← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 23

Sashe 3

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanason Abdurrashid saboda shine yadauko irin halinshi, duk da Aliyu ma babu wanda ze iya gane wane irin haline dashi. Amma duk wanda zeganshi ze iya cemasa yanada halin kirki. Amma azahirin gaskiya komai irin halin maihaifiyarshi yadauko. Aliyu yanada zuciya da kuma hassada, sede yanada boye abu aranshi. Hakan yasa yakema yaynshi soyayyar karya wanda shikuma yayan nashi atunaninshi ta gaskiyace. Hakan yasa yake matukar sonshi. Yagirmeshi da shekara 4.
Ayanzu suna kasar waje suna karatunsu, inda Abdurrashid yake karantar bussiness, shikuma Aliyu Computer. Inda Abdurrashid yake gab da gamawa. Halima kuma tagama secondary dinta, bayan tagama ne H. Farida tacema Alhaji yasama mata gurbin karatu. Yace tafito de da mijin Aure bayason diyarshi tawuce karatu batare datayi aure ba. Bahakan taso ba, amma sanin halin mijinsu yasa tacema diyar tata tafiddo da miji. Dama Halima kwata kwata bata dauko halin uwarsu ba. Tanada hkr.
Bayan kwana 2 maneman auranta. Suka kawo kudin aure

Urs NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹 nah
Marubuciyar Zamani
NABILA,RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

25.......30
Agurin bikin Halima ne Abdurrashid yahadu da Fatima wadda takasance diya agurin abokin Abbansu, Alhaji Abbati kuma mamanta kawar H. Maryam ce suna zaune a katsina, tagama karatun diploma inda takaranci fannin girke girke. Ana soyayya ta kullu atsakaninsu. Bayan bikine harsun koma Karatunsu a inda. Abdurrashid yake semister din karshe, Ummanshi yafadama tafadima Abbansu yanemar mashi auran Fatima (ZARAH) lokacin dasukaji maganar bakaramun dadi duka iyayen sukaji ba. Banu bata lokaci akatsaida magana daya gama service dinshi za,ayi biki.

H. Farida tana da kawa me suna Lami. Duk wata hanyar banza lami ce take dora Farida abisa, itace tafara koya mata bin bokaye lokacin da taga H. Maryam bayan ta yaye. Danta kuma tasamu wani cikin. Ana tarakata gurin boka yayi mata asiri suka zubar da cikin kuma tahanata daukar wani cikin. Lami tana da diya daya mesuna Khadija tagirmi Aliyu kusan sa,ar Abdurrashid ce itama tayi karatun F,C,E ana cikin garin katsina, kuma tanada kawa mesuna Bilkisu sede ita tunda suka gama karatu tayi aure a Abuja. Khadija batajin magana mahaifinta yarasu wanda Lami ce tayi sanadiyyar mutuwarshi dan suci dukiya. Khadija taso tayi aure ganin datayi kawarta tayi aure amma Lami tahanata saboda tanada burin yahada ta aure da Aliyu dandan kawarta farida.

Kwanci tashi babu wuya agurin Allah Abdurrashid yagama karatunshi harya kusa gama service dinshi, inda yakeyi a Abuja a wani kamfanin Abokin Abbansu.lokacin yakusa gamawa bikinshi da Fatima sauran kadan. Anan abokin Abbanshi yabashi wani gida flat house ana yake zaune.

Lokacin daya gama Abokin Abbanshi yadaukeshi aiki akamfaninshi saboda yaga yanada rikon gaskiya da amana. Kuma yace yacigaba dazama agidan kafin yayi nashi

Aliyu yadawo bikin yayanshi bakin ciki duk yadami zuciyarshi, ganin yayanshi har yasamu aiki a Abuja, gashi kuma harzeyi aure. Momynshi ce tayita bashi hkr kuma tafada mashi yanzu shine babba agida se binda yayi. Dawannan tunanin ya hkra.

