← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 23

Sashe 23

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Alh. Abbati yace nasande abokina ya amince, Asma,u kin amince ko seya biya cin hanci? Dasauri ta tashi tana murmushi tashige daki. Umman Nabeel tace tonima na amince mata, amma Alhaji bamuji kace komai ba. Murmushi yayi yace ina ganin magriba takusa ko. Dariya suka sa.

Alh. Abbati yace Alhamdulillahi, Allah mungode maka, insha Allah da munkoma za,a daura aure ta tare ko abokina? Abba yayi murmushi yace Allah yakaimu. Ansar yace uhm gaji su Abba anaso ana kaiwa kasuwa, pillown kujera Abba yadauko yawurgeshi dashi, tashi yayi yaruga yana dariya. Kowama dariyar yakeyi (HAPPY FAMILY😘😘😘)

Washe gari jirgin karfe 7 sukabi, kowa kuka yakeyi, saboda zaman dasukayi sun saba. Zaune suke aharabar gidan su Umar. Ansar yakallesu yace Yakamata ayi hanzarin maidani sabon gidana fa, dan banaso sabon yarona yazo akusa dasu Abba.
Nabeel yayi dariya yace dadina da kai saurin zakuwa, inama laifin kabari ta haihu bayan suna se ku koma, amma yanzu dan rashin kunya zaka ce amai daka. Umar yace kyaleshi Nabeel, kasan shi beda kunya, gara yatafi tunkafin yayima su Abba wata rashin kunyar.

Dariya Ansar yayi yace wlh kabini ahankali kasande nakusa zama Baba. Umar yace nima nakusa zama ai, kuma insha Allah sena rigaka saboda dama shigar sauri kamun nagirmeka. Ansar yace wasa kakeyi nizan rigaka. Nabeel yace nikuma zan zama atsakiya zanga wanda zefara zama Dady.

Ansar yace Nabeel saura wata 6 bikinka ko? Umar yace kaji mugu, yazaka rika kara mshi kwanaki. Nabeel yace kyaleshi matarka ce saura shakara 2 ta haihu. Dariya suka sa, Nabeel yace saura 3 weeks.

Ansar yace idan kaci sa,a banshiga sahun iyaye ba, tozamuyi kara,i, idan kuma nashiga sede inzama waliyinka...... Duka Nabeel yakai mashi yana dariya yace wlh bakada kirki Ansar yace wlh kadena saurin dukana, Umar yafada maka da andukeni ake samun mata. Dariya sukasa suduka. Umar yace yama sunanta? Nabeel yace HANAN. Ansar yace kaji wani suna sekace a China,,,,,,,,, haka sukayita fira daganan suka tashi zuwa sabon gidan Ansar dan susa afara gyarashi.

Bayan kwana 4 komai ya kammala agidan Ansar, komai sabo akasa acikin gidan, haka suka tare shida shatunshi, su Umar ma sunkoma gidansu, anan su Ansar suka bude sabon shafin rayuwa. Soyayya da shakuwa. Takara shiga tsakaninsu.

Seda yayi sati biyu sannan yakoma aiki, duk wani gyare gyare sunyishi kamar yanda Abba yace, wani abokinshi yabama rikon dayan kamfaninshi, sosai yake kula dashi, ma aikatan ma sunajin dadin aiki dashi. Yanzu hankalin Ansar akwance yake bashida wata matsala, arzikinshi se karuwa yakeyi.
Anyi bikin Abba da Asma,u. Inda ta tare agidanshi dayayima gyara, anan suke shan amarcinsu.
Nabeel ma anyi bikinshi shida Hanan, sosai su Ansar sukayi mashi hidima, Abba ma yazo daurin aure,dan zumuncinsu sukeyi sosai. Shatu, Jimmala da Hanan suma sun hada kansu suna zumunci sosai.

