Sashe 40
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
maganar da maman Ibrahim tayi yasa Rufy dariya Bayan sunje asibin duk wani gwaje gwaje da Yakamata ambata anyi kuma abinda suka tunani ya tabbata ciki ne da ita har na wata uku lokacin da wannan albishir ya isa kenan Ibrahim suma ne kawai baiba sabida tsabar farin ciki Rufy kuwa banda shafa cikin ba abinda take wai itama yau tana auke da an ta na kanta mallakin ta alhamdulilah ya Allah Allah Nagode maka da kabani wannan kyauta Abinda take iya cewa kenan Ibrahim kuwa yana fitowa wayar hafiz ya kira ya fadamai sosai shima ya nuna jin dadin sa tare da fatan Allah ya bawa faridan shi shima Daga nan wayar umman shi ya kira tana daga wa abinda ya fara cewa "Mama munje an duba ta kumaa sun tabbatar min d tana da ciki har wata uku nima kwanan nan zan zam Baba.. "To rasa kunya naji sai ka kashe wayar Cewar maman Ibrahim tana kashe ta cike da farin cikin wannan lamari Sai yanzu ya tuna maman shi ce da kunya ya tsaya wannan zancen da ita Kafin su dawo daga asibiti gaba aya kowa yasan halin da ake cikin suna zuwa aka fara kaffa kaffa da ita kowa sai tan bayarta yake akwai abinda take so tun tanajin kunya har ta ware Nan fa su Farida suka sata agaba sai tsokanar ta suke suna fa "Ai dama tunda ta fara wannan fushin da wani banason anshin abu nasan anyi kamu allo ta fa a raga SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce Paid page 85&86 __________Alhamdulillah an gama biki lafiya amarya gidan ta su Rufy ansha ziyara sosai gidan yan uwa da dangin miji duk su ukun suke zuwa inda suka je har gidan su hafiz da Abdullahi mijin jamsy Shirye shiryen koma wa Lagos suke amma ta Kaduna zasu biya gidan su Farida ,sosai jikin ja msy yayi mugun sanyi ganin yadda duk inda suka je daga cikin dangin kowa ake kar ar su hannu biyu sai taji inama itama aje nata dangin A yaune motar su ta tashi zuwa Kaduna duk su shidan kasan cewar motar gidan su Ibrahim ce jif babba mai gida uku hakan yasa matan suka zauna gidan baya mazan kuma. Suna tsakiya sai driva a gaba Hira suke sosai cike da nishadi Rufy ce ta kalli jamsy tana fa "Besty kamar a hanyar Kaduna kika ce garin ku yake ko? "Eh meyasa kika tanbaya "Dama naga munzo ta wajan ne shine nayi tunanin mai zai hana muje kema kiga gida ko hubby Ta arasa maganar tana zura hannu inda Ibrahim ya ke "Haka ne baby kinyi magana mai kyau gaskiya ya kamat ace Jamila kinje gida bai kamata ki ri e mahaifin ki arai haka ba Tunda suka fara maganar bata ce komai ba sai hawaye da ya fara biyo fuskar ta tana tuno da rayuwar ta ta baya Kukan da ta fara ne Abdullahi yasa baki nan suka shiga bata hakuri da tausar ta akan ta yafewa mahaifin ta domin duk tsiya shiga haife ta Da haka ne suka samu ta sakko inda ta shiga yiwa drive kwatancan hanyar zuwa gidan nasu Cikin lokaci alilan sai gasu sun bayya na agidan su jamsy sosai gaban ta yake faduwa domin bata san me zata tarar ba Gidan ta gani gaba aya ya canza kamar ba shiba da yake shekarun da yawa kusan shekara bakwai rabon ta da garin Yara suka gani sunzo sun zagaye motar dan haka Abdullahi yace "Ko zamu aika yaran nan su yimana sallama da shi "A'a su sauka su shiga gidan idan yaso in yana nan zai fito ai "Cewar hafiz Hakan akai su ukun suka nufi cikin gidan ,gaban jamsy banda faduwa ba abinda yake cike da tsoro ,sallama sukayi sai dai shiru ba wanda ya amsa ganin haka yasa suka kalli juna kafin su sake hada baki wajan yin sallamar Wata yar matashi ya ce ta fito daga aki hannun ta rige da yaro tana jijjiga shi ,mutuwar tsaye jamsy tayi ganin Yar uwar ta ce da suke uwa daya uba daya Ummi "Bayin Allah ku kuma daga ina dan gaskiya ban waye ku ba , Ummi ta fa a tana karaso wa tsakar gidan Duk gaba aya shiru sukayi ganin haka yasa Farida cewa "dan Allah nan ne gidan malam Sani? "Eh nan ne sai dai kuma shi baban baya nan sai zuwa dare zai dawo amma sai lafiya ko dan gaskiya ban ta a ganin ku ba ? Farida ce tace ,"jamsy yi magana mana kika yi shiru Ganin kamar bata jiba yasa Rufy ta ta a ta tana fa in "besty kiyi magana mana kin tsaya kamar status "Cikin rawar murya mai alamar karyewar zuciya da nuna raunin ta a fili tace,"Ummi baki gane niba? Ummi da ta maida hankali wajan yaron dake hannun da sauri ta ago kanta jin Muryar da ko a mafarki bata ta a zato ba ,domin ta dade da cire rai akan Yar uwar Tata bazata ta a dawowa gare su ba "Yaya Jamila kece ko mafarki nake dan Allah idan mafarki