← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 25

Sashe 2

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai dan riko jaraba ne kuma
masifa ne saboda idan ka zuba masa ido ya
lalace laifinka za a gani ace ka bar da ya lalace,
idan kuma ka na yi masa fada nan ma baka
tsira ba sai ace dan ba kai ka haife shi ba
shiyasa kake takura masa, ai sharrin dan riko
yawa ne dashi, sai dai kawai fatan samun sauki
a wurin Allah, ni dai duk wanda yasa duniya ta
zageni bazan yafe masa ba, karasawa ciki
kuluwa tayi ta sauke ruwan ta fara hada wuta a
murhu domin ta dora tuwon sayarwa yayin da
ita kuma iyatu har yanzu ba ta bar bakinta ya
huta ba sai masifa take ta yi, yo dama waye zai
rungumi dan kishiya ai sai wawa shashasha
saboda dan ma ko ka rike shi ba fita za kayi ba
wani dan ma in mai bakin hali ne Allah Allah
yake ya samu duniya domin ya wulakanta ka,
sallamar maryama ce ta katse iyatu daga
babatun da ta ke yi ita dai kuluwa iyatu har
mamaki take bata saboda kwata kwata bata
gajiya da surutu ga masifa idan aka yi mata abu
ta kama mita wuni za tayi tana abu daya.

Inda
kuluwa take maryama ta karaso tana cewa
kuluwa kinga har mun taso daga makarantar a
hanya na hadu da shamsu yace nazo na kiraki,
wa zaki Kira?

Iyatu ta fada cike da fada to wlh
daga yau babu ke babu gidan nan munafuka,
dama ashe kece kike hure mata kunne ko?

To
maza zo ki fice kije ki ce masa ba zata zo ba
kuma maza yaje ya nemi matar auran sa amma
ba wannan marar asalin ba ehe, kallonta
maryama tayi iyatu ni kuma me nayi miki?

Daga
shigowa ta zaki fada ni da fada kuma naga ai ni
ba wani abu na cewa kuluwan ba da zaki ce ina
zuga ta, ke maryama ni kike fadawa haka?

Saboda tsabar baki da kunya ko, to tun kafin
ranki ya baci ki bar min gida idan ba haka ba
duk abinda ya biyo baya ke kika jawa kanki,
juyawa maryama tayi zan bar miki gida amma
ina so ki sani duk abinda mutum ya shuka shi
zai girba tana gama fadin haka ta juya tabar
gidan, take iyatu ta hayayyako ta fara bala'i tare
da jan zaninta tana fadin bari naje na jawa uwar
taki kunne kar na kara ganin kafarki a gidan nan
tunda abin babu mutunci, nagaji da wannan cin
kashin da ake min idan da saninta gwara naji,
dagowa da kanta kuluwa tayi tabi bayan iyatu
da kallo daidai lokacin da take fita daga soron
gidan tasan halin iyatu sarai dama dan ta raba
su da maryama da shamsu ne yasa ta takalar
fadan, saboda ita dai duk wanda zai kaunaci
kuluwa to ita kuma shine abokin gabarta,figar
mayafin tayi ta fita tana ta ruwan bala'i ita kam
kuluwa ko ba a fada mata ba tasan gidan su
maryama ta tafi kai togaciya, haka taci gaba da
hada wutar har ta kama ta dora tuwon
sayarwar, mahaifinta ne ya fito daga cikin daki
ya karaso in da take sannu kuluwa kiyi ta hakuri
kinji, komai na duniya yana da iyakar sa shiyasa
zaki ji kullum bani da magana sai kiyi hakuri
domin shi hakuri baya baci kuma komai yayi
farko zai yi karshe ni kaina kin ga hakuri nake
da ita amma duk da haka bata barni ba, share
kwallar idon ta tayi tace babu komai baba insha
Allahu zan ci gaba da hakuri kamar yadda ka
bukata, yawwa hawwa'u Allah yayi miki albarka
ya baki kyakkyawan rabo duniya da lahira, amin
baba tafada tana hawaye, to me ya naji kana sa
mata albarka ni kuma sai ka tsine min ai,
muryar iyatu suka jiyo daga soro tana magana
cikin fushi, in banda munafurci meye zaka wani
zo ka saka yarinya a gaba kana zagina a
wurinta ko dan ka iya ha'inci sai nayi magana
kuma ace ni masifaffiya ce to wlh na fara gajiya
ehe, shi dai baban kuluwa sa kai yayi ya fice
daga cikin gidan ya bar iyatu tana ta masifa
wanda hakan ya zame mata jiki domin kullum
wuni za tayi tana babatu a unguwar duk makota
suna jinta sai kace ita kadai ce mata, juyowa ga
kuluwa tayi tafara yi mata fada duk abinki dai
ba zaki auri shamsu ba ke da aure sai dai kiga a
nayi amma ba dai ke kiyi ba ita dai kuluwa bata
ce komai ba taci gaba da girkin da take yi.

Mangarubar fari ta gama tuwon ta zuba a
fanteka ta dauka ta nufi dandali inda a ka'ida
can take kaiwa kullum da daddare, tana zuwa
tuwon ya kare, kudin da shamsu ya bawa mairo
ta bata ta dauka ta siyi abinci taci tayi kat, tana
shirin harhada kwanukan ta ne mairo tazo inda
take cike da damuwa akan fuskarta, kuluwa kinji
abinda iyatu taje ta fada a gidanmu dazu?

Girgiza kai kuluwa tayi me tace?

