Sashe 30
Secondary School Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai dan Allah Jamila ana dole ne soyayya a da naso ki amma yanzu banayi to kuma sai ki damu rayuwa ta ki hanani sakat dan masifa duk kinbi kin isheni duk inda naje sai kinje ,a hakan kike tunanin zan so ki baki da aji kwata kwata idan kina son yin mutunci da daraja a wajan saurayi ki bari shi ya biki bawai ke kiyi ta bin shi ba har wani gari Sosai maganar Ibrahim tayiwa jamsy zafi sai dai kuma bata tunanin wannan ihun nasa sai sa ta daina binshi domin kuwa sosai take kuma tayiwa kanta alkawarin sai ta aure shi ko ta halin a ne ko da kuwa zatai yawo tsirara Tana gama wannan tunanin ta juya ta fice mai a office ba tare da tace mai komai ba da karfi ta buga mai kofar Da kallo ya bita yana tsana tsaki hadi da fadin"ace mutum sam bashi da zuciya a rayuwar sa Haka Ibrahim ya wuni da abubuwa kala biyu a zuciyar sa tunanin jamsy da Rufy sai dai kuma na Rufy yafi karfi domin idan ya tuna ta a yadda sukayi yau da safe sai ya tsinci kanshi cikin wani irin yanayi mai wahalar misal mutuwa idan ya tuna yadda tace mai Please sai kawai yaji jikin sa yahau wani irin yamami Tsintar kanshi yayi kawai da son siya mata Chocolate din da take so dan haka ya tashi daga daga cikin masu aikin wajan ya aika ya siyomai kwalin da aya sai bayan ya aika ne kuma yake ganin to wai meyasa ma yake son siya matan gashi tunanin ta duk ya dame shi ganin abin yana neman kamar yin karfi ne yasa ya tashi office din Hafiz ya tafi ko zai samu ya man ta ************Tsaf Rufy ta zaiya newa Farida yadda sukayi da Ibrahim yau da safe ai kuwa sun sha dariya kamar me nan Farida take ara bata wasu shawarwarin, sannan kuma ta kawo mata wasu daga cikin irin turaren da itake amfani da shi Har sauri yake ya shigo gida sanda ya dawo cike da tunanin ko tayi bacci sabida goma saura bai ta a kai wannan lokacin awaje ba,zaune ya same ta tana danna wayar hannun ta duk da cewa ba babba bace amma gema take aciki Jiyayi kawai ya sauke ajiyar zuciya wadda har sai da ta fito fili, Rufy dake zaune ne ta tashi tsaye tana fa "Ina ka tsaya kai dare haka gaba aya kasa hankali na ya tashi duk wannan maganar tanayi ne bayan ta kar i jakar hannun sa, Sannan ta mika hannu zata cire mai ri...... SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce Paid page 65&66 _________Kamar yadda suka tsara da Farida yaune take so ta fara shiga akin Ibrahim sai dai ta rasa ta ina zata fara domin wani irin tsoro ne yake kamata duk da Farida tana karfa fa mata guiwa dan haka ta shirya tunkarar Ibrahim don kar ar mukullin dakin sai dai wata zuciyar tana fa a mata ai karta bari yasan ne zatayi wannan tunanin shiya dauke mata hankali har lokacin ya kure bata gama abin karya wa ba Shi kuma gogan yana can zaman jiran dan zuwa yanzu ya riga da ya saba da cikin girkin ta har takai idan ba abincin ta yaci ba sai yaji kamar baya koshi dan yasha zuwa aiki ya dawo haka ba tare da yaci komai ba bayan lemo Cikin sauri sauri ganin ya wuce lokacin da yake fita har an fara kiran shi a waya ta shirya mai abincin mainar masa tayi da miya sai kuwa ruwan tea da yasha kayan amshi sai tashi suke,ganin lokacin ya kure ne yasa ta shirya mai acikin foodflas ta ce ya tafi da shi kada makarar tayi yawa, to wannan dalili yaja har ya manta bai rufe dakin nashi ba Yana fita ta lura mai rufe ba har sai da tayi tsallan murna kamar yasan abinda take da bu ata kenan,zama tayi ta karya Sannan ta gyara gidan ko ina yayi fess kafin ta fara kokarin shiga dakin nashi a karo na farko sabida ta gyara mai Kamshin turaran shine ya fara mata sallama wadda harsai da ta rufe idon ta sabida turaran badai kamshi ba irin kamshin nan mai sanyaya zuciyar masoya kai harma makiyan ko da cikin fushi kajishi sai ya shiga ranka Fesss ta samu dakin ba wani datti sabida Ibrahim badai tsafta ba amma duk da haka ta shiga gyara sosai ko ina ya kuma yin haske ta dakko sabon zanin gado cikin wadan da tasiya ta shinfi a mai ta wanko toilet din fess sannan ta kunna turaran wuta dakin ya dau kanshi mai kwantar da hankali Lokacin da taga ma duka abinda take azahar tayi dan haka sallah kawai tayi ta zauna karatu har akai la'asar sannan ta tashi a wajan kitchen ta shiga domin tunanin abinda zata dafa ta bure Ibrahim zuwa yanzu itama ta fara jin kanata a matsayin matar aure kamar kowacce mace ba kamar da ba da take wa kanta kallon