ne karku tashe ni,yaya Jamila nayi neman ki amma ban ganki ba kullum zuciya ta gayamin take zaki dawo sai dai tsawan shekaru shiru ba ko labarin ki ,dan Allah karki kuma tafiya ki barni Tunda Ummi ta fara magana jamsy take kuka su Rufy na taya ta ,da sauri taje ta rungume Ummi tana da "Ummi nice ba mafarki kike ba ,yaya jamilar kice nadawo ummi bana fatan na kuma tafiya na barki yar uwa ta tayi kewar ki sosai Wata irin rungume juna da sukayi ne yasa yaron hannun Ummi ya fara kuka ganin kamar basusan yanayi bane yasa Farida kar ar shi ta fara jijjiga shi "Wai kuwa lafiyar ki kalau Ummi kika bar yaron nan yana kuka haka har waje nifa dadi na da ke wawta wallahi Wata babbar macece wadda ashekara zatayi Kusan hamsin ta shigo tana wannan maganar ,kota kan abinda matar take fa a Ummi bata biba ta nufe ta da gudu tana fa "Umma Hassana kinga abinda nake gani yau gaskiya ne ba mafarki ba yaya Jamila ce ta dawo gida Wadda aka kira da umma Hassana da sauri ta ara so wajan da jamsy take "Da gaske Jamila tace wannan,Jamila meyasa kika gujemu dan mahaifin ki yace ki tafi hakan bayana nufin cewa muma muntsane kiba ,jamila munyi neman ki sau ba adadi sai dai bamu same kiba... Garan muryar da akayi ne daga waje yasa tayi shiru da maganar da take Baba ne ya shigo cikin gidan hannun sa dauke da ledoji Wani irin mummunar fa uwar gaba ce ta kama jamsy domin bata san yadda zasu kaya da mahaifin nata ba ,domin zai iya yiwuwa har yanzu bai huce ba ,cike da tsoro ta fara ja da baya inda shi kuma yake ara shigowa cikin gidan ba tare da ya lura da ita ba ya dai ga mutane a waje sun gaisa sukace wajan shi suka zo yace musu yana zuwa Da gudu jamsy ta ara sa inda yake ta ri afafun sa tana sakin kuka mai ta a zuciya sosai take kukan tana fa "Baba Dan girman Allah kayi hakuri ka yafemin wallahi ba laifina bane na tuba bazan sake ba Dan Allah karka sake korata a karo na biyu Tunda ta fara magana yaji wani irin abu azuciyar shi domin Muryar ya ka ai ta tabbatar mai da cewa wannan jamilar shice Kafafunsa ya janye daga cikin hannun ta yana ja da baya ..... SECONDARY SCHOOL (Love& romantic story) Shalele ce Paid page 87&88 ________Zaune suke a kofar dakin sunyi jugum jugum gaba aya abin duniya ya ishe su gani yadda cikin lokaci alilan yanayin halittar su ya sauya "Fatima(Aunty) ya jamata zuwa yanzu mu fara shirin koma wa gida tunda dai kina ganin yadda bayin Allahn nan suke awai niya damu abin ya isa kuma kinga ba arfi ne da suba Aunty ce ta juyo tana kallon kawar tata da fuskar ta da gaba aya ta canza mama sabida wutar da ta kona ta ce "Yanzu a haka kike so kice na shirya mu koma cikin gari da wannan fuskar ,tukunna kina tunanin madugu ya daina neman mune? "Haba dai neman me zai mana bayan a gabansu yaran nasa mutarmu ta kama da wuta dan haka duk zatan su mun mutu yanzu ,dan haka zamu koma cikin yan uwan mu domin zama anan bazai mana ba Da wannan tunanin su anty da fuska ta kone suka fara shirin barin garin cike da kewar yan garin domin sunyi musu halacci kuma sun tafi da alkawarin zasu dinga zuwa suna gaisawa *********Tashi tsaye jamsy tayi tana girgiza kai hade da fa "Baba kayiwa girman Allah kaya femin wallahi idan baka yafemin ba bazan ta a samun rahma ba idan na mutu Baki du su Rufy suka shiga bashi harda Ummi da umma Hassana ganin haka yasa baban ya daga musu hannu dan haka suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su sai ajiyar zuciya kawai da akeji "Tare kuke da wa an can mazan na waje ? Baba ya jufo tan bayar yana kallon jamsy ,kai ta daga mai dan haka yace "Mamana jiki ce su shigo ,da sauri Ummi tayi hanyar waje domin kiran su Ibrahim Tabarma umma Hassana ta shinfi a babba yadda kowa zai zauna Baba ne ya fara zama a tsakiya Sannan kowa ya zauna matan nadaga an garan hagun sa sai maza a dama ,gyaran murya yayi kafin ya fara magana "Bayin Allah ban waye kuba kuma kunce waje na kuma zo daga ina kenan ? Kai duk suka sunkuyar su duka ganin yadda fuskar sa take ba wasa kafin Ibrahim cikin sanyin murya yafara magana "Baba ni sunana Ibrahim Wannan matata ce sunan ta Rufaida ,ya fa a yana nuna ta muna zaune ne a garin Kano Hafiz ne ya kar a inda shima ya gabatar da kansa tare da matar sa kafin Ibrahim ya fara magana cike da tunanin abinda sirikin nasa zaice dan da gani ba shida wasa "Baba ni kuma sunana Ibrahim nine Wanda na aure Jamila,daga haka yaja baki yayi shiru Kallon ta umma Hassana tayi ita da Ummi jin