← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 23

Sashe 10

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shatu ce tare da kawarta Jimmala zata rakata rafi dibar ruwa. Jimmala tace waini shatu meyasa baki son kula lado, kinfasan irin son da yake maki, duk rugar nan kowa yasan yana sonki amma kinki bashi dama.
Wlh kinji dadinki shatu mutane da yawa suna sonki amma bansan meyasa baki kula suba, kuma nide nasan bakida wani saurayi bare kice shine dalilin rashin bama lado fuska. Kina gani duk kawayenmu sunyi aure sunbarmu har kannammu sun fara tsayawa da samari amma munkasa fidda miji. Koni dakikaga ina kula babawo bawani sonshi nakeyi ba, amma banason ace banida saurayin dayake zuwa gurina fira ne.

Shatu tayi murmushi tace jimmala kema de kinsan arayuwata babu abinda na tsana kamar kazanta, shikuma Lado mugun kazamine, gashi rago aradu dummun son dayakemun bazan iya auranshi ba.
Kuma ni bazan iya auren wanda zuciyana bata so, nafison nasamu wanda nake so sosai sannan in aure shi, nasan komunyi aure zamu kula da junanmu, kuma Jimmala ai so shine aure.
Ina baki shawara kada son aure yasaki kifitar da Babawo amatsayin wanda zaki aura, bayan kuma nasan bason shi kike ba, kuma ai Baffanki baya maki fada akan aure ko? Kuma nima Baffana yace baze aura mun wanda bana so na, harse ranar dana amsa da bakina inason wani sannan ze aura munshi.

Jimmala tace toshikenan Shatu tunda kema byanzu zakiyi aure ba nima bazan kara daga hankalina saboda aure ba. Haka suka isa bakin rafi ta debo ruwan suka wuce gida.
Jimmala tace danayi wanka anjima zanzo kirakani tallar nono, Shatu tace tosekinzo, tashige gida itama ta wuce. Tana shiga taga Baffanta yadawo yakawo yan shila, tace sannu Baffa, yace yuwa shatu harkin dawo, tace e. Inne tace yauwa shatu dauki yan shilan nan ki gyarasu kidora kafin rana tayi ko, tace to Inne. Sallama sukaji anayi daga waje, Baffa ya amsa yafita. Abokinshi yagani Garbati, bayan sungaisa suka zauna bisa dakali. Garbati yace Malam Buba kaganni da safe ko? Yace wlh kuwa, waini kuwa Shatu bata fada maka Lado dan wjena yana sonta ba,jiya yasameni wai inzo innemasa auren shatu agurinka, kuma gashi de tagama karatun ta nasan kuma babu wani mezuwa gurinta.

Malam Buba yayi murmushi yace shikenan Garbati zan tambayeta idan hartana sonshi ai babu damuwa kaga semu kara dankwan zumunci ko. Amma idan har bata sonshi to gsky sede yayi hkr, dannayi alkawarin bazan taba bama shatu wanda bata so ba. Garbati yace toshikenan nagode nizan koma, sallama yayi mashi yatafi.

Shiru shatu tayi bayan tagama jin abinda Baffanta yace. Inne tace kiyi magana mana Shatu ana tambayarki. Nide gaskiya bana sonshi Baffa, shatu tafada tana turo baki. Murmushi yayi yace shikenan kwantar da hankalinki tunda baki sonshi, dama nafada mashi inde kikace baki sonshi sede yayi hakuri. Allah yakawo maki mafi alkahairi, tashi tayi tafita tana murmushi.

Iman ce zaune adaki ita da kawarta Hauwa, Iman tace wlh kawata ina cikin matsala, Hauwa tace ke kuwa wace irin matsala ce haka take damunki kina zaune gidan mijinki ke kadai, yana matukar sonki yana baki kome kike bukata, sannan kuma gaki ga iyayenki. Koni danake shirin auren me mata bana cew ina cikin matsala, seke Iman? Bazaki gane bane, matsalata bazan iya fadama kowa ba dan nasan duk wanda nafada mawa baze bani goyon bayan abinda nakeso ba. Shiyasa nakiraki nace kizo.
To inajinki Iman. Cikine dani Hauwa kuma inatsoron. In haihu da wuri Yaya yafara neman karo aure. Ciki Iman? Lallai dole kice kina cikin matsala, kamar ke kina wayayya acikin garin Abuja kuma kinada miji me kudi harki bari ciki yashiga jikinki, haba Iman karki bani kunya mana, nisam wlh na manta, naso tunkafin aurenku narakaki ansa maki robar hana daukar ciki.
Amma aure ko shekara beyiba afara maganar ciki, kema kinyi ganganci, yanzu zaki shiga sahun manyan mata, gsky dole innemo babbar kawa abikina, haba Iman kin manta irin casun damukace zamuyi abikina, harfa kara,i kikace zakiyi tunda bakiyi abikinki ba.

