← Book details Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 23

Sashe 19

Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanin halinshi yasa nakoma kauyen mu dazama, haka mamana tarasu, tundaga lokacin nashiga matsala ga ciwo babu kudin magani narasa inda zansa raina, wata rana nafito bakin titi mota ta kadeni, haka nayita jinya karayar danayi akafa batasamun kulawa hakan yasa kafar ta rube danaje asibiti sede aka yankemun.
Nashiga tashin hankali ga tunanin bayin Allah dana cuta,hakan yasa nayanke shawara inzo innemi yafiyar Ansar kuma intona ma Aliyu asiri, jiya nashigo garin da dare, shine yau nafito bara insamu abinda zanci sannan inje innemi Ansar, segashi Allah yahada ni daku.

Mamaki sosai yakamasu,kowa yarasa abinda ze fada. Nabeel ne yayi karfin halin fadin, tunda kariga da kadauki fansa akan Aliyu ai base ka nemi yafiyar Ansar ba. Fafilo ya kalleshi cikin rashin fahimta yace bangane me kake nufi ba. Nabeel yayi murmushi yace duk abinda kafada gashinan ahannuna, kuma ba Audio nayi ba vedio ne, kaga idan mukaje kotu seka fada mana yanda akayi karataya ma Ansar laifin kisan Aliyu.

Cike da mamaki Fafilo ya kalli Nabeel, yace dan Allah kafadamun abinda kake nufi, wlh bansan komai akan abinda kake fada ba.

Umar ya gyara zama, anan. Yafada ma Fafilo duk abinda yake faruwa. Nabeel yace Fafilo dan Allah kada kabamu wahala kafada mana kaine ka kashe Aliyu? Kasande ko baka fada ba, idan muka kaika kotu akaji abinda kayi dole se anyanke maka,hukuncin kisa, gara kafada mana gsky.

Kuka fafilo yakeyi sosai, Dr, yace kayi hakuri bazamu cutar da kai ba, domin muna cikin tashin hankali, munrasa mafita segashi Allah yakawo mana kai, katemaka kafada mana gaskiya.
Fafilo yace wlh bana tsoron ayankemun hukuncin kisa, idan har hakan zesa Allah ya yafemun laifin dana yimasa, wannan shine babban dalilin dayasani nashigo domin in kwance duk wani kulli da mukayi,segashi kuna fadamun wanda yayi duk wannan laifin ya mutu.

Wlh tallahi kunji na rantse maku banida masaniya akan mutuwar Aliyu,wannan abinda nafada maku shine kadai abinda nasan na aikata, kuma ashirye nake inje kotu domin infadi komai danasani, kaiconka Aliyu, naso ace yana raye domin in tona mashi asirin a bainar jama,a kowa yasan mugayen halayenshi, gakiya kayi mutuwar wulakanci.

Shiru ne yabiyo bayan maganar da Fafilo yayi, Dr, yanisa yace Innalillahi wainna ilaihirraji,un. Haryanzu bamu sami shadar dazata hana ayanke ma Ansar hukunci ba, duk da munsami makami hakan bazesa alkali yaki yankema Ansar hukunci ba, tunda babu shari,ar data ce wani yadauki doka da hannunshi.

Nabeel yace ina ganin mutafi dashi gida yazauna acan har muje kotu tunda de yace ashirye yake daya fadi gaskiya, insha Allah kafin akoma kotu zamu sami wata shedar, haka suka tafi da Fafilo suna mejin dadi da godema Allah akan wannan nasara dasuka fara samu.

H. Farida ce dasu Lami afalo zaune, Farida tace wlh nakosa ayankema wancan shegen yaron hukunci ko zamu samu dukiya, babu rabon Aliyu yaci wannan dukiyar bawan Allah duk irin burin dayaci akanta sede ni inci mashi, gaskiya Lami kawance dake akwai dadi, shiyasa akullum nake kara sonki, kinga yanzu semu ci dukiyarmu hankali kwance, tunda ,ya,ya na da jikana zasu samu kaso me tsoko. Allah de yasa Iman ta haiho mana namiji yanda zamu cinye dukiyar duka.

