Sashe 20
Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nabeel yace Shatu gobe dole kiyi sammako,kije kidauko Cameran, nasan dawuri zasu tafi kotu, kuma khadija tayarda dake, nasan zata iya barmaki makulli, suna tafiya kicire Cameran, zanyima. yaya Fadeel magana kitafi da wayarki zanbashi no, ki kina gamawa ki kirasa zezo yadauke ki sekutaho kotun, wayarshi yadauko yace takaranto mashi no, ta. Umar ne yafada mashi, bayan yayi saving yayi mata VTU, yace ga kudi nan natura maki koda baki da kudi awayar.
Kiransu As,mau Dr, yayi awaya yace suzo falonshi. Bayan sunzo yayi nasu bayanin da Shatu tayi masu, kowa farin ciki yakeyi dajin wannan nasara da aka samu, suka addu,ar samun sa,a.
Nabeel yace Dady bara intafi, zanfadama Yaya Fadeel duk yanda zasuyi goben. Dr, yace to sannu Nabeel kana kokari kaima Allah yabiyaka. Umar yatashi yaraka shi,
Asma,u tace Dr, ko afada ma Alhaji? Yace a,a wannan maganar idan har tafita daga gidan nan tana iya yaduwa cikin daren nan, saboda nasan Abba yanzu yana tare da matarshi, idan har nafada mashi yana iya sanar da ita, kuma kinsan tana iya fada masu Lami, gara idan munhadu gobe infada mashi kada se anje kotun yagani daga sama, nasan bazeji dadi ba. Tashi sukayi kowa yaje yayi alwala suka kabbara sallah.
Tun karfe 7 Shatu ta isa kofar gidan su khadija, lokacin dataje suna cin abinci kasancewar dawuri sukeso su fita, mamakine yakamata ganin Iman tana kara gyara tsummuna acikinta, shigowarta yasa tayi saurin sakin rigarta. Bayan sungaisa taji Lami tana cewa Iman zauna ahanklaifa kinsan ba,ason me ciki yana abu dasauri. Kara kallon Iman Shatu tayi tana mamakin abinda tagani shi ake kira da ciki.
Khadija tace Shatu sarkin aiki, harkinzo? Ta e wlh ai naji kince zaku fita dawuri. Khadija tace ai bazamu tsaya jiran kigama ba, kawai zan barmaki makulli, kuma gashi hada megadi zamu tafi.
Lami ta harari Shatu, itade haka kawai taji bata kwanta mata, yar kauye da ita amma jikinta be nuna alamun wahala ba, se wani haske ma takedashi kamar yar hutu, yatsina fuska tayi tace, kiyi mata kwatancen kotun idan tagama seta kai maki can, tunda babu wanda besan babbar kotu ba.
Dan bamusan lokacin dawowarmu ba, kuma baza abarta tayi tazama iya kadai agida ba. Haka kawai in banda abunki ma Khadija dasaurin yarda wai harzaki bar ma me aiki makullin gidanki, ta tafi kawai idan mundawo semuyi aikin da kanmu gobe tazo tayibaikin.
Wata irin zufa ce tafara fitoma Shatu jin abinda Lami take fada, acikin zuciyarta tafara addu,ar neman sa,a
Lami tacigaba da fada, kinsan fa bakauyen mutum ba abun yarda bane, nide hankalina be kwata abata makulli,ba.
Khadija tace kai momy, wlh nayarda da ita, babu ruwanta, Iman tace ai babu abinda zatayi kawai abata mana. Lami tace tonaji, amma ki kulle dakunanki da store idan yaso idan ta gama seta kulle kofar falon.
Ajiyar zuciya Shatu tayi, Khadija tace toshikenan momy. Bayan sungama komai ta kulle ko ina tabata makullan falon tace idan kinje kina shiga kitambayi inda ake shari,a da kinshiga layin farko daga can gaba. Muna nan azaune.
Seda Shatu ta tabbatar suntafi sannan taciro cameran takira Fadeel tace mashi tagama, yace tajirashi gashi nan zuwa go slow ne yadanyi yawa. Ganin haka Shatu taje tayi aikinta tagama komai tazauna zaman jiranshi.
Kotu tacika makil da jama,a kowa yanason yaji karshen shari,ar, kakannin Ansar sunzo daga katsina harda sauran yan uwansu, Halima ma tazo, danginshi na Safana duk sunzo, Bilkisu kawar khadija da diyarta Hauwa suma sunzo, Hauwa tana tare da Iman, kowa yashiga ciki suka zauna.
