Sashe 23
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunda ga falon yake jiyo nishi yan tashi ya zata munshari ne dan haka yaja tsaki ya samu waje ya zauna, jin abin bana are bane gashi hadda kamar kuka kuka yake ji hakan yasa ya nufi akin ta Yana bude kofar yadda yaga tana rawar sanyi ne gashi da alama da er take numfashi yasa ya shiga dakin da sauri tsayawa yayi yana arewa inda take kallo ganin kan an abin da take kwance tasa hijjabin ta taa rufe afafun ta amma ina sanyi takeji dan garin sanyi ake sosai "Rufaida ya fa a da dan karfi sosai yaji wani iri sabida yaune ya fara kiran sunan ta dan ko a rayuwar su ta Kano sai dai yace mata keee er ta bu e idon ta da suka yi mata nauyi gashi duk sunyi ja kan hancin tama yayi jawurr kamar an shafa mata barkono "Tashi muje asibiti kina nan zaune da ciwo salon ki mutu ace nine ko Ba abinda take fahimta sabida numfashin ta aya fara kokarin auke wa ,ki tashi nace ko kika tsaya kallo na ewa tayi jikin ta na rawa sai dai gama tashin ta keda wuya wani jiri ya dibe ta ta tafi luuuu zata fa i da sauri ya riko ta jikin sa ta fa o jin alamar kamar ajiyar zuciya ne yasa ya kalle ta da sauri bata numfashi ya fa a da karfi Jijjiga ta ya fara yi sai dai ko matsawa batayi gaba aya jikin ta ya saki nan fa zuciyar shi ta shiga bugawa " kardai ta mutu,ya fa a cikin tsoro... Ganin abin bamai yiwuwa bane yasa ya rungume ta yayi waje da gudu da ita a kirjin shi. KANO TA DABO TUNBIN GIWA ______Tunda jirginsu ya tashi take tsaye a wajan kamar an dasa ta ta rasa mema zata ce Ibrahim ya watsa mata asa a ido gaban Rufy bazai kar i ticket din ta ya Bata ba shine Suka tafi suka barta awajan Kuma ma har Chocolate ya siya mata a gaban ta sai tayi magana yace ba sonta yake ba ,ai kuwa wallahi bai isa ba duk abinda zai faru sai dai ya faru dan san naa biku Lagos din nan domin Ibrahim ba da Rufy ya dace ba dani ya dace Ta fa a cikin karaji wanda ya janyo hankalin wasu dake wajan kanta,ganin an fara kallon tane yasa ta bar wajan Tafe take cikin napep amma tunanin abinda zata cewa awayan ta take zasu auke ta ma ar yaciya ko kuma su ce dama Ib da take cewa bata ita yake ba SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce Paid page 53&54 _____________"Rankaya dade ka kwantar da hankalin ka munyi nasarar ceto rayuwar ta kuma munyi nasara alhamdulilah yanzu haka bacci take yi Ajiyar zuciya Ibrahim ya sauke afili sannan ya kalli likitar dake mai bayanin yace "To amma likita mai ya kawo auke War numfashin nata haka lokaci ka "Eh abisa binciken da mukayi ya nuna mana cewa limoniyar da take fama da ita ne ya haifar mata da haka muna abisa alamu tana amfani da kayan sanyi ko ruwa ko kwanciya cikin Ac da makaman tan haka "Limoniya kuma? Ibrahim ya fa a a fili ba tare da ya sani ba domin a iya sanin sa iyayan Rufaida basu fa a mai tana fama da wannan cutar b.. "Rankaya dade ko bakasan tana da cutar bane naga kamar kana mamakin jin hakan? Kallon likitar Ibrahim yayi yana tashi daga kujerar da yake yana fa "A'a bakomai nasan da ita...amma yanzu zan iya gani ta "Eh bamatsala zaka iya zuwa amma kada ka tashe ta a barcin sabida ana bu atar ta samu hutu i sashshe Cikin akin da aka kwantar da Rufy ya shiga kasan cewar asibitin na kudi ne dan haka a special room aka kwantar da ita ita ka ai ce aciki Ahankula ya shiga ciki sabida kada yayi motsi wara ta tashi,zama yayi yana kallon ta abinda ya bashi mamaki yadda ba'a fa amai tana da Wannan matsala ba Tashi yayi ya nufi gida zai dakko mata kayan sawa sabida na jikin ta na bacci ne da ta sa doguwar riga yana zuwa gida direct akin ta ya nufa dai dai lokacin hafiz ya kira shi a waya sabida kwata kwata baiji shiba tun jiya da yamma gashi har gari ya waye fa a mai yayi Rufaida da ce ba lafiya suna asibiti zasu zo shida matar shi yace mai sannan sukayi sallama e trollyn ta yayi doguwar rigar atamfa ya daukar mata tunanin daukar mata yayi ta samu ta canza na jikin ta bra ya daga sama sosai abin ya bashi mamaki ganin ta babba me hakan yake nufi kenan tana da nono kome,ganin tunanin bazai kai mai bane yasa ya dauka kawai zai fita kuma sai ya tsaya yana arewa akin kallo Kwata kwata baiga katifa ba sai wannan kafet in daya gani kenan hakan na nufin akai take kwata ba tare da shinfi a ba,jiyayi tausayin ta ya kamashi domin baiyi zatan haka take kwana ba ya zata