← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 25

Sashe 6

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mom ce
ta nufo dakin domin dubashi tana shiga ta
ganshi kwance yana bacci inda yake kwance ta
karasa ta cire masa takalman dake kafarsa taja
blanket ta rufe shi ta juya ta fita tana murmushi
domin babu abinda take so irin taga junior cikin
farin ciki da nishadi, tana zuwa falo taci karo da
kawarta hajiya yabi, barka da zuwa mutanen
jidda, mom ta fada tana murmushi, yawwa
barkanki dai hajiya Fati, wuri suka samu suka
zazzauna, momyn junior ga sakon naki ya iso
sarkar da na siyo miki agaskiya mai tsada ce
kuma ba ta kananan mutane bace, karbar sarkar
mom tayi ta fara duddubata yar siririya amma
da gani mai tsada ce, yawwa hajiya yabi dadina
dake kin iya zabe, dama junior ne zai bawa
wata girlfriend dinshi a matsayin gift saboda
zata yi birthday ne next week, mom ta fada
cikeda farin ciki, kallonta hajiya yabi ta danyi, ni
kuwa hajiya fati sai nake ganin kamar abinda
kike yi kuskure ne saboda su yara tasu kyau
take bata karko domin duk yadda ka dorasu
haka suke tashi, shi junior yanzu bai san rayuwa
ba saboda baku koyar dashi ba, abin takaici ne
ace wai kina goya masa baya akan yayi abota
da wata ya mace wadda baki san ko wacece ba
alhalin shi kuma yana baligi, hajiya Fati bafa ya
mace bace kadai ke dauko abin magana ba wlh
da namiji ma yana daukowa kuma ya kamata ki
rinka bincikar abokansa saboda bada kowa zaki
barshi yayi abota tunda har yanzu junior yarone
karami bana tunanin ya wuce 27, take fuskar
mom ta sauya bacin rai karara ya bayyana akan
fuskar ta, hajiya yabi dama abinda ya kawoki
kenan?

Kinzo ne kici min fuska ki zage dana
tatas?

Daidai lokacin junior ya fito daga daki
daga shi sai dan karamin blue din wando da
rigarsa yar karama irin na yan ball, tsayawa yayi
ba tareda ya kalli ko inda hajiya yabi take ba
yace mom wai dan Allah wacce talkative din
kika samune haka?

Haba wannan matar ta cika
surutu tun ina bacci take damuna har sai da ta
tasheni, gaskiya ni ban son irin wannan mom,
adaina tashina da surutu, cikin kwantar da
hankali mom tace yi hakuri yarona, koma ka
sake kwanciya kaji, mom ai kun riga da kun
tasheni kawai, ni yanzu filin ball zanje.

Yana gama fadin haka ya juya ya fita yana
hararar hajiya yabi saboda duk maganganun
data fada acikin kunnensa ne, duk ya jisu, yana
fita mom tace hajiya yabi naji maganarki kuma
nagode amma dan Allah idan babu damuwa
daga yau kar ki kara zuwa gidana, yanzu bari na
kawo miki kudin sarkarki, rike baki hajiya yabi
tayi hajiya fati daga fadar gaskiya?

Allah ya
huci zuciyarki,ba tareda mom tace komai ba ta
mike ta nufi dakinta mintuna kadan sai gata
rikeda kudi rafa rafa sababbi fil, mikawa hajiya
yabi tayi, gashi hajiya nagode, tashi hajiya yabi
tayi shikenan hajiya fati ubangiji Allah ya sada
mu da alkairi, amin mom ta fada lokacin da take
barin falon
[1/30, 7:33 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
3�3�

Junior yana fita ya dauki bicycle dinsa ja
domin dama wani lokacin akan keke yake yawo,
filin kwallon unguwarsu bobo ya nufa wato
sharada, yana tafe yana jin kidan da ya kure
acikin wayarsa ya cuccusa earphone acikin
kunnensa, daf da wata kwana ya hango kuluwa,
kunu yasha itama tana hangoshi tasha kunu ta
bata rai, wucewa yayi ba tareda ya kalletaba,
itama bata kalleshi ba ta wuce dama lokacin
islamiyya zataje Kuma ita kadai take zuwa
domin ummi ita tayi sauka tuntuni, filin kwallon
kusa da gidansu bobo junior ya karasa yana
zuwa aka fara ihu, saboda ganinsa, sauka yayi
daga keken ya shiga filin wasan, take aka fara
wasa mai zafi sai daf da magrib sannan suka
bar ball din shi kuwa dama junior salla ba wani
damunsa tayi ba saboda bai ma cika yinta ba,
mota bobo ya dauka yake biye dashi shikuma
yana kan keke yana kuma buga kwallo da
kafarsa, dai dai kwanar dazu da yaga kuluwa
yanzu ma nan ya ganota, da saninsa ya daki
ball din da karfi taje ta doki keyar kuluwa da
sauri ta juyo, ganin junior ya sata daure fuska,
bobo ne ya bude motarsa ya fito, yauma an
samu akasi matar junior, da sauri junior ya
kalleshi what?

God forbid me zanyi da bakar
fata, wata harara kuluwa ta aika masa sannan
tace ai ko Senior ne bashida wannan matsayin
balle wani Junior, God forbid me zanyi da jan
lebe?

Tsaki junior yaja dalla bobo muje kar kasa
wannan village girl din ta bata min rai a banza,
gaka nan dan kauye tafada tana murguda baki.

