Sashe 26
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sabida tunanin da ya addabi walwar sa zuciyar shi ce ta tanbaye shi "A ina jamsy tasan cewa Rufy ba budurwa bace? Girgiza kai yayi alamar bai sani ba dan shi dai yasan bai gaya mata ba iyaka yace auren ha i akai musu ba tare da suna san juna ba shike nan to amma a ina ta samo wannan maganar tabbas akwai wata a asa Da sauri ya tashi tsaye wajan jamsy zashi ya jiyo inda taji wannan labarin Wayar ta ce tayi ara dai dai sanda ta fito daga wanka aran kiran ne yasa ta ara so da sauri sabida mutum aya ne yake da wanann ringtone din da sauri ta "Kizo mu hadu inda muka hadu jiya yanzu ina jiran ki Iya abinda yace kenan ya kashe wayar Da sauri ta fara shiryawa sabida karta atamai lokaci Bayan ta gama ne ta fara yiwa wanda ke kwance kan gadon magana "Alhaji nifa na shirya ka sallameni zan wuce ana jirana i wanda ta kira da alhajin ya dakko ya bata zasu kai dubu hamsin ta kar a tayi gaba dan burin ta taje taji kiran me Ibrahim yake mata Lokacin ta ta ara so harya tashi zai tafi dan ya gaji da jira gashi yana da aiki a office ya fito Bako sallama haka ta zauna a wajan tana fa "Sorry baby na barka kana jirana wanka nake ne lokacin Okay kawai ya iya ce mata ya tsaya yana are mata kallo jamsy ba mummuna bace sai dai tayi kama da wa an da idon su ya bude ga bakinta yayi kamar tana san wani abu,ganin kamar zan shiga zargi kuma yasan ba kyau hakan yasa ya kawar da wannan tunanin ya fara mata magana "Dama akan maganar da mukayi jiya ne tabbas nayi tunani abinda kika fa a gaskiya ne sai dai kuma wani abu da ya bani mamaki taya akwai kikasan Rufaida ba budurwa bace waya fa a miki ? Ya jefa mata tanbayar yana tsare ta da ido "A'a...ba kaine ba ka fa amin lokacin da muka hadu da kai Ta fa a cike da alamun rashin gaskiya tare da ita "Ni kuma jamsy gaskiya ki sake tunani dan banyi wannan maganar da ke ba kwata kwata sai dai idan wani wajan kika jiyo Shiru tayi tana tunani "Nashiga uku surutu na zai jawomin ya gano koni wacce amma bazan bar hakan ta faru ba dole na san mafita "Kinyi shiru kin barni ina magana ni ka ai a ina kikaji wannan maganar? Ya sake jefa mata tanbaya "Tunani nake sai dai kuma baby na kasa tunawa sai nake ganin kamar kaine ka fa amin idan ba haka ba a ina zanji "Kinga a rayuwa ta banason munafirci idan har kinaso ala a ta da ke ta dore to tabbas ki fito ki fa amin gaskiyar inda kikaji wannan maganar Daga haka ya tashi yabar wajan Zama tayi ta zuba tagumi garin neman hanyar shiga tana neman ta fita yanzu me zata ce mai idan ya kuma tanbaya tabbas ya zama dole tasan abinyi kafin lokacin *********** Sanda suka dawo gida sosai yadda hafiz da matar shi suka tari juna ya burge Rufy da Ibrahim sabida sun nuna iya wannan yinin sunyi kewar junan su Wannan shine karon farko da Rufy ta ta a kar ar jakar Ibrahim bayan ya dawo, shima sabida matar hafiz ta mata nuni da hakan ne Dan haka ta kar e tana fa in sannu da zuwa sai yaga abin wani iri sabida bai saba ba,hanyar akin shi tayi cike da fargaba domin wannan shine karon farko da zata shigar mai Bayan ta dawo ne ta tarar matar hafiz ta zubawa mijin ta abinci sannan ta sa hannu sun fara ci suna hira Zubawa Ibrahim Rufy tayi dan wannan shine karo na farko da ta fara zubamai abinci tashi ta so yi zata bar wajan matar hafiz tace "A'a ina kuma zaki ke da kike ta cewa yunwa kike ji kisa hannu kici idan kun gama sai ku rakamu mu tafi karmu ta kure ango da amaryar sa Ta ara sa maganar tana dariya asa asa "Da gaskiyar ki sweetie Dan da ganin abokin nan nawa kinsan lamarin sa ba sauki Hafiz ya fa a yana mai dariyar shakiyan ci Gaba daya kunya ce ta rufe Rufy jin maganar da sukeyi duk sai tayi wata irin kunya ta kamata gashi hannun ta cikin kwano aya da Ibrahim duk sai ta jita a takure "A'a amarya ya dai naji kinyi shiru ko duk cikin salon korar mune Matar hafiz ta fa a tana dariya Rasa abin fa a yasa Rufy cewa "A'a kuyi zaman ku ba komai To bayan sun gama cikin abincin ne Ibrahim ya tashi zai rakasu amma matar hafiz tace Rufy ta tawo suje tare mana daga nan ta ga gari "Yawwa Ibrahim gobe zanje siyayya kaga zai muje tare da amarya sabida nasan itama baza ta rasa abinda zata siya ba koya kika ce Ta fa a tana kallon Rufy da kanta yake a asa "A'a