← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 23

Sashe 18

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai tsaye gidan su Dr. Usman suka wuce, suna zuwa suka sami kowa yana gida, tun abakin kofa Shatu tafarajin faduwar gaba. Haka tayi masu jagora ita da Umma suka shiga yayin da nabeel ke tsaye awaje.

Sallamar dasukayi ce tasa mutanen falon saurin tashi suna mamakin ganin Shatu. Anan kowa yafara murnar dawowarta.

Bayan sungaisane Shatu tayi masu bayanin Umma tace akwai namijin yana waje, Dr, yace ma Umar yaje yashigo dashi. Yana fita yayi tsaye yana mamakin ganin wanda yake jingine ajikin mota.
Da mamaki suke kallon junansu. Umar yace Barrister Nabeel? Dariya yayi yataho suka tafa da hannu, yace nine de ba mafarki ba. Umar yace ashe zamu kara haduwa? Rabona da kai tunda muka gama makaranta.

Haka suka shiga ciki suna gaisawa, bayan sungama gaisawa anan Umma tayi masu bayanin abinda yafaru da Shatu, ta kuma basu hakuri, hartake sheda masu cikin dake jikinta da kuma abinda likita yace.
Dr. Usman yayi murmushi yace ai babu komai muma muna godiya, Allah yaraba lafiya.
Shatu de shiru tayi hankalinta yakasa kwanciya ganin bataga Ansar ba. Kuma mamaki takeyi ganin su aunty Asma,u agidan, tunda tashigo kuma taga kowa hankalinshi atashe.ga Jimmala,takasa hada ido da ita.

Matsawa tayi kusa da Amina tace Umma ina Yaya Ansar? Shiru tayi mata idonta yana kawo kwalla, kuka Shatu tafarayi tana fadin dama naji ajikina Yaya Ansar yarasu, wani irin kuka tasaka. Dr, yace Shatu kiyi shiru ba mutuwa yayi ba.

Anan yafada masu duk abinda yafaru, amma insha Allah komai zezo da sauki kada kisa kanki cikin damuwa, kowa yasan Ansar baze iya aikata kisaba.
Kuka shatu tarikayi, umma, Nabeel ma seda tayi kuka.

Dr, yace Umar dama kunsan juna ne? Umar yace tare mukayi school of law dashi, sanda natafi yin masters a london shikuma yaje America, acan yayi masters dinshi.
Kace shima lawyer ne, Nabeel yace wlh kuwa Abba, ina aiki a babbar kotu a kaduna, yanzu haka ma ina neman transfer indawo Abuja.
Dr, yace Allah yatemaka, suka ce ameen.

Nabeel yace dama hutu nakeyi, kuma insha Allah nima zan bada tawa gudunmuwar. Sundade suna tattaunawa ,sannan yatshi domin maida Umma gida yace zedawo sucigaba da binciken shida Umar. Sosai sukaji dadin zuwan Nabeel, saboda Umar tausayin Ansar yahanashi tsayawa yayi aiki sosai.

Da dare suna zaune afalo Dr, yace ma shatu tashirya amsa tambayoyin da za,ayi mata akotu dan za,a kirata tafadi abubuwan data sani. Yace kada kiji tsoro, nasan wannan shine shigarki kotu na farko, inaso kinutsu babu wanda ze maki wani abu.
Tace insha Allah zanyi duk abinda nasan zefitar da yaya Ansar,
Dr. Yace Allah yashige mana gaba, sukace ameen.

Urs
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
[7/2, 10:39 AM] YAYA HAYAT: 🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@( H,O,N,A)

130.....135

Haka suka cigaba da zaman jimami, gidan rasuwa kuwa kowa ya watse tunda akayi 3, Lami ce kadai tayi saura agidan diyarta, se Iman wadda tunda abun yafaru tadawo part dinsu dazama. Asma,u kuma tana gidan Dr. Usman dan tace bazata iya zama agidan su khadija ba.

Farida da mijinta suna part din Ansar dan se angama shari,a zasu tafi, Mahaifan Umman Ansar sun koma sunce se ranar da za,ayi shari,a takarshe zasu dawo.