Keda kanki kikacemun momynki bata son yawan haihuwa shiyasa tunda tayi daya tadena, saboda bata son ta tsufa dawuri, yanzu duk wanda ya kalleta bazece ita ta haifeki ba, kuma kowane irin taro zata iya cin gayunta taje babu wani goyo dazatayi.
Iman kamar ztayi kuk tace toni yazanyi, kullum se momy ta tambayeni haryanzu banda ciki, sudukansu suna matukar son insamu ciki. Aiko dakinfara laulayi Ansar yadena cin abincinki, sede yaje yaci nawaje, daga can kuma yasamu wata. Karyane wlh Ansar nawane ni kadai, babu macen data isa tarabeshi. Idan ko hakane dole kizubar da cikin jikinki tunkafin kowa yasan dashi.

Iman tace wlh idan su momy sukaji zasu batamun rai, kuma kinga idan har nayi bari dole aje asibiti nasan kuma Dr. Ze fada masu maganin zubar da ciki nasha.
Karki damu idan wannan ne, ranar dazaki sha maganin kizo gidammu daga can muwuce asibiti ayi maki wankin mahaifa idan kika huta asamaki wannan robar hana daukar ciki ki koma gida. Kinga babu wanda yasani. Shikenan kisamo maganin gobe se inshigo naji Yaya Ansar yace gobe wani guri zasuje shida Umar kinga ba,a gida ze wuni ba semuje kawai. Wani irin shu,umin murmushi Hauwa tayi najin dadi tace sekinzo.

Sallam Jimmala tayi agidan su Shatu, bayan sun gaisa da Inne Shatu tafito tace dama kenake jira tundazu, Inne muntafi, Inne tace kuyi sauri kada yamma tayi maku kunji, suka ce to inne, suka fita suna fira.

Tafe suke amota Ansar ne,yake tukin sundawo daga wajen gari shida Umar, wani fili da Ansar yasiya domin yin gidan kaji shine sukaje gani. Ansar ya kalli. Umar yace abokina yakamata kaima fa ka kyalesu Dady hakanan katafi gidanka. Ko sokakeyi seka tsufa sannan kayi aure? Murmushi Umar yayi yace ammade kaima kasan haryanzu bansami wadda nakeso ba ko,kaima shigar sauri kamun tunda de kasan na girmeka. Amma karigani aure. Ansar yayi dariya yace Ada ba, amma yanzu kam ni magidanci ne nan da dan lokaci kadan zan zama Baba. Duka Umar yakai mashi, saurin gocewa Ansar yayi yana dariya.
Dede lokacin su Shatu zasu tsallaka titi kenan, cikin sauri Jimmala tayi baya, tana kiran Shatu ganin mota tayo kanta. Umar yace Ansar gabanka...... dasauri yadauka kan motar ma duk dahaka seda ya kafe Shatu, da kyar yasamu motar ta tsaya, fitowa sukayi suka nufi Shatu wadda take kwance asume, Jimmala se kuka takeyi. Suna zuwa Ansar yadauketa yasata amota, Umar yakarbi Nonon Jimmala yasashi bayan boot itama tashiga tana ta kuka suka nufi cikin gari domin su kaita asibiti.

Urs. 😘😘😘😘💋💋💋💋💋💋💋
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

85.....90

Suna zuwa kai tsaye asibitin su Umar suka nufa. Kaitsaye aka ansheta aka nufi emergency da ita suka fara bata temakon gaggawa.
Umar yakira. Dadynshi ya fada mashi, yana zuwa ya shiga cikin dakin. Ansar se kuka yakeyi dama shi abin kuka baya mashi kadan, Jimmala ma se kuka takeyi, ha Shatu kwance, kuma gashi bata sayar da nononta ba, babban abinda yafi daga mata hankali magriba tafarayi, tunanin halin da Baffan Shatu da Inne zasu shiga kawai takeyi.

