Sashe 13
Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallamar su Ansar tajiyo daga falo, fitowa tayi tana amsawa, A,a yau su Umar ne agidan mu? Wlh kuwa Momy , zama sukayi bayan sun gaisa. Ansar yace momy ke kadai kina ta aiki gidan shiru haka? Tace wlh kuwa gani nan duk nagaji da aiki gyaran kitchen nakeyi.
Sonake insamu me aiki ko wanke wanke da shara tarika mun dan duk cikin aikin gida bana sonsu. Ita de Iman tace bata so. Umar yayi saurin dago kai ya kalli khadija yace aikuwa. Ummata ma megadin ta tasa yasamo mata me aiki idan kina so zanyi mata magana seta samo maki.
Murmushi khadija tayi tace kai amma wlh dana gode, idan ka koma kayi mata magana dan Allah kada kamanta. Tunda ita bataso setayi ta fama da aiki ai, tunda Allah yayita da kishi. Murmushi Ansar yayi yace momy Uncle yana nan kuwa? Naje office ance baya nan. Ai kam yanzu yadawo amma gaskiya bacci yakeyi, sede anjima kadawo idan yatashi, ko kuma zan fada mashi seya kiraka idan ya farka.
Sallama sukayi mata tace Umar kada fa kamanta, yace insha Allahu bazan manta ba.
Suna fitowa Ansar yakalli Umar yace wlh abokina bansan lokacin daka fara karya ba, nide tunda nake bantaba ganin wata me aiki agidan Umma ba, amma naji kana maganar wai tana da ita, har zaka saka tasamo mata. Murmushi Umar yayi yace dazufa kake cemun ni lawyer ne in samo mana mafita ko? To kaxuba ido kasha kallo inaso ne inkawo maka Shatunka akusa da kai. Ansar yace kan uba. Wai Shatun tawa zaka kawo amatsayin me aiki? Umar yace kaide kayi hakuri kabimu ayanda mukace, dan dazu nafara yima Abba maganar yace musameshi agida, kawai de nafara kawo tawa shawarar ne, kuma nasan shima Abba zekarbeta hannu 2 tunda ba fanninshi bane. Ansar yace shikenan Allah yayi mana jagora.
Iman ce zaune ita da kawarta Hauwa taxo kawo mata I,V na bikinta, iman tace wlh Hauwa gurin bokan momynki nakeso kirakani yabani maganin dazan mallake Ansar da yanda zedena ganin kowace mace agabanshi, bare kuma wata rana yasa ran yimani kishiya, dan kinsan namiji ba abun yarda bane.
Shiru Hauwa tayi azuciyarta tana mefadin lallai ma wannan Iman din, kinsamu kin auri me kudi wanda haryafi mijin dazan aura kudi, sannan ke daya ce agidanki ni kuma nice ma ta 3 sannan kike fadin inrakaki kisamo maganin mallaka.
Wlh babu maganin dazaki samu, insha Allah yanda zan zauna da kishiya kema wata rana se mijinki yayi maki.
Iman tace kinyi shiru Hauwa. Murmushi tayi tace kawai dariya ma ni kika bani, wai keda atunaninki hakanan kike zaune da Ansar babu magani. Ai kila dayanzu yafara maganar aure yanda yake yaro me tashen kudi kema kinsan yan matan Abuja bazasu kyale makishi ba.
Tun kafin aurenku lokacin kuna zaman mutuwa momynki tasa momyta taje gurin boka ta anso mata maganin mallaka kuma maganin beda makari. Kimayi shiru da bakinki kada kifada ma momynki tayi tunanin ko yakare tasa kuje guein wani bokan kuma kinsan wannan bokan ba,a hada maganinshi dana wani. Kuma asirin jikin Ansar idan yakare duk abinda kuka mashi baze kamashi ba.
Kinga keza,a bari da danasani tunda de momy baza,ayi mata wata kishiya ba. Saboda haka kotayi naki magana kuje gurin wani bokan kice mata muna zuwa dake. Dariya Iman tayi ta rungumota tana fadi wlh shiyasa. Nake sonki kawata. Allah yabarmu tare, naji dadi dazakiyi aure a Abuja wlh. Wani shu,umin murmushi Hauwa tayi taname ajiyar zuciya.
