, a zuwanshi na biyu kuwa da ta kalli cikin idanunshi da ya sakawa kwalli sai ta ji wani sashe na hankalinta ya kau, abun bai tsaya a nan ba domin kuwa bayan tafiyanshi duk waɗanda suka zo sai ta koresu kuma abun mamaki Mama ta daina cewa komai, hakan yasa babu mai zuwa gurinta a yanzu sai Hussaini mai baƙar jaraba da kuma Salisu mai kwalli a ido.

Juwairiyya tana shigowa gida ta kai jakanta ɗaki kana ta fito tsakar gida ta ɗaura musu abincin rana wanda shinkafa ce da wake da mai da yaji. Tun da ta dawo Nan bata fito ba hakan yasa bayan ta sauƙe abincin ta gama rabiya ta kai mata nata har ɗakinta ta ajiye ta sameta tana bacci, bata tasheta ba ta fice don zuwa gyaran ɗakin Mama, tana gamawa Maman ta dawo daga aiki wanda kai tsaye ta wuce ɗakin Nan don dubata da yake ta kwana da zazzaɓi. A nan ta tarar da gawar mahaifiyar tata wacce ta mutu cikin baccinta, tana hawaye ta gyara mata kwanciyarta sannan ta lulluɓeta ta fita zuwa ɗakinta ta samu Juwairiyya na adana tsintsiya don ta gama mata sharan.

"Mama me ya faru kike kuka?" Juwairiyya ta tambaya cikin kiÉ—ima don ta jima bata ga mahaifiyarta tana kuka ba.

"Allah Ya yiwa Nan rasuwa, wahalarta ta ƙare. Ki kira kannena a waya ki faɗa musu." Tana faɗin hakan ta fice ta koma ɗakin Nan ta bar Juwairiyya itama hawayen na zuba a idanunta.

Ya za'a yi Mama ta barta da wannan aikin? Me yasa ita ba zata kirasu ta faÉ—a musu ba sai ita? Me zata ce musu? Tana tsaye a gurin Mama ta dawo ta É—auki wayar ta fara kiransu tana faÉ—a musu don kamar itama ta ga ita ya dace ta kirasu ba Juwairiyya ba. Wannan abincin da ba'a ci shi cikin daÉ—in rai ba kenan, ana sallar la'asar kuwa aka kai Nan makwancinta na gaskiya.

Mum Fateey 👌

TAFIYAR MU

Suwaiba Muhammad
(Mum Fateey) 09023713064

(13)
Bayan rasuwar Nan da sati biyu Mama ta koma bakin aikinta, hakan yasa in zasu fita sai dai su rufe gidan tunda babu kowa a ciki domin Surayya yini take a school sai yamma take dawowa, Walid kuma da Mama ta lura zai fi ƙarfinta sai ta mayar dashi boarding school na wani babban malamin addini da yake can Kano, cikin ikon Allah kuwa ya fara nitsuwa domin bayan karatu da ake koya musu a can har da tarbiyya. Idan kuma Juwairiyya bata da lectures sai ya kasance ita ɗaya za'a bari a gida, wannan tsarin yasa Mama ta tashi haiƙan da cewa Juwairiyya ta zaɓi miji tayi aure bata son zamanta ita kaɗai a gidan.

Yau Salisu ya kawowa Juwairiyya ziyara wanda da ya aiko yaro cewa yana waje sai da zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske kamar kullum, domin ta lura kamar shakkarshi take ji bata kuma iya mishi musu. Sau da dama sai ta fita da niyyar korarshi sai ta kasa, haka zai gama surutunshi ya tafi tana biye mishi domin kuwa bata son ta ɓata mishi rai.

Fuskarta babu walwala ta fita ta sameshi a cikin motarshi yana zaune, gaisheshi ta yi daga waje ya ƙi amsawa kana ya dubeta a lalace yace,

"Ki shigo motar mu yi hira."

Girgiza kanta tayi alamar a'a amma kuwa zuciyarta lugude take yi don bata san yanda Salisu zai É—auki hakan ba. Gimtse fuskarshi yayi sosai ya dubeta a karo na biyu ya gyara zamanshi ya ce,

"Ki shigo bana son musu Juwairiyya. In kuma kina son raina ya ɓaci ne to bismillah."

Kamar zata yi kuka haka ta shiga cikin motar wanda zata iya rantsuwa bata taɓa shiga motar duk wani mai nemanta ba sai a kanshi. Zuciyarta ta haneta ya fi sau a ƙirga amma kuwa gangan jikinta ya kasa kin aikata abun da aka umurceta a kai ɗin. Suna hiran kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ji ya kamo hannunta ya fara murzawa, wannan abun da ya mata shi yasa ta zabura ta kwace hannun nata tana mai jin tsanarshi a cikin zuciyarta. Zagi da baƙaƙen maganganu kuwa babu irin wanda bai zo cikin zuciyarta ba amma ta kasa furtawa a harshenta, ji tayi hawaye sun taru a idanunta tana jin ta tsani kanta da shi Salisun amma babu yanda ta iya.

"Yaya dai?" Ya tambayeta kamar bai san me yayi ba.

"Don Allah kar ka sake taɓani wallahi bana so." Ta faɗa a sanyaye kamar mai neman gafara.

"To don na riƙe hannunki shine ya zama laifi? Ba aurenki zan yi ba?" Ya tambayeta kamar mai yin faɗa.