Kallo junior ya bita dashi, kiyi hakuri matar
junior bobo ya fada yana dariya, kallonsa bobo
yayi Allah kiyaye na auri yar kauye, ni ma babu
abinda zanyi dakai, kudai yi hakuri domin ba
asan inda rana zata fadi ba, a yamma saboda
acan ta saba faduwa kuluwa ta fada tareda
daukar hanyar gida, tana zuwa gida ta fara
bawa ummi labari, ummi ina dan rainin hankalin
nan na rannan dana fada miki?

To yauma mun
sake haduwa munyi fada, dariya ummi tayi your
fighting partner??

Mijinki zaki cemin ai sai nafi
ganewa, sai kiyi kuma, nama fasa baki labarin,
kuluwa ta fada tana hararar ummi.

Shi kam junior kekensa ya murza ya tafi ba
tareda ya cewa bobo komai ba yana tafe yana
jin wakar p square if do me i do you man......!

Bobo kuma yana binsa har suka karasa gidansu
junior anan suka rabuda bobo shi ya shiga gida
bobo kuma ya juya.
[1/30, 7:40 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
3�4�

Junior yana shiga cikin gidan ya wuce falon
mom Wanda yake tafkeken gaske, kan dining ya
hau ya fara kokarin duba abinda zai ci, shinkafa
ya diba yar kadan wanda ba zata fi cokali biyar
ba ya fara ci ahankali, fuskar kuluwa ya hango
lokacin da take musu masifa shida bobo "yi
hakuri matar junior" maganar da bobo ya fada
ta dawo masa cikin kunnensa," ni me zanyi da
jan lebe" amsar da ta bawa bobo itace ta sake
dawo masa, murmushi yayi shi kadai lallai
wannan yarinyar itama tana ji da kanta, fitowar
mom ce ta katse masa tunaninsa, junior whats
it?

Naga kanata murmushi kai Kadai, babu
komai mom amma dai kawai yau babu abinda
ke damuna shiyasa naji inata annashuwa,
murmushi mom tayi to ga sarkar nan can an
kawo maka wadda zaka bawa teemah gift din
birthday dinta, tnx mom amma matar nan ta
dazu ta bata min rai, meyasa mutane suke da
munafurci ne mom?

Nifa abinda ake min a garin
nan ya fara damuna, wlhi matar nan ta dazu
taci darajarki mom da sai na zageta, kayi hakuri
junior, mutane sun sako min kai a gaba, na rasa
me ka tare musu, tsaki junior ya danyi tareda
tashi ya nufi dakinsa yana zuwa ya haye
gadonsa ya dauki remote ya kamo tashar music
ya fara kalla.

Koda dare yayi kuluwa bata iya runtsawa ba,
tunanin junior kawai take yi, kuma shi take ta
hangowa a idonta, zaune ta tashi tabi ummi da
kallo wadda ke ta sharar baccinta, junior dinnan
fa daga gani ba shiryayye bane kuma ba nagari
bane saboda yadda yake sa sarka da dan kunne
kai idan ba sani ma kayi ba bazaka taba
tsammanin musulmi bane saboda yadda yake
dabi'unsa da halayyar sa, kuma da gani bayaji
sannan kuma gagararre ne, to ni yanzu meye
nawa na tunaninsa?

Ta fada acikin ranta,
komawa tayi ta kwanta duk kuwa da cewar ba
iya baccin zatayi ba, babu shakka junior ya
hadu iya haduwa to amma anya zai so mace
kamata wadda ta fito daga kauye??

Tambayar
da tayi ta yiwa kanta kenan amma kuma bata
da amsa.

Abangaren junior shima hakan take domin koda
ya kwanta domin yin bacci kasawa yayi, tunanin
kuluwa ne ya addabi ruhinsa, hakika yasan ya
kamu da sonta to amma taya zai furta mata?

Shifa yanmata hadaddu ma sune ke cewa suna
sonsa ba shine yake cewa yana sonsu ba, ruf da
ciki ya juya yayi, yafara shafa keyarsa, tab
wannan shine gamo ya fada ahankali, daren
ranar da kyar ya samu bacci ya dauke
shi,washe gari kuwa sai da yakai 11 akwance
yana ta bacci, bayan ya tashi ne yayi wanka ya
shirya cikin bakin boxer da jar t shirt mai hoton
yan yatsu ajiki, tulin sumarsa ya fara tajewa da
cumb bayan ya makala dan karamin dan
kunnensa ajikin kunnensa na hagu sannan yasa
katuwar sarkarsa wadda tsayinta yazo har kan
kirjinsa, cumb din ya dauka ya nufi falo yana
tafe yana taje sumarsa yana wakar if u see this
baby o.oh she was chop my money, because i
don't care, don't care, falon dad dinsa ya nufa
yana mai ci gaba da tajar sumarsa, afalo ya
tarar dasu dad and mom dinsa suna kan dining
suna yin breakfast, good morning dad, mom
good morning ya fada lokacin da yake Jan
kujerar da zai zauna, morning junior, dad ya
fada yana dafa kafadar junior tareda dan
murmushi, har an tashi??

Dad na tashi dakyar
saboda ina son naje na koyawa dokina tsere,
bana son na barshi haka, yana da kyau ai hakan,
dad ya fada, junior me zaka ci?

Mom ta
tambaye shi, mom ki barni yanzu babu abinda
zan iya ci saboda koko kawai nake son sha,
koko junior??

To ni yanzu ina zan samo maka
koko junior??
Chapter 6 · 0% Book details