← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 25

Sashe 25

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Me kike sha'awa?" Gashi yanzu mom ta
hanata aiki babu wani abun da take yi in banda
dawainiyar junior gashi kusan kullum sai sun fita
yawon zaga gari ita dashi.

Sannu ahankali
cikinta ya girma cikin kulawa da koshin lafiya,
alokacin taga gata wurin junior domin komai
shine yake yi mata tundaga kan wanka, wanki,
yanke farce, tsifa, shaving, gyaran daki, girki,
komai shine yake yi mata domin yana mutukar
tausaya mata, lokacin da cikinta ya shiga wata
tara da kwana goma ta tashi da azababben
ciwo, cikin rudewa junior ya dauketa ya kaita
standard hospital suna zuwa akayi maternity da
ita, gefe junior ya koma ya kasa zaune ya kasa
tsaye gashi saboda tsabar rudewa da burkicewa
ma ya manto phone dinsa agida balle ya kira
mom, mintuna kadan nurse ta fito ta kirashi tare
da yi masa albishir din kuluwa ta sauka lafiya ta
haifi yaronta namiji, "zan iya ganinta?" "No
kabari yanzu mun shigar da ita dakin hutu sai
nan da 20 minutes zaka iya ganinta" da sauri ya
juya ya nufi motarsa ya shiga dagudu ya figi
motar ya nufi gidan mom yana zuwa ya sameta
ta caba ado tana zaune tana waya "mom, mom
where are you?

Jikinta yaje ya fada yana
dariya,"mom yarki ta haihu yanzu" cikeda murna
mom ta tashi "dagaske junior?

Me ta Haifa?"
"Mom an samu little junior" da sauri mom ta
nufi dakinta taje ta dauko mayafinta ta fito
gashi lokacin dad baya nan ya tafi taron siyasa
mintuna kadan suka isa asibitin lokacin har an
fara shiga ganin masu haihuwa, suna shiga
dakin da kuluwa take junior yaje ya rungumeta
ko kunyar mom bai jiba "sannu jidda na nagode,
nagode jidda" hannunta ya kama ya rike cikin
nasa,"sannu hawwa, sannu kinji" mom tafada
tare da karasawa inda jaririn yake ta daukoshi
bashida maraba da junior lokacin data
haifeshi,gefen gadon ta samu ta zauna tana
murmushi "like a father like a son" hannun
kuluwa ya saki duk idonsa ya ciko da kwallar
farin ciki ashe dama zai ga danshi na kanshi?

Karbar jaririn yayi daga hannun mom ya fara
kallonsa.

Ganin bata da matsalar komai yasa
aka basu sallama, gidan mom suka wuce direct
nanfa junior ya fara tambayar mom "mom to
kuma nida wa za abarni agidan?" "Kai kasani
mom ta fada tana dariya tana rike da jaririn
"shikenan mom tunda yanzu kin daina sona"
junior ya fada cike da shagwaba.

Suna zuwa gida suka wuce side din mom wani
daki dake kusa da nata ta bude musu kayan
jarirai ne aciki iri iri da kayan wasansu nan aka
shiga nunawa kuluwa gata ita da jaririnta, kafin
wani lokaci sai ga su Anty Salma da Ummi
amarya, nan Ummi ta dauki yaron tana Santi,
yamma tana yi sai ga iyatu tazo domin tace
itace zata yiwa yarta wanka, tunda aka yi
haihuwar junior yayi wahalar gani saboda dakin
nata kullum acike yake da jama'a gata dai
kuluwa ta Ganshi har sai da tayi kuka domin
dad din junior gida ya bata sukutum da
makudan kudi ita kuwa mom wata dankareriyar
sarkar gold ta biliyoyin kudi ta siyo mata ga
dinkunan da tasha fiyeda kala 50 yaronta kuwa
abun ba acewa komai, kwananta biyar da
haihuwa kawarta Mairo tazo gashi ta taho mata
da kayan gyara nan suka hadu da Ummi da ita
suka sha cafta, ranar suna yaro yaci suna
Muhammad zasu kirashi da haisam, tunda akayi
suna junior ke bin mom kan ta bashi matarsa su
tafi amma mom taki tace sai sunyi 40 domin
har yanzu iyatu na nan tana gyara kuluwa dama
babanta yazo yaga jaririn ya koma.

