← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 23

Sashe 12

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansar yana fitowa daga masallaci yakoma yayi wanka yacema. Iman anyi mashi waya ankai daya daga cikin ma aikatanshi asibiti yayi hadari zeje yaduboshi daga can kuma ze wuce office suna da meeting karfe 8. Iman tace to ka aiko driver ya ansar maka abinci ko
Aa kibarshi kidafa dede naki zansha coffee kawai, shikenan seka dawo.

Yana shiga cikin asibitin yahadu dasu Baffa suna fitowa daga masallaci bayan sungaisa ya tmabayi jikin shatu, sukace da sauki. Wucewa sukayi dakin shatu, Ansar yagaida Inne, itama ta gaishe dasu Baffa suka tambayi jikin Shatu. Harkasa Shatu ta duka tagaishe dasu Baffa, cike da fara,a suka amsa suna mata yajiki. Juyowa tayi tagaishe da Ansar murmushi yayi ya ansa yana tambayarta jiki, cike da kunya ta amsa.

Baffa da su Inne suka fito suka dawo falon kusa da dakin suka zauna. Matsowa Ansar yayi yazauna bisa gadon yana kallon Shatu, munyi waya da likita yace senan da sati guda za,a sallameki, ido ta waro tana kallonshi, nide gskya nagaji dan zama ana. Kingaji da ganina zakice, girgiza kai tayi. Emana gashi kinason tafiya kibarni, ko ina kike Shatu sena biki sede ki koreni. Murmushi tayi tace bama zan koreka ba. Amma idan mazo samarinki bazasu mun duka ba ko? Aradu banda saurayi kuma ka tambayi Jimmala kaji.

Wani sanyi yaji daya gane bata kula samari, shide kome Shatu zatayi yana burgeshi, harbeson yadena kallonta. Wayarshi yadauko yana daukarta hoto, Shatu tace. Yaya menene wannan? Kinaso kiga komenene? E to matso kigani vedion dayayi mata jiya ya kunna mata, kallon kanta takeyi se dariya take tace La yaushe kasakani aciki? Kullum ma idan nazo gurinki zanrika sakaki ciki saboda idan bama tare se inrika kallonki.

Yanzu kona koma rugarmu zaka rika kallona? Emana, baki ta turo tace shikenan kai zaka rika ganina ni kuma..... kema kina son ganina ne? Rufe fuskarta tayi tana murmushi. Kinga da garinku. Akwai irin wannan dakema nabaki semurika magana kullum. Amma idan kika koma zankawo maki wani abu da,ake daukar mutane shima zaki rika kallona.( Camera).

Haka sukayi tafira dayake Shatu akwai saurin sabo dan danan suka saba da Ansar,gurin karfe 7 Umar. Yashigo kawo masu abinci tunda yaga su Baffa afalo yasan Ansar yana ciki, bayan sungama gaisawa yashiga ciki.

Dariya Umar yayi, yace wlh harzan kiraka ince zanbiyo mutaho tare natuna da mutunniyar kawai nataho.
Ashe kai kana nan kana kallon tv, kamanta jinya nakeyi dole kaganni anan. Cike da kunya shatu ta gaishe shi, lfy lau Shatun Ansar yajiki? Fuskarta tarufe, Ansar yace Kai amma dole inbaka kyauta sunan nan yayi dadyi. Nifa bahaka ake cemun ba, tafada kamar zatayi kuka, to ya ake fada maki? SHATU DIYAR MAHARBI fa ake cemun, cike da shagwaba. Umar yace Baffa maharbi ne? Kai ta daga mashi tana murmushi. Hmmmm ai naga alama ke yar gata ce agurin Baffa.

Bara inkira dady yazo yabaku sallama naga kin warke, dasauri Ansar yarikeshi yana fadin wlh kai dan bukulu ne, ta ina tawarke yarinya ta kwana batayi bacci ba. Dariya Umar yayi. Yace kun kwana bakuyi bacci ba de, kawai tun asuba kazo ka kori yan tsofaffi katsare yarinya kana mata surutu, to wlh se an sallameta Jimmala tana can tanajiran in maida mata kawarta.

