← Book details Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 26

Sashe 1

Tafiyar Mu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read


Bismillahir Rahmanir Rahim

  (1)
4:00pm
    Ruwa ne yake ke sauƙa daga sararin samaniya a garin Gombe, hakan yasa baza ka ji sautin komai ba sai ƙaran ruwan dake dukan rufin gidajen mutane dalilin kowa ya shige cikin gidansa. A wannan daddaɗan yanayin kuma a wata unguwa da ake kira Tumfure wasu ma'aurata ke zaune a wani babban falo akan kujera ɗaya, manne suke da juna a lulluɓe da wani ƙaramin bargo suna magana jefi-jefi dalilin kallon TV da suke yi bai bari sun samu hankalin junansu ba, ana gama film ɗin da suke kallo suka ja ajiyar zuciya a tare kana suka dubi juna suna murmushi.

Mijin ne ya gyarawa matarsa zaman bargon ganin ƙafarta ɗaya ta fita daga ciki, bayan yayi na'am da aikinshi sai ya dubeta da tsantsar soyayyarta a kwayar idanunshi.

"Riya kin koya mini kallo, and the worst part of it shine wai Korean Series nake zama ina kalla ni Hafiz." Ya nuna kanshi da yatsa don emphasizing maganarshi.

  Wacce ya kira da Riyan ta kama yatsar tashi tayi saurin kaiwa bakinta ta ciza wanda hakan yasa Hafiz ya janye cikin jin zafin cizon yana dubawa yana kuma ƙoƙarin tsumewa amma yanayinshi ya fallasashi, wato murmushin da yake yi har yanzu bai bar fuskarshi ba.

"Sorry." Ta furta tana kama kunnenta ɗaya tana dariya ƙasa-ƙasa.

"Kin ɗauki bashi kuma zan rama a lokacin da baki yi tsammani ba, I swear." Ya ƙarisa maganan yana ɗanɗana yatsarshi a harshenshi alamar rantsuwa.

Murmusawa tayi wanda har sai da fararen hakwaranta suka bayyana gefen kumatunta É—aya kuma ya lotsa.

"You look childish idan kayi wannan abun. Amma Bee ba nace kayi haƙuri ba?" Ta zumburo baki cikin shagwaɓa wanda hakan yasa Hafiz ya girgiza kanshi.

"Duk maganar da zaki faɗa ki faɗa amma ba zan haƙura ba sai na rama, shiyasa na rantse. Oya ki tashi mu yi sallah mu je gaishe da Muhammad, bana son har a sallameshi baki je ba." Ya miƙe tsaye tare da miƙa mata hannunshi ɗaya ta kama kana ta tashi suka fuskanci juna bayan ta yaye bargon daga jikinta gaba ɗata ta ajiye a gefe.

Ido ta tsura mishi tana kallon surarshi dake burgeta tun mafarin haɗuwarsu. Hafiz baƙi ne mai tsantsar kyau a idanunta, ba kuma irin wanda ake faɗa a littafin Hausa da za'a ce ya zarce tunanin mai tunani ba, a'a, shi Hafiz ɗinta daidai ne wanda bata son a ƙara mishi komai haka kuma bata son a rageshi da komai. A gurinta Hafiz shine perfect example na namijin duniya da kowacce mace zata yi farin cikin samu. Dalilin tsayinshi yafi nata yasa dole sai da tayi ɗagelgel ta tsaya kan yatsun ƙafafunta kafin ta samu damar kissing ɗin bakinshi mai faɗi game da duhu.

  Idanunshi ya lumshe yayi saurin zagayeta da hannayenshi wanda hakan yasa ta mannu da jikinshi har tana dafa ƙirjinshi a yayin da itama take rufe nata idanun. Sun kai minti ɗaya a haka suna exploring jikin juna kafin Hafiz ya sunkuceta duk da nauyinta yayi ɗaki da ita.

A kan gado ya direta yana ƙoƙarin cire singlet ɗin jikinshi ta tashi zaune tare da mishi farii da ido tace,

"Bee kace zamu je asibiti gaisuwa fa!"

