← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren su kuluwa kuwa kayayyaki sosai
mahaifiyar mijinta ta siya mata tun anan tasan
dan nasu dan gatane kuma suna ji dashi, ga
manyan mata da mom din angon ta gaggayoto
aka zo aka gudanar da wani hadadden lunching
wanda aranar aka shirya kuluwa cikin leshi pink
mai tsadar gaske, ba karamin kyau kuluwa ba,
kwansu 3 agidan aka rakata gidanta wanda yake
girke a unguwar shagari quarters, uwar mijinta
da kanta takaita gidan wanda aka gyarashi
yasha kayan alatun more rayuwa, dan zamanta
agidan su mijin nata taga abubuwan ban
mamaki kala kala domin uwar mijin nata itace
ta zage ta gyarata tsaf tayi mata gyara na
musamman ta tsumu gaskiya wannan matar
tana ji da dan nata.

Tunda aka kaita ummi tatafi
tabarta amma har lokacin kuluwa ko hawaye
batayi ba sai dai tasan tana son junior kuma
gashi ta rasashi, washe gari sai ga anty salma
da ummi sun dawo, kayane cikin viva na mata
anty salma ta kawo mata tareda yi mata
bayninsu dalla dalla, wlh idan baki sha ba
nadawo sai naci mutuncinki, to anty tafada tana
kallon kayan, bayan su anty salma sun tafi ne
tafita gidan nata ta fara zazzagawa, gidane
katon gaske wanda ya amsa sunansa gida, ga
ma'aikata masu tarin yawa komai yi mata za
ayi.

Ranar litinin da daddare junior ya sauka akasar
Nigeria, gidansu yaje nan mom ta rungumeshi
da murna tareda yi masa albishir na auren da
sukayi masa, wanka yayi yaci abinci ya shirya
ya nufi gidan nasa lokacin karfe 10 na dare,
lokacin da ya shiga gidan jin jikinsa yayi yai
sanyi ahaka ya karasa amma bai shiga sashen
amarya ba sashensa ya wuce ya kwanta saboda
agajiye yake sosai.

Kamar kowanne dare yauma kuluwa tayi
shirinta na bacci jin alamun shigowar mota
gidan yasata kudundunewa tareda kankame
jikinta wuri daya tana addu'ar Allah yasa ba
angon bane yadawo, tunanin junior ta fara Allah
sarki junior narasaka har abada duk irin son da
nake yi maka ashe bazan sameka ba, idonta ta
rufe ta fara hango rabuwar su, junior akwai kyau
saboda duk budurwar da ta ganshi sai ta fada
mata tace mata wannan saurayin naki
kyakkyawa ne,shiyasa wani lokacin take kishin
zuwansa b.u.k dinma.
[1/31, 8:45 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
4�7�

Hawayene suka fara sauka akan kumatunta,
juyawa tayi ta rungume filo, duk rayuwarta ta
tsarata ne kan zata yita da junior kuma taga
alamun nasara domin yana jin maganar ta kuma
yana daukar shawarar da duk ta bashi, gashi
kanta tsaye take fada masa maganar da ranta
ke so wacce ya kamata ace yayi fushi amma sai
kaga bai yi fushin ba da alama dai ba mai saurin
fushi bane kuma bashida zazzafar zuciya.

Tunanin wani lokaci da yaje b.u.k tafara, suna
tsaye suna yar hirarsu ta duniya dan ba za ace
ta soyayya ba domin duk cikinsu har yau babu
wanda ya taba tona asirin zuciyar sa, wayarsa
ce tayi yar kara ya daga, hello teemah, kin samu
sakona?

Yayi miki kuwa?

Ya suka zama?

Sun
kara girma?

No dan Allah kiyi using da wannan
abun ke naki sun cika kanana da yawa, kallonsa
kawai kuluwa ta tsaya yi ya wani saka hularsa
agefe shi yadda ake saka hular ma ba haka yake
saka tashi ba amma yadda yasaka tasan sai ta
bada wani style na musamman kuma tayi masa
kyau sosai, kashe wayar yayi yana dariya, amma
ita kuluwa ta cika fam tayi dam sai tattare girar
sama da ta kasa take yi tasha dogon hijabi har
kasa babu abinda ake gani ajikinta daga
fuskarta shikenan dan ko hannunta ba a gani,
shi kansa Junior duk da bai taba ganin surar
jikinta ba amma yasan ta mallaki komai na ya
mace gata yar lukuta kamar ummi A'isha,
harararsa tayi meye haka?

Wlh kaji kunyar
duniya data lahira, me nayi??

Kawai dan kinji ina
yin waya sai kice haka?

