← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zaune suke aharabar gidan Abdurrashid suna fira,Dr. Usman yabude baki zeyi magana kenan sukaga megadi yabude gate, wata dankareriyar mota ce tashigo, baki suka saki suna kallonta, jira kawai suke suga wanda ze fito daga cikinta. Dr. Usman yace kai abokina wane attajirin me kudi yau kasamu agidan........😳😳😳😳😳😳 saurin mikewa Dr. Usman yayi ganin wanda yafito daga cikin motar. Bakowa bane se Aliyu Alkali.
Abdurrashid dan mamaki yama kasa mikewa. Karasowa yayi yana fara,a yace sannunku da hutawa Yaya, murmushi yayi yace Aliyu har kadawo? Kai ya sosa yace wlh kuwa,
Yaya dama zuwa nayi nakarbo motata yanzu akamun waya ta iso, tundazu ma natafi su suka batamun lokaci harda ta Khadija na bada order amma wai sunce tata se jibi.
Abdurrashid yace siyomaku kayi? Yadukar da kai yace wlh kuwa, na dade ina tara kudin nan se yau Allah yayi suka hadu shine nasiyo mana mota. Amma gsky tayi kyau sosai Allah yasa rai akayi mawa, Allah ya tsare. Dr. Usman yace gsky Aliyu kashigo gari, wannan mota haka, ai ko acikin Abuja se manyan masu kudi suke hawanta. Allah yasa alheri. Ameen yace yana me tsinewa Dr. Aranshi, wucewa ciki yayi yabarsu anan.

Dr. Usman ya kalli abokinshi yace kagani ko, ina jiya kake fadimun Aliyu yazo maka da maganar beda kudi kamar zeyi maka kuka kadauki dubu 100 kabashi, wlh ko jikina duka kunnuwane bazan yarda da kudinshi dayake samu yatara yasaya masu mota ba. Wannan motar miliyoyi ce fa.
Kumafa idan baka manta ba kwanaki nace maka naganshi yaje bank yayi depositing kudi masu yawa sede shi beganni ba, inazuwa lokacin yatafi accounter yake fadamun yanzu Aliyu yatafi kila kaine ka aikoshi nace masa kila ba, haryake cemun amma kuma a account dinshi yace asaka kudin. Lokacin dana tambayeka ko kai ka aikeshi da kudi kacemun aa.
Harcemaka nayi katuhumeshi kacemun inkyaleshi.
Murmushi yayi yace Nikai na nagama lura da duk irin canjin hali na Aliyu, kawai bana son kudi su hadani da dan uwa na. Amma ba komai akwai Allah.
Dr. Usman yace shikenan Allah yashiryeshi. Kasan saura kwana 5 su Ansar da Umar su dawo ko? Yace haka ne jiya munyi waya da Ansar, Ummanshi ma tace mune zamuje mudauko su. Dr. Usman yace dan Allah ku kyalesu driver yadaukosu.

Dariya Abdurrashid yayi yace kaima kasan Fatima bazata yarda ba. Dr. Yace aishikenan adawo lfy amma ba inda zanje, haka suka ciganba da firansu.

Fatima ta goge hawayen dasuka zubo mata bayan tagama jin bayanin da mijinta yayi mata akan irin canjin daya gani agurin Aliyu. Tace wlh nima nadade ina ganin wasu abubuwa gameda Khadija ita da kawarta Bilkisu.
Kawai de nayi shiru bana son yawan tsegumi ne, akwai wata rana fa nafito nagansu suna binne wani abu agurin lambu, wlh na tsorata sosai gaskiya mukara dagewa da addu,a kamar yanda Umma tace.

Yace bakomai zamu cigaba da addu,a mude murikesu da zuciya daya. Dazu munyi waya da Ansar, murmushi tasaki tace wlh nakosa yadawo, dariya yayi yace nima haka.

Su Iman se shirye shiryen biki sukeyi ita da kawrta Hauwa, ko party kala 4 zasuyi kuma kowanne da ankonshi. Lami tana aiko mata da duk wani magani wanda zesa mallaki Ansar. Farinciki sukeyi burinsu yakusa cika.

Ana gobe su Ansar zasu dawo da dare Abdurrashid yafito yanufi part din Aliyu zasuyi wata magana, dan yakira wayarshi bata shiga. Yazo kwankwasawa kenan yaji su suna wata magana wadda tayi bala,in tada mashi da hankali. Saurin jingina yayi da bango danji yakeyi kamarze fadi.

