← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 23

Sashe 6

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan wasu shekaru Ansar nagaya fito daga cikin hall bakinshi yakasa rufuwa yanufo gurin family dinshi dasukaxo tayashi murnar kammala degree dinshi na farko akan bussiness Administration, Abokinshi kuma amininshi. Umar yataho da sauri suka rungume juna kasancewar shi Umar yariga Ansar gamawa shi under law yayi karatunshi. Dariya Ansar yayi yana kara rike Umar suka nufi gurin iyayensu. Anan sukayi ta daukar pictures.
Tsaye take ta rungume hannu tazubama Ansar ido, shikwai taje kallo tana murmushi. Iman kenan wadda harta gama secondary school dinta. Kallonshi takeyi yanda yayi kyau sosai, kayan sunmashi kyau. Hure mata ido taji anyi tare da kamo kafadarta. Hannunta yakamo yace my little baby wannan kallon fa. Dariya tayi ta turo baki tace to idan bankalli yayana ba wazan kalla? Murmushi yayi yace gaskiya babu kanwata. Zatayi magana kenan taji muryar wata yar course din su Ansar tana fadin ina kashiga tundazu ina nemanka mudauki pisc, yace wlh ina tare da family nane, hannu iman yasaki yana fadin muje.
Wani irin bakin ciki ne yakama Iman nan da nan taji saukar wahaye. Abisa fuskarta, hannun momynta taji tana goge mata fuska, tace haba Iman yau ranar murna ce meye naki na kuka haka? Bakinta ta turo tafadi mata abinda yafaru, dariya khadija tayi tace aiba budurwar shi bace yar ajinsuce kuma kowa haka yakeyi kawai hoton bankwana zasuyi. Ai kema kinsan duk duniya ke kadai Ansar yakeso ko? Dariya Iman tayi tana boyae fuskarta abayan khadija. Haka aka gama suka wuce gida.

Bayan kwana biyu Aliyu yasamu yayanshi da maganar saka ranar bikin ,ya,yansu, Aliyu yace yaya dama cewa nayi tunda Ansar yagama karatunshi meze hana ayi bikinsu da Iman inyaso agidanshi tayi karatunta. Murmushi yayanshi yayi yace hakan ma dede ne, amma bari idan nakoma gida zantambayi Ansar inji minene shawararshi akan bikin, duk da suna son junansu gara aji ra,ayinshi tunda kaga shima masters ze wuce ko? Aliyu kam bahaka yaso yaji daga bakin yayanshi ba, sede babu yanda ya iya murmushi yayi yace ai bkomai yaya duk abinda kace hakan za,ayi.

Bayan Abdurrashid yadawo gida yaci abinci suna zaune afalo Ya kalli Ansar yafada mashi yanda sukayi da Uncle dinshi. Ansar cike da shagwaba ya kalli Abbanshi yace Abba Aure kuma? Yace emana ko baka sonta ne, yace Abba inasonta mana kowama ai yasan banida matar data wuce iman, amma gaskiya nafiso tagama karatunta agida kafin muyi aure, nima kaga dana gama service dina masters zanwuce kaga fa umar har yatafi damma de shekarunshi sunfi nawa konaje,ma atare zamu gama.
Kuma ni gaskiya idan na auri Iman babu wani karatun dazatayi kawai tagama abunta agida tunda tacemun diploma zatayi kaga sanda zangama itama tagama ko Abba.
Ummanshi tayi dariya tace to sannu sarkin kishi, yanzufa kana maganar shekara 3 kenan 1 service. 2 masters haba Ansar kafin lokacin ai har jika kila nasamu ko. Abbanshi yace aa hajiya karki takurama yarona duk abinda yakeso shi za,ayi mashi, shiyasama ko sanda Aliyu yazomun da maganar nace yabari inji ra,ayinshi. Murmushi tayi tace wato abunma son kaine ko, Ansar yayi dariya yadora kanshi bisa cinyarta yace ha Ummata ai kowa yason kece tagaban goshi....🙊🙊🙊🙊 rufe bakinshi yayi daya kalli Abbanshi yatashi ya ruga dakinshi yana dariya. Abbanshi yace dawo ai nafasa bin shawararka ta Ummanka za,abi.

Kwance take bisa cinyar momynta tana ta kuka saboda bayanin da Aliyu yayi masu akan aurensu. Khadija tace wlh Alhaji narasa yanda akayi Yaya baya daukar duk wata shawara tazaka bashi tunkafin Ansar yagirma yafi daukar shawarar Dr. Usman, bare kuma yanzu danshi yagirma, Aliyu yace kibari nasan matakin dazan dauka.