Dariya Ansar yasa yace zama kayi bayani. Ashede bani kadai da kado ta biyu ba, kila wani ma ta daya yasamu. Fita sukayi su Baffa suka shigo domin karyawa, gidan su Umar suka wuce dansu ci abinci. Ansar naga alama kana tsoron kishin Iman, kuma gashi naga alamar kafada tarkon soyayya, murmushi kawai Ansar yayi bece masa komai ba.

Karfe 10 suka fito domin an sallamesu, Su Baffa se godiya sukema Dr. Usman shima godiya yayi masu kuma yakara basu hakuri.
Motar Ansar da umar suka shiga dan daya tamasu kadan, Shatu ce zaune agaban motar Ansar haka suka tafi suduka basajin dadin rabuwar dazasuyi.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

95.....100

Suna isa rugar su Shatu akofar gidan suka iske Jimmala tayi tagumi. Ai tana ganin motoci dasauri ta mike tanufi gurinsu.
Suna fitowa Suka rungume juna ita da Shatu, kowa se murnar ganin dan uwanshi yakeyi. Baffa yabude yagidan yace ma su Ansar su shigo, yace to Baffa muna zuwa, sallama sukayi da Mati yawuce gidanshi suna tayi mashi godiya.

Umar kuwa yana can gurin kallon Jimmala, shide tun ranar daya ganta yaji ta kwanta mashi, dan itama Jimmala akwai kyau, kuma tanada tsafta, duk da batayi boko ba amma tanada ilimin addini dede gwargwado.

Ansar yace kisaketa kada ki kadamun ita kinsan fa bata ida warkewa ba. Cike da kunya Shatu tasaki Jimmala tana murmushi, Jimmala ce ta juyo tagaishe su.
Umar yace ai naga alama kinga kawarki harkin manta dani, murmushi tayi tace aradu bahaka bane, tunjiya nake cikin damuwa rashin sanin halin datake ciki.
Shatu tace ai nawarke, kuzo mushiga ciki, sundade suna fira kafin sukayi masu sallama, kudi masu yawa Ansar yabama Baffa. Godiya sukayi masu sannan suka fito. Har bakin mota su Shatu suka rakosu. Ansar ya matsa kusa da Shatu. Kallonta yayi fuskar sa cike da damuwa yace gobe zandawo ko bakison ganina? Murmushi tayi tana wasa da hannunta tace inaso mana. Shikenan gobe zantaho maki da wannan abun dakirika daukata ( Camera) nima kinji, kai ta daga mashi, juyawa yayi yana murmushi yanufi motarshi. Kallon Umar yayi wanda bema daniyar tafiya yace to kai. Akaramakallahu nide nawuce. Dariya Umar yayi yace tojirani tunda kai kagama. Haka sukayi sallama suka tafi.

Kai tsaye office din Ansar suka wuce, nayan sun zauna ne Umar ya kalli Ansar yace wai dan Allah meke tsakaninka da Shatu? Abinda ke tsakaninka da Jimmala shine. Ansar yace wlh abokina nafada tarkon So, Allah ne ya sakamun son Shatu arai na lokaci guda.

Tunda nake banta ba tsintar kaina cikin irin wannan yanayin ba se haduwata da Shatu. Wlh ko Iman damuka dade muna soyayya banajin haka agareta. Seyanzu nagane ya ainihin so yake, tabbasa nasan soyayyata da Iman akwai Shakuwa da kuma soyayyar yan uwantaka.

Amma yanda nakejin son Shatu araina acikin kwana daya wlh inaji bazan iya rabuwa da ita ba. Ajiyar zuciya Umar yayi ya kalli Ansar cike da tausayi yace to yanzu yazamuyi da Uncle Aliyu, Momy da kuma uwar gayyar Iman sarkin kishi? Ansar yace nikaina abinda nake tunani kenan Iman tanada mugun kishi, ko maganar mace bataso inkawo mata.

Ranar nan da momy tashigo taganta tana ta aiki tacemun yakamata insamo mata me aiki saboda aiki karyayi mata yawa. Wlh bakaga yanda Iman tayi ba kamar wadda akace za,ayi mata kwace harda kukanta wai ita bata so. Hakanan momy ta kyaleta.

Amma yanzu shawara zaka kawomun dan duk mun kiahin Iman bazan iya hakura da Shatu ba, saboda haka kai nake sauraro amatsayinka na lawyer.

