Sashe 14
Shatu Diyar Maharbi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune suke saman wani dutse gefen rafi. Hannunshi yasa acikin aljihu yaciro wata karamar camera, kunnata yayi yaseta Shatu yana daukar ta. Murmushi tayi, tace lah! Yaya Ansar ka kawomun abunda zan rika daukar ka? Dariya yayi ganin yanda take murna, Matso ingwada maki yanda ake amfani da ita.
Zama tayi akusa dashi yana koya mata, dan danan, ta iya dama Shatu akwai kokari, amsa tayi taje jikin wata bishiya ta makala ta sannan tadawo tazauna akusa dashi. Kallon mamaki yabita dashi, yace meyasa bazaki riketa ahannunki kirika daukata ba? Murmushi tayi tace idan ahannuna ne kai kadai zanrika dauka, amma idan na ajeta acan zata rika daukar mu gaba daya. Kaga idan katafi se inrika kallon mu ko? Murmushi yayi yace Shatu kina da kwakwalwa, inama ace kinyi karatu menisa da mutane, sunkaru dake sosai. Shatu tace ai wanda nayi ya isheni nafiso incigaba da karatun addini shinafi so, amma na boko gara inzauna inkula da kai. Yace Allah Shatu nah? 🙈 saurin rufe fuska tayi tana murmushi. Haka suka cigaba da firansu sannan Shatu taciro cemeran suka tafi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya suna ta shirye shiryen biki, yayin da wasu kuma suketa kulla munafunci.
Har katin daurin aure an buga, sede na Umar da Jimmala kawai suka buga domin boye na Ansar sukeyi.
Iman yanzu takara kwantar da hankalinta, ganin haryanzu Ansar beyi mata maganar mace. Koda yakawo mata I,V din Umar masifa yayi tayi wai shi dakyar ze iya zuwa daurin aure kauye, da kyar Iman tabashi hkr ya yarda zeje, amma yace mata baze tsaya daukar amarya ba. Sosai taji dadin furucinshi, shikuwa dadi yaji ganin tayarda da maganarshi, se kuma tabashi tausayi ganin yanda take nuna kishin shi. Sede kuma yanda yakeson Shatu baze iya hakura ba. Duk yawan tafiyar dayakeyi baya damunta, acewarta tayarda da aikin boka, shikuwa akoda yaushe shida Umar suna hanyar garinsu Shatu.
Inne tadage tanata cikin gyaran amare da irin kayan gyaransu na fulani. Ana saura kwana daya daurin aurensu Dr. Usman yatafi safana domin amsa kiran da Abba yakeyi mashi.
Zaune suke afalonshi, Abban hakalli Dr, yace dalilin dayasa nakiraka. Shine inaso kamar yanda kace aboye wannan aure na Ansar nima nayi tunani sosai nafara ganin alamomi. Domin ayanzu Allah yafara haskamun abubuwan dasuka shigemun duhu, nasaka malamai suyi ta addu,a akan al,amarin family na, insha Allahu za,a samu nasara.
Shima Aliyu ina sane da abinda yakeyi agame da kamfanin Ansar dana bashi riko, aboye nasa arika bincikarmun shi, kuma inasamun bayanai masu kyau. Amma kamar yanda kace abar maganar se ankara samun hujja to hakan za,ayi kacigaba da duk wani shiri naka, nayarda da kai kuma nasan kobanda rai kai me iya rikemun family na ne, Allah yayi mana jagora. Gobe insha Allah zamu taho nida Alhaji Abbati daurin auren, fatana kada Aliyu yace zeje daurin auren gidanka. Godiya Dr. Usman yayi mashi yakawo kudi yabashi sannan yawuce gidan Asma,u suka gaisa itama takara bashi shawara, daga can yawuce Abuja.
Dr. Usman ne tsaye shida Aliyu, bayan sungama gaisawa yabashi I,v na daurin auren Umar, fatan alkhairi yayi mashi, sannan yace, wlh Dr, gobe akwai wani guri dazamuje tunda safe, kuma bana tunanin zamu dawo dawuri amun hakuri dan Allah. Ajiyar zuciya Dr, yayi yace ai bakomai seka dawo. Sallama yayi mashi yatafi yana murnar rashin zuwanshi. Ko akamfaninsu Ansar babu wanda ya gayyata.
