Sashe 19
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hello Ammy na , Rufy ta fa a cikin sanyin murya "Na'am Rufaida sai yau kika tuna dani ko? "A'a wallahi ammy bani da waya ne shiyasa "To yanzu banda abinki Rufaida ai saiki kar i wayar mijin ki kira mu da ita "Shiyasa ai na kar a yanzu baya dawowa da wuri ne shiyasa kuma nasan lokacin kunyi bacci "To ai shike nan,ina fatan dai kuna zaune lafiya ke da maigidan naki? "Eh Ammy bawata matsala muna zaune lafiya "To ai shike nan haka akeso Allah ya kara muku zaman lafiya da hakuri da juna Ameen Ammy na ,daga haka kuma suka ta a hira ka an ta uwa da a sannan sukayi sallama ,sosai Rufy taji da in wayar da tayi da ammyn ta sai hakan ya rage mata kaso da yawa na damuwar ta Tunda suka fara wayar Ibrahim yake kallon ta asa asa bai ta a lura da yanayin ta haka ba sai yau sosai yarinyar ta bashi tausayi baiyi tunanin yarinya ce haka ba sai yau dan fuskar ta ta nuna kuruciyar ta sosai gashi dama ya lura bata d hayaniya ko kadan komai nata a nutse takeyi Yana wannan tunanin har bai san ta araso inda yake ba sai da tayi magana sau biyu sannan ya lura basar wa yayi sabida karta gane meya ke yi **************Kwanan indo uku a asibiti kafin aka sallame ta zuwa gida,kafin lokacin kuwa tuni zance ya cika gari abinka da kauye wannan gayawa wannan kowa yasan abinda ya faru ,kafin su baro asibitin kuwa mutane da yawa anxo dubiya da masu dubiyar da kuma masu zuwa gulma su samu abin ya awa a gari Mai ni a yaji labarin da ke yawo a gari cewa indo tayi cikin shege ai kuwa nan da nan ya fara tunanin yadda zai fitar da kanshi,sai dai kuma bai samu mafita ba da ta wuce ya bar garin kafin amai tonan asiri dama kuma ba an garin bane zuwa yayi ya samu akin da yake kwana shine ya fara sana'ar ni Safiyar da aka sallami indo daga asibiti shi kuma ya ha a kayansa tun dare ba tare da kowa ya sani ba ana shiga Masallaci sallar asuba ya hau mashin insa yabar garin Tunda abin ya faru Inna batace da indo komai ba taja bakin ta tayi shiru sabida suna asibiti tabari su koma gida sannan su hadu Suna komawa gida ta samu waje ta kwanta sabida har lokacin jikin ta ba kwari "Uban waye zai gera miki gidan ai yanzu ba batun ke yarinya ce dan kin zama uwar mata maza tashi wallahi tun kafin nazo wajan Inna ta fa a cikin fa a da hargagi "Dan Allah inna kiyi hakuri wallahi jikina ba kwari idan na tashi zan iya faduwa "Iye sannu to wallahi ki tashi tun kafin nazo kanki lokacin da kika bu ewa ato afafuwan ki ai bakiji zaki fa in ba sai yanzu da nace zakiyi aiki ko dan kinga yanzu mun zama aya dake, wallahi to uban ki zanci yanzun nan Jiki ba ari haka indo ta tashi ganin ba wasa a maganar inna ,da er tayi sharar tanayi tana hutawa sabida rashin kwarin jiki,kafin ta gama kuwa gaba aya taya wujiga wujiga sai hawaye take sharewa ga wani irin warnafi da take fama dashi tun safe ta rasa neke mata da ***********"Shike nan nagode da abinda Hauwa'u tayimin Allah shaida ne nanata tarbiyya dai dai gwar gwado kuma nayi kokarin ganin na sauke nauyin ta dake kaina,abinda tayi taje bazan mata baki ba amma duniya makaranta ce mai hankali shi zai gane sanda duniyar tayi mata juyin waina ta dawo gida ,dan haka ban umarci kowa agidan nan da ya neme ta ba taje ta rayu da wacce ta za a kuma tayi rayuwar ta yadda take so tunda hakan shi take ganin yayi mata "Amma a ganina hakan bashine mafita ba habibu domin kuwa zata samu damar cigaba da rayuwar yadda ta ga dama ne a matsayin mu na iyaye hakan bai kamata ba gaskiya "To auwalu ya kake so nayi ita da kanta tana hakan shine dai dai da ita to sai take tayi duniya ce ta ishet a riga da wando,amma wallahi duk wanda ya nemeta acikin ku banya fe ba kun daiji na fa a muku Daga haka baban jidda yasa kai yabar gidan "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allah kayi mana maganin wannan masifa da ta tunkaro mu Zubaida abinda nake so dake dan Allah ki yafewa Hauwa'u abinda tayi idan ba haka ba wallahi abin zai mata yawa ke uwa ce kiyafe mata sai kiyi ta addu'a Allah ya dawo da hankalin ta gida muma kuma zamu dage insha Allahu komai zaizo da sauki Cewar baban zeey "Shike nan baban Zainab naya fe mata Allah kuma ya yafe mata amma wallahi ni kadai nasan zafin da kirjina yakemin akan ta "Nasani Zubaida amma haka za'ai hakuri ayita addu'a har Allah yasa adace mutanan nan basu da Imani basa tsayawa haka suna ha awa da asiri acikin lamarin su BAYAN WATA BIYU Zuwa wannan lokaci abubuwa da yawa sun faru ciki kuwa harda