Sashe 16
Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon barrister yayi yace bakada hurumin dazaka ce Ansar shine yakashe Aliyu, ko wace irin sheda kuwa gareka, Aliyu da nane, haka kuma Ansar jikana ne, saboda haka babu wanda zangoyama baya, amma inaso ka adana kalamanka aje kotu, saboda alkali ne kadai yakeda ikon yanke hukunci, kasan ance shari,a sabanin hankali, kar kamanta fannina ne.
Ajiyar zuciya barrister yayi yana goge zufar data fito mashi, ayi hakuri Abba shine abinda yafada. Abba yace Dr za,a iya tafiya da gawar domin a suturta ta? Dr. Usman wanda idonshi yayi ja, saboda bacin rai, yace E Abba, anan aka bama D,P,O duk kanin takardun awon da akayi, sannan aka bada gawar Aliyu.
H. Farida se kuka takeyi tana fadin wlh yanda aka kashemun da dole ne shima a kashe shi, Lami ce tayi ta lallashinta haka suka nufi gida da gawar, cikin lokaci kankani aka shiryashi aka nufi gidanshi na gaskiya dashi, mata se kuka sukeyi, idan kaga khadija kamar zatayi hauka.
Tunda safe Shatu takejin faduwar gaba, saboda mummunan mafarkin datayi da Ansar, hakan yasa rana tana fara dagawa tace na su Baffa zata tafi. Baffa yace shatu bazaki bari kici abincin rana ba? Tace ai Ansar yace intaho dawuri. Inne tace malam kabarta ta tafi ai yayi ma da har yabarta ta kwana. Baffa yace toshikenan, dogara sandarshi yayi yaleka yasamu yaro yace yakira mashi me mashin.
Bayan me mashin yaxo ne Shatu tafito domin yakaita bakin titi tasamu mota, kamar zatayi kuka tayima su Baffa sallama ta tafi. Suna zuwa ya ajeta yakoma, mota tagani tasa hannu ta tsaidata, tasayawa tayi tanajiran Shatu ta tsallako dayake adayan barin take, cikin sauri Shatu tanufi titi domin tsallakawa. Muryar mutanen motar taji suna cemata ta tsaya ga mota nan, amma ina hankalinta yatafi wajen zuwa yashiga mota. Karar burki naji, ashe wata mota ce ta taho bata ga Shatu ba seda tazo gab da ita sannan tayi kokarin taka burki. Amma ina seda ta bugeta, nan take shatu tafadi agurin asume.
Mutanen waccan motar suka fito suka nufi gurinta, dasauri wani matashi yafito daga cikin motar data buge Shatu, hakuri yafara bama masu motar, yace subar mashi ita yakaita asibiti, daukarta yayi yasata amota, mutanan sukayi mashi Allah ya kyauta, shi kuma yanufi cikin gari da ita domin yakaita asibiti.
Bayan sundawo daga kai Aliyu makabarta suka dan zauna karbar gaisuwa, daganan kuma suka tashi suka nufi police station gurin Ansar, amota ne Dr. Usman yace wlh da ace bada hannuna nayi awon tomb print na Ansar ba, bazan taba yarda cewa hoton hannunshi ne ajiki ba.
Abban safana yagoge kwallar data fito mashi yace, Allah nagode maka, nikuma irin tawa kaddarar kenan, kallan Dr, yayi yace amma inaso inji daukar da barrister yace yayi lokacin da Ansar yashake Aliyu.
Nasan dole muji abinda yahadasu har Ansar ya iya shake shi. Ahaka suka isa office din D,P,O. Bayan sungama gaisawa Abba yace inaso dan Allah ayi gaggawar shigar da kara kotu, kasan mutanenka basuda tausayi idan suka kama me laifi, gara amikashi kotu dan asamu damar yin bincike sosai. D,P,O yace bakomai Allah yakaimu.
Gurin Ansar suka nufa, azaune suka iskeshi yahada kai da kafafunshi. Ansar, yaji Abban safana yana kiranshi, saurin dago kai yayi, wani kuka ne yaxo mashi, matsowa yayi yafada jikinshi yacigaba da kuka uana fadin wlh Abba banine na kashe shi ba, nasan de na shakeshi lokacin danaji yana waya da abokinshi barrister yana fada mashi shine yasa aka kashe su Abba da Umma, amma wlh bankasheshi da wuka ba. Nan take Umar yaciro takarda da biro yafara daukar bayanin da ansar yakeyi.