Washe gari tunda safe Ansar yayi wanka, tsaye yake bakin madubi yasha wata babbar riga ta farar shadda me tsada yayi kyau sosai, yakawo hula yasaka. Iman tana bisa gado tana kallonshi se bata rai yakeyi kamar zeyi kuka. Dariya tayi yajuyo yana kallonta, tace wlh dear dariya kake bani, naga kana shiri kamar zakayi kuka, gashi kasha kyau kamar kaine angon. Ansar yace kinsan iri daya Umar yayi mana,tace gaskiya kayi kyau har nafara kishin yanmatan dazasu ganka. Fuska ya bata yace Allah ya kyauta mezanyi da matan kauye, damma auren Umar ne da ana daurawa zantahowata. Amma koyanzu babu macen dazan dauko ango kawai zandauko mudawo. Rungumeshi tayi tana mashi kiss a baki, tace nagode mijina Allah yabarmun kai. Har mota tarakashi yatafi.
Karfe 12 dede aka daura auren Ansar da Shatu, se Umar da jimmala, akan sadaki naira dubu 50, mutane dayawa sun halarci daurin auren, bayan angama cin abinci Abban safana da Alhaji Abbati mahaifin Umman Ansar da Dr. Usman suka kira su Ansar suka zauna kasan bishiya.
Abban safana yakalli su Ansar yace yanzude andaura aure dama kai Ansar kayi kari ne, Umar kuma yanzu kayi, sbd haka inaso ku nutsu, kusan cewa girma yakamaku banason abinda zekawo wani abu atsakanin matanku, kuzauna lfy.
Kai kuma Ansar inaso kabi duk wani abu da Dr. Zefada maka, watarana zakaci ribar abun, kayi hakuri komai me wucewa ne. Anan Alh. Abbati shima yayi masu nasiha, daga nan suka yi sallama dasu Baffa Dr. Usman yadaukesu domin kaisu air pot dama ajirgi sukazo.
Karfe 2 aka fito da amare, Shatu se kuka takeyi, Inne ma kasa hakura tayi,ko fitowa tsakar gida batayi ba, Shatu tana ganin Baffa taje ta rikeshi tana kuka, duk dauriya irin tashi shima seda yayi kuka saboda bakaramin sabo sukayi da Shatu ba. Haka aka sakasu mota tare da yan rakiya suka wuce Abuja.
Kowa gidan ta aka kaita, yan uwa se yaba irin kayan da akayimasu sukeyi, ga gida yayi kyau, duk da tsakanin gidan Umar babu nisa da gidan Iyayenshi, dan kusa da sabon gidan Ansar ne dan atare Dr. Usman da Abban Ansar suka sayi filin, sede ita Shatu acikin gidan su Umar aka ajeta a dayan part din. Khadija da Iman babu wanda yazo gidan su Umar duk da Amina ta gayya cesu, sede khadija tayi mata waya batajin dadi amma gobe ita da Iman zasu shigo. Duk da ba gaskiya tafada ba, acewarta gara tabari se gobe tasan yan kauyen sun koma, dan batason ganinsu. Amina tace ai bakomai se kunzo.
Karfe 4 na yamma mota tazo daukar yan uwansu shatu da Jimmala domin komawa dasu, dan Dr. Yace babu wanda ze kwana.
Ansar ne yashigo gida yana sauri, Iman tace lfy naganka haka? Yace yanzun nan akamun waya Allah ma yaso mundawo dawuri da anta kirana ba,a samuba sbd inda mukaje babu ntwk. Wata tafiyace takamani yau din nan zamuje China akwai wasu baki dazamu gana dasu kuma zamuyi sati guda, shine aka kirani ake fadamun anjima karfe 8 nadare jirginmu ze tashi. Ko Umar ma sede hakuri nabashi nataho.