Urs
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

Kuyi hakuri da wannan bayawa tnx
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@(H,O,N,A)

This page belongs to my belove brother UMMARU SANDA👱🏻👱🏻

60.....65

Aliyu yace Iman kiyi hakuri kinji ina me tabbatar maki bakida mijin daya wuce Ansar, dagowa tayi tana share hawayen idonta tace yanzu dady yaje kasar waje yahadu dawata harya manta dani fa? Khadija tayi murmushi tace Iman Ansar be isa yaki aurenki ba,ki kyaleshi shekara 3 kamar gobe ne agurin Allah kinga kema lokacin kingama karatunki tunda kince diploma zakayi, nima nafison kiwuce karatun ki kara gogewa, kafin kiyi aure dan wayewar secondary ba wayewa bace.
Kuma kinji yace bazakiyi karatu agidanshi ba,murmushi Iman tayi ta tashi tashige daki. Dariya Aliyu yayi yace munkusa shigowa duniya kwanan nan, Yaya ka kuka da kanka.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya inda Iman tasamu gurbin shiga makaranta zatayi diploma 2 years. Ansar gab yake da gama service dinshi inda Abbanshi yafara nema masa admission akasar da Umar yake masters dinshi.
Abdurrashid ne zaune a office din Dr. Usman, yace wlh Dr. Wani abune yake damuna a kamfanina, ribar da ake samu ada yanzu ko rabinta ba,a samu, danayi magana Aliyu yacemun wai ansamu asara ne. Dr. Usman yace abokina tun yaushe maka karika bin diddikin Aliyu kacemun ai kayarda dashi akwai ranar da agabana yakawo maka wasu files yace kasa hannu, ina ganinka ko dubawa bakayi ba kawai kasa mashi hannu. Namaka magana kacemun ai bawani abu bane. Wlh dan Adam ba abun yarda bane. Abdurrashid yayi murmushi. Yace ni kaina nafara zargin Aliyu, sede banaso saboda abin duniya muyi rigima dashi abinda bamu taba yiba, kuma kasan yana bani girma kamar nine na haifeshi, yanzu de abinda nakeso da kai ga wadannan files din ka ajemun agurinka muhimman takadduna ne na kadarorina, original din,dukkansu namayarda sunan Ansar ajiki, kaboyesu agurinka, nafiso seya yakara hankali sannan inbashi su ahannunshi, idan muna raye,idan kuma ta Allah takasance banaso banason kabama kowa su se ranar da Ansar yazama babba.

Dariya Dr. Usman yayi yace wannan jawabi haka abokina kamar me bada wasiyya, kode kafara jiyo kamshin lahirane. Murmushi Abdurrashid yayi. Yace ai dole ne narika fadin abinda ke cikin zuciyata, rashin fada shine yake kawo matsaloli dayawa. Idan baka mantaba nafada maka ana gobe Umma ta zata rasu takirani tafadamun akwai abinda takeson fadamun idan tadawo. Amma se Allah yadauki ranta. Dr. Usman yace hakane Allah de yajikan umma, mukuma muci gaba da addu,a Allah yadoramu akan makiyanmu.

Ayau ne Ansar yasamu admission tare da visa dinshi daze tafi karo karatunshi a london. Sosai Abbanshi yakeyi mashi nasiha akan yaji tsoron Allah kada yabiyema turawa da yan matan banza, kayi abinda ya kaika, kuma akwai Umar yana can, duk da yariga ka tafiya amma idan kamaida hankali tare zaku gama tunda shekarunka 2 ne nashi kuma 3, gashi har yaci 1. Allah yabada sa,a.
Itama Ummanshi nasiha tayi mashi sosai, Aliyu ne yashigo da sallama anan Yayanshi yake fada mashi maganar tafiyar Ansar. Shima nasiha yayi mashi. Abbanshi yace yaje yafara shiri jibi zetafi.