Wlh kuluwa
iyatu tayi duk wani rashin mutunci da kika sani
tare da gargadin shamsu wai babu shi babu ke
kuma baki ji zagin da tayiwa iyayen mu ba to
shine mahaifin mu yace da shamsu kar ya kara
kulaki, wasu hawaye ne suka gangaro akan
kumatun kuluwa lallai iyatu ta gama nuna mata
kiyayya saboda tunda ta rabata da shamsu ta
gama da rayuwar ta,share mata hawayen mairo
tayi tace kiyi hakuri kuluwa Allah yasa haka
shine mafi alkairi, amin mairo nagode kuluwa ta
fada tare da kinkimar kayanta ta nufi gida tana
hawaye.

A haka rayuwar kuluwa taci gaba da guduna
cikin ukuba da matsati gashi kaf garin babu
saurayin da yake zuwa wurinta saboda kowa
tsoron masifar iyatu yake domin dama iya
shamsu ne ya jajurce to shima iyatu ta raba su
kullum kuluwa cikin kuka take mahaifin ta kuwa
hakuri kawai yake bata acikin wannan halin ne
aka sanya ranar bikin mairo wadda sai alokacin
kuluwa taji hankalinta ya tashi saboda ita da
mairo ne kawai suka rage gashi mairon ma zata
tafi ta barta nan tabi ta rarrame har mahaifinta
ya fahimta ya kirata yayi mata nasiha da cewa
tayi hakuri in Allah ya yarda za tayi aure wanda
za tayi alfahari da mijin, nasihar mahaifin ta
tadauka ta dangana yayinda iyatu ita kuma ta
samu nayi kullum habaici wai kuluwa tayi bakin
jini bata da saurayi gashi shekarunta 19,kuluwa
tun abin yana damunta har ta hakura.

Yau da
gobe babu wahala har lokacin bikin mairo yazo
haka aka sha hidimar biki aka kaita dakin
mijinta, bayan bikin da kwana 2 ne kuluwa ta
dawo daga talla ta ratsa ta gidan mairo,
tsayawa tayi tana kallon dakin mairo wanda
yasha kwanukan silba da su dan cana ga
gadonta mai runfa na karfe, Allah ya sanya
alheri mairo kuluwa tafada kamar za tayi kuka
dan tausayin kanta saboda ita tasan babu
wanda zai yi mata wannan kayan domin
babanta ba shi da hali, zaunar ta mairo tayi ta
fara bata labarin irin bakar wuyar da tasha a
daren farkonta nan da nan kuluwa tsoro ya
shigeta take taji ta fara tsoron maza saboda
wannan labarin da mairo ta bata saboda tace
mata akwai wuya, yan kayayyakin ta ta dauka
ta nufi gida tana tafe tana cewa lallai maza
ashe abin tsoro ne, tana zuwa kofar gida ta ga
wata dalleliyar mota mai kyau sabuwa dal, gidan
ta shiga tana shiga taga iyatu a tsakar gida
hankalin ta ashe kamar wadda yan sanda suka
kama, jin sallamar ta ya sanya mahaifin ta
fitowa daga cikin turakar sa ga wata mata
kyakkyawa yar gayu a biye dashi, kallon kulawa
matar tayi tace wannan ce hawwan?

Lallai
hawwa ta girma, amma nayi mamaki ace
yarinya kamar wannan bata zuwa makaranta,
babu komai Salma ai mun gama magana dake
kuje kawai nagode Allah ya bar zumunci, kallon
kuluwa yayi yace hawwa ga yar uwata Salma
nan da nake baki labari yau tazo zata tafi dake
birni zakije kiyi karatu Salma kanwata ce uwa
daya uba daya dan Allah ki riketa a matsayin
uwa, to abba kuluwa ta fada cikin farin ciki
saboda zata bar masifar iyatu, cizon yatsa iyatu
ta fara yanzu ina ji ina gani zata tafi da yarinyar
nan ta zama irin ta?

Inama na barta ta auri
shamsun ta kare rayuwar ta a wahala ta fada
acikin zuciyar ta, maza shiga ki dauko kayanki
inji mahaifin ta, no basai ta dauki komai ba yar
gayun ta fada tana murmushi, kama hannun
kuluwa tayi tace to zo mu tafi hawwa nan fa
iyatu ta biyo su kamar zata kurma ihu tana ji
tana gani kuluwa ta shige mota ta dare
luntsumemiyar kujera.

Ku biyoni masu karatu dan jin ci gaban labarin,
hakika nasan za kuyi alfahari da wannan labarin
na Ummi A'isha. [1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha:
🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�1�
~~~Wani bakin ciki ne ya turnuke iyatu take ta
fara masifa tamkar wata zautacciya munafuki
dama nasan wata kulalliyar ka kulla saboda
yarinyar tana yi min talla tana dan samo min
kwabo shine kake bakin ciki, to ai gani nayi dai
hawwa yata ce ba taki ba ko?

Kuma bake ce
kika haifa min ita ba dan haka baki isa kiyi min
iko da ita ba yana gama fadin haka ya shige
cikin gida nan fa ta bishi tana cewa eh dama ai
ka saba yi min gorin haihuwa dan yanzu kayi ba
zan ji ciwo ba, shi dai baban kuluwa bai sake
tanka mata ba saboda yau burinsa ya cika ya
raba kuluwa da wahalar iyatu.
*************
Gudu anty salma take shararawa a motar ta
kamar ba mace ba saboda yadda take tuki babu
tsoro a take da ita, sai da suka dan yi nisa
sannan ta jiyo ta dubi kuluwa tace hawwa
yanzu za kije Inda zaki samu sauyin rayuwa
kuma insha Allah zan cikawa yaya burinsa na
son yaga kin samu kyakkyawar rayuwa.
🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�2�
Chapter 2 · 0% Book details