Urs
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@(H,O,N,A)
100.....105
Zaune suke afalon Dr. Usman, Amina ma tana gefenshi. Murmushi Dr. Yayi dayagama jin bayanin Umar, Amina ce tafara magana. A gsky abu yayi kyau,Allah yasa alkhairi.
Dr. Yace Ameen, amma Ansar kamar yanda Umar yafada inaganin haka za,ayi dan ita ce kadai hanya mafi sauki dazamuci ribar abinda muke so.
Kuma sekayi hakuri, kasan duk meson yaci riba arayuwarshi dole seyayi hkr kana yaci nasara. Akwai abinda muka sani wanda kai baka sanshi ba, kuma bana so infada maka abinda banida tabbas, amma da sannu zaka fahimci komai, nafiso kafin kowa yagane abinda nake tunani ta hanyar samun kwakwkwarar sheda.
Kuma insha Allahu munsami hanyar dazata kawo mana sauki gurin binciken mu. Kuma insha Allah gobe zamuje can garin su Shatun zanga Baffanta da kuma Baffan Jimmala tun Allah yasa shima Umar yasamo mana aurika acan.
Anjima zankira Abban safana zamuyi magana dashi Itama Aunty Asma,u zan fada mata, kuma nasan zasu bada goyan baya, banaso kabari su Aliyu su san da maganar.
Inaso kome muka shirya kabimu ayanda mukace, nan gaba zaka fahimci dalilinmu. Kuma bayan aurenku dole sekayi hkr Shatu tayi aiki agidan Aliyu. Akwai hikimar yin hakan,
Kuma ba,a can zata rika kwana ba, za,a fada masu tanada miji, inaso wancan part din da Umar zetashi tunda ciki da falo ne kuma akwai kitchen aciki se akawo Shatu ciki, banaso yan uwanta sugane abinda muke shiryawa, zanyi masu kayan daki ita da Jimmala
Idan yaso duk ranar dazaka kwana gurinta seka kirkiri tafiya,wannan kuma Umar seka samo masa yanda zeyi, dan fanninka ne. Kuma ita ma Shatun bayan bikin zan fada mata komai nasan zata fahim cemu Insha Allah. Kuma tare za,ayi bikinka dana Umar bana so yawuce wata 1. Anan ansar yayi mashi godiya. Yatashi yatafi.
Bayan Umar yadawo daga rakiyarsa ne suka zauna suka cigaba da tattaunawa. Dr. Usman yace naji dadin wannan al,amari sosai. Kuma nasan Allah ne yashirya mana haka, nadade ina addu,ar samun mafita, saboda banida wata hujja akan abinda nake zargi. Nayi alkawarin sena tonama Aliyu asiri, duk atunaninshi bansan meyake aikatawa ba. Se duniya tasan halin dayake ciki, nasan yanzu banda hujja amma nakusa samota sena makashi a kotu. Amina ma taji dadin wannan abu addu,ar samun nasara tayi.
Anan yakira Abban safana sundade yana mashi bayani shima yaji dadi sosai, kuma yabada goyon baya. Asma,u yakira itama yayi mata bayani. Taji dadi tayi masu addu,ar samun nasara. Hamdala Dr. Yayi yace Munkusa cimma burinmu Allah zeshige mana gaba. Umar idan kalura da Ansar ya yarda da Aliyu sosai kamar yanda babanshi ya yarda dashi, nasan kome zamu fada mashi baze yarda ba. Umar yace nima nataba yimashi magana akan gidansu. Nace yarika lura sosai, amma harseda yayi mun fushi akan maganar. Shiyasa nima naji dadin haduwarshi da Shatu. Kuma nasan bazata bamu matsala ba.
Washe gari haka Dr. Usman yakira wani abokinshi suka tafi rugar su Shatu. Tare dasu Ansar suka tafi saboda basu san gidan ba. Motar suce agaba, suna binsu abaya. Haka suka isa kofar gidan su Shatu. Yaro suka samu yayi masu sallama. Baffa ne yaleko, ai yana ganin su Ansar yataho yana washe baki, bayan sungaisa yakoma gida yayi masu shimfida azaure, sannan yayi masu iso. Su Ansar suka nufi cikin gida, awani daki aka yimasu shimfida suma. Anan Baffa yasa inne tadamo fura dama yakawo yanshila ansoyasu basu kai ga ciba, hadasu yasa aka hada masu, su dr. Ya kaima nasu, ita kuma inne ta kaima su Ansar.
