← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 25

Sashe 10

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kuluwa yayi ta danyi kiba kuma ta sake
zama budurwa cikakkiya, tana sanye da leshi
blue da farin hijabi mai hannu, takalminta ma
fari ne, so yanzu kin zama budurwa babu
maganar saka uniform ko??

Ya fada yana
kallonta, kallonsa tayi ta basar malam lfy?

Ido
ya dan kashe mata tareda duban kawar tata,
baiwar Allah dan bamu wuri zamu yi magana,
tafiya maimuna s alkali tayi ta barsu a tsaye,
baki gane ni ba??

Dan Allah kibani number
wayarki zamuyi magana, nifa banida waya kuma
dan Allah kar ka sake kulani saboda mutane
suna ganina da mutumci yanzu kuma idan suka
ganni da mai dankunne a tsaye zasu yi min
fassara kuma mutuncina zai ragu a idonsu, ras
yaji gabansa ya fadi, anya kuwa wannan
yarinyar zata soshi?

Ya tambayi kansa, oh dan
nasa earring da chain shine mutumcinki zai
zube?

Basu kadai ba har wannan kayan jikin
naka duk Suna iya janyo min zubewar mutunci,
ok to yanzu dai ki bari muyi magana, da wa?

Dake mana, a'a kabari duk lokacin da kayi shiga
irin ta mutanen kirki sai kazo muyi magana,
tana gama fadar haka ta wuceshi tayi tafiyar ta,
gosh!

Ya fada tareda dunkule hannunsa ya
naushi iska, cikin mota ya koma duk jin zaman
yake ya isheshi, wato kenan idan nacire chain
dinnan da dan kunnen nan zata tsaya ta saurare
ni?

It seems kamar wannan shigar da nayi ne
bata so, zancen zuci yayi tayi har bobo yazo ya
sameshi, jikinsa a sanyaye yaja motar suka fita
suka nufi gida, yana zuwa gida ya fada akan
kujera a falo lokacin mom bata ciki tana side din
dad, nan ya zauna har tazo ta sameshi kamar
marar lafiya ya zama, junior lafiya?

Mom ta
tambayeshi cikeda rudu, lafiya lau mom, dad
yadawo?

Eh ya dawo dazu, mom dan Allah
manyan kaya nake so tun daga shaddodi har
yadika, to junior nima dama na dade ina son
naganka da irin kayan da yayan manya suke
sakawa amma tunda yanzu da kanka kana so
shikenan bari ina zuwa, daki mom ta shiga ta
dauki wayarta takira tailor din dake yi mata dinki
yana dauka tace dashi yaje kasuwa ya siyowa
junior shaddodi masu tsada da hadaddun yadika
adinka masa idan angama an kawo zata biya
kudin, murna ta fara yi oh junior an fara girma
da hankali da alama yanzu nutsuwa ta soma
shigarsa, falo ta koma inda yake.

Tana komawa ta sameshi yana waya da teemah
big girl, zama tayi akusa dashi, kansa ya dora
akan cinyar mom, mom yanzu idan nasamu
mata zaku yimin aure??

Me zai hana junior na,
ai zanso naga matarka da yayanka, uhm amma
mom nifa ba yaro daya zan haifa ba ni dayawa
nake so, shafa kansa mom tayi Allah ya amsa
junior dama yanda kake kai daya agidan nan
Allah yasa yara dayawa zaka haifa, amin mom,
farin cikine ya shiga ransa domin sai yanzu yaji
yana son yin aure kuma yaji yana sha'awar ya
fara saka manyan kaya.

Kwana biyu junior yana gida babu inda yake
zuwa har sai da aka kawo masa kayansa,aranar
ya yi wanka ya shirya cikin shadda sky blue mai
tsada, baisa dankunne da sarka ba, sai da yasha
turare sannan yayiwa mom sallama ya fita
kallonsa mom tayi to kodai junior ya fara neman
auren ne??

Motarsa ya dauka mai kyau kirar
corotoure ya nufi b.u.k ko takan bobo bai bi ba,
a admin block yau ma yayi packing yana nan
zaune yana tunanin abinyi kamar daga sama sai
ya hango su kuluwa su uku wadda suka fito
daga wani office,
sai raba ido takai ta inda zata ga junior domin
tunda abin ya faru kullum idan tazo sch bata
samun nutsuwa duk tunaninta junior fushi yayi,
ranar kasa bacci tayi saboda tana gudun kar ya
subuce mata, yana ganinsu ya fito daga cikin
motar, ganinsa kawai tayi a gabansu amma tuni
ta gane shi, kallon juna suka fara daga ita har
shi, yayi kyau sosai yayi wani irin kwarjini,
Gashi da kalar yan gayu domin kana ganinsa
kasan dan gayune, barka da fitowa ya fada cikin
muryarsa mai tsananin dadi da zaki, kallon
kawayenta tayi kuyi gaba sai na taho ina zuwa,
suna wucewa ya kalleta pls mu shiga cikin mota
because am not comfortable for this hustle and
bustle, wurin naku yayi hayaniya da yawa ni
kuma bana sonta, kamar ba zata shiga ba sai
kuma dai taga rashin dacewar haka, gidan baya
ta shiga shi kuma yana gaba a mazaunin driver,
malama har yau fa ban san sunanki ba, sunana
hawwa ta fada a hankali kai kuma ya sunanka?

Sunana Abdulrahman, sunanka junior dai tafada
tana kallonsa, eh wannan sunan da mom dina
take kirana dashi ne.
[1/31, 8:14 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
4�2�

Kallonsa kuluwa tayi da alama dai yana ji da
mom dinnan nashi sannan kuma tana gatale shi
abisa dukkanin alamu, maijidda me yasa kika ki
saurarata rannan??