Dariya Umar yayi yace gaskiya ne, yanzu kam bazeyiwu ka kalli Uncle da Matarshi kace kanason zaka yima diyarsu kishiya, abun da kunya sosai. Amma ina da shawara guda 1, kasan me ake cema auren SIRRI? Toshiyakamata kayi,dan ita kadai ce hanyar dazaka mallaki shatu.

Kuma bazaka tare da Shatu agidanka ba, dole munemi wani gurin, Ansar yace haba Umar ina murna nayi aure kuma sekace wai auren sirri. Wlh wannan shawara ita kadai ce mesauki. Amma anjima da dare muje musami su Dady na da maganar nasan komai zezo dasauki. Shikenan Allah yakaimu, sallama yayi mashi shima yawuce office dinshi.

Aliyu ne zaune a office din abokinshi barrister Saddik, yana kallon wasu takaddu yana murmushi. Yace gskya abokina kayi kokari sosai, babu wanda ze kalli takaddun nan yace bana gaskiya bane, shiyasa nake son harka da kai. Kaga koyanzu nafito nace wancan kamfanin nawa ne babu wanda ze karyatani. Mutum daya ne kuma yana rami, shine Yaya,

Kaga zance dama dasunana yasa ajikin takaddun kamfanin. Tunda babu wanda yasan inda nashi takaddun suke, nafi zaton sunbata tun lokacin da sukayi hadarin nan, dan nasan suna cikin motarshi. Kuma nasa anduba mun cikin motar babusu sede wasu aka gani suma kuma duk sun yage.

Duk inda nake tunanin ganinsu anduba babu, har Iman nasa tadubamun dakin mijinta amma tace babu su.
Dariya barrister Saddik yayi yace kada kadamun kanka Aliyu, inde kana tare dani kamar ka mallaki dukiyar Ansar kagama ne, mune fa masu maida karya tazamo gaskiya, gaskiya kuma tazamo karya.

Saboda haka kada kadamu, tunda har ka iya kashe yayanka mallakar dukiyarshi bazata maka wahala ba. Godiya sosai yayi mashi ya kawo kudi masu yawa yabashi sannan yawuce gida.

Koda Khadija taga takaddun. Bakaramun murna tayi ba. Tace haba yanzu nafara ganin munshigo gari. Ni yanzu babban burina wancan sabon gidan na Ansar da,aka gina mashi. Sonake Iman tayi duk yanda zatayi tasa shi yamaida sunanta ajikin takaddun.

Aliyu yace ina tunanin gabadaya takaddun kadarorin yaya sun bace lokacindayayi. Hadari. Amma kamar yanda barrister yamaida,mun wannan takaddun kamfanin da sunana haka zansashi yayi mani wasu takaddun gidan da sunana kinga komai zedawo mallakina kenan. Domin momy na takawomun wannan shawarar kuma gashinan nafara samun nasara.

Khadija ta hade rai, tace bangane da sunanka ba. Ai ko mutuwa Ansar yayi akaje kotu idan alkali yaga sunanka ajikin takardar gidan mijin diyarka yasan badede bane. Amma idan sunan Iman ne ajiki fa? Kowa yasan akwai kyauta tsakanin miji da mata.
Cike da bacin rai Aliyu yace ai ba takaddun gaskiya bane bare ace za aga sa hannun mijinta ajiki, nine nan zansa hannu da kaina, kuma idan nasamu kudi ai kamar kunsamu ne ko.
Ganin yanda yake masifa yasa khadija matsowa kusa dashi tayi kasa da murya tace aa nifa bahaka nake nufi ba megidana nakaina, ai duk abinda kasamu muma namune kayi hakuri bazan kara ba. Tashi yayi yana fadin ai nafiso duk wata dukiya ta yaya takoma da sunana saboda nima nasha wahala wajen tara ta. Yace bara inshiga ciki inason inyi magana da momy ne. Dakinta itama ta wuce takira momynta tana kuka.

Duk abinda yafaru khadija tafada mata, shiru naga tayi tana sauraronta, nikam nakasa jiyo me akafada, ta dade tana yimata bayani sannan naga khadija tana murmushi. Haka sukayi sallama tafito tacigaba da aikinta.
Chapter 12 · 0% Book details