Bayan alkali yashigo sannan aka shigo da Ansar, duk yayi baki yarame, kowa yaganshi seyayi mashi kuka. Dr, nazune kusa da Abban Safana bayan yagama fada mashi abinda yafaru, sosai yayi murna da jin wannan al,amari.
Bayan anyi shiru ne magatarkarda yatashi yakaranto karar da za,a cigaba da sauraro.
Alkali yanemi barrister Umar daya. Cigaba da kawo shedar shi, Umar yatashi yace inason ganin Iman matar Ansar zanyimata yan tambayoyi ya megirma me shari,a. Kotu tana son ganin Iman.
Kozaki iya fadama kotu ainihin sunanki?
Goge hawayen dake idonta tayi tace , sunana Farida Aliyu Alkali, kuma ni matar wanda yakashemun mahaifice.
Malama Iman, alokacin da Ansar yashigo gida yana kuka, bayan yakoma dakinshi, dakika ajemashi ruwa kika fita kinkarajin motsin fitarshi?
E lokacin ina daki nakasa bacci saboda naga Yaya Ansar yana kuka kuma naje gurinshi yakoroni, hakan yasa nakasa yin bacci. Ina zaune naji motsin mutum yafita, bayan wani lokaci kuma senaji ansake dawowa kamar ana gudu naji anbude dakinshi anshige, daga nan ba,a kra fita ba. Ashe lokacin ne yafita yakashemun Babana.
Amma meyasa lokacin da kikaji anbude kofa baki fito ba, tunda kinsan halin dakika barshi aciki?
Nide kawai tsoro naji, tunda muke beta mun tsawa ba, shiyasa naji tsoron kada infita ya dukeni.
Mungode Iman, zaki iya tafiya.
Nabeel ne yakalli agogon hannunshi yaga haryanzu su Shatu basu iso ba, kuma saura mutum 1 Umar yagama fiddo da shedarshi, fita yayi yakira Fadeel yace mashi sunkusa kara sowa.
Umar yabukaci ganin Fafilo agaban kotu, wata irin faduwar gaba khadija taji lokacin da aka kira sunan fafilo, azuciyarta take tunanin meyakawoshi kotu.
Bayan yafito ne, Umar yace yafadi sunanshi,
Ni sunana Lukman, amma ana kirana da Fafilo.
Fafilo menene alakarka da marigayi Aliyu?
Nide naksance yaronshi ne, duk wani mugun aiki idan yatashi niyake sakawa inmashi. Tundaga sata harzuwa kisan kai. Hakan yasani naje na kwance ma Dan uwanshi. Burkin mota alokacin dazasu je dauko dansu daya dawo daga makaranta.
Bayan nazo nasheda mashi sunyi hadari yasani inbisu asibiti intabbatar da sun mutu kafin inbar gurin.
Kuma shine yasani nakashe accounter din Yayanshi wanda yaje ciro makudan kudi abanki, ni kuma na kashe shi na amshe kudin.
Bayan ya sallameni kudi masu yawa yace zekara nemana idan wani aikin yataso.
Tundaga lokacin bekara nemana ba, nashiga matsala naje nasameshi agida shida abokinshi suna shirya yanda zasu kashe Ansar, ana narokeshi kudi yamun korar wulakanci yakoreni.
Tundaga nan bansake ganinshi ba, se labarin mutuwarshi. Hakan yasa nazo infadi gaskiyar abinda yafaru, kuma ashirye nake in amshi duk wani hukunci daza,amun.
Gaba daya kotun tadauki hayaniya, khadija zufa kawai takeyi itada lami da Farida, saukinsu daya ba,a kira sunansu ba. Lami tace ki kwantar da hnklnki tunda wanda ya aikata laifin bayanan, kuma dole ayankema Ansr hukunci tunda harya dauki doka ahannunshi.
Abban Safana dukewa yayi yana kuka kamar karamin yaro, Alhaji Abbati ne yarika bashi hkr.
Mikewa Farida tayi tace wlh karya yakeyi Aliyu baze kashe dan uwanshi ba, kawai sunrasa abinfada ne.... Alkali ya daka mata tsawa yace kotu ba kasuwa bace dazaki tashi kina magana haka. Komawa tayi ta zauna tana maida numfashi.
Ganin kotu ta ymutse yasa Alkali ybada hutun minti 20.