Sai da ta danyi Jim sannan
tace masa, kaga nan ai wurin mutane ne
dayawa kai kuma ranar a yadda ki fito gaskiya
bai dace ba amma yau dressing dinka yayi
daidai dana mutanen kirki amma idan kaji
haushi kayi hakuri, no ba haushi naji ba wlh dadi
naji yadda kika fadamin gaskiyarki kuma naji kin
burgeni shiyasa nake son ki zama friend dina
idan har ba zan takura miki ba, dan murmushi
tayi bana yin abota da maza amma kai bazan ki
ba, saboda me?

Saboda wani dalili, to nagode
da wannan alfarmar da kika yimin, kibani phone
number dinki, ai na fada maka banida waya, ok
idan na siyo miki zaki karba?

No ai agida ne har
yanzu ba za abarmu mu rike wayar ba, to ba
damuwa zan iya zuwa gidanku?

A'a ba za
abarni na fito ba, to zan rinka zuwa nan din,
babu damuwa sai kazo, to yanzu zanje natafi
sai na dawo, ok babu damuwa, nagode, fita tayi
ta nufi wurin da kawayenta suke shi kuma junior
sai da ya dade a zaune kafin ya tafi, tafiya
kuluwa kawai take amma tunanin junior ne yake
ratsata koda taje wurin kawayenta ma tambayar
ta suka fara yi wai ina tasamo wannan mai
kyan?

Murmushi kawai tayi mijina ne tafada ba
tareda ta sani ba, mijinki?

Sai asannan tasan
maganar ta fito, acikin ranta tace Allah ya amsa
domin abokinsa da matar junior ya kirani bazan
taba mantawa ba, ummi ma dana bata labarinsa
cemin tayi mijina ne, duk acikin zuciyarta take
wadannan bayanan.

Abangaren junior kuwa wurin bobo ya nufa
bayan yabar wurin kuluwa, labarin kuluwa ya
fara bawa bobo, bobo in banda dariya babu
abinda yake yi.

Tun daga wannan ranar junior ya ke zuwa wurin
kuluwa a makarantar su yanzu sunyi mutukar
sabo da junansu kuma sun shaku kowa yana
tsananin son dan uwansa amma har yau babu
wanda ya furta, ita kuluwa tana ganin a
matsayinta na mace ai bai kamata tace tana
sonsa ba, shi kuma junior yana ganin shi duk
wadda yayi mata itace take cewa tana sonsa
amma shi baya furtawa mace kalmar so sai dai
idan bada gaske yake ba sai ya fada amma shi
baya cewa mace yana sonta,yau ma tsaye suke
ajikin motarsa yana sanye cikin farin boyel
yasha kyau har ya gaji duk wanda zai wuce sai
ya kallesu amma mafi akasari junior suke kallo
ba kuluwan ba domin junior ya hadu iya haduwa
komai nasa ya tsaru, kallon hannunsa kuluwa
tayi, junior ya kamata ka yanke farcenka fa kaga
yadda yayi zako zako, oh yah zan je na yanke
sai nakoma gida mom dina zata yanke min,
yanken farcen ma mom ce take yi maka?

Eh nifa komai mom dina ce ke yimin, ke barima
kiji ni ko abinci mom dina ce ke bani wlh,babu
abinda nake yi, yanken farce, abinci da sauran
wadannan small small things din duk mom ce ke
yimin, to kuma idan ka koma ghana waye ke yi
maka??

Farce Patricia ce ke yanke min, take
kuluwa ta hade rai ta bata fuska, wacece haka?

Junior wai meyasa kai baka jin tsoron mace ta
tabaka?

Babu kyau fa wlh akwai wani hadisi
dana taba karantawa da mutum ya taba matar
da ba tasa ba...

To ke wai wa ya ce miki tabata
nayi?

To in ba tabata kayiba me kayi?

Allah ya
baki hakuri, yabaka hakuri dai, amma dan Allah
kasamu islamiyya ka rinka zuwa kana jin hadisai
da fassarar littafi mai tsarki, nagode da wannan
shawara, zan barki haka zanje gida kin san jibi
zanje ghana, gabanta taji ya fadi saboda sai duk
taji hankalinta ya tashi da zai tafi, ina sonka
junior ta fada aranta, meyasa zaka barni?

Takara fada acikin ranta, sai nazo sallama gobe,
ok babu damuwa, sallama suka yi yatafi.

Tunda yaje gida ya zauna yayi tagumi domin ya
rasa yadda zaiyi da son kuluwa dake azalzalarsa
gashi shikuma yarasa dalilin da yasa yake
nauyin bakin sanar mata da sirrin ranshi, washe
gari haka ya shirya yana cikeda damuwa ya nufi
b.u.k amma kananan kaya yasa yayi kyau sosai
amma sumar sa tana nan tuli guda yakasa
askewa domin yana son sumar nan bayajin zai
iya asketa, inda suka saba zama yauma anan
suka zauna kowannensu zuciyar sa cikeda
kuncin rabuwa da junansu da za suyi, kamar
marassa lafiya suka dan taba hira,
kallonta junior yayi kinga gobe zan koma ghana,
eh nasani Allah yakaika lafiya sannan kuma
akoda yaushe ka rinka tuna hakkin Allah akanka,
ka tsare hakkokin Allah da suke kanka, insha
Allah ya fada yana kallonta da idanuwansa
wadanda suka danyi ja, ita kanta kuluwa ji take
kamar ta fashe da kuka, sanin idan yaci gaba da
ganin kuluwa zai iya yin kuka agabanta yasa shi
yi mata sallama ya tafi.
[1/31, 8:18 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
4�3�
Chapter 10 · 0% Book details