Aliyu yace wai dama ke kindauka duk ladabin danake ma yaya na gaskiya ne,wlh tunranar dana taso gidammu naga irin son da Abbanmu yake mashi nakejin haushin shi,duk duniya babu wanda na tsana kamrshi.
Dalilin dayasani na karanci computer tun lokacin danaji yace kamfani yakeson yayi aiki idan yayi kudi kuma yagina nashi. Nafison duk inda yashiga nima inshiga, banaso inga yafini ko kadan, amma haryanzu nakasa kamo kafarshi akudi, dalilin dayasa danaji zefitar da makudan kudi yasayi kaya yasa nasace su, atunanina zesamu karayar arziki. Amma kamar kara yawan kudin nayi.

Yanzu abudaya nakeso akwai wani hard disk dake office dinshi duk wani bayanai nashi suna ciki, nasan matukar nasamu wannan disk din yagama yawo. Kinsan kuma gobe.............. kasa tsayawa yayi yaji sauran maganar saboda wani irin jiri dayaji yana dibarshi, dasauri yanufi part dinshi.

Ina godiya metarin yawa gareku masoyana.

Kucigaba da kasancewa dani domin jinyanda zata kasance.😘😘😘😘😘😘

Taku akullum
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹 nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Wannan shafi nakune kawayena Billy maizare, Waleeda, Yusraty, da Kawata mutanen SAMIYYA SAMBISA😊😊😊😊😘😘

75.......80

A falo yakwanta bisa kujera saboda kanshi dayaji yana sara mashi, cikin sauri Fatima tamatso kusa dashi tana tambayarshi abinda kedamunshi. Da kyar yace mikomun ruwa, seda yayi addu,a yatofa sannan yasha, acikin ranshi yarika fadin innalillahi wainna ilaihirraji,un.
A sannu yarika jin nutsuwa tana saukar mashi. Labari yabama Fatima duk irin abinda yaji Aliyu yana fada, kuka tasaka tana fadin wlh Alhaji tsoro nakeji kada suyi maka wani abu. Kamota yayi yana shafa bayanta yace kada kidamu Allah yafisu. Kuma Aliyu be isa yamun wani abuba seda izinin Allah.
Mukullin motarshi yadauko tace inazakaje kuma? Yace office zanje yanzu zandawo kinji, ki kulle gidan idan nadawo zanmaki waya. Kuka tasa mashi wlh ni tsoro nakeji. Murmushi yayi yace dauko hijabinki mutafi.

Fita sukayi suka nufi kamfaninshi, suna zuwa bayan sungaisa da megadi yashiga office dinshi yaciro hard disk sin jikin computer dinshi yafito suka tafi. Fatima ta kalleshi tace kode muwuce gidansu Dr. Kabashi ajiya? Yace kinga yanzu yana office munyi waya dashi daxu yacemun yau sunada wani aiki dazasuyi ma wasu mutane da aka kawo sunyi accident kuma karfe 11 zasu shiga, yanzu kam kinga 10 tayi banason indaga mashi hankali, gobe sena bashi.
Suna zuwa gida yashiga dakinshi yasamu wani guri yaboyeshi, sannan suka kwanta, aranar haka yakwana sam bacci yaki daukarshi. Daga karshe yatashi yadauro alwala yafara nafila.