Hafiz da kashi casa'in na hankalinshi na ga abun da yake muradin yi ya hayo kan gadon yana cewa,

"That could wait, but for now let's make love."

Wani shu'umin murmushi tayi domin tun farko ƙudurinta kenan na hanasu fitan, babu wani dogon bayani ta biye mishi suka yada zango a sansanin ma'aurata.

Awanni biyu da haka ruwan saman ya tsaya wanda hakan kuma yayi daidai da ƙarfe shida na yammacin asabar, Hafiz da matarshi ce suka fito daga cikin gidansu sun yi wanka sun shirya tana kulle ƙofa tana zumbura baki. Hankali kwance kuma cikin jindaɗin yanayin daminar Hafiz ya shiga cikin motarsa ta gani ta faɗa a gari da ke harabar gidan ya kunnata, maigadinsu na jin ƙarar motar ya fito daga ɗakinsa ya fara ƙoƙarin buɗe musu gate.

Second biyar da haka itama buɗe gaban motar ta shiga tana kallon window fuskarta a kwaye. Briefly Hafiz ya dubeta a yayin da yake yin reverse zai fita daga gidan, murmushi yayi bai ce komai ba har suka fita daga gidan ya ɗagawa maigadin nasu hannu bayan ya aiko mishi da gaisuwa. Sai da suka fara tafiya ya ɗaura hannunshi ɗaya kan cinyarta yana mata tafiyan tsutsa yana kuma ƙara yin gaba wanda hakan ya fara canja mata yanayinta cikin ƙanƙanin lokaci.

  Ture hannun nashi tayi tana ƙara zumburo bakinta ita ala dole tayi fushi amma shi bai bar murmusawa ba, a ƙarshe ma mayar da hannunshi yayi yana mai cigaba da tsokanarta.

"Allah ka bari bana so."

"Allah ka bari bana so." Ya kwaikwayi muryarta yana dariya kaɗan har Adam apple ɗinshi yana sama yana ƙasa.

"This is not funny." Ta faÉ—a tana fuskantarshi a karo na farko tun shiganta cikin motar, harara ta dalla mishi wanda ya mayar mata da martanin alamar kiss har da hurawa a gareta.

Kwafa tayi ta harɗe hannayenta saman ƙirjinta ta ƙara juyar da kanta ga window tana kallon gidajen da suke wucewa har suka hau titi tafiyarsu ta daidaita.

"Seriously me yasa bakya son zuwa gaisheshi? Mutum ya kwanta bashi da lafiya har kwana uku kuma kina ƙawance da matarshi amma kice baza kije ki gaisheshi ba? Ranar da aka kwantar dashi nace ki kirashi kika ƙi, jiya nace muje in kaiki amma kika ce kanki na ciwo, yau kuma kika shammaceni na kwashi gara wai duk don kar mu je amma baki san na gane wayon naki ba and here we are, mun kashe arna kuma mun fito gaisuwan. Yanzu ki faɗa mini dalilinki na tsanarshi Juwairiyya, wallahi wani lokaci har kunya nake ji idan naga kina mishi wasu halayen, ke ko kunyar matarshi bakya yi?" Ya ƙarisa maganan fuskarshi babu yabo babu fallasa domin tun ba yau ba yake sane da rashin jituwan da ke tsakanin matarsa da babban abokinsa.

First impression ɗin Muhammad a gurin Juwairiyya shi ya jawo duk wannan bashin gaban, faɗan da Hafiz ya yiwa Muhammad yasa yayi ƙoƙarin gyarawa amma ko da ya nuna sakin fuskarsa ga Juwairiyya wacce take cike da haushinshi sai ta basar ta nuna bata san yana yi ba.

Hafiz ya so tankwara matarsa amma abun ya garara domin ta kafu ne a kan dalilanta na wasu halayyar Muhammad É—in wanÉ—anda shi haka ya tashi da
su babu mai canjashi kamar yanda itama tana da wasu halayen da mutane basa so kuma ba zata canja ba.