Oho maka amma wlh ka
rage sabon Allah domin kaima zaka haifa
shiyasa nake tausayawa matarka domin bata yi
sa'ar miji ba, nikuma kinga nayi sa'ar mata
saboda matata wlh mahaddaciya ce mai son
addini, she's pious lady, baki kuluwa ta tabe,
Allah wadaran naka ya lalace tana gama fadin
haka ta juya tayi tafiyar ta,
murmushi junior yayi yakoma cikin motarsa ya
zauna, a tunanin kuluwa daga ranar ba zai sake
dawowa ba amma sai gashi ya dawo, maimakon
ita tabashi hakuri shine ya fara bata hakuri akan
abunda ya faru jiya, kuma tun daga lokacin da
ta hanashi saka sarka da dan kunne ba sake
ganinsa dasu ba, suma ce dai yakasa askewa
[1/31, 8:53 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
4�8�

Tun daga lokacin ya daina yawo da boxer da
yar t shirt sai dai agida, amma komawar sa
ghana bai daina yawo da sarka da dan kunne
ba, tunanin junior tayi ta tayi barkatai har bacci
ya dauke ta.

A dakin junior kuwa kwance yake cikin bargo
gashi ana dan yin sanyi a garin,tunanin jiddan
sa ya fara, bashida niyyar yin jayayya da auren
da su dad dinsa suka yi masa domin yasan dan
suna sonsa ne asalima SANADIN GATAN da
suke yi masa ne yasasu aura masa matar da
suka aura masa ahalin yanzu, sai dai fatansa
Allah yasa jidda ta yarda tazo a second wife dan
yaga kamar tana da kishi, kudundunewa yayi
sosai kamar wani karamin yaro saboda shi ko
agida alokacin sanyi mom ta rinka kai komo
kenan akansa saboda tasan akwai shi da jin
sanyi shiyasa a dakinsa na gida harda heater
sannan blanket dinsa ma mai heater ne yanda
idan yaji babu sauki zai jona shi ajikin socket
yasha duminsa, amma gashi anan babu ko
daya.

Baccine yayi awon gaba dashi sai dai sanyi
yakasa barinsa ya sake har gari ya waye bai yi
wani baccin kirki ba, sai 11 yatashi alokacin
yayi wanka yayi sallar safe ya fito zuwa falo,
yana tafiya da cumb a hannunsa yana taje
sumar kansa,
ita kuwa kuluwa tun asuba ta tashi tayi salla ta
koma ta kwanta domin babu abinda take yi
komai akwai masu yi mata hatta girki kuku ne
ke yi mata shi, sai 9 ta tashi tayi wanka tasa
atamfarta rigada skirt tasa hijab ta fito zuwa
kitchen daidai lokacin junior ya fito,yana ta fito
da bakinsa kamar yadda al'adar sa take saboda
bashida abunyi kullum daga waka sai fito,
buruntun da yaji anayi acikin kitchen ne yasa shi
shiga kitchen din, bayanta ya hango tana hada
tea hello!

Ya fada ahankali, juyowa tayi caraf
suka hada ido, me yakawo ka gidana da
sassafe?

Tafada tana kallonsa, shigowa cikin
kitchen din yayi daga shi sai boxer baki da shirt
fara, ke zan cewa me ya kawoki gidana da
sassafe ko kin san matar tawa ne?

Oh kenan
kaine angon?

Kenan kece amaryar?

That's
great, juyawa kuluwa tayi cikeda farin ciki amma
duk farin cikin da take ciki junior ya fita domin
shi ji yayi tamkar ya zuba ruwa akasa yasha
dan murna, haba shiyasa ko sau daya bai ji ya
tsani auren ba ashe jiddanshi ce matar, ajikin
bango ya jingina bayan ya harde hannuwan shi
a kirjinsa kai Allah shine abun godiya ya fada
acikin zuciyarshi, juyowa kuluwa tayi da cup
guda biyu rike a hannunta, muje falo ta fada
lokacin data wuce gaba, bin bayanta yayi har
cikin falo,ga tea ta mika masa, kai ya girgiza ni
bazan sha tea ba, to me zaka sha??

Ni koko zan
sha ya fada yana lasar lebenshi kamar wani
maye,kaji ai, ni yanzu ina zan samo wani koko,
ka karbi tea din kasha, kwanciya yayi akan
kujerar nafada miki ni koko zan sha, tom kayi
hakuri na sa kuku ya dafa maka wani abun, ke
nifa agida komai mom ce ke bani har abinci, da
safe ni bana shan tea,to me kake ci?

Dankali da
miya zaki min kuma ki bani koko, nifa na fada
maka banida koko ko gasara bani da ita, acikin
ransa yayi magana ke kuwa kike da ita kuma
nasan kokonki ba irin na sauran bane saboda ke
naki fresh one ne, tashi yayi ya kalleta ina zuwa
zanje gidan mom yanzu, gidan mom da safen
nan junior?

Eh ai dole naje saboda akwai kayan
kwