← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 25

Sashe 17

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe 1 na rana suka sauka a garin ciyako,
nan driver ya shigar mata da kayanta, iyatu tana
kwance ba ta da lafiya tun sati biyu da suka
wuce ko tashi bata iya yi, babanta kuma yana
zaune a tsakar gida, ganinta ya sashi fara fara'a
"yau su hawwa'u ne agidan?", "eh nice baba",
karasawa tayi ta durkusa agabansa, driver ne ya
shigo da akwatinta bayan sun gaisa da babanta
yace "hajiya da akwai wani abu ko na tafi?"
"A'a malam Isah kaje kawai Allah ya kiyaye
hanya", "amin amin hajiya" ya fada tareda dan
russunawa.
[2/6, 6:27 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�5�

Cike da annuri mahaifinta ya dubeta "kuluwa
kinga abinda nake fada miki da jimawa ko?

Dama nasan insha Allahu rayuwarki ba zata
tozarta ba kuma naji dadin hakan, Allah ya barki
da mijinki lfy", "amin baba" kuluwa ta fada tana
sunkuyar da kai, "baba iyatu bata da lafiya ne?",
"Eh tafi kwana 10 akwance da a asibiti ma take
to jiya sai suka sallamomu suka ce mu dawo
gida", "ayya Allah ya bata lafiya baba", "amin
hawwa'u ina mijin naki?", "Baba yana can a
Ghana sai ya dawo zai zo mu tafi tare", "to
shikenan abu yayi kyau, Allah ya dawo dashi
lafiya", "amin baba", kayanta ta kinkima takai
dakin iyatu ta ajiye ta kwanta dan ta huta amma
tunanin junior ya hanata, tabbas duk labaran da
taji an bayar akan junior gaskiya ne sai dai ita
kuma wannan ba zai zama dalilin da zai Sa ta
rabu dashi ba, sai dai tayi alqawarin nuna masa
bacin ranta,iyatu ce ta motsa ta kalleta baki a
karkace, "kuluwa yaushe kika zo?", "Sannu iyatu,
ya jikin naki?", "Da sauki", "dazu Nazo iyatu
Ashe baki ji dadi ba?"
"Wlh", "to Allah yasa kaffara ne", "amin hawwa,
dan Allah kiyi hakuri ki yafe min nasan duk
hakkin ki ne yake bibiyata", "babu komai iyatu
na yafe miki duniya da lahira", "nagode kuluwa
Allah yayi miki albarka", "amin iyatu, Allah ya
baki lafiya".

Tunda kuluwa tazo gidan kullum
itace ke jinyar iyatu har tayi sati daya da zuwa,
duk ta shiga damuwa amma kuma babu halin ta
fita tunda bata sanar da junior ba kuma tasan
fita ba tareda izinin miji ba laifi ne babba, yaro
ta samu ta aika shi gidan mairo tace "yace
mata tazo gari", aranar da yamma sai ga mairo
agidan da yaranta, dakin baban kuluwa suka
shiga suka fara chafta, "kuluwa amarya ya mijin
naki?", "lafiya yake Mairo, Ashe dai haka aure
yake da dadi Mairo?

Ai ban gane ba har sai da
nayi", "kuluwa ai kedai ki bari amma gaskiya
aure yayi, naga ma kamar ciki ne dake", "wlh
Mairo ni banida wani ciki yanzu ma fashin salla
nake yi", "ah to zan kawo miki kayan gyara kin
San idan mace ta gama tana dan budewa, dan
haka zan aiko miki da bagaruwa da ganyen
magarya da zarar kin gama ki tafasa kiyi amfani
dashi", "to Mairo na gode", kuluwa ta fada,
"dama kina amfani da almiski ko?" "Eh tun kafin
nayi aure ina using dashi", "yawwa to kici gaba
zaki bani labari", dariya kuluwa tayi saboda ba
zata iya fadawa Mairo Cewar har yau babu
abinda ya gudana tsakaninta da junior ba, nan
dai suka sha hirarsu Mairo ta tafi daf da
magriba.

Kwanan kuluwa 10 a ciyako junior ya sauka a
Nigeria, yadda bata sanarwa da kowa ba haka
shima bai sanar da mom cewar bata nan ba,
aranar da yazo da yake zuwan safe yayi ya nufi
gidan mom, rungume shi mom tayi, "barka da
dawowa junior na, ina matar taka?

Ta fara
laulayi ko?" Murmushi junior yayi "mom ita ko
ciki ma bata dashi", "me kace junior?

Har
yanzu?", "Wlh mom ni har yau babu abinda ya
shiga tsakaninmu saboda da zarar naje da
niyyar kusantar ta kasawa nakeyi", "amma junior
me yasa tun lokacin baka sanar dani ba?

Kai
junior har yanzu na fahimci kuruciya na
damunka, ba a boye irin wannan matsalar, ni ya
kamata ka sanarwa tunda nice na haifeka amma
insha Allahu za a samu waraka, zauna ina
zuwa".