Bayan su dr. Sungama ne Baffa yakoma suka kara gaisawa, anan abokin Dr. Usman yayi ma Baffa bayanin abinda yake tafe dasu. Farin ciki Baffa yayi jin mutane masu mutunci sunzo neman iri agurinshi, bama shi kadai ba, hada abokinshi.
Baffa yace alhamdulillahi gaskiya naji dadin wannan bayani naku. Kuma tunda Jimmala na diyata bace yakamata idan mungama inrakaku gidan shi matin dan shima afita hakkinshi ko? Dr. Usman yace haka ne, Baffa yace sede wani hanzari ba gudu ba. Gaskiya nariga nayima Shatu alkawarin bazan taba amsar maganar aurenta ba harse idan ta amince. Duk da nasan zamusha zagi agurin mutane idan sukaji zamu aurar da ,ya,yanmu a birni. Amma hakan bazesa idan har ta amince inkasa bata abinda takeso ba, dan nasaba dama da surutun yan garin nan. Baffa yace kudan jirani inshiga inji tabakinta ko.
Adakin Inne yasamesu, anan yayi masu bayanin zuwan su, dukar da kai Shatu tayi tana wasa da hannunta. Inne tace to Shatu kinyi shiru bakice komai ba, kobaki sonshi? Baffa yace kada ki kwari kanki fa, kuma kada ki kalli mutunci dasukayi mana ki amince da abinda bakiso, kinsan de bazan maki dole ba. Shi aure dan soyayyane idan babu ita auren ma baya dadewa babu kamar na wannan zamanin. Kina sonshi? Murmushi Shatu tayi takife kanta bisa cinyar Inne, dariya Inne tayi tace dama ance shiru ma magana ce. Baffa yace a,a kila de akwai wanda takeso, bara inje inbasu hakuri. Dasauri Shatu tadago tace aradu Baffa bahaka bane, yace nafiso inji da bakinki kin amince? Kai tadaga tana murmushi. Tashi tayi tanufi waje, Inne tace aini tunbayau ba nagane Shatu tana son Ansar, kuma naji dadi sosai da akace abokinshi yana son Jimmala, hankalina zefi kwanciya idan suna tare. Baffa yace inaso kitoshe kunnuwanki akan duk abinda mutane zasu fada. Insha Allah alkhairi ne zebiyo baya.
Hamdala su Dr. Usman sukayi dasukaji bayanin Baffa, tashi sukayi suka nufi gidan Mati. Acan ma de haka ta kasance, bayan antambayi Jimmala ta amince, sosai Mati da matarshi sukaji dadi.
Anan Su Dr. Usman suka nemi asa masu rana nan da wata 1. Baffa yace to bara mukira yan uwa se ayi komai agabansu. Dr. Usman yace kuma bana so kuyi komai, nizanyi masu duk abinda ake bukata. Godiya sosai sukayi masu, sannan Baffa yasa aka kira yan,uwa.
Nayan lokaci kadan kowa ya hallara, kuma akayi masu bayani, duk da sunji haushi amma ganin fuskar manyan mutane yasa suka boye haushinsu. Anan take aka saka rana wata 1. Kudin nemana aure suka bayar suka yimasu godiya sannan sukafito.
Akofar gida suka samu au Ansar. Dr. Usman yace to kuzo mutafi ko, Ansar yace Abba har zaku koma ne? Dr, yace bangane zamu koma ba, tare dasu wa mukazo? Abokinshi yace dan Allah rabu dashi sekun taho kasan mezasuyi ne. Murmushi Dr. Yayi anan Baffa yakawo masu zuma,da kwai, Mati kuma yakawo masu nono, haka sukatafi suna godiya.
Yaro Ansar yasa yakira mashi Shatu, Umar kuma yawuce gidan su Jimmala dayake babu nisa, Ansar yace kasanse babu ntwk anan ko, kuma bakin ruwa muzamu tafi nan da minti 30 muhadu anan. Umar yace to yawuce.