Ranar da
yamma mom bata nan ya shiga gidan ganin
mom bata nan ya sashi tayarwa da kuluwa daru,
jikinta ya shiga ya fara kissing dinta tareda
shasshafa ta dakyar ta samu ya iya hakura ya
kyaleta.

Kullum junior yana gidan mom manne da
kuluwa da haisam har suka yi 40 alokacin ya
tada rikici dole mom ta barsu suka tarkata suka
tafi, suna zuwa gida ya dauki haisam "ke ko
nemana ma ba kyayi ko?" "Waya fada maka
wallahi nayi missing dinka mijina" "zaki fada
musu ne bari muje ciki" suna shiga dakinsa yaje
ya kwantar da haisam wanda yake ta sharar
baccinsa ya nufi dakin kuluwa tana tsaye tana
waya da Ummi lokacin da ya shiga dama gata
katuwa yanzu da ta haihu sai ta kuma zama
katuwa sosai,"malama kizo kiyi biyan bashi" ya
fada a hankali, wayar ta kashe ta karasa jikinsa
ta fara shafashi tana kissing dinsa shi dai junior
kamar wani soko haka ya zama nan suka fara
nunawa junansu yanda sukayi missing juna.

Rayuwar junior da kuluwa yanzu ta zama abun
kwatance ga wasu domin suna zaune lafiya da
juna yanzu haisam yana da watanni biyar bul
bul dashi komai nasa irin na junior, tare dashi
suke renon haisam kusan kowanne lokaci yana
tare dashi ko ya kaishi gidan mom ko kuma
yafita dashi ganin gari abun nasu gwanin dadi
amma har yanzu junior bai daina buga kwallo
ba, idan ka Ganshi tsaf dashi kamar wani
saurayi,Sam bai yi kama da magidanta ba,
kuluwa kuwa an zama manyan mata domin duk
wanda ya ganta yasan tana hutawa kuma ta
zamto shalele wurin mijinta.

Sai da haisam ya
shekara biyu sannan ta yayeshi nan kuma ta
fara wani laulayin lokacin har ta gama degree
dinta itama Ummi ta haifi yarta mace, ita dai
kuluwa haihuwa ko yau ko gobe amma hakan
bai hanata hidima da junior ba domin ko yanzu
ma kwance yake jikinta yana lalubarta hannunsa
ta rike "bazaka barni na huta ba?" "Sorry baby
na kokon zaki sammin dan kadan" murmushi
tayi tareda rungumeshi ajikinta.

ALHAMDULILLAH!

Anan nakawo karshen labarin SANADIN GATA
duk wanda ya sarrafa min shi ta wata hanya
ban yafe ba.

SANADIN GATA TUKWICI NE GAREKI
Uwar dakina
HAUWA M JABO ( kuluwan junior) Mrs...

To be.

KUNA INA?

Kawayena na kaina
Khadija Sidi kawata
Teemah cool kawata
Ummu Samha kawata
Chucu masoyiyar asali
Nana Chocho kawata
Fido sodangi kawata
Mamie hamma kawata
Sady kawata
Hafsat Bunza kawata
Maman Kdj kawata
Hajara Gamji kawata
JINJINA AGAREKU
Baby pherty
Maman Shakur
Sallyn junior
Kdeeyn junior
Futhan junior
Lubieen junior
Mom Halamcy
Maman Ansar ( Yar garinmu)
Hafsat mai sheriff
FATAN ALKAIRI GAREKI
Cwt namcy A'isha Dansabo lemu
GAISUWA GA TAKWARORIN KULUWA
Hauwa (hawyn junior)
Hauwaty
Kulu hydar
Jiddah m husain
Kina Raina Babbar yaya, abar alfahari na
ADDA BENAXIR OMAR
Kawata kinfi ta kowa
KAUSAR LUV, u are always in my mind, Luv you
kawata!

Allah ya barmu tare eva,gaisuwarki ta
musamman ce yan matan faruku!.

Gaisuwa mai tarin yawa ga masoyan junior,
musamman wadanda suka kaunace shi da
kuluwa, junior loves you too!

LITTATTAFAN MARUBUCIYAR
~Biyayyar Iyaye
~Sultan
~Bakin Alqalami
~Mace guda daya tilo
~Benaxir ko Kausar
~Kausar Yar autar mata
~Sai naga Benaxir Omar
~Kwarya tabi Kwarya
~Ruwan Dare
~Aure yakin mata
~Alheri Danko ne!
~Sanadin gata!
Chapter 25 · 0% Book details