Duk da Hanan tafisu wayewa bata nuna masu wani wariya, dan suma yanzu babu wanda zece yan kauye ne, sede idan akazo fannin boko anan ake ganewa, baramma Jimmala, amma fannin islamiya suna da kokari sosai.

Duk kudin dasuke samu kauyensu suke gyarawa, domin mazajensu suntemaka masu sunbude masana,antu na mata agarinsu. Duk yanda Dr, yaso sirikanshi sudawo birni basu yarda ba. Acewar Baffa yafison yazauna cikin danginshi, hakan yasa suka gyara masu gidansu shida Mal. Mati, ginin zamani, harda soler aciki, dan yanzu mutanen garin basa zuwa rafi dibar ruwa. Mutanen garin suna matukar girmama su Baffa, acewarsu sune sanadiyar samun canjin rayuwa.

Agidan yari kuwa su Lami sunfita hayyacinsu, duniya takoya masu darasi, dan sunhadu da wadan da suka fisu duniyanci. Iman duk tafisu lalacewa, domin ita kullum cikin kuka take saboda tunanin Ansar.

Bayan wata tara Shatu tahaifi yan biyu kyawawa, dasu, dukansu maza, kowa yayi murna, Ansar kamar zemaidasu ciki saboda murna. Yakira Nabeel yana dariya yace kayarda yanzu nine babba.
Ranar suna yara suka sunan Dadyn Ansar da Dadyn umar.
Abdurrashid ana kiransa (Waleed)
Usman ana kiranshi ( Shaheed)

Dr. Usman yaji dadin karar da Ansar yayi mashi. Umar ma yaji dadi sosai, taro yayi taro, Jimmala da Hanan sunyi kokari Jimmala ma tana jan kafa dan cikinta ya tsufa. Har iyayen Jimmala sunzo, inne ko cewa tayi bazata jeba.

Da dare suna kwance Ansar yana makale da Shatu dan yara sunyi bacci, kallonta yayi yace Shatu na nagode, bansan dame zan saka maki ba, takarda yamika mata yace wannan kujerar makka ce ta mutum 4 nabiyama Baffa, Inne, da iyayen Jimmla. Saura keda Jimmala idan kuka yaye yaranku inhar baku sami wani cikin ba, semutafi. Shatu ta turo baki tace dan Allah inason zuwa, kobamu yayesu ba, semu ciresu afara basu abinci. Dariya yayi yace senaga yanda jikinsu yake. Rungumeshi tayi tana masa godiya.
Bayan sunan Shatu da Sati 1 Jimmala ta haihu,itama tasamu Mace. Umar se murna yakeyi, yakira yan uwa yafada masu. Ranar suna yarinya taci sunan Amina ana kiranta da (Umaimah). Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya cike da so da kauna, Hanan ma tahaifi mace mesuna Fadeela, dan Nabeel yace bazeyima Ummanshi takwara ba seyafara yima Yayanshi Fadeel.
Baffa dasukaji zasuje makka har kuka sukayi, adalilin haihuwa zeje kasa me tsarki.

Bayan shekara 15. Tsaye suke bakin gate din gidan yari, sunajiran Iman, Abban Safana Yace Alhamdulillahi Allah yanuna mun zuwan wannan rana,gashi nazo da kaina domin daukar Iman....... shiru yayi domin hango wata tafito daga cikin gidan, Iman ce tafito idan kaganta sekace ta tsufa.
Da kuka ta iso gurinsu, kowa seda yazubar mata da kwalla, haka suka nufi gida.
Bayan Amina tasata tayi wanka taci abinci, Dr, yakawo mata magunguna tasha, Afalo ta iske su dukansu, zama tayi takara gaishe dasu, Ansar harbeson kallonta, sbd yanda takoma, tundazu yakasa tsaida hawayen dasuke zuba a idonshi, tausayinta sosai yakeyi.

Abba yayi gyaran murya yace Iman, base na kara yimaki wani bayani me tsawo ba, dan yanzu kinsan menene rayuwa, sede inkara baki shawara akan kiji tsoron Allah aduk inda kike, kuma kiguji sharrin kawa.