Girgiza kanta tayi sannan ta É—ago fuskarta wacce tayi kalar tausayi ainun ta ce,

"Na sani amma ni bana jin daɗi ana taɓani ne. Kayi haƙuri."

"To naji ba zan sake ba, amma dai ki barni in riƙe hannun naki one last time. In kin barni na riƙe ba zan ƙara tambayarki ba." Ya faɗa yana mai ware tafin hannunshi akan ta ɗaura nata a kai.

Miƙar da hannunta tayi don yin abun da ya buƙaceta da yi amma suka ji an kwala mata kira da wata kakkausar murya wacce ta sa hanjin cikinta suka kaɗa.

"Juwairiyya!" Da sauri ta juyo a razane tana ganin mutumin da yayi kiran nata.

Muhammad ne tsaye a bakin window ta gefen Salisu da alama ya ji kuma ya ga duk abun da ya faru. Fuskar nan tashi ta turnuƙe har sai da tayi jaa tsabar ɓacin rai yana tsaye yana kallonsu.

"Ki fito daga motar É—an iskan nan." Ya umurceta yana nuna Salisu da yatsa.

Har ta juya da niyyar fita sai kuma ta juyo tana kallon Salisu kamar mai neman izininshi shi kuma Muhammad yake kallo yana mishi wata murmushin mugunta.

"In fita?" Ta tambayi Salisu domin kuwa itama tana son fitan bata son ƙara ko second ɗaya ne a ciki.

Bai amsa ba sai da ya É—auki seconds talatin suna kallon-kallon tsakaninshi da Muhammad sannan ya gyaÉ—a mata kai ta fita da sauri ta samu guri ta tsaya tana kallonsu.

Sai a lokacin Muhammad ya dubeta kamar wanda zai daketa ya ce,

"Yanzu ke baki ji kunya ba? Yanzu wannan mutumin ne zai sa ki saɓawa ubangijinki? Ina hankalinki da iliminki yake?"

"Mallam kai waye zaka zo har ƙofar gidansu kana zaginta? Ta sanka ne ko ƙarfin hali ne irin naku na ƴan sa ido?"

"Ba da kai nake yi ba, ka kuma riƙe sauran guntun mutuncinka." Da haka ya ƙara maida dubanshi kan Juwairiyya wacce ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta amma idanunta na zubar da hawaye.

"Wannan ba halinki bane kar kuma ki bari wani ya zo ya ɓata miki tarbiyyar da aka jima ana baki. This is not you at all! Me yake damunki?"

"Don Allah ka tafi." Ta samu kanta da faÉ—i ba tare da ta kalleshi ba.

"Mallam ka ji tace ka tafi." FaÉ—in Salisu yana kaÉ—a kanshi kamar yana jindaÉ—in draman da suke yi.

Takawa Muhammad yayi da niyyar zuwa gurinta amma tayi saurin dakatar dashi ta hanyar É—aga mishi hannu tana cewa,

"Just ka tafi, ba ya buƙatar ganinka a nan."

"Something is wrong with you, this ain't you! Yaushe kika damu da abun da wani yake so?"

Wannan magana yasa ta harareshi sannan tace,

"Wato a haka ka É—aukeni? Muguwa wacce kanta ta sani bata damu da wasu ba?"

Zai yi magana Salisu ya rigashi don ya lura spotlight É—in ya bar kanshi ya koma kansu, hakan bai mishi daÉ—i ba don haka yace,

"Juwairiyya ki shiga gida sai gobe idan na dawo." Yana gama magana ƙafafunta suka fara takawa ta nufi cikin gida.

Muhammad da hakan ya bashi mamaki yayi mata magana na ƙarshe don ya ga reaction ɗinta ya ce,

"Muhammad Hafiz bashi da lafiya suna kwance a asibiti, mamanshi tace tana son ganinki."

Tsayawa tayi cakk sannan ta juyo fuskarta ɗauke da matuƙar damuwa ta ce,

"Subhanallahi me ya sameshi?"

"Juwairiyya ki koma cikin gida bana son tsayuwarki da wannan mutumin. Ki kirasu a waya ki gaishesu ya isa." Faɗin Salisu a hasale domin zuwan Muhammad yana ƙoƙarin ɓata mishi shirinshi.

Bata ƙara magana ba ta shige cikin gida da sauri, hakan yasa Muhammad ya juyo ya kalli Salisu wanda shima shi yake kallo irin 'me zaka yi akai?' Bai ce komai ba ya shige motarshi ya tafi, ganin haka yasa shima Salisu ya kaɗa tashi motar ya bar unguwar yana ayyanawa a ranshi cewa Juwairiyya ta fara mishi musu ya kamata ya ƙara ɗaukan mataki a kanta.

Da daren ranar aka aiko wani yaro gurin Juwairiyya da wani leda babba tare da wani guntun note a paper wanda ta karanta kamar haka...

'Ina ta duba hanyarki amma baki zo ba, jikin Hafiz har yayi sauƙi an sallamemu. Amma kafin nan sai da muka haɗa maganin da na gida kamar mayu ne suke son tsoritashi. Ga wannan ganyen magarya ne da wasu haɗi da aka yi don kare jikin mutum daga miyagun mutane, its 100% halal and sunnah kuma na karya sihiri ne. Ki tafasa ganyen kiyi wanka dashi sai kuma ki dinga karanta waɗannan addu'o'in a ruwa kina sha.'
Chapter 22 · 0% Book details