Abban safana yace ya isa haka dena kuka Ansar, babu wanda ze yanke maka hukunci harse an tabbatar da gasky, inaso kafadamana duk abinda yafaru dakaje gidan Aliyu.
Anan Ansar yafadamasu duk yanda akayi, har kiran da Iman tace Aliyu yana yi mashi, yace kuma sanda megadi yafito dani wlh be mutu ba Abba. Umar yace Ansar dakaje gida baka sake komawa gurinshi ba? Kai ya girgiza yace ni baccima na kwanta tunda nagama sallar. Kuka yacigaba dayi yana fadin shikenan Umar nima kasheni za,ayi.
Kowa agurin seda yazubar mashi da kwalla, umar yace Ansar nizan tsaya maka,inaso kowace irin tambaya barrister zeyi maka kada ka canza daga abinda kafada daga farko, domin yawan canza magana yanasa adauki mutum makaryaci.
Dr. Usman yace kada kadamu idan de akan gaskiyar ka kake babu abinda ze faru da kai, kadage da addu,a muma zamu cigaba da Fadama Allah komai zeyi dede.
Ansar yakalli Umar yace Shatu tadawo kuwa? Dan tundazu nakejin jikina yana bani kamar tana cikin matsala, dan Allah kaje gidansu kadauko mun ita bana so ta taho amotar haya. Tausayinshi ne yakama su, yana cikin matsala amma hankalinshi yana gurin Shatu. Umar yace babu damuwa yanzu zanje indaukota. Hakuri sukayi tabashi sannan sukace Umar yaje yasiyo mashi abinci, bayan yaci dakyar ma ya iyaci sannan suka taci, kowa yana cike da damuwa.
H. Farida tace Khadija kince akwai barrister abokin Aliyu ko? Tace E, anjima zezo domin yafadamun gobe za,a fara shiga kotu, farida tace yauwa gara yazo dan wlh bazan yafe kisan da akayi ma Aliyu ba, senaga ankashe Ansar sannan hankalina ze kwanta. Halima tace haba momy agidan mutuwa fa muke. Farida tace dalla can rufemun baki, wlh da ba idona biyu na haifeki ba cewa zanyi masanye akamun, dannaga bakiyo hali naba, kina mace keyakamata ace kinyo halina, amma sede Aliyu ne yayi kuma gashinan ankashemun shi. Dukar da kanta kasa tayi kwalla tana fito mata a ido, tadade tanajin haushin irin wannan hali na momynsu.
Suna zuwa asibiti aka karbeta aka mufi emergency da ita. Waya yaciro yakira Ummanshi yafada mata abinda yafaru, yafada mata asibitin dasuke. Zama yayi agurin kwalla nata fita daga idonshi, tsoronshi daya kada yakashe diyar mutane, gashi bema son daga inda take ba, har jakarta yaduba koze samu wayarta amma babu, domin Shatu agida tabar wayarta saboda garinsu babu ntwk.
Saurin tashi yayi ganin Ummanshi da yayanshi sunnufo gurinshi, suna zuwa yafada jikin Ummanshi yakara sa kuka yana fadin shikenan Umma nakasheta, kamashi tayi suka zauna tace waya ce maka ta mutu? Yace Umma tundazu fa babu wanda yafito, tace to kayi hakuri insha Allahu babu abinda ze faru da ita. Yayanshi yace. Haba autan Umma meyasa kacika saurin. Kuka, kayi shiru kaji Nabeel.
