Sashe 39
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kinje sanin kanki ne an hanaki fita da daddare dan haka ki hakura . Cewar mama Sosai taji haushin hanata zuwan da akai , cikin daki ta koma cike da acin rai tare da burin gobe da safe da wuri zata tafi wajan ar uwar ta dan ko wanka bazatai ba idan taje can tay SECONDARY SCHOOL (Love& romantic story) Shalele ce Paid page 81&82 ___________To dama haka rayuwa take komai mai wuce wane ,haka Rufy da jamsy da kuma Farida suka cigaba da rayuwar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali tare da mazajan su Mota ce take ta faman sharara gudu kamar zata tashi sama sosai take gudu wanda duk mai hankali yagani yasaan gudun bana lafiya bane daga gani,tun suna tafiya ta cikin gari har suka dawo daji suke shiga wanda ba gida gaba ba gida baya ,motar dake gaban ce taje ta daki wani dutse nan da nan tahau gangarawa acikin dajin tana karo da bishiyu tana kaiwa ga wata bishiya ne ta tsaya take agun ta fara ci da wuta Tun farkon sanda motar tayi karo da dutsen mutanan daya motar suka tsaya da gudun fitowa sukai dan ganin ina wannan motar take gangarawa akan idon su ta kama da wuta sannan naga sun juya suna kallon juna mazane guda uku dan haka suka jinjina hannu alamar yayi kyau sannan suka juya da baya domin fita daga cikin dajin Kasan cewar dajin akwai mutane a cikin sa daga wani angare hakan yasa tun sanda motocin suka shigo suka uya domin an saba kawo musu hari ko kuma azo ayi kisan kai awajan jin arar da sukayi ne na budurwar motar da kuma kanawar ta da wuta ne yasa suka fito da sauri dan ganin abinda ke faruwa har tafiyar wa an can mazan sun gani dan haka suka gane na cikin motar da take ci da wuta biyo su akai Wajan motar suka matsa dan ganin ko za'a iya samon wanda yayi rai aciki mutum daya ne wanda har wani wajan daga jikin sa ya fara ci da wuta gani alamar yana da rai dan sai aga hannu yake alamar taimako yasa sukayi arin alle kofar su fito da shi Wasu daga cikin sune suka fara zagaye dajin ko Allah zaisa su samu wani abun ,daga can bayan dutse duk hango afar mutum da sauri suka duba,macece kwance cikin jini itama tana numfashi dan haka aka dauke su zuwa cikin gari Sosai suka tausaya musu domin ita wadda ta kone macece amma gaba daya fuskar ta ya lalace da hannun ta guda aya bayan kuma anana ananan gurare Ita kuma ayar karaya ce har uku wanda daya daga ciki sai dai acire hannun dan bazai koma ba ga kuma a afar ta har waje biyu sai kukkurejewa da tayi ,gaba aya dai sun fita hayyacin su dan ba mai gane su ,sosai wadan nan bayin Allah suka taimake su Bayan kwana uku zuwa lokacin jikin nasu yayi sauki sai mai kuna da take ta fama abun a fuskar ta ,wadan nan mutane da suka taimake su sun nemi suji wanne da liline yasa aka biyu su gashi su mata ba maza ba bare ace fadan daba Sun fa a musu sudai basu san ko suwaye suka biyo su ba kawai dai sunsan cewa ana binsu ne Daga haka mutanen basu kuma tanbayar su komai ba duk da bai zama lallai abin da suka fa a musu gaskiya ne ba ************Yau tunda ta tashi gaba aya bata jin dadin jikin ta sai a hankali gashi suna ta shirye shiryen tafiya Kano za'ai bikin anwar ta kasan cewar bata da ishashshiyar lafiya hakan yasa komai sai a hankali take yi Tunda ta fara ha a kayan yake kallon ta kwata kwata ya kasa gane mata kwana biyun nan duk ta canza ga wani hali da takeyi wanda ba nata ba abu kadan zai fa a mata tahau fushi ko yanzun nan ta fara masifa,kallon ta yayi yana fa "Wai kuwa anya baby lafiyar ki kalau kuwa gaba aya kinyi wani iri idan Kanon ne ba eson zuwa kiyi zaman ki ni sai muje da su hafiz kawai? "Ba haka bane hubby wallahi kawai jina nake duk wani iri ga raina a ace kamar na sa kuka ... "Kuka kuma baby muna zaune alau ko na miki wani laifin ne ban sani ba ? "Eh wallahi hubby k...... Wayar Ibrahim ce tayi ara dan haka tayi shiru daga maganar da take ,dagawa yayi ganin wanda yake kiran "munriga da mun shirya arfe biyar jirgin mu zai tashi insha Allahu,daga haka ya kashe wayar yana kallon Rufy dake tsaye "Baby kiyi sauri kinga hafiz yace yanzu zasu fito suje su tawo da Jamila sai su wuce airport muje mu same su acan gashi naga saura awa aya jirgin mu ya tashi Bayan saukar su Rufy a garin Kano direct gidan su aka wuce da su kasan cewar gobe za'a fara biki dama kuma Farida ba ar Kano bace a Kaduna hafiz ya auro ta Sosai Ammy ta nuna farin cikin ganin yaran cikin kwanciyar hankali da alama ba wata