Wani murmushin rainin wayo Lami tayi ta dubi. Su Khadija, sannan tace, Farida kenan, seyanzu nake kara godema Allah daya bani diya mace, kinsan hausawa suna cewa daka haifi shugaban kasa gara ka haifa mashi mata. Dole ne inyi alfahari dasamun diya mace, tunda gashi ta dalilinta zanfita daga cikin talauci, inbar garin kaka da kakanni, indawo cikin birni, Farida tace Lami bangane abinda kike nufi ba,Lami tace babu komai Farida kawaide kinsan da diyata da jikata sun sami abun duniya tunda ba miji gare ni ba, ai dole inyi yawona ko? Shiru. Farida tayi tana kallonsu suna dariya, cike da bacin rai ta tashi tanufi part din dasuke zaune. Lami tace bakiga komai ba ma, wlh sekinyi kuka inde nice, ai dama nafada maki ba amun haka.

Zaune suke afalon Amina, Shatu tana kwance bisa kujera jimmala kuma tana kitchen. Asma,u tace Shatu hakuri zakiyi kije kiyima Khadija gaisuwa kinga kince mata kwana 1 zakiyi kada taga kindade tadauka ko kindena aikin ne.
Goge idonta tayi tace Aunty yanzu aikina beda wani amfani agidan, dama saboda Yaya Ansar nakeyinshi, gashi kuma yanzu yana kulle ai kinga babu amfanin inci gaba.

A,a Shatu yanzu ne ma yakamata kije kiyi aiki, Dr. Usman yafada wanda shigowarsu kenan yaji suna maganar, bayan sun zauna ne, yacigaba dacewa, kila ta dalilin zuwanki musami wani abun, duk da gobe ne za,a shiga kotu, amma wlh jikina yana bani akwai wani munafunci da matan gidan can sukeyi,tunda fafilo yace mun hada khadija asa hannun gurin kisan abokina, ko jiya dana gama sallah na kwanta nayi mafarki me cike da alkhairi sede rashin sanin fassarar mafarki yasa kawai nayi addu,ar zabin alkhairi daga Allah.

Asma,u tace bangane Khadija tana da sa hannu akisan Abdurrashid ba?
Anan Dr, yafada masu duk abinda Fafilo yafada masu, yace ma Umar yashigo dashi, kuka sosai sukayi dasukaji Aliyu ne sanadiyar mutuwar Yayanshi.

Asma,u tace duniya abin tsoro ce, inama ace Aliyu be mutu ba, wlh dayaga wulakanci tun aduniya, aini ko mamanshi wlh banyarda da ita ba, amma babu komai akwai Allah.
Waya tadauko zata kira Abban Safana, Dr, yayi saurin hanata, yace. Kada kisa shock yakamashi dama yana cikin tashin hankali, kibarshi idan aka gama komai daga baya zeji.

Haka sukayita jimamin al,amarin, Umar yashigar da Fafilo wani daki awaje ya kaimashi abinci da ruwa. Da kyar suka shawo kan Shatu ta tashi tasake kaya zuwa irin kayan datake sawa suka tafi tare da Amina.
Afalo suka samesu harda kawar khadija Bilkisu suna zaune tare da karamin danta yana zaune yanata wasa da waya. Bayan sun gaisa ne, Shatu ta kalli Khadija tace Aunty Ya hakuri , ashe Alhaji yarasu? Khadija tace wlh kuwa Shatu aranar da kika tafi da dare dan yayanshi yazo ya kasheshi. Wasu zafafan hawayene suka zubo ma shatu jin abinda khadija tace. Khadija tace kiyi hkr shima ai gobe za,a kashe shi, fashewa tayi da kuka.
Bilkisu tace Allah sarki daga gani de Uban gidanki yana yimata abin alheri, kalli yanda take kuka. Khadija tace aidole kinsan Aliyu akwai son kyautata ma mutane. Tace yajikin Baffan naki? Tace yaji sauki jikinne ma yahanani dawowa dawuri. Khadija tace wayyo Allah yakara sauki, suka ce Ameen. Sun dade kafin sukayi masu sallama zasu tafi, Shatu tace gobe zanzo in Allah yakaimu. Khadija tace babu damuwa amma kizo dawuri sbd. Zamu fita zuwa kotu da safe. Har sun kai bakin kofa yaron Bilkisu yace Momy kamomun camera awayrki indauki hoto, bilkisu tace oh kai boy kaide ace bakada aiki sedaukar hoto.