Ansar da Iman ne zaune adakinshi se kuka takeyi yana lallashinta, ganin taki yinshiru ne yasashi matsawa kusa da ita yajawota ya rungumeta yaci gaba da lallashinta. Ai tunda tajita ajikinshi seta kara saka wani sabon kukan na shagwaba, haka tarika mutsu mutsu ajikinshi, tun yana daurewa harbeson lokacin da yakamo fuskarta yahada bakinshi da nata guri guda yana kissing ba. Nan take kukan ya tsaya salo ya canza.
Sosai suke kissing junansu, Ansar yamanta aduniyar da yake, kasancewar wannan ce rana tafarko daya taba kissing wata ,ya mace arayuwarshi, shiko hannun mace yarike dan jindadi betaba yiba, ko Iman iyakarshi da ita yarike mata hannu. Amma ayau dayajishi awata duniya tadaban gaba daya yamanta da kanshi, ita kuwa Iman dama abinda ta dade tana nema agurinshi kenan, dan tasha ganin kawarta Hauwa sunayi ita da saurayinta a makaranta. Ayau data samu dama shiyasa tacigaba da nunama Ansar salo,nadaban, shikuwa gogan naku yafara fita hayyacinshi haryafara kokarin rabata da kayanta, ita ko hartaya shi takeyi.

Karar buga kofa tare da muryar Ummanshi ne yadawo dashi daga duniyar daya fada. Ansar katashi Abbanka yana kira, kasamemu adakinshi. Saurin sakin Iman yayi yana maida numfashi, itako bahaka taso ba, tayi niyar kome zefaru bazata hanashi ba, tunda de shizata aura. Akasalance yace Allah yasomu Umma tazo danayi barna. Murmushi tayi tace aide nizaka,aura ko Yaya? Yace haka ne amma tunda ba,a daura ba babu kyau, tashi kiyi sauri kifita kada umma taganki kinsan zatayi mana fada tunda tahanaki shigarmun daki ko, ina fita kema kifita idan nadawo zankiraki kinji.

Adaki yasamu iyayenshi, yazauna. Suka cigaba da fira kasancewar gobe ne zetafi, sosai Abbanshi yaketa fada mashi abubuwa harda maganar kamfaninshi da aka kusa gama gininshi Ummanshi ma haka tayi ta bashi shawara. Kwanciya yayi bisa cinyar ummanshi yasa kuka, jawoshi Abbanshi yayi yamaidashi bisa cinyarshi yadora kanshi bisa yanata lallashinshi. Su duka kuka sukeyi kamar kada subarshi yatafi😭😭😭😭😭😭 gwanin ban tausayi, nikaina seda na matse yan hawayena. Abisa cinyar Abbanshi yayi bacci, kasa tadashi yayi kara gyara mashi kwanciyama yayi,Fatima takawo mashi pillow shima ya kwanta itama akusa da mijinta taje ta kwanta.

Da safe bayan yayi wanka Ummanshi tagama shirya mashi kayanshi da kyar suka lallabashi yaci abinci, shida Ummanshi kuka kawai sukeyi, shima Abbanshi daurewa kawai yakeyi. Tunda yatashi betaba yina kwana daya batare da iyayenshi ba. Amma gashi yau zetafi har tsawon shekara 2. Kuma Abbanshi yace bayaso yadawo gida harse yagama.

Aliyu ne da iyalanshi suka shigo falon khadija tace Ansar wannan kuka haka kamar ance bazaka dawo ba, Aliyu yace ai rabuwa da iyaye babu dadi, muma haka mukayi. Dariya suka saka,Iman itama idanuwanta duk sunyi ja. Khadija tamika mashi dambun naman data yimashi , Aliyu ma kudi yasaka mashi a aljihunshi. Sosai yayanshi yaji dadin abinda sukayi mashi.

Sallamar su Dr. Usman da matarshi sukaji, bayan sungama gaisawa Dr. Usman yace to tshi mutafi kunwani sashi atsakiya kamr zaku maidashi ciki. Dariya sukayi da haka suka nufi motocinsu domin rakiya.
A canma kuka sukayi tayi lokacin da aka kira Ansar Iman makaleshi tayi tana kuka da kyar aka cireta ajikinshi, Ummanshi yaje ya rungume yana kuka, Dr. Usman ne yakama hannunshi seda yakaishi harbakin jirgin sannan yasakeshi. Shima kanshi seda idanunshi suka kawo ruwa ganin yanda abokinshi yashige mota yana kuka.😭😭😭😭😭😭

Suna gani harjirgin su yadaga✈✈✈✈✈✈✈✈✈✈ sede muce asauka lafiya Ansar.

Urs.
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

Luv u all😍😍😍😍😍😍
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)
Chapter 6 · 0% Book details