"He is always grumpy kullum mutum a tsume kamar kashi, ga É—an banzan wulakanci ana gaisheshi ba zai amsawa mutum da murya babba ba sai kace shi mace ce. Na rasa yaya aka yi ka iya abokantaka da wannan mutumin for all these years. You are nothing like him, kana da sakin fuska shi kuma kullum a tsume yake, kana da son mutane amma shi wulakanta mutane yake yi wanda har matarshi bai bari ba. Kana da son taimako shi kuma idan ya ga mutum na neman taimako baya ko tsayawa zai yi wucewarsa."

Murmusawa kawai Hafiz yayi hankalinshi na kan titi ya
ce,

"First of all, thanks for the compliments. Wasu abubuwan da kika faɗa a kanshi haka ne wasu kuma ba haka bane, yana da wasa da dariya da kuma son mutane wanda ya ga sun dace da shiga circle ɗinshi. Batun taimako kuma sau nawa zan faɗa miki ki daina judging mutum akan laifi ɗaya? Don kawai bai miki taimako sau ɗaya ba a rayuwarki bashi zai sa kice kullum haka yake ko kuma haka yake da kowa ba. I know he is different kuma ba kamar ni yake ba, but that's how he is! And ba zai yiwu a canjashi ya zama yanda ake so ba don bakwa son halayenshi. And idan kika yi haƙuri sai kiga ya sake miki fuska ku zauna ana raha tare."

"Allah ya sauwaƙe. Kuma dama kai kullum cikin karesa kake yi kamar biyanka yake. Ni nafi tausayawa matarshi da Allah ya haɗata da Rock irinsa." Faɗin Juwairiyya tana dunƙule hannunta guri guda don misalta yanda yake.

  Wannan karon dariya Hafiz yayi yana kaɗa kanshi yace,

"Wallahi duk ranar da ya ji kina kiranshi da sunan Rock ɓatawarku zata fi na yanzu."

Itama Juwairiyya dariya tayi a karon farko tana hasashen yanda lukutar fuskar Muhammad zata turnuƙe idan ya ji. Ai kuwa nan take ta ayyana a ranta watarana sai ta faɗa ɗin yaji, domin idan hakan zai ɓata mishi rai ita daɗi zata ji. Tuni ta manta da wani ɓacin rai na tilastata da Hafiz yayi kan zuwa gaisuwan suka cigaba da hiransu gwanin ban sha'awa har suka tsaya a bakin hanya suka sayi fruits suka wuce asibitin FTH (Federal teaching hospital).

Hafiz ne ya musu jagora hannunshi ɗauke da ledan da suka sayi fruits ɗin yayin da ɗayan hannunsa yake riƙe da na Juwairiyya wacce ke fatan Allah yasa an sallami Muhammad ba sai sun haɗu dashi ba. Male ward suka shiga daga nan kuma suka kutsa kai cikin side room B inda suka samu Salima matar Muhammad tana tattare kayansu tana sakawa a wani babban leda, shi kuma mara lafiyan yana kwance akan gado ya kuma ɗaura hannunshi daya a kanshi alamar yana tunani.

  Shigowar Hafiz da Juwairiyya yasa Salima ta dakata daga tattaren kana ta faɗaɗa fara'arta tana musu barka da zuwa.

"Ya jikin naka?" Faɗin Hafiz yana isa bakin gadon ya miƙawa abokin nashi hannu suka yi musabaha bayan ya tashi ya zauna.

"Da sauƙi sun sallamemu, yanzu tafiya gida zamu yi." Muhammad ya bashi amsa yana duban Salima wacce ta tsaya magana da Juwairiyya ta daina aikin da take yi.

"To Allah ya ƙara sauƙi. Kace da mun ƙara minti kaɗan baza mu zo mu sameku ba."

"Kai ma rigima ce tasa ka dawo, ɗazu da safe kafin ka tafi office ka zo mun gaisa. Da mun tafi kam, don wannan mai nawar ta kasa gama kimtsa kayan ne amma da tuni mun isa gida." Yayi maganar da ƙarfi yanda Salima zata ji yana kuma aika mata wani mugun kallo.
Chapter 1 · 0% Book details