gaskiya dai ko ba komai ai ta zaga garin Lagos ba kullum ace tana gida ba Hafiz ya fa a shima "To shike nan Allah ya kaimu gobe sai kuje tare Cewar Ibrahim dai dai lokacin da suka fito waje Haka suka tafi suna hira duk da ba baki Rufy take sawa ba iya ka tayi murmushi kawai sabida gaba daya idan hafiz da matar shi sukayi wata maganar kunya suke sata ji su kuwa ko a jikin su harkar su kawai suke Bayan sun rasasu sun dawo ne suna cikin tafi ba hira suke ba amma kasan cewar sun jero daga nesa sai kazata hira suke Chocolate din da ya ta a siya mata ya gano irin ta dana haka yace jirani ina zuwa daga haka ya tsallaka titin wajan Tun bayan rabuwar su da su hafiz jamsy ta hango su ita kuma suna tare da wani sabon Alhaji da suka hadu sosai ganin Ibrahim da Rufy ya bata mamaki kuma ya ata mata rai domin ba haka taso ganin su ba Ganin ya barta awajan ne yasa ta tsaida su suma dan ganin ina zashi wajan mai Chocolate din da taga yaje ne ya bata mamaki kenan yasan abinda Rufy take so "Kardai har sunma fara soyayya,ta tanbayi kanta Da sauri ta girgiza kai tana fa in ina hakan bazai taba yiwuwa ba wallahi ni kadai ce matar da ta dace Ibrahim yaso SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce _____________Daga inda take tsaye taga Ibrahim ya mi a wa Rufaida ladar hannun sa sosai yaji zuciyar ta ta mata zafi dan haka ta ciro waya ta kira shi Jin arar shigowar kirane yasa shi ciro wayar daga aljihu ganin wadda ke kiran hakan yasa yaja tsaki ya katse kiran nata sannan ya mai da wayar aljihu Duk abinda ke faruwa jamsy na kallo har tsakin da yayi mata sosai abin ya bata mamaki to me hakan yake nufi Ibrahim ya fara soyayya da Rufy kome Lokacin da suka koma gida Rufy zata shiga daga tunawa da ledar da ya bata yasa ta koma da baya tana fa in gashi ka manta baka kar a ba Ta fa a tana mi amai ledar hannun ta "Naki ne dan kuma bakyaso sai ki zubar Daga haka ya shige akin sa Da kallo Rufy ta bishi wannan mutum kwai ba in halin tsiya Ta fa a tana rakashi da harara Sai da ta gama duk abinda zatai ta kwanta kenan sai duk abinda ya faru azu ya fara dawo mata yadda suka ci abinci kwano aya duk da ita batafi lauma hudu tayi ba amma duk sai taji wani abu da ban Ganin wannan tunani zai arfi a zuciyar tane yasa ta dakko ledar da ya bata ba tare da ya fa a mata meye aciki ba Dubawa tayi Chocolate ce kuma wadda take so sosai wani irin farin ciki ne taji ya kawo mata ziyara domin batayi zato ba sosai kyautar tashi ta burge ta Fuska ta narkar alamar shagwa a tana fa "Ai bansan ita ka siyomin ba nake cewa mai ba in hali Please sorry Duk wannan maganar tana yinta ne kamar yana gaban ta,ganin abin nata yana neman yin yawa ne yasa ta mari fuskar ta tana fa in Rufy ki dawo hankalin ki mana wannan haukan fa To wash gari kamar yadda Farida matar hafiz ta fa a hakan ne ya kasan ce domin kuwa lokaci da hafiz zai fita tare suka tawo ya kawo ta gidan Ibrahim,lokacin ita Rufy tama manta sunyi wannan maganar dan tayi zatan wasa takeyi Lokacin da Ibrahim ya fito da shirin fita ne ya samu hafiz da matar shi zaune suna hira sai Rufy dake gefe tana sa baki lokaci lokaci "Yawwa ango muma fa zuwa anjima zamu shiga kasu ni da sister dan haka a cika mana aljihu koya kika ce ar uwa Ta arasa maganar tana kallon Rufy da kanta yake sunkuye Ita dai Rufy bata ce komai ba tana jinsu sunayi "A'a gaskiya nifa banason yawo kuma dai kinsan bata son sanyi Ibrahim ya fa a duk dan kar Rufy ta fita "A'a dan Allah karka mana haka tun jiya muka fa a yanzu dai abinda zamuyi zamu dawo da wuri ko sis Dan Allah kiyi magana mana Ta fa a tana ta a Rufy da kanta yake "Dan Allah ya..ya.. ka barmu muje Wannan maganar ta yita ne cike da inar dole ga farga ba ha i da tsoro Tsaya wa yayi yana kallon ta ganin tace mai yaya To a gidan uban wa ya zama ya'yan ta ko dai kalan dangi take ne Hafiz da ya gaji da tsaiwa ne yace "dan Allah ka sallame ta mu tafi kafi kowa sanin muna da aiki yau din nan Jin hafiz yasa baki ne yasa shi ciro kudi daga aljihu dubu sittin ne dan haka ya mi a musu yana fa "Nasan dai duk abinda zaku siya sun isheku Bayan ta fiyar su wajan aiki ne suma suka shiga kasuwa sosai Rufy taji da in fitar domin koba komai ta bu e ido amma ace tunda suka zo kullum tana gida tsawan wata aya kenan