Sashe 5
Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune suke gaban boka👹👹👹👹Lami tace kawata na rako Allah gafarta boka, munaso akashe mana kishiyarta ne. Wata irin dariya yayi yace ciwo kikeso asa mata ko kuma guba zan baki kisa mata taci ta mutu? Farida tace nafison ayimata kisan da babu wanda zetaba zargina akan mutuwarta. Kasa yabuga sannan ya kalleta yace kishiyarki zatayi tafiya gobe ko? E e hakane. Kutashi kutafi zamu tura mata bakaken aljanu su kasheta ahanyarta ta tafiya goben. Farida tace inason duk wata soyayya da mijina yake mata tadawo kaina kobayan mutuwarta. Sona ya lunka nata, magani yabata yace tazuba mashi a abinci komai zeyi dede. Kudi masu yawa suka aje mashi suka tafi.
H. Farida tace gida yakusa zama,nawa, Allah ma yasa tare da wannan yarinyar Saratu zata tafi idan yaso su mutu tare. Kinsan Alhaji da kawaici kobayan ta mutu yana iya hana uwarta ta dauketa tunda dama yan uwa ne. Nafison dagani se dangina acikin gidanan.
Lami tace kinga yanzu Khadija ta kusa haihuwa, farida. Tace ai wlh saura Wannan shegen dan nata shima zamuzo kanshi ne. Naga dukiyarshi se kara yawa takeyi, yamaida mun yaro kamar masinja ni wlh Lami imbadan kincemun inbar Aliyu yacigaba da aikin a kamfaninshi ba da tuni nasa yabar masa abunsa,. Lami tayi murmushi tace kawata haryanzu baki gama gogewa da duniya ba, wata rana da bakinki zaki fadamun. Idan kika ga Aliyu da khadija acikin daula, kinsan aduniya duk abind mutum yasamu seda yayi hakuri sannan yasa meshi
Abdurrashid ne kwance bisa cinyar Fatima yana waya da Ummanshi. Tace Kanajina ko gobe idan Allah ya kaimu zanje katsina bikin diyar kawata akeyi amma kwana daya zanyi idan nadawo inason ganinka akwai maganar dazamuyi, yace to Umma Allah yadawo dake lfy. Ina Fatima? Yace gatanan, bata wayar to bayan sungama gaisawa tace Fatima ina fatan bakyayin wasa da addu,a ko, tace e Umma munayi, tace yauwa fatima ki kara hakuri akan wanda kikeyi kinji, tace to, ina Ansar fa, yana islamiyya to idan yadawo agaidamunshi. Haka sukayi sallam Abdurrashid duk bayajin dadi.
Washe gari da safe driver daze kaita yazo daukarta, tare suka fito da Saratu zata biya takaita gidansu saboda islamiyya. Alhaji Audu yace ni wlh Mryam duk banason tafiyar nan, murmushi tayi tace Alhaji gobe nefa zandawo kuma baga Farida nan ba. Jawota yayi jikinshi yana murmushi yace haka ne amma ai kowa da nashi bangaren🙊🙊🙊🙊 nace tofa ashe soyayya de bata tsufa.
Tace bara naje nayima. farida sallama, tana shiga ta isketa itada kawarta lami ga dukkan alamu ana ta kwana. Cikin sakin fuska Farida tace Hajiya harkinfito tace e wlh yanzu zantafi, lekowama nayi inmaki sallama. Farida tace tomuje inrakaki. Lami tace to. H. Maryam saduwar alkhairi, murmushi tayi tace Ameen. Hakanan Lami tafice mata arai, jiya tazo shigowa falon Farida taji suna wata magana kuma akan danta taji suna maganar duk dabaduka zancen tajiba. Amma ta fahimci abinda suke nufi. Shiyasama tace tana son ganin danta idan ta dawo.