An daura auran Abdurrashid da Fatima inda ta tare a Abuja, Abdurrashid yana da aboki kuma amini me suna Dr. Usman, a ana Abuja suka hadu dashi har suka kulla abota. Dr. Usman yana aiki a private hospital dinshi anan Abuja, yana zaune agidanshi tare da matarshi Amina da yaronsu Umar wanda befi shekara 1 ba.
Bayan bikinsu ne Dr. Usman da Abdurrashid suka hada matansu kuma akayi sa,a halinsu yazo daya. Amina macece me kirki. Haka suka cigaba da zumuncinsu tana koyama Fatima duk wani abu dabata sani ba.
Haka zamansu yakasance cike da so da kauna.

H. Farida ce zaune adakinta itada. Kawarta Lami. Farida tace wlh kawata banso yaron nan yasamu aiki a Abuja ba, inaso mu koma gurin boka kawai akashemun shi danni nafison inga dana yana hutawa da ace dan dan watane yakecikin daula. Ki kalli irin kudin da Alhaji yakashe abikinshi. Ko bikin Halima datake mace ba,ayi mata wannan barin kudin ba seshi. Lami tayi murmushi tace ai kawata keki kayi sake, tayama za,ayi inada yara har 2 agida kuma inzauna nice abaya, Farida tace ai saukina ma daya yanzu Aliyu shikadai ze zauna agidan dayagama karatunshi. Lami tace wannan ba shawara bace, yanda danta yayi service a Abuja har yasamu aiki, kema kicema mijinki yasama mashi aiki acan, wlh idan kika bari Aliyu yazauna agida kece da bacin rai, da yazama driver Alhaji da dan aiken gida. Ai gara yatafi can Abuja suyi aiki tare da Danta anan ne zefi sanin halin dayake ciki. Kinga shima Aliyu semu hadashi aure da Khadijata sutafi can abunsu, kinga duk wani plan dimmu zetafi adede kenan. Dariya Farida tayi tace wlh shiyasa nakesonki kawata. Yanzu kuwa zankira Aliyu in masa maganar Khadija nasan baze kiba
Haka takira Aliyu tafada mashi duk yanda sukayi da Kawarta. Sosai yayi farin ciki da wannan shawarar. Kuma yayi na,am dazancen Khadija, yace atura mashi no ta ana take suka turamashi no ta.

H. Maryam ce xaune afalon megidanta takawo mashi abinci. Bayan yagama cine take fada mashi tanaso ta dauko diyar kanwarta Asma,u mesuna Saratu. Sbd tana tausayin kanwarta mijinta ya mutu yabar mata yara har 3 kuma takiyin wani auren, shine tacema Alhaji nagaji dazaman shiru babu wani yaro akusa dani. Murmushi Alhaji yayi yace ai dama tunda Auta yatafi dole kisamu yarriko, ai babu komai anjima semuje mudaukota. Godiya tayi mashi.

Urs. NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹 nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)
This page belongs to u my bestie ZARAH B...B

30......35
Hajiya Farida ta kalli megidanta tace Alhaji Yaronka fa yasamo mana surika. Murmushi yayi yace a ina kuma yasamota? Diyar Lami ce khadija, Alhaji yace a gsky nayi farinciki Allah yasa ayi damu. Ameen Alhaji, nace meze hana A aika anema masa auranta idan yaso yana gama karatunshi ayi biki tunda saura. Wata 3 yagama. Alhaji yatashi zaune yace ammade kinsan ko Abdurrashid dayayi aure seda yagama service dinshi sannan ko.
Kibari kawai yagama se ayi bikin. Matsowa tayi kusa dashi kamar zata shige jikinshi, tayi kasa da murya, Ammade Alhaji kasan Abdurrashid babu abinda yafiso kamar yaga Aliyu akusa dashi, ko jiya damukayi waya yacemun da Aliyu yagama karatunshi can zetafi yayi service dinshi yafiso yazauna kusa dashi.
Alhaji yayi murmushi yace ai yaran nan suna son junansu, bakomai zanyi magana da kawunsu yaje yanema masa auranta. Amma kafin nan zamuyi magana da Abdurrashid. Rungumeshi tayi tace nagode Alhaji🙊🙊🙊😆😆😆