akwai katifa a akin nata Yana fitowa ya shiga taxi wayar shi tayi ara baban sa ya gani dan haka ya daga da sauri gai sawa sukayi yana tanbayar shi ina Rufaidan Shiru yayi yana tunanin ya fa a mai ko yayi shiru kawai sai ya yanke shawarar fa amai Dan haka yace "Baba dama Rufaida tana da limoniya amma su kawu basu fa amin ba? Ya fa a kasan cewar haka yake kiran mahaifin Rufaida a matsayin sa na abokin baban shi "A'a Ibrahim ni nasan Rufaida tana da wannan matsalar kuma lokacin auren ku sai da kawun ka yace na fa ama dan yasan baka sani ba amma sai na mance yanzun wani abune ya faru da ita? "Eh dama... shiru yayi domin baisan me zai ce ya sa Meta ba Eh me naji kayi shiru wani abunne? "Dama Baba ban sani bane ita kuma bata fa amin ba kasan Lagos da yawan ruwa ga sanyi da ake fama dashi shine take mura da mukaje asibiti ake fa amin "Ayya Allah sarki yarinyar kirki badai hakuri ba Allah ya bata lafiya dan Allah ku zauna lafiya Rufaida yarinyar kirki ce bata da hayaniya ko ka an ga hakuri "Shike nan Baba zamuyi magana anjima zan koma wajan ta ne tana asibiti, daga haka ya kashe wayar ajiyar zuciya yayi yana fa in ji yadda yake ya bonta baisan ba haka take ba Koda ya koma asibitin lokacin ta farka likitan da ta duba tace awajan ta tana mata tambayoyi ta War ware sai dai jikin ba kwari ko kadan dan haka tace zasu kwana sai gobe su tafi gida Shiga yayi da ledar kayan ta likitan ya mi awa tace "A'a ai matar kace dan haka ka kama ta ta shiga ban aki tayi wanka idan kuma baza ta iya ba sai kayi mata meye aciki Tana gama fa a ta fice tana musu dariya Shiru akin yayi ba kwanda yake cewa da kowa komai sai arar fanka kawai ake ji kasan cewar ana rana sosai,ganin bashi da niyyar yi mata magana ne yasa tace "Ina kwana? cikin sanyin murya dake nuna alamar rashin lafiya Batare da ya amsa mata ba ya mi a mata ledar da ya zubo mata kayan sawar ta aciki "Gashi sai kiyi wanka ki chanza yanzu hafiz zasu zo da abinci sai kici Sak kowa tayi daga kan gadon ahankali sai dai kuma da ta tashi nan jiri ya e ta zata fa i yayi saurin ri o ta dai dai lokacin hafiz da matar shi suka shigo cikin akin. __________"zaune take ta zuba tagumi gaba aya abin duniya ya isheta bata da burin da ya wuce ta zama ar jarida sai dai kuma kwata kwata bataga alamar burin ta zai cika ba domin gaba aya tunda aka mata auren nan shike nan gaba aya burin ta bataga alamar zai cika ba komai na rayuwar ta ya lalace duk wani farin ciki da nishe ya aura ce mata...... Babban tashin hankalin ta rashin sanin inda ar uwar ta kuma aminiyar ta jidda take shiya sa gaba aya abubuwa sunyi mata yawa duk ta rame tayi wani irin a i abin tausayi,yanzu haka watan ta biyu da aure amma har yanzu bata je gida ba sabida mama tace kada ta kuskura tazo idan ba wani abune ya faru ba,shiyasa gaba aya rayuwar tayi mata zafi Malam Umar shine mijin da zeey take aure malamin islamiyya ne ba wani mai kudi bane yana dai da rufin asiri dai dai gwargwado abinci baya yanke wa agidan sa koda kuwa ba dadi dama ya dade yana don zeey ta i yadda amma saboda tana gani kamar basu dace ba,lokacin da baban ta ya ce mai yazo zai bashi auren ta sosai yayi farin ciki sai dai kuma ance mai ita yanzu ba budurwa bace sai da aka fa amai duk abinda ya faru gudun kada yace an cuce shi sannan ya amince akai musu auren Yana da mata guda aya da yara gida aya aka hadusu da zeey dan haka hidimar gidan tayiwa zeey yawa sabida girki aya suke yi _______________"To yanzu da kike Wannan maganar ina zaki samu kudin da zaki tafi Lagos ajirgi? "Kasan Allah bash saina bisu Lagos din nan karkaji yadda zuciya ta takemin zafi yadda ya nuna Rufy tafini mahimmanci harda hawa jirgi ya barni a wajan "Yazakiyi abinda ya faru ai ya faru yanzu sai ki shiryawa dawowar su kisan abinyi Amma binsu bashine mafita ba "Ni duk ba Wannan ne ya tsaya min araiba bash tunda suka tafi kwata kwata bai kirani ba ni na i kiran shi sabida na nuna nayi fushi ya bani hakuri shine shima ya share ni watakon bani da matsayi ya samu matar shi ko Ko a online bayamin magana kuma yana hawa bare yace bayayi "To ai ke saiki kirashi tunda ke kike bu atar shi bashike nan ba Waya jamsy ta auka ta danna kiran wayar Ibrahim dai dai lokacin shi kuma ya fita siyo maganin da aka rubutawa Rufy kuma yabar wayar a wajan dan haka har kiran ya katse ba'a aga ba dan haka ta sake