Wani Dr, ne yafito yana kokarin cire safar hannunshi, yanufi office dinshi, dasauri. Suka bishi, bayan yawanke hannunshi ne yazauna sannan yace Hajiya alhamdulillahi mun samu damar tsaida cikin dayayi kokarin zubewa, kuma jikinta dasauki bawani matsala tasamu ba, kawai gurjewa ce tayi, se kuma razanar datayi. Amma insha Allah kowane lokaci zata iya farkawa, sede duk da haka za,a bata bed rest na kwana 3 kafin asallameta. Sede akula da ita sosai, domin cikin dake jikinta. Godiya sukayi mashi sannan yarubuta masu magungunan daza,a siyo mata, tare da bill din kudin dazasu biya, dakin da aka kaita suka wuce, umma tace ma Nabeel,yatafi gida yayi wanka tabar me aiki tana abinci idan tagama sekataho dashi. Kai kuma Fareed jeka biya kudin kasiyo magungunan.
Barrister saddik ne zaune afalon khadija, farida tace barrister inafatan kagama hada duk wata shedar dazaka gabatar akotu? Murmushi yayi yace Momy kada kidamu wannan shari,ar me saukice, danni bantaba yin shari,a mesaukin taba, saboda komai afili yake domin ina me tabbatar maki shari,ar nan bazata wuce kwana 2 ba za,a yanke hukunci. Godiya suka yi mashi sannan yatafi.
Seda Shatu tashare awa 3 sannan ta farfado, sede haryanzu bata gama dawowa hayyacinta ba, hakan yasa Umma tace Fareed yakira mata Dr. Yana zuwa yaga halin da take yayi saurin yimata allura, nan take takara komawa bacci. Yace kada kudamu zata warware insha Allah. Nabeel ne yashigo dauke da kular abinci, yace Umma har yanzu bata tashi ba? Tace ta farka amma yanzu aka kara yimata allura, buza abinci tayi tace taho kaci abinci nasan babu abinda kaci. Yace Umma kibari tafarka sannan, amsar abincin Fareed yayi yajawoshi suka zauna yafara bashi abaki, da kyar yarika amsar abincin, Umma se dariya take masu.
Dr. Usman ne da Umar damatarshi da Asma,u da Jimmala duk sun sha kuka, suna zaune afalo, Dr, yace Umar inafatan kasamu hujjar dazaka tsaya da ita gobe akotu? Kasan semunyi da gaske saboda sunfimu kwararan hujjoji, namu gaba daya abaki suke, su kuma nasu azahiri suke. Umar yagoge hawayen dasuka zubo mashi yace wlh Abba ni kaina tsoron shiga kotu nakeyi gobe, saboda bawata hujja me karfi gareniba, naso ace anbar shiga kotun dawuri kila damunsamu hujja, amma gobe zan roka adaga mana shari,ar. Tausayin Ansar nakeji, Dr. Yace haba Umar amatsayinka na lawyer be kamata kayi saurin karaya dawuri haka ba, insha Allahu zamu sami hujja me karfi. Amma ya akayi dakaje dauko Shatu baku dawo tare ba? Umar ya girgiza kai yana kuka yace , ina zuwa bayan mungaisa da baffa tunkafin inmashi maganar Shatu yace mun ai dazunnan ita yasa me mashin yakaita bakin titi ta tafi gida, dan tace Ansar yace tadawo da wuri.
Ganin Baffa besan abinda yafaru ba, yasa nace mashi nima zuwa nayi induba jikinshi, anan nayi mashi sallama nataho, koda naje gurin Ansar nafada mashi danaje nasameta kwance bata da lafiya, se nace ma Baffa. Ansar yace abarta zuwa kwana 2 idan tasamu sauki za,a zo adauketa. Danaga hankalinshi yakwanta sena taho.
Innalillahi wa inna ilaihirraji,un shine abinda kowa nafalon yake fada, Jimmala kuwa kuka tasaka. Dr. Usman yace to Allah gamu gareka, me kuma yafaru da Shatu?
Urs
NABILA, RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)
125.....130
Babbar kotu dake garin Abuja cike take da mutane, domin kowa so yake yaji yanda shari,ar zata kasance. Zaune suke acikin kotun kowa da abunda yake fada, shiru ne yabiyo baya lokacin da alkali yashigo cikin kotu. Bayan yazauna akashigo da Ansar wanda yaci duka fuskarshi duk ta kumbura, yan uwanshi gaba daya seda su kayimashi kuka,Umar kasa kallon Ansar yayi saboda idanuwanshi cike suke da kwllah.