Ummi A'isha[2/8, 8:43 PM] Ummi A'isha:
SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�6�

Tashi mom tayi ta nufi dakinta ta dauko
gyalenta "maza tashi muje", tashi junior yayi
yabi bayanta, "dauko mota kazo mu tafi",
motarsa ya dauko mom ta shiga yaja suka fita
daga gidan, unguwa uku suka je wurin wani
malamin zaure, yana da almajirai fiyeda guda
Dari sai karatu suke tayi a kofar gidan nassa,
lokacin da suka shiga wurinshi mom da kanta
tayi masa bayanin komai, girgiza kai yayi
"tabbas ana samun irin wannan matsalar amma
ba komai bane face sihiri dan haka sai a kula da
yawaita addu'o'i da ambaton Allah a kowanne
irin lokaci", tunani junior ya fara tabbas teemah
ce tayi masa wannan aikin, rubutu malamin yayi
a allo ya wankewa junior yasha "yace insha
Allah za asamu waraka amma asa acikin rai
sauki daga Allah yake domin shi keda ikon
warkarwa ko kuma dorawa", "to Malam na gode
yanzu menene abun sadaka?" "Hajiya ko naira
Dari kika bayar ta isa", "a'a Malam ga wannan
dai Allah ya saka da alkairi", tashi suka yi suka
fito junior na gaba mom tana biye dashi, bayan
sun koma gida ne yake sanar da mom cewa "zai
tafi ciyako yanzu saboda kuluwa ma tana can
ganin gida", adawo lafiya mom tayi masa ya
tafi,gidansa ya koma yayi wanka ya dauki duk
abinda zai bukata ya kama hanyar chiyako.

Karfe 5 na yamma ya shiga cikin kauyen, sai
da yayi tambaya kafin ya samo gidan su
kuluwar, kansa tsaye ya shiga gidan bayan ya yi
packing din motarsa a kofar gidan, lokacin da ya
shiga kuluwa tana tsakar gida tana tafasa
bagaruwa da ganyen magaryar da Mairo ta
kawo mata, babanta kuma yana kishingide,
sallama yayi cikin muryarsa mai sa kukuwa jin
kasala, take ta gane shine, "sannu da zuwa",
babanta ya fada bayan ya amsa sallamar tasa,
"karaso karaso mutanen turai, ni ai rabon da na
ganka tun baka fi shekara uku ba", kusa da
baban junior yaje ya zauna ya fara gaisheshi ita
dai kuluwa dan kar agane tsakaninta da junior
akwai matsala ne ya sata yi masa sannu da
zuwa gamida gaisheshi amma duk fuskarta babu
walwala, daki ta koma ta dauro zani tazo ta
juye kayan data dafa ta shiga wanka duk junior
yana kallonta amma sai hirar su suke yi shida
babanta.

Har dare yayi junior suna tare da
baban kuluwa hatta salla tare suka yi duk
kuluwa tana jinsu lokacin da take yin abinci, sai
da suka ta da sallar magrib sannan ta dan samu
damar kallon junior tunda lokacin suna salla
tasan ba ganinta zai yi ba, yana sanye da
manyan kaya milk colour din yadi da hula yayi
wani fresh dashi gashi fatarsa tayi haske, daki
ta wuce wurin iyatu suka fara hira domin yanzu
ta dan samu sauki sosai.

Bayan ta gama girkin
ne ta zuba musu shida baban ta kai musu ta
koma daki bata san lokacin da suka gama hirar
da babanta ba saboda ita tana yin sallar isha
tayi bacci dama lokacin iyatu ta dade da bacci
da yake lokacin sanyi ne.

Cikin bacci taji anyi sama da ita kamar a
mafarki, tsorata tayi sosai sai kuma taji kamshin
turaren sa, da saura kadan ta kurma ihu, a dan
dakin dake cikin soro ya shigar da ita dama
anan yayi masauki, dakin duhu didim ga uban
sanyi saboda ko kofa babu aciki, gashi iya
tabarma kawai ce aciki sai dan abun rufar da
bashida wani kauri, ko pillow babu,ga uban
sauro, tausayin junior taji ya shigeta musamman
ma da ta tino irin gatan da yake dashi, agida
dakinsa ko na sarki iyakaci kenan amma yau
gashi ya na kwance akan tabarma alhalin shi
gadonsa ma ba a kasar nan aka sai masa ba,
kwantar da ita yayi ajikinsa, yafara kissing din
wuyanta da fuskarta "jidda meye haka??

Me
yasa zaki yi min haka?", "Me nayi maka?

Ai ni
banyi maka komai ba saboda dama can nasan
ba sona kake yi ba", "wa ya fada miki bana
sonki?", "Ai da kana sona da zan sani, dama ko
Kalmar so baka taba furta min ba", kansa ya
dora a tsakiyar na shanunta ya shafo fuskarta
"wlhi jidda ina sonki, ke kadai ce macen da
gangar jikina da ruhina ke so, wlh ina sonki har
acikin raina", "ai junior duk abinda zaka fada ni
yanzu bazan yarda da kai ba saboda nasan duk
ba gaskiya bane", hannunsa yasa ya damko na
shanunta guda daya "wlh gaskiya nake fada
miki ki yarda dani", "wlhi bazan yarda dakai ba
junior saboda baka da gaskiya ko kadan, akwai
wacce kake so na sani to nima ina da wanda
nake so tun kafin na aure ka, dan haka ka
sakeni nima na auri mai sona, ka sakeni, dama
can ni shamsu nake so",wai ji yayi kamar ta
zuba masa wuta hannunsa junior ya janye daga
kan dukiyar fulaninta ya matsa daga jikinta
"tashi ki fice min anan" ya fada cikin tsawa,
"nace ki tashi ki fita, i said get out" ya sake
fada cikin tsawa, tashi tayi ta fita jikinta har
rawa yake yi saboda tsoron junior bata taba
Sanin haka yake ba, dakin iyatu ta koma ta
kwanta ta fara kukan zuci har tsawon wani
lokaci, shima junior hakan take saboda kalaman
kuluwa sunyi mutukar yi masa zafi, "shi zata
kalla tace ya saketa saboda da taga ya kasa
biya mata bukatar ta?" Hawaye ya fara zubarwa
saboda bacin rai,wannan shine karo na farko da
yayi kuka tun tasowar shi domin SANADIN GATA
yasa iyayensa kauracewa duk wani abu wanda
zai iya sashi kuka, daren ranar bai yi bacci ba.
Chapter 17 · 0% Book details