Gidan Kanwarta Asma,u suka wuce, Asma,u tace wai Aunty kina nufin bada saratu zakije ba? Tace wlh kuwa naga yau akwai makaranta gobema haka kada inyimata asarar karatu. Nikuma bazan iya barinta gurin Farida ba. Asma,u tace nifa kyauta nabaki saratu bawai aroba, kawai kuyi tafiyarku ai fashin kwana. 2 ne kawai, ke saratu shiga kidauko kayanki kutafi. Maryam takalli kanwarta tace wlh Asma,u akwai abinda ke damuna akan Farida da kawarta ne jiya naji suna magana akan Abdurrashid, amma nayi mashi waya nace idan nadawo yazo semu zonan infada maku maganar. Asma,u tace bakomai Aunty kiyi hkr Allah yafisu sekun dawo.
Haka suka yi sallama suka tafi, saratu ce agaba ita kuma tana baya. Sunkai dede wani gari ahanyar katsina mesuna kurfi wata irin guguwa ta rufemasu gaban motarsu, nan take motar takwacema driver din tayi cikin gonaki, tana zuwa tabugi. Wani dutse takama da wuta.
Urs
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)
This page is for all my Friends at RAZ and House of Novella, tnx for ur concern😍😍😍
50.......55
Dakyar mutane suka samu suka kashe wutar motar,sede gaba dayansu sun mutu acikin su Fuskar H. Maryam ce kawai ake ganewa sosai, jakar H. Maryam wadda tunsadda motar tafara wuncilawa cikin gonakin tafado waje, ita wani daga cikin mutanen yadauko, aciki suka sami wayarta. Daukarsu akayi aka kaisu asibitin cikin gari.
Suna zuwa asibitin wanda yasamu wayar yaduba last call dinta yaduba, ganin no Abdurrashid yayi hakan yasa yakira yasheda masa mewayar tasamu hadari, kwatancen garin yayi mashi yafada masa suna general hospital. Hankalin Abdurrashid bakarmin tashi yayi ba, nan yakira Abbanshi yafada mashi. Sosai shima hankalinshi yatashi, dan danan yakira dan uwanshi yaxo yatuka motar suka tafi.
Aliyu yakira yafada mashi su shirya zasu tafi safana yanzu, waya yayi yace asama masu jirgi, babu bata lokaci suka shirya, abokinshi yakira yafada mawa Dr. Usman, hakuri yayi ta bashi yace mashi zasu taho gobe.
Lokacin dasuka je asibitin aka nuna masu gawarwakin Alhaji tunda ya kalli fuskar Maryam ana yayi kamr ze fadi kaninshi ne yayi saurin rikoshi yazaunar dashi. Kuka sosai yakeyi kamar karamin yaro, bayan likita yazo ne aka gama komai aka basu gawarwakin saboda da sanarya likitan yace abasu ambulance ta kai masu gawar gida.
Tunkafin suje yakira Asma,u yace taje gida ashirya komai gasunan zuwa, kuma tafada ma yan uwa. Abokinshi Alhaji Abbati yakira da diyarshi Halima duk yafada masu.
Lokacin da su Abdurrashid suka iso gidan yacika da mutane dan har angama shiryasu sallah kadai za,ayi masu Alhaji yace ajirasu Abdurrashid suzo. Da kyar Abdurrashid yashiga cikin gidan. Kuka kawai yakeyi, yana zuwa Yanufi gawar Ummanshi budewar dazeyi yasaki wani irin kara yafadi agurin yana kuka kamar mace. Asma,u ce tazo tayi saurin rikeshi tana kuka, Su Aliyu da Khadija da Fatima suma duk kuka sukeyi, saboda Aliyu besan. momynshi bace tasa aka kashe Umman yayanshi ba.
Su hajiya Farida da Lami kuwa suma suna gefe, idan kaga yanda Farida take kuka seka dauka na gaske ne.
Haka aka daukesu aka fita dasu danyi masu sallah ana gamawa akatafi dasu gidansu na gaskiya😭😭😭😭😭.
Kowa kuka yakeyi bayan sun dawo aka zauna zaman karbar gaisuwa, Abdurrashid yakoma gefe yazauna kuka kawai yakeyi. Aliyu ne yakoma kusa dashi yana lallashin shi.
Washe gari da safe Abdurrashid yana zaune adakinshi na da Asma,u tashigo da abinci dakyar tasamu yasha ruwan tea din, suna nan tana kara bashi hakuri su Dr. Usman suka zo, ana Dr. Yaci gaba da bashi hkr.
