← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 23

Sashe 11

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khadija ce da Iman zaune afalo, Khadija ta kalli Iman tace ya kika baro Bilkisun? Tace lafiya lau tana gaisheki, waini naga kamar bakijin dadi tunda kika shigo naga fuskarki ta canza. Iman tace lafiyata lau kawai se munshiga gari nida Hauwa ne nagaji. Kuma inazuwa gida seda nayi aiki dan bansamuyi da safe ba nafita, duka kayan kitchen dina seda na gogesu na share falo da yana, dan Yaya Ansar jiya yacemun ingoge saman falon yayi kura, hadashi duk ya gajiyar dani wlh.
Khadija tace tunyaushe nake fama dake kibari akawo maki me aiki amma kikace wai bakiso, Iman ta turo baki tace haba momy ni wlh. Banyarda wata mace tashigomun gida ba, amatsayin me aiki, hakanan kawai ta auremun mji.
Dariya khadija tayi tace to sarkin kishi, aisekiyi tazama kina wahala, nikam bazan iya ba sawa zanyi asamomun me aiki. Aike momy dasauki dady tsoho ne mezeyi da aure yanzu. Wlh karya kikeyi mijina ba tsoho bane, dariya Iman tayi tace aishikenan Allah yasa kisamu me hankali. Wai ni Iman lafiya naga har magriba tayi amma Ansar bedawo ba, kuma kince tunsafe suka fita shida Umar.
Waifa momy wajen gari sukaje sunje gano wani fili dayakeso yayi gidan kaji. Hmmmm, kide zauna nan haryanzu kinkasa karbar komai daga gurinsa bare kifara kasuwanci gashi nan shi semena hanyar kudi yakeyi ya kyaleki. Kina ganin yanda nake karbar kudi gurin dadynki ina harkata amma ke kintsaya dadi soyayya ko? Iman tace momy kawai abinda nake jirane, kema kinsan duk yanda nakesonshi nafison kudinshi dashi. Akwai plan din damuke shiryawa nida Hauwa. Dariya tayi tace yauwa kokefa, ai dama nasan barewa bazatayi gudu ba danta yayi rarrafe.

Dr. Usman ne yafito daga dakin da aka kai shatu, yanufi office dinshi, cikin sauri Ansar yabi bayanshi, bayan ya wanke hannunshi yazauna, Ansar kamar zeyi kuka ya kalleshi yace Dady ta mutu ko? Murmushi yayi yace Ansar naga alama bakada dauriya kamar mace, to bata mutu ba, kuma bawani ciwo tajiba kawai yar gurjewa ce tayi dan motar bata mugeta sosai ba, se kuma razanar datayi saboda da alama bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba, hakan yasa tayi doguwar suma.
Amma yanzu anyimata allurai, kuma anyi dressing gurin ciwon, inasha Allahu zuwa gobe ma za,a iya sallamar ta. Ansar yace Alhamdulilah, wlh harnaji dadi. Dr. Yace bara naje gida insa Ummanku ta dafa masu abinci kafin su Umar suzo se yadauko masu tunda ba,a cikin gari suke ba.
Sallamar su Umar ce ta katse masu maganar dasukeyi, bayan sun gaisa ne Umar yace yajikin nata? Dr. Yakalli su Baffa wanda duk hankalinsu atashe yake, seda yakara gaisawa dasu sannan yayi masu bayanin jikinta. Kuma yace zuwa gobe ma zasu iya tafiya. Sosai Baffa yaji dadi yarika yima dr. Godiya, Yace ai mune da godiya, hakuri yakara mabasu. Baffa yace ai bakomai Allah yabata lafiya,
Anan suka wuce dakin da aka kwantar da shatu, anan sukayi masu sallama sukace zasuje su dawo.