Cak Shatu ta tsaya jin anyi maganar abun daukar hoto. Saurin juyawa tayi. Tana kallon labulen dake jikin falon. Wani murmushi naga tayi sannan tajuya suka fita.

Urs,
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[7/2, 10:39 AM] YAYA HAYAT: 🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@ ( H,O,N,A)

Nayi mistake ana jiya nasa 135.....136 to 140 ne. Inafatan za,a gane. Tnx all my lovly family and friends😘😘.

140.....145

Shatu ce tsaye adaki takasa zaune takasa tsaye jiaran dawowar su Umar kawai takeyi, takira no shi bata shiga. Har akayi Isha,i basu dawo ba, su kuwa suna can hankalinsu atashe domin gobe ne shiga kotu.

Se karfe 9 suka dawo jiki babu kwari, bayan sunci abinci Umar yakalli Dadynshi hawaye suna fita daga idonshi yace, dady shikenan gobe za,a yanke ma Ansar hukunci, munkasa samun hujjar dazamu kareshi. Kuka me karfi ya kwace mashi, Nabeel ya matso kusa dashi yana lallashin shi.

Dr, shima kukan yakeyi, yace Allah gamu gareka, Allah kakawo mana hanya mafi sauki domin ceton bawanka daga hukuncin abinda beyiba. Turo kofar da,akayi dasauri yasa suka maida hankalinsu akallon kofar.
Shatu ce tashigo tana murna tana fadin Yaya Umar wlh natuno, ai dasauri Umar yakaraso gabanta, besan lokacin daya kamota yazaunar da ita bisa kujera shi kuma yazauna akasa kusa da kafaunta, kamar meneman tuba.

Dr, cike da doki yace Shatu mekika tuno fada mana,dan Allah domin yanzu bamuda sauran karfin guiwa.

Shatu tace, lokacin ina gida kafin muyi aure Yaya Ansar yataba bani wata camera wadda ake daukar hoto, tunda naganshi yadaukeni awayarshi nace masa nima inaso in rika daukarshi idan yatafi se narika kallo, hakan yasa yakawomun camera har yakoyamun yanda ake amfani da ita, tun bayan munyi aure bankara dauko taba.

Aranar danaji firan su Aunty lokacin ina toilet banji abinda suka fada daga farko ba, sede karshen abinda Aunty tafada, hakan yasa nashiga damuwa dan ganine nake ba maganar H. Farida danaji sunayi kadai sukayi ba, hankalina yatashi narasa mesuke kullawa.

Awashe garin ranar tafiya takamani zuwa gida dubo jikin Baffa, hankalina yatashi ganin zanyi kwana daya bansan mezasu iya fada ba wanda bazanji ba tunda bananan, ina dauko kayana dazanyi tafiya dasu kawai naci karo da Camera ta, cike da farinciki nadauketa.

Hakan yasa nayi sammako tunda safe naje gidan,bayan mungaisa tace inshiga inyi aikina tunda unguwa zantafi, idan tagama zatayi sauran, ciki takoma tace zata wanke bandaki.
Tana shiga nayi saurin jawo teburin dake falo natakashi na seta Camera abayan labule ta yanda babu wanda ze ganta, seda na tabbata tafara aiki sannan naje nayi aikina, kwata kwata namanta dana aje ta sejiya da Umma tace muje inmasu gaisuwa harzamu fita naji wani yaro yana maganar akunna mashi Camera yadauki hoto, alokacin na tuna na ajeta. Saurin duba inda na ajeta nayi, abun mamaki naganta tana gurin.

Gaba dayansu hamdala sukayi, suna cike da farin ciki. Dr, yace lallai kam duk wanda ya aikata wannan aiki camera ta daukeshi, saboda Afalo khadija tace ankashe Aliyu abisa doguwar kujera. Allah mungode maka, lallai Shatu kin cika yar halak, babu abinda zamuce maki sede godiya.
Hakika shigowarki rayuwarmu babbar nasara ce da alkairi, Allah yabiyaki da mafificin alkhairinsa, kowa yace ameen. Dr, yace dole yau muyi sallar godiya ga ubangijinmu dan shine yaji kanmu har yakawo mana wannan hanya mafi sauki.
Chapter 19 · 0% Book details