Yanzu ina iyayen naki suke? Kwllan dake idonta tagoge, tace. Ai duk sun mutu, mutuwar wulakanci, momynta ce kawai tarage itama gara mutuwarta da halin datake ciki. Dan Allah kuyafemun, wlh naga rayuwa, Kusa da Ansar taje wanda sautin kukanshi yakaru kamar karamin yaro, tace Yaya Ansar dan Allah kayafemun, nasan bazan gama da duniya lfy ba idan namutu da hakkinka. Kuka sosai tarikayi. Dakyar Ansar yace ya yafe mata. Kowa kuka yakeyi,
Abba yace zamutafi Safana dake Da kinsamu sauki akwai wani mutum dana bashi aurenki, dan bazanso kizauna agida ba, nasan damuwa zatayi maki yawa, amma idan kina gidan mijinki zakisamu sauki sosai, Sunanshi Kabeer, babban mutum ne, amma kuma ba tsoho bane, yanada mata 2 da yara 6 ina fatan zabin dana yimaki yayi, amma idan kinada magana kiyi bazan yimaki dole, ba.
Iman tace Abba banida wani zabi daya wuce naku, Allah yasa haka shine mafi alkhairi, kuka sosai tasaka, wai yau itace da auran kauye, kuma cikin mata 2. Lalai taga rayuwa, kuma duk wanda yabiyema son zuciyarshi dana sani ce zata biyo bayanshi.

Abba yace ma Umar yakira yaran duka, dan dama shine yace sufita, dan bayaso suji labarin daya wuce.

Bayan sunshigo Abba yafara gabatar dasu agurin Iman, mutum 3 naga yanuna amatsayin yayan Ansar.
Waleed
Shaheed
Mimie wadda taci sunan Inne

Guda 2 kuma na Umar ne,

Umaimah
Abdulhakim

2 yan mata kuma na Nabeel ne
Aiman
Husnah

Waleed , Shaheed da umaimah da Aiman. Duksungama secondary, har sunshiga universty, sauran kuma suna secondary dan haihuwar basosai suke yinta ba, suma suna planing.

Murmushi Iman tayi tana goge idonta tace Allah yaraya, ana suduka suka matsa kusa da ita suna gaisheta.

Bayan sati 3 akayi bikin Iman da Kabeer. Sosai take girmama kishiyoyinta, suma basuda tashin hankali, Iman tashiryu sosai, har islamiya ta koma, batada aikin yi se neman gafara, sede haryanzu son Ansar yana ranta. Takara yarda Son Zuciya bacinta

Soyayya tashiga tsakanin Waleed da Umaimah, shaheed kuma da aiman. Iyayensu bakaramun dadi sukaji ba, dan yanzu gida yazama. Happy family.

Ansar ne da Shatu kwance ,Ansar yarungume Shatu yace yakamata fa kiyima Auta kawa, shatu tace amma mace nikeso, kuma sunana za,a sa.
Dariya yayi yace semusaka SHATU DIYAR ANSAR, tunda kema yanzu kinzama SHATU MATAR ANSAR dariya sukayi yaja bargo yarufesu.

Nima hakan yasa nayarda birona narufo masu kofar inamasu fatan alkhairi.

AlHAMDULILLAHI
Anan nakawo karshen littafina me suna SHATU DIYAR MAHARBI
Ina mika godiyata ga dukkan masoyana.
Jinjina gareku yan
HOUSE OF NOVELLA
RAZ
NWA
dasauran ma,abota karatun littafina.
Jinjina ga kawata
ZARAH B..B
dasauran. Kawayena. Dasauran yan uwana.

Semun hadu bayan sallah a sabon littafina me suna
A MAKABARTA AKA HAIFENI
NAGODE
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

Love u all my fans😘😘😘😘
Chapter 23 · 0% Book details