Yana gama sallar asuba yadauko wayarshi yakira Dr. Usman sede wayarshi akulle, ashe a office ya manta da ita jiya dasuka gama aiki, shiru yayi yadauko Qur,ani yafara karantawa.
Segurin karfe 10 yatashi yayi wanka, Bayan yakarya ne Yakira Abbanshi suka gaisa yake tambayarshi yaune Ansar zedawo ko? Yace e Abba anjima da yamma zamu daukosu. Anan suka cigaba da fira kusan awarau 1 suna waya, asannan ne yaji dadin zuciyarshi.
Auntynshi Asma,u yakira suka gaisa yafada mata Yafara gano irin Abubuwan da Aliyu yake mashi aKamfani, sede sam yakasa fada mata abunda yaji Aliyu yana fada jiya, gani yake kamar zata fadama Abbansu, shikuma bayason abinda zesa Abbansu yasan sunfara samun matsala da kaninshi, anan takara bashi shawara.
Suna gama waya Aliyu yayi sallama zama yayi yace ina kwana yaya, yakalleshi da kyar ya iya amsa nashi, yace Aliyu katashi lfy? Yace lfy lau. Yaya yau bazakaje office Bane? Naga baka shirya ba. Kasan yau shalele zedawo muna shirya mashi abun tarbane. Wani shu,umin murmushi Aliyu yayi wanda shikadai yasan meyake nufi.
Yace gaskiyane yaya, ai Iman ma tana can tun asuba ta tashi tana ta hidimar abinci. Nima ai saboda akwai wani aiki dazanyi a office dana jira muntafi tare. Aa gara kaje ka kulamun da office tunda kai kadai nafi yarda da kai. Shiyasa nake kara jan hankalinka akan jin tsoron Allah. Saurin dago kanshi yayi nan da nan zufa tafara fito mashi. Murmushi Abdurrashid yayi yace nasan kana iya kokarinka Aliyu kuma nasan bazaka taba cuta taba, shiyasa nake alfahari da kai amatsayinka na kanina. Nasan ko na raina zaka iya kulamun da iyalina.
Gabadaya jikin Aliyu yayi sanyi, tashi yayi yace to yaya Allah yatsare sekundawo, har yakai bakin kofa yadawo ya tsaya. Lafiya de Aliyu ko akwai wani abune? Bakomai yaya sekundawo. Aa banyarda ba kode kudi kake bukata? Aa yaya kawai de bakomai tashi yayi yaje daki yadauko mashi dubu 50 yabashi ansa kasaka a aljihunka, karba yayi yana godiya. Wasu irin hawaye ne yaji sun taho mashi, dasauri yafita. Fatima tashigo tace Awannan zamanin masu irin halinka daban suke Alhaji. Allah yabiyaka da mafificin alkhairinsa. Yace Ameen matata. Wayarshi yadauko yakira Dr. Usman amma akashe. Yace dauko wayarki ki kiramun Amina inji lfy dr. Yake kuwa. Bayan sungaisa tabashi ita. Yace Amina lafiyar Dr. Kuwa tunjiya nake kiranshi akashe. Tace wlh jiya a office yamanta wayar jiya, yau kuma tun karfe 9 aka aiko masinjanshi ya fada mashi karfe 10 suna da meeting da baki. Yace shikenan idan yadawo kifada mashi idan nadawo daga dauko su Ansar zanzo ganinshi bayan isha,i akwai maganar dazamuyi. Nan sukayi sallama.

Aliyu yana fita zama yayi cikin mota bason lokacin da kuka yazo mashi ba, kuka kawai yakeyi zuciyarshi tayi mashi baki, jinjina irin abunda suka sa ayima yayanshi da matarshi yakeyi, anya ze iya kashe dan uwanshi jini daya? Wanda yakesonshi kamar dan cikinshi,gabadaya jikinshi yayi sanyi, nan take yafita yakoma gida. Khadija tamike tsaye tana huci bayan tagama jin bayanin Aliyu, tace haba Alhaji kasan kuwa abinda kake fada? Anan takira mamanshi tafada mata abinda ke faruwa. Da kyar auka shawo kanshi ya amince. Baze hana Fafilo aiwatar da abinda yasashi ba.

Karfe 4 suka fito domin tafiya dauko su Ansar, megadi yaje yabude mashi gate, anan yadauko kudi masu yawa yabashi. Godiya yayi mashi suka wuce, ashe tafiyar kenan.😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

CIGABAN LABARI

Kubiyoni a page na gaba domin jin yanda zata kasance.

Ina godiya gareku masoyana,😘😘😘😘😘😘😘.
Urs NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹 nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

80.....85

Haka Ansar yaciga da rayuwa shida Iman cikin kwanciyar hankali, beda abokin shawara se Umar. Idan kuma maganar babbace seya fadama Dr. Usman ko Asma,u, domin Dr. Usman yahanashi fadama Aliyu komai gameda rayuwarshi ko kuma abinda kamfaninshi yake ciki, dan soda yawa Aliyu yana zuwa gurin Ansar ya tambayeshi yanda kamfanin yake ciki, sede kawai Ansar yace masa lafiya lau, duk yanda Aliyu yaso yasamu damar fahimtar wani abu daga kamfanin tagurin Ansar abu ya faskara, sede ta gurin manager, shima kuma tunda dr. Usman yaga abokin Aliyu ne dama kuma shi yakawoshi yahana Ansar sakar mashi komai.
Chapter 9 · 0% Book details