aurar da zeey da akai ga wani abokin baban ta amatsayin bazawara,mutumin yana da mata guda aya da yara takwas,ba wani zaman dadi zeey takeyi ba sabida ba sonshi take ba ga kuma aikin gida da take fama dashi sabida yara kamar jaka haka zatai ta aiki sosai ta rame tazama abin tausayi gashi tun sanda abin ya faru maman ta ta daina mata magana sai sama sama shima din sau idan magana mai mahimmanci ce ko waya ta kira sai dai umman jidda ta aga su gaisa Haryanzu kuma ba labarin jidda zuwa lokacin umman ta ta fara fitar da rai daga dawowar ta ganin lokaci ara gaba yake *********Indo ciki ya fito har yakai wata biyar suna fama da habaicin yan gari gashi inna bata daina fushi da ita ba babane kawai wani lokacin yake nuna tausayin sa akan ta shima ba kullum ba Ba inda indo take zuwa kullum tana gida sabida tana fita za'a fara nunata yara kuma su hau yimata wa a ba inda take zuwa ta samu sassauci sai dai idan inna bata nan ne take samun damar watayawa acikin gidan Haryau kuma su inna basu tanbaye ta waya mata cikin ba sunja baki sunyi shiru,ta aika wajan mai ni a ance mata ai yabar garin *****Zaune take afalon kallo take sai dai kuma ba abinda take fahimta sabida yanda tayi nisa acikin tunani jin an daki kujerar da take kaine yasa ta daga da sauri jamsy ta gani tsaye akanta "Jamsy lafiya meya kawo ki gida na kuma? "Aaa to yaushe kuma yazama gidan ki har kinsamu matsayi kenan.. "Kinga ba wannan ba dan Allah dan Annabi ki taimaka ki koma abinda kikamin arayuwa ma ya isa basai kin hanani zaman aure ba kwata kwata kin hana rayuwa ta farin ciki wallahi ina dana sanin sanin ki arayuwa "Au danasani harkin fara kenan to kishirya da saura dan bakiga komai ba wallahi "To dan Allah menayi miki haka ki fa amin sai na nemi afwar ki kawai shikenan "Ina aiba batun afwa wallahi,kuma mafa ni ba'abin da kikamin kawai dai laifin wani ne ya shafe ki "Kamar ya kenan ban gane ba laifin waye ya shafe ni haka? "No,idan lokacin yayi zaki sani ne yanzu dai bani hanya na wuce ciki dadirona nake jira watakon mijin kiii Da kallo kawai Rufy ta bi jamsy ganin wannan irin bariki haka agaban ta take cewa mijin ta dadiron ta,ko da yake ba arya tayi ba shine amma ai taji kunyar ta koba koma SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce Paid page 47&48 -----------------Duk abin da ke faruwa tsakanin jamsy da Rufy Ibrahim yana kallo ta window kasan cewar yana aki dama kuma yasan da zuwan jamsy dan sai da sukayi waya yace mata yana gida sannan ta tawo Ibrahim mutum ne Maison mace yar gayu mai yawan amfani da kayan yale yale sannan yana son mace mai aji sai dai kuma kwata kwata jamsy bata amfani da wannan kayan yale yalen Bai kuma san dalili ba kawai dai yasan yana son jamsy har Yana iya jin kamar bazai iya rayuwa ba ita ba Zakuyi tunanin Ibrahim da jamsy suna kusan tare junan su sai dai kwata kwata abin ba haka yake ba hasalima bayan romance ba abinda ya ta a shiga tsakanin su Ada Ibrahim yayi neman mata amma tun sanda aka ce zaiyi aure ya daina ya tuba sai dai shigowar jamsy cikin rayuwar sa ta nemi mai da shi ruwa duk da har yanzu ha an ta bai cimma ruwa ba Aduk sanda Ibrahim da jamsy suka kasan ce waje aya tana kokarin ganin ya kusan ceta sai dai har yanzu abin ya i yiwuwa duk da shima Ibrahim abin yasa ransa amma da zarar yayi yunkurin kusan tar ta sai yaji abun ya fita daga ranshi Abun da baku sani ba shine Ibrahim yana tsoron jamsy kamar Mala'ikan mutuwa kwata kwata baya son acin ranta wannan yasa jamsy take yadda taga dama dashi "Wai dama kana ciki amma kana kallo matar ka tana neman tamin rashin kunya,koma dai kai kasa tane? Jamsy ta fa a tana tsare shi da ido "Haba dai ya za'ai nasa ta tayi miki wani abu ai kema dai wasa kike ina kallon ku dan inga abinda zai faru idan naga zata wuce gona da iri na taso "Uhmm kamar gaske sai wata magana kake sanin kanka ne nidai nafi karfin wulakan ci wallahi "To yanzu kuma wani abun ne ya faru ke da baki raina abin magana ko kadan! "Shike nan naji bakomai ai ni nakawo kaina watakon matar ka kake karewa ko bakomai , yanzu dai ya maganar zuwa shopping din? "Chabb kinsan Allah na manta na miki alkawari kuma yanzu haka karfe takwas na dare jirgin mu zai daga zuwa Legos zanje wani aiki "What?kasan zakaje wani waje sannan kamin alkawari,tukunna ma kai da wa zakuje naji kana maganar jirgin ku? "A'a bangane ni dawa ba da nida waye acikin gidan nan kinsan dai ba yadda za'ai na tafi na barta ita kadai hasalima iyayan mu nayi musu karyar muna can