Yan uwa da abokan arxiki duk sunzo masu gaisuwa harda yan gurin aikinshi duk sunzo. Haka aka cigaba da zaman gaisuwa, har akayi 7.
Alhaji Audu ne yatara iyalenshi a falo yakara yimasu nasiha da ban hakuri akan rashin dasukayi. Sannan yacema su Aliyu su shirya gobe su koma tunda anyi sadakar 7, haka kowa yatashi cike da dmwa bakamr Alhaji Audu wanda yaji mutuwar tadawo mashi sabuwa.
Adaki Asma,u tasamu Abdurrashid, tace mashi ana gobe Aunty maryam zatayi tafiya tacemun kunyi waya ko? Yace mata e tace idan tadawo inzo akwai maganar dazamuyi, yafada yana goge kwalla,
Tace hakane nima ranar daxata tafi tabiyo gidana ta aje saratu amma dayake itama ajalinta yakirata nace sutafi tare. Nima tafada mun tanada damuwa. Kuma ba akan kowa bane se kishiyarta Farida taji suna wata magana da kawarta Lami, kuma akanka ne, shine takeson tafada mana abinda taji idan tadawo. Amma dayake. Lokacinta yayi bata samu damar fadaba Allah yadauke abunshi.
Saboda haka abinda nakeso da kai kacigaba da addu,a kasan kanada makiya sosai, yace insha Allah Aunty zanyi yanda kika ce. Allah sarki Umma ashe shiyasa duk sanda mukayi waya. Maganarta daya mudage da addu,a akanmu da Ansar. Bakomai insha Allahu dana koma zansa ayi saukar Qur,ani kuma muma zamu cigaba dayi. Haka suka cigaba da tattaunawa.
Farida tace wlh Lami seyanzu naji dadi araina da wannan bakar matar tabar gidan, yanzu zasama Alhaji Maganin nan a abinci yaci shima kona samu saukin juyashi dannaga haryanzu yaki sakewa. Dariya Lami tayi tace kina shagalinki Kawata, wlh saura kisamu duniya ki manta dani, tace haba wace ni.
Bayan dawowarsu ne da kwana 7 Khadija ta haifi diya mace, kowa yayi murna ranar suna aka kara maida mata sunan Farida( IMAN).
Haka rayuwa tacigaba da tafiya Ansar yakara girma sosai yake maida hankalinshi akaratunshi,Abdurrashid Arziki sekara hawa yakeyi, yana kokarin ganin ya kyauta tama Aliyu da matarshi, idan mota ze sake tare yake sake masu. Kudin dayake bashi shida matarshi sunada yawa yanda yake bama matarshi duk wata haka yake bama khadija, tunda aka haifi Iman yace yadauke ma Aliyu komai na rayuwarta shine zeyi. Amma yarasa me Aliyu yakeyi da kudi, haryanzu yakasa tara kudi shima yatsaya da kafafuwanshi.
Hatta . H. Farida yamayar da ita tamkar ummanshi itama duk wata yana tura mata kudi Amma su akullum neman hanyar dazasu ga bayansu sukeyi
Abdurrashid kullum ya kwanta bacci seyayi mafarki da ummanshi tanamasa tuni da addu,a. Auntynshi Asma,u yakira yafada mata Asma,u tace nifa aganina ka kara zuba ido akan Aliyu nibanyarda dashi da matarshi ba. Murmushi yayi yace haba Aunty ni wlh nayarda da Aliyu, yana sona sosai baze iya cutar dani ba, kawai de kinsan mafarki yanda yake. Zandage da addu,a kamar yanda umma tace, Asma,u azuciyarta tace nasan dama bazaka yarda da duk wani abu dazan fada maka akan Aliyu ba, saboda sungama siye zuciyarka da makircinsu. Afili kuma tace shikenan Allah yayi mana jagora, amma kome yake faruwa kasanr dani yace to, sallama yayi mata.
Urs NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
( Nabelert Lady)
@ (H,O,N,A)
55.......60
Life move on