Koda Ansar yaje gida be fadama Iman abinda yafaru ba, dan yasan halinta batason yarika kawo mata maganar mace acikin gidanta. Bayan takawo mashi abinci da kyar yaci saboda damuwar datake damunshi, amma dayake Iman irin matan nan ne dabasu cika kula da halin da mijinsu yake cikiba. Haka tazauna. Tayi tamasa surutu. Tashi yayi yashiga wanka, bayan yafito yashirya
Yadauki key din motarshi yafito. Iman tace inazakaje kuma yanzufa karfe 8? Jawota yayi yace yanzu Dadyn Umar yakirani yace inzo akwai maganar dazmuyi, kema kinsan ai banason barinki ke daya ko, idan kuma zakije zomutafi. Dayake yasan bata son zuwa gidan shiyasa yace mata haka dan karta zargi wani abu. Tace a,a dear kawai kaje seka dawo amma ni kwanciya zanyi, nagaji dayawa, shikenan bara na kulleki tawaje idan nadawo basena tadaki ba. Kiss yayi mata a kumatunta yafita.

Urs

NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@(H,O,N,A)

90.....95

Budewar idon Shatu yayi dede da shigowar Ansar, idanuwansu ne suka sarke aguri guda. Wani irin bakon al,amarine yaziyarci zuciyoyinsu, musammama Shatu wadda bata taba cintar kanta cikin irin wannan yanayin ba.

Sudukansu sunkasa dauke idanuwansu daga kallon juna, Inne ce ganin kallon yaki karewa tayi saurin matsowa gurin Shatu tana fadin sannu Shatu kin farka?

Saurin dukar da kanta tayi tana wasa da hannunta, Baffa yace yajikin Shatu, ahankali tace dasauki Baffa, sallama Ansar yayi yashigo hannunshi rike da ledoji da kular abincin da ya karbo gidansu Umar.Bayan sungama gaisawa ya tambayi jikin Shatu, sannan yamika ma Inne ledar, godiya suka mashi. Umar ne yashigo shima hannunshi rike da ledar ruwa, bayan ya ajene yakoma kiran nurse.

Ansar se kallon Shatu yakeyi, ita ko Shatu duk kunya ta kamata saboda babu dankwali akanta gashinta duk ya zuba abayanta, gwanin ban sha,awa.
Murmushi yayi yace sannu Shatu yajikin? Jitayi kamar yafi kowa iya kiran sunanta, ahankali tace dasauki tana me kulle idonta dan kunyar kallon dayake mata takeyi.
Shikuwa duk dadi yakamashi saboda yaga tana jin kunyarshi, yanason mace me kunya, bayan nurse tashigo tacire mata drip din hannunta, tace abata abinci taci idan tagama za,a zo abata magani.

Umar yace ma Inne tarakata bandaki tayi wanka Shatu tayi saurin rufe ido, Umar yayi murmushi yace Ansar mujirasu awaje ko. Ansar yace ma Baffa ga abinci nan kuci, Baffa yayi mashi godiya suka fita.

Aliyu ne zaune a office din manager Ansar, wai kai haryanzu baka samomin wannan files din dana ce maka ka dubomun ba? Wlh ina ganin fa files din nan basa cikin office din Ansar, saboda babu neman dabanyi masu ba amma babusu. Mtssss tsaki Aliyu yaja,yace wlh hada wani hard disk nake nema wanda yaya yaboye duk wani sirrin kada rorinshi aciki amma banganshi ba. Kuma ina tsoron in tambayi Ansar yafara zargin wani abu,

Ko kuma yafada ma wannan Dr. Usman din,manager yace wlh wannan dr, din duk yabi yatsare komai yanda kasan shine me kamfanin, shima fa yakamata kadauki mataki akanshi.

Banaso wani abu yakara faruwa akan wani nakusa damu, mutane zasu fara zargin wani abu, ka kyaleshi idan yasan wata ai besan wata ba. Lokaci kawai nake jira dagshi har Ansar din megaba daya zanmasu.

Shiyasa nake sonka Oga harka da kai akwai karuwa, amma naji yan kamfaninka suna korafin ba,a basu albashinsu akan kari. E ai nacema accounter yayi kokari yabiyasu yau harda na wancan watan, nasan idan maganar taje gurin Abba ze batamun rai, kuma ze iya sawa amashi binciken kamfanin. Shiyasa narage dibar kudin kamfanin inaso sudan taru.

Bayan tafito daga wanka Inne tabude ledar da Ansar yabata tamiko mata wata doguwar riga me hade da dankwali, amsa tayi takoma ciki tasaka sannan tafito, rigar tayi mata kyau sosai sekace balarabiya, Inne da Baffa ma sunyaba da rigar. Mati yayi murmushi yace lallai Shatu jiki yayi sauki, Baffa yace seyanzu naji hankalina ya kwanta wlh. Allah de yakara tsaremu.