Abdurrashid kudi sun zauna mashi sunada wata 5 da bikinsu yagina katon gidanshi a unguwar metama. Part 2 yayi hade da boys quaters, komai iri daya yazuba aciki, adayan part din suka tare shida Fatima dayan kuma yace na Aliyu ne.
Yabude kamfani yanzu haka shine director na kamfanin, office din manager kuwa yace na Aliyu ne. Yabiya masu hajji shida Fatima bayan sundawo ne tafara laulayi suna zuwa asibitin Dr. Usman yasa akayi mata test nan take aka gano tana da ciki wata 3, bakaramin murna Abdurrashid yayi ba Ummanshi yakira yafada mata.

Haka suka cigaba da renon cikin Fatima, Amina matar Dr. Usman tana kulawa da ita sosai. Bayan kawun su Aliyu sunje nema mashi auren khadija gurin yayan Babanta. Nan take ya amince masu, sbd shima yagaji da irin halayen khadija, ana yawan kawo mashi kararta, amma dayake uwarta ta daure mata gindi shiyasa batajin tsoronshi.

Ansa bikinsu yana gama makaranta da sati biyu. Sosai Lami tafara gyara diyarta, saboda khadija tayi duniyancinta kuma uwar tasan duk abinda takeyi dan har ciki seda ta zubar. Hakan yasa ta turata
meduguri gidan kawarta danta gyarata, kuma taje gurin boka ta amso mata maganin mallaka da wanda za,a rufe mashi baki kada yagane ba virgin bace.

Kullum suna tare da kawarta Bilkisu. Awaya suna shirye shiryen bikinsu. Gyara na musamman takesha, soyayya sukasha ita da angonta. Duk tagama rudashi da kalar soyayyarta irin ta yan duniya, shiko Aliyu dama abinda yakeso kenan yaga ana kulawa dashi. Duk wasu kudi dayake samu ita yake turo mawa shiyasa take kara sonshi.

Ayaune Aliyu yadawo gida yagama karatunshi. H. Farida murna kamar zataci kanta se shirye shiye take mashi. Shima yayi farin ciki da ganinta, har kanwarshi Halima seda tazo mashi sannu dazuwa, tare da danta me suna Abdulhakeem, kasancewar ba irin halin uwarta gareta ba yasa take zaune lfy da mjinta.

Tun ana saura sati 1 biki Abdurrashid da matarshi sukazo Safana. Agurin H.Maryam Fatima tasauka alokacin cikinta yana wata na 7, sosai H. Maryam take kula da ita, tahana ta komai. Haka aka cigaba da hidimar biki inda Khadija da kawayenta sukayi party har kala 2, kawarta Bilkisu ma tazo ita da diyarta Hauwa me shekara 2. Aranar asabar aka daura auren Aliyu Abdullahi Alkali da Khadija Muhammad, akan sadaki dubu 50. Wanda yayan ango ne yabiya.

Bayan Alhaji Audu yayi masu nasiha misalin karfe 4 aka dauki amarya kasancewar ta jirgi suka tafi yasa ba,a kwashi mutane dayawa ba. Ko kawayenta Bilkisu da wata kawarta Samiyya aka dauka, su Abdurrashid ma duk tare suka tafi.

Semuce Allah yabada zaman lafiya aci agonci da amarci lafiya.

Urs. NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

This page belongs to my belove sisters Farida, Maryam, Halima & Amee girl.

35.....40

Bayan wata 1 da bikinsu, soyayya sosai suke sha, Aliyu yafara service dinshi a kamfanin yayanshi hade da aikinshi amatsayinshi na manager. Sosai yakwantar da kai yana aikinsa yana me biyayya ga yayanshi kamar gaske, mutane dayawa suna sha,awarsu.
Abangaren khadija da Fatima kuwa zama sukeyi na mutunta juna, kasan cewar Fatima tanada halin kirki yasa taja khadija jikinta kamar wata yar uwarta, itama khadija tanuna mana duniyanci suke zaune lafiya. Babu wanda zece akwai wani abu azuciyar ta, ita da mijinta.
Chapter 3 · 0% Book details