yar aikinsa Moi moi tayi musu yaji hanta sannan tayi miyar albasa sai tashin kanshi take sannan tayi zobo mai sanyi abindai gwanin sha'awa (mata mu dinga yi muna canza girki kar ace kullum muke nan cin shinkafa Yasin zaki gundiri oga Lokacin da ta gama anyi magariba dan haka tayi wanka kafin tayi Sallah zama tayi ta shafe jikin ta da mayuka masu kamshi da sa laushin fata powder tashafa kadan sannan ta feshe jikin ta da turaruka masu tsada da dadin kamshi Doguwar riga ta dakko mai karamin hannu bata kai mata har kasa ba amma dai ta sauka sosai rigar mai laushi ce hakan yasa ta biji kinta ta kwanta Tsayawa tayi tana kare wa kanta kallo sai taga kamar ba ita ba yadda lokaci aya ta canza fatarta har wani laushi take gashi ta kwanta luf luf kamar ba ita ba hakan Yasa sai take ganin abun wani iri Falo ta dawo ta zauna zaman jiran dawowar sa bata dade sosai ba ya shigo gidan bakinsa dauke da sallama,tunda ya shigo yake kallon ta ganin tayi wani irin kyau fiye da ko yaushe Tashi tayi hadda dan saurin ta wajan karasa wa inda yake tana fa in Yaya sannun da zuwa ,ji yayi wani abu ya tsargamai tun daga kafar shi har cikin walwa sabida yadda tayi maganar kamar da gayya ta fa a cikin wani irin salo mai daukar hankali Jakar hannun sa ta kar a sannan ta wuce ta barshi tsaye a wajan da kallo ya bita ganin yadda take juya mazaune take yaji wani arin abu ya taso mai ********Kaya suke ha awa cikin trolly da alama tafiya zasuyi zuwa wani wajan,jidda ce zaune gaba aya abin duniya ya isheta domin kwana biyu gaba aya bata gane kan Antyn tata sabida gaba aya ta canza kamar ba ita ba yanzu ta daina mata walwala kamar da sannan a gaban ta shekaran jiya tashi wata awar ta wadda a da kwata kwata bata ta a yadda ga ci wata idan ba jidda ba kallon Antyn tayi tana fa "Momsy wai ina zamu jene naga sai zuba kayana kike cikin trolly ? "Jidda ba inda zani kece dai lokaci yayi da zaki koma gidan ku da zaman "A'a momsy bangane ba ina kuma zan koma dama ina da inda yafi nan ne Please kimin bayani! "Ya isa jidda ya kama ta ki gane ni ba momsyn ki bace ni Auntyn kice munyi rayuwa ne na wani lokaci tare to yanzu komai yazo karshe dan haka zaki koma ga iyayan ki na ainihi "Amma mommy Naga... "Please jidda ki daka tamin banason yawan magana dan Allah na fa a miki zaki tafi gidan ku cikin yan uwan ki wannan shine kawai magana Zaman darshan jidda tayi hawaye na biyo fuskar ta domin gaba aya kanta ya kulle idan momsy ba ita ce maman ta ba to wace kenan, tana ina kuma yanzu me takeyi,me hakan yake nufi Abinka da Wadda kanta ba dai dai ba nan da nan kuwa taji kanta ya fara ciwo sabida tunanin da ta damu walwar ta da shi Kamar yadda Aunty ta fa a da kanta tasa jidda a moto bayan sallar magariba suka tafi unguwar su lokacin ba nuta ne sosai sabida duhu da gari ya fara Kwata kwata jidda kin yadda tayi ta fito daga motar har saida Aunty ta Mata tsawa sannun ta fita,kayan sawar ta ta fito mata da su sannan ta nuna mata gidan bayan ta shiga Mota tana fa "Nan shine gidan ku ki shiga ciki zakiga yan uwan ki Daga haka ta ja motar ta tabar wajan ba tare da ta jira abinda jidda zata ce mata ba Tun lokacin da motar ta tsaya a kofar gidan Baba zeey na kallon abinda ke faruwa tare da baban jidda kasan cewar suna daga wajan bishiya a zaune kallon ikon Allah suka tsaya yi ganin macece ta kako jidda kuma har ana kokawar fito da ita daga mota Ganin tatafi tabar jiddan a tsaye a wajan ne kuma ita ko motsawa bata yiba ne yasa baban zeey cewa "Ya kamata mu tashi muje don ganin meke faruwa Sosai sukayi mamakin ganin jidda ce dan duk zaman da suke Basu san wa aka sauke ba Baban zeey ne yakai hannu ya ta ota domin tabbatar da cewa ita din yake gani Da sauri ta kwace hannun ta tana fa in karka kuma ta ani,sosai yadda tayi maganar abin ya basu mamaki hadi da tsoro anya wannan jiddan su ce idan kuwa ita ce to lallai akwai ayar tanbaya akan ta domin kuwa kanta ba kalau yake ba ar aka samu ta shiga gidan shima da kokawa dan har baban ta yayi fushi yace a barta taje duk inda zata tunda bata da mutunci Sai da baban zeey ya bashi hakuri tare da maman zeey da umman jidda da ta fara kuka tun sanda ta ganta sannan ya hakura Tunda aka shigo da ita gidan take kuka kamar ranta zai fita sabida tsabar kuka a haka aka kwana batayi bacci ba suma kuma bata bassu sunyi baccin ba SECONDARY SCHOOL (Love & romantic story) Shalele ce Paid page