Iman tace yanzu shikenan tafiya zakayi kabarni ni daya. Gaskiya sede mutafi tare, wani miyau Ansar yahadiye sannan yace kinga har nasamu Visa, kuma tafiyace ta maza, ahotel zamu sauka kuma duk daki mutum 2 ne ai kinga bazanje dake ba, ko sokike akallemun ke? Murmushi tayi tace a,a to kiyi hkr kinji, tace toshikenan, yace yauwa kokefa, bara inshiga wanka hadamun kayana ajaka, amma kanana sufi yawa, tace to.
Yana gama shiryawa yace bara yaje yafadama Uncle. Bayan yagama fadamashi Aliyu yayi wani irin farin cike ne yakama Aliyu, ganin zasu samu damar cin dukiyar kamfaninshi.
Afili kuma yace to Allah yabada sa,a ka kira Manager kafada masa yaci gaba da kula da harkokin kamfaninka. Kuma kabashi komai kada seka tafi arika neman kudi. Godiya Ansar yayi mashi yayima Khadija sallama yafito. Manager yakira yafada mashi komai sannan yawuce gida. Kudi masu yawan gaske yabama Iman, dan danan ta washe tafara murna. Kallonta kawai Ansar yayi ganin yanda takeyi saboda taga kudi,har mota tarakashi, seda yatafi sannan tanufi gida tahada kayanta tawuce part din iyayenta kamar yanda Ansar yace.
Urs
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹
SHATU DIYAR MAHARBI
🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹🏹nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI,U ZANGO
(Nabeelert Lady)
@( H,O,N,A)
105.....110
Koda Iman taje part din iyayenta zaune tasamesu afalo. Aliyu yakalli khadija yace yanzu ne muke da damar dibar kudin Ansar. Iman inaso kishiga dakin mijinki kidauko mun duk wasu muhimman takaddu dakika gani, gobe zankira manager tunda babu aiki muje office fin Ansar can ma muduba. Khadija tayi murmushi tace wlh ni kudima nakeso kamar million 5, Bilkisu zataje dubai, inaso inbata sakon wasu kaya ne. Aliyu yace abinda yafi haka ma zaki samu, kede kibari komai ya dedeta.
Ansar yana zuwa gidanshi kaitsaye daki yanufa ganin bakowa a falon, sautin kukan Shatu . Dasauri yanufi bakin gado,jawota yayi yafara lallashi. Yace haba my Shatu wannan kuka haka ko kinaso kanki yayi maki ciwo ne? Fuskarta yabude, turo baki tayi tace nide Baffana.
Murmushi yayi yace bakison zama dani kenan? Ta girgiza kanta, yace yauwa kinga yanzu nine mijinki, zanzamo maki Baffa da kuma Inne, ko bakiso? Tace inaso. Yace to goge idonki muje muyi alwala kinga anfara kiran sallar magriba.
Yana fitowa yace mata zeje masallaci tayi sallah da anyi isha,i zedawo gida. Seda yayi sallar isha,i sannan yawuce gidan Umar dan beganshi a masallaci ba. Yana zuwa yasameshi yana shirin shiga gida.
Ansar yace yau ga ango marar kunya, wato kai bazaka jirama azo araka kaba, kaine ma zaka kai kanka kuma kasiyi bakin da kanka, yau ga farin shiga, ni gani nakeyi duk kawani rude.
Dariya Umar yayi yace wlh Ansar ka rai nani dayawa, kamanta ni yayanka ne. Gara mani danake sabon shiga, kaifa yanda kake farin ciki kamar yau kataba aure. Ansar yace nikam ai jina nake kamar yau nazo duniyar, nadade ban tsinci kaina cikin irin wannan yanayin ba seyau. Ansar yace banganka a masallaci ba. Umar yace lafiya lau wlh nagaji ne shiyasa nayi sallah awannan masallacin, yanzu ma nakira dady. Nayi masu seda safe.
Ansar yace wlh baka da kunya, wato yaude ka nunama,dady kaima kayi gida. Umar yace ina fatan komai yayi dede agurin sarkin kishi Iman? Dariya yayi yace dafarko tafara kawo matsala amma ina bata kudi tamanta da wata damuwa, Umar yace ai Iman mayyar kudice. Ansar yace to sarkin sa ido inaruwanka? Babu ruwana kam, yanzu yazakyi da kiran waya? Ansar yace shine nazo intambayeka ai.