Abinci Inne tazuba mata domin su sunci nasu, bayan tagama cine, Inne ta gyara gurin, Baffa yaleka yakirawo su Ansar, koda suka shigo Shatu tana ramakon sallolin dabatayi ba. Kallon bayanta kawai Ansar yakeyi domin yakosa tagama ya kalli fuskarta yaga yanda rigar tayi mata.
Umar yakira. Nurse tashigo da magunguna, seda tagama sallar sannan nurse din tamatso domin bata magani. Wayrshi Ansar yafiddo yarika yima shatu vedio ganin yanda take karbar magani cike da shagwaba, murmushi kawai yakeyi yana kallonta tacikin wayarshi.

Umar yamatso zeyi nashi magana, mamaki ne yakamashi ganin abinda yakeyi, murmushi kawai yayi ya kyaleshi, da kyar tagama shan maganin, Inne da Baffa se lallashinta sukeyi ita kuma tana ta zuba masu shagwaba. Yana gamawa yayi saving awani guri sannan yasama folder din pass word.

Baffa yace Ansar yakamata kutafi gida kuma kuhuta haka nan dare yayi ko? Umar yace to Baffa muje innuna maku dakin dakin dazaku kwanta. Se Inne da Shatu su kwana anan ko, fita sukayi, Inne kuma tashige bandaki ganin Ansar befita ba, tasan akwai dalili.

Tana shiga ya matso kusa da gadon Shatu ita kuma tana wasa da yatsunta, murmushi yayi yace meyasa bakison magani? Shiru tayi batace komai ba. Allura ma za,a maki gobe kishirya, dasauri tazaro ido tana kallonshi, shagwabe fuska tayi kamar zatayi kuka tace nide wlh banison allura, dariya yakama yimata ganin yanda take magana cikin shagwaba, wani irin farin ciki yakeji kamar kada yatafi yabarta haka yakeji. Cikin sanyin murya yace Shatuuuu seda tsigar jikinta ta tashi jinyanda yakira sunanta.
Ido tadago tana kallonshi tana murmushi yace tafiya zanyi, gashi kuma gobe za,a sallameki kuma banason intafi inbarki. Yanda yayi maganar kamar wani yaro, itama jitayi kamar kada yatafi, tunda take arayuwarta bata taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayin ba dan tana magana da namiji. Shiru sukayi suna kallon junansu.
Shigowar Umar ne ya katse masu kallon dasukeyi, Murmushi yayi yace idan kagama kallon TV, semutafi ko? Shafa kanshi yayi yace wlh Umar kai dan iska ne, komawa yayi yaduka dede kunnen ta yace ki kwanta kiyi bacci kinji Shatu, saurin rufe ido tayi tana murmushi. Tana jinsu har suka fita sannan ta bude idonta tana dariya kasa kasa. Har mota su Baffa suka rakasu suna masu godiya. Baffa yashigo ganin shatu tana murmushi yakalli Inne yace waini wannan murmushin na menene Shatu? Inne tace nima haka nafito naganta, kila duk na Ansar ne, saurin juyawa tayi ta kwanta.

Tafiya sukeyi Ansar se murmushi yakeyi shi kadai yana kallon vedion dayayi ma Shatu. Umar yace wai ni nakasa gane wannan yanayin da abokina yake ciki ba. Duka Ansar ya kaimashi yace kaifa dan sa ido ne ko. Umar yayi dariya yace naga alama dazu ka dakeni munkade ta 2 yanzu kuma kila ta 3 kakeson mukade. Dariya suka sa dukansu.
Aranar haka Ansar da Shatu suka kwana cike da tunanin junansu, daya kulle ido ita yake gani. Gudun kada Iman tafarka yasa yatashi yanufi dakinshi haka yayi ta kallon shatu yana jin dadi, ganin bazeyi bacci ba yatashi yayo alwala yafara nafila.

Washe gari tunda asuba Shatu tayi wanka tamayar da rigar da Ansar yakawo mata, sannan tayi sallah.
Chapter 11 · 0% Book details