Lami ce dasu khadija zaune afalo, khadija tace ma Iman kulle mana kofar, duk wanda ze shigo ya kwan kwasa saboda yan gulma.
Lami tace ayanzu hankalina yafara kwanciya dan gab muke da shiga sabuwar rayuwa, saboda haka da anyanke ma Ansar hukunci kema Iman wannan cikin naki dawuri zaki haifeshi, dama Ansar ne kadai yasan watannin cikin, bazamu zauna ace se kin haihu sannan araba gado, nasan dole za,a tambayeki watan cikin nawa. Kice yashiga watan haihuwarshi, tunda kowa yaga cikin yayi girma.

Khadija tace nasan rataye Ansar za,ayi ko kuma aharbeshi, karshen me zuciya kenan, gashi nan ta kaishi tabaroshi.
Kuka Iman tasa, kallonta kawai suka tsaya sunayi, Lami tace lafiyarki ke kuma kika samana kuka alokacin dayakamata kiyi murna.

Iman tace shikenan momy yanzu kashe Yaya Ansar za,ayi? Baki suka rike suna mamakin abinda ta fada.
Lami tace yanzu Iman har Ansar yafi ubanki? Ace mutum yakashe maka mahaifi sannan karika tausayinshi.
Iman tace bahaka bane wlh kawai tausayi yabani, kalli fa duk yanda suka jimashi ciwo. Khadija tace lallai Iman, wlh kina so insaba maki akan wannan maganar, idan ke nakisan zagin uba ba ni nasan dadin miji, kinfi kowa sanin burin mu nason ci dukiyar mijinki, amma yanzu kikawo mana zancan banza.

Idan tausayinsa kikeyi kibishi idan yaso muse muci dukiyar.

Iman tagoge idonta tace haba momy kema kinsan inason inganni cikin daula, kuma bawai. Nace kada akashe shi bane kawai naji tausanshi ne.
Amma nima inason inga nashigo gari mana.
Dariya suka lami tace ashede kema kinason kudi. Yanzune zannuna ma Farida amfanin haihuwar mace, dan wlh daga lokacin da aka raba gado daga ranar munrabu, kodayake ma ai Abuja zandawo.

Tafe suke zasu gurin Ansar, Shatu gani take kamar ba,a sauri, Ansar dinta kawai takeson gani. Suna shiga aka bude masu dakin dayake, dasauri Shatu tanufi gurinshi tana kuka, jikinshi tafada tanacigaba da kuka. Dayake daga ita se su Umar da Nabeel suka je.
Dagashi har ita kuka sukeyi, seda suka sa su Umar kuka, Ansar yadago Shatu yana goge mata hawaye bakinsu yahade, yana kara rungumeta, gabadaya yamanta a inda yake, Nabeel ne yaja Umar suka fita, seda umar yayi murmushi.

Sundade ahaka, ganin yana so yawuce gona da iri ne yasa Shatu tayi saurin kwace jikinta, shikanshi dan sandan dayake bakin kofar seda ya matsa yabasu guri.
Kallonta kawai Ansar yake, tunda abun yafaru se yanzu yaji wata natsuwa tana saukar mashi, hada murmushin jindadi yakeyi.

Kamota yayi ya rungumeta, ahankali yace dama zasu kulle mu na awa 1 wlh, murmushi tayi ta tura fuskarta akirjinshi. Wlh Shatuna banine na kashe shi ba, kawai de sharri akamun, kuma akayi amfani da abinda yahada mu.

Bakinshi ta rufe da hannunta, tace nasani bazaka iya kashe kiyashi ba bare mutum, kayi hakuri insha Allah muna tare da nasara, wlh dama zasu barni anan dana tayaka zama.

Murmushi yayi yace bazanso ace matata abin alfaharina tazauna a cell ba. Kiyi hakuri komai zewuce, idan kuma sunci nasara akanmu anyankemun..... saurin rufe bakinshi tayi tana kuka.
Umar ne da Nabeel suka shigo, Umar yace abokina yau kuma antuna amarci ne? To kayi mata ahankali dan ba ita kadai bace.
Dasauri Ansar yadago Shatu wadda ta kulle idonta dan kunya, seyanzu ta tuna tare suke da mutane.

Ansar yace da gaske Shatu kina dauke da ajiyata? Kankameta yayi yana dariya wadda rabon dayayita tunkafin wannan abun yafaru, shikanshi Umar yaji dadin ganin dan uwanshi yau cikin farin ciki.