matsala tsakanin su da mazajan su ,dakin Rufy na da suka shiga wanka sukai sannan sukayi sallah abinci aka kawo musu amma sai dai Rufy tace bataci fura da nono take so ,jamsy ce ta tsaya tana kallon ta ganin abinda take sone fa wato funkaso da miyar taushe amma tace bata ci kasa shiru tayi dan haka tace "Wai kuwa besty lafiyar ki kalau yau kece kike cewa ba yason funkaso to ko dai yayan nawa yayi ajiya ne bamu sani ba Wata uwar harara Rufy ta yi mata tana fa "Kin manta abinda yafi ajiya yayi ba ajiya ba Farida da jamsy ne suka sa dariya bayan sun fara cin funkason suna fa "To meye kuma na fa a daga magana nifa dadi na da masu aramin ciki masifa wallahi ,cewar Farida ,nan ma dariya jamsy tayi tana fa in,wai wayaga idon besty a lebouroom chabbbb Ai gaba aya wannan hirar da su Farida suke nan da nan Rufy ta ciki tayi fammm kamar zata fashe saboda masifa su kuwa sun samu abinyi sai tsokanar ta suke Washe gari aka tashi ana ta shirye shiryen biki domin yaune zasuyi coktel party kowa yana ta kazar kazar da walwala amma badda Rufy Anty lami ce anwar Ammy tace "wai kuwa Yaya fati kin lura da yanayin Rufaida gaba aya kamar mai aramin ciki duk ta an yace tayi wani iri Ammy dake zaune tana ha a kaya tayi dariya tana "Fati ai Rufaida kadai kika lura da ita sabida nata yafi fitowa fili amma duk su ukun da alamar tambaya akansu ,sai dai kuma ina tunanin basusan da cikin ba suma da alama "Gaskiyar ki Yaya sai yanzu da kika fa a na lura ita Rufaida da gani gado zatai laulayi mai sa fushi irin nawa Ta ara sa maganar tana kallon su daga inda suke zaune su ukun suna hira SECONDARY SCHOOL (Love& romantic story) JAMA'A MUN KAWO *Cornflakes *Cocopops *Madara *Macaroni *Taliya *Kwaki *Busashshen kifi *Kayan kitchen *Kayan bacci Muna bada kwata ,rabin kwano,kwano,rabin buhu,buhu Shalele ce Paid page 83&84 _________Masha Allah anata biki cikin kwanciyar hankali an sha shagali yadda ya kamata yau ne kuma za'a daura aure inda daga nan kuma biki ya are da yamma za'a wuce da amarya dakin mijin ta Rufy tun da ta tashi take ta fama da zazzabi sama sama ga ciwan kai sai take ala anta hakan da hayaniyar gidan biki ,lokacin da yan aurin aure suka dawo kowa ya fito anata hotuna su Farida ansha kyau Abdullahi ma yazo mijin jamsy jiya da daddre Tun fitowar su Farida da jamsy Ibrahim yake zuba idon ganin tauraruwar shi ta bayya na amma shiru har aka fara daukar hoto hakuri ya kasa dan haka ya matsa inda jamsy suke tsaya ita da Abdullahi suna magana yana tanbayar ina Rufy bai ganta ba Kallon shi tayi tana fadin "ayya wallahi besty tun safe batajin dadi tana aki a kwace bacci take Da sauri Ibrahim yasa kai zuwa cikin falon dan ganin halin da babyn sa take ciki dan gaba aya ma ya manta gidan sirikan sa ne Dai dai lokacin da ya isa kofar akin zai shiga ne anwar Ammy ta fito daga ciki ,take yaji wata irin kunya ya rufe shi domin baiyi zaton da mutum a ciki ba "Anty ina wuni..,ya fa a yana sosai kai alamar yaji kunya Dariya tayi tana fa in malam Ibrahim watakon tun da ka auke min yarinya ta shike nan kayi wuyar gani ai shike nan ka shigo garin amma ko nema babu ka shiga tana ciki bacci take Dariya yayi yana tura kofar tare da fa in insha Allahu anty kafin mu koma zamu zo mu wunar miki Bakin gadon da take kwance ya zauna yana are mata kallo wani irin kyau yaga ta ara gashi tayi haske sosai har aukar ido take Tafin hannun ta ya kama sosai ya tsora ta ganin yadda yayi fari kamar ba jini jikin ta gashi yayi zafi Kama mata hannun da yayi yasa ta farka ganin shine yasa ta sakar mishi murmushi tana fa "Habby ya akai ka shigo nan ? "Ba wannan ba baby kinsan baki da lafiya amma baki fa amin ba kawai sai ki kwanta A aki "Hubby bafa wani abu bane zazza i ne kawai muma ai anty ta bani pracetamol nasha kuma nasan zai sauka "Gaskiya baby ban yadda ba kawai ki tashi mu tafi asibiti yafi Ganin da gaske yake hakan yasa ta hakura ta tashi suka tafi su tafi asibitin ,a hanya suka hadu da maman shi tana shirin shigowa falon dan haka tace "A'a sai ina kuma haka naga ka rakito ta ita da batajin dadi ina zaka kaita? "Mama asibiti zankai ta sabida naga kamar da ba jini jikin ta duk tayi wani irin haske ta kode "To gwani na gwanaye ita ta fa a maka bata da jinin ko kai ne kuma ai tasha magani zazzabin zai.sauka "Amma kuma mama... ,"Kaga daka ta yanzu jeka samo mata maltina da madara tasha dan ba abinda taci tun safe idan yaso kwatafi wajan bokan Turai din Sosai