Umar ne yace kiyi shiru kinga ba mutuwa tayi ba, addu,a zaki rika yimata zata tashi kinji, Jimmala tace wlh tsoro nakeyi kada ta mutu, Baffanta dama bayason tana zuwa saboda nice ma yake barinta tana rakoni, gashi nan tsautsayi yafada akanta, ni dama nice aka kade. Yanzu suna can hankalinsi nasan yatashi.
Umar yace kidena fadar haka babu wanda yake tsallake kaddararsa, ina zuwa. Gurin Ansar yanufa, murmushi yayi ganin yanda yake kuka kamar mace. Haba Maza kayi shiru mana ai seka sa kawarta tayi tunanin mutuwa tayi ko? Ansar yace Umar idan ta mutu fa? Insha Allahu ma bazata mutu ba. Bara naje nakaita gida domin inyi masu bayani kada suji shiru hankalinsu yatashi. Shikenan kuyi sauri, idan kunfita kayi sadaka da nonon su sekabata kudin, Umar yace to.

Suna fita yadauko nonon yabama wasu mutane sannan suka tafi, kudi yadauko har 2000 yabata, Jimmala tace ai wannan kudin sunyi yawa, Umar yace bakomai kirike sauran.
Bayan su Iman da Hauwa sunje asibiti akayima cikin yazube akayi mata wankin ciki. Anan ta huta sannan suka wuce bangaren yan family planing, ana aka sama roba(inplanon), suka wuce gida.

Baffane yaketa zarya acikin gida ganin har ankusa magriba amma su Shatu basu dawo ba. Inne tace dan Allah malam kasamu guri kazauna,in sha Allah ma zasu dawo. Baffa yace bazan iya zama ba, tunda Shatu take bata taba kai kamar yanzu bata dawo gida ba, kuma jikina yana bani wani abu yasamu Shatuna. Bara naje nayi sallah idan nadawo basu dawo ba se inbi hanya.

Haka jimmala tayita mashi kwatancen gidan harsuka iso.
Baffane tsaye akofar gidanshi yana jiran mahaifin Jimmala yazo sutafi, dan yaje gida ya kai sako.
Ganin mota tana nufoshi yasa ya maida hankalinshi ga kallonta, bayan sun tsaya Jimmala da Umar suka fito,ai da sauri Baffa yataho ganin Jimmala ita kadai, dede lokacin mahaifin Jimmala shima yakaraso, malam Mati.

Baffa ya kalli Jimmala datake ta kuka cikin tashin hankali yace Jimmala Shatu ta tamutu ko? Aini dama nasani, tundazu jikina yake bani wani abu yasamu Shatu ta, oh, Allah sarki Shatu, kuka ne yaci karfinsa, Umar ne da Mati suka matso kusa dashi,Umar yace Baffa bata mutu ba, tsautsayi ne yafaru tana asibiti jikinta ma dasauki.
Baffa yakara sa kuka yace shikenan, shiyasa dama na hana Shatu zuwa bakin titi amma tace tanason zuwa gashinan yanzu abunda yafaru da ita. Mati yace kayi hakuri Buba muje muga halin data ke ciki, yaro yanzu yajikin Shatun? Umar yace dasauki tana asibiti dama munzo ne mufada maku dan kada kuji shiru, inyaso semutafi tare kuga jikin nata, Baffa yasauke ajiyar zuciya. Yace to bari infadama mahaifiyarta semu tafi tare.
Mati yace Jimmala ke kitafi gida seki fadama Innarki zamuje cikin birni idan da hali zamu dawo kila kuma se gobe, Juyawa tayi tafara tafiya,Umar yabi bayanta da kallo, can yace Jimmala,babu sallama, juyowa tayi tasa hannunta tarufe fuskarta tana murmushi tace Allah ya kiyaye hanya, saurin juyawa tayi ta tafi. Murmushi yayi dan ta burgeshi yanda yaga tana jin kunyarshi. Haka Baffa da Inne suka fito Inne se kuka takeyi, Baffa ne ya kulle gidan suka shiga mota suka tafi.
Chapter 10 · 0% Book details