Nabeel yace yakamata muyi mutafi kunga suna ganin mutuncinmu. Anan Umar yagabatar da Nabeel agurin Ansar, suka gaisa. Nabeel ykara yima Ansar yan tambayoyi, bayan sungama sukayi mashi sallama Shatu se kuka takeyi shima yana tayata.

Suna hanyarsu ta komawa ne, Umar yace agaskiya Nabeel inajin tsoron shiga kotu, saboda bamuda wasu hujjoji masu kwari, Nabeel yace hakane gaskiya, nima ina tsoron hakan, domin duk hujjar dasuka bayar tafi tamu karfi sosai.

Umar kuka yasaka, yana fadinwlh banida amfani Nabeel tunda harnakasa tsayama Abokina kuma dan Uwa na, Shatu cikin kuka tace dan Allah kada kubari akashemun Yaya Ansar.

Nabeel yace insha Allahu zamu sami nasara, inaso kifadamun abubuwan dakika sani lokacin dakina aiki agidan Aliyu.

Anan Shatu tafada mashi duk irin abubuwan data keji suna fada idan tana gida. Daga karshe tace ana saura kwana daya inyi tafiya H. Lami tazo gidan, suna zaune afalo suna magana, nikuma alokacin nashiga bandaki, ina fitowa. Naji khadija tana fadin semun nuna ma Farida haihuwar mace ma tanada rana.

Iyakar abinda naji kenan. Nabeel yayi murmushi yace dama babu jituwa tsakanin Farida da Lamin ne? Shatu tace nide nasan kawarta ce amma bansan meyahadasu ba. Nabeel yace yanzu iyakar shedar dakika sani kenan? Tace E. Kai yagirgiza yace gaskiya wannan bazata iya zama sheda akotu ba. Koda ace mutum daya ne yaga wanda yakashe Aliyu shedarshi bazata wadatar ba, bare kuma wannan, gaba daya shedar damuke da ita iyakarta baki, sukuma tasu afili take, ita kuma kotu bata amfani da abinda bata gani ba. Agaskiya semun dage da addu,a Allah yashige mana gaba.

Washe gari da safe Umar da Nabeel da Dr. Usman suka fita zasuje office, suna tafiya suna kara tattaunawa sunzo dede. Danger suka tsaya sunajiran abasu hannu.
Ta bayan motar inda Dr, yake zaune wani yazo yana bara, sauke glass Dr, yayi yamika mashi sadaka.

Ne anshi kudin ba yatsaya yana kallon Dr. Lafiya de malam ko kudin sunmaka kadan ne? Kwalla mutumin yagoge yace dan Allah malam kaine abokin Alhaji Abdurrashid yayan Aliyu ko? Dr. Usman yace E nine, yace idan bazaka damuba akwai maganar dazan fada maka.
Bude mashi mota Dr, yayi yashigo suka wuce.

Kuyi hakuri da wannan. Luv u all😘😘😘

Urs
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/2, 10:39 AM] YAYA HAYAT: 🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ (H,O,N,A)

Thanks all my friends for u,r concern. Am feeling better😘😘😘

135.....136

Bayan sunje office din Umar,Dr. Usman ya kalli mutumin dasuka taho dashi yace bawan Allah ina sauraronka.
Hawayen dasuka zubo mashi ne ya goge yace, nide sunana Fafilo, kuma ni yaron Aliyu ne kanin marigayi abokinka, nasanka ne alokacin da aka kawo abokinka da matarshi asibiti sunyi hadari.

Ni kuma alokacin nabiyo sahunsu kamar yanda aka umarce ni, anan naganka kana kuka, hakan yasa nagane kai abokinshi ne.
Dr, yace Fafilo duk kasaka mu acikin duhu,me kake so kafada ne?
Anan fafilo yabasu labarin duk irin aikin da Aliyu yakesa shi yana yi mashi, har kudin da aka sace ma Abdurrashid. Yace daga nashiga matsala ankwantar da mamana asibiti naje nasameshi shida wani abokin shi alokacin suna shirya yanda zasu kashe Ansar.
Bayan mungaisa ne nafada mashi abinda ketafe dani, rufe ido yayi ya munrashin mutunci kuma yakoreni, yace idan har nabari yakara ganina acikin garin nan seya sa ankasheni.
Chapter 18 · 0% Book details