Kowa fitowa yayi yana gadar albarkacin bakinshi, Ansar zama yayi agurin yana wani irin kuka meban tausayi, gashide angane wanda yakashe mashi iyaye, amma kuma baya gurin,sannan gashi shi kuma anja mashi sharri, wanda ya tabbatar da andawo za,a yanke mashi hukunci, tunda ba,a samu shedar dazata nuna bashi yakashe Aliyu ba.
Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/2, 10:39 AM] YAYA HAYAT: 🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@ ( H,O,N,A)
145.....150
Haka kowa yafito waje, hankalinsu Khadija yafara tashi ganin anfara kawo hujjar dazata iya tona masu asiri. Lami ta matsa kusa da Farida tace bana son kina magana akotu, domin wanda aka tonama asiri baya duniyar, kuma laifinshi baze shafeki ba, gara kiyi shiru tunkafin allura ta tono galma.
Kallonta farida tayi da mamaki tace mekike nufi da haka? Murmushi tayi tace ina nufin batun kishiyarki Maryam, tana kaiwa nan tawuce gaba tana murmushi. Wata irin zufa ce tarika fitoma Farida jin abinda Lami tafada.
Nabeel ne da Umar abakin gate sukaje taho dasu Shatu, tahanyar baya suka bi dasu, wani daki suka samu, anan sukayi saurin kunna Cameran sbd saura mintuna kadan akoma. Shatu kuma Umar yanuna mata inda su Khadija suke taje ta kai masu makulli. Da harara Lami tabita tace wlh nide zuciyata takasa yarda da wannan yar fulanin, munafukai nesu. Shiru Shatu tayi tawuce ta koma gurinsu Umar.
Mamaki ne yakamasu lokacin dasuka kalli abinda ke cikin cameran, wasu hawayen farin ciki ne yarika zuboma Umar, sunyi matukar farin ciki da wannan sheda dasuka samu, cike da kwarin guiwa suka koma kotu, Nabeel kuma yaje yaduko kayan dazasu hada aciki kowa yasamu ganin abinda ke cikin cameran.
Bayan kowa ya nutsu alkali yace barrister Umar kai muke sauraro, tashi yayi cike da kwarin guiwa, fuskarshi dauke da murmushi, barrister Saddik wanda yafara tsorata da Umar, yakara kallonshi, zufa yaji tana fito mashi.
Umar yace ya megirma me shari,a inason afitomun da SHATU BUBA DIYAR MAHARBI, akwai tambayoyin dazan yimata.
Alkali...kotu tanason ganin Shatu,
Sam khadija bata kawo komai ba jin ance Shatu, lokaci guda Khadija tamike tsaye ganin wadda batayi tsammanin gani ba, segata tafito tana shirin bada sheda, Lami ce tajawota tazauna, kuka sosai khadija takeyi, Lami tace menafada maki? Kiyi shiru nasan bawata sheda me karfi zata bayar ba, khadija tace momy idan kuma tanajin duk irin maganganun damukeyi nida Aliyu fa, kinsan dole nima amun hukunci. Kiyi shiru bama zata fada ba. Iman wadda tundazu tafara kuka ganin halin da ake ciki, tace Allah yasa batasan cewar cikin karya gareni ba, kinga ko dazu data shigo tasameni ina saka tsumma.
Umar yace kozaki iya fada ma kotu cikekken sunanki da kuma tarihinki ko ke wacece?
Sunana A,ISHA ABUBAKAR WADDA AKAFI KIRA DA SHATU BUBA DIYAR MAHARBI.
Kuma ni matar wadda ake zargi ce wato Ansar....... karyane yame shari,a, Ansar beda wata mata ce Iman,,,,, Alkali yace ki nutsu kotu bagurin wasa bane, Lami tazaunar da Khadija wadda ta tashi tayi magana, Kuka sosai Iman takeyi, Hauwa na lallashinta, aranta kuwa farinciki ne tana yima Iman Allah yakara.
Umar yace amtsayinki na matar Ansar, me ya kaiki yin aikatau agidan kawunshi? Objection my lord, muna magana ne akan kisan da Ansar yayi, bekamata brr. Umar yakawo wani zance na daban ba.
Korafi be karbuba, maganarshi tana kan hanya, cikagaba da tambayarka brr. Umar.
Munajinki Shatu......
Anan Shatu tafada ma kotu komai, har irin maganganun datakeji agidan khadija ita da Aliyu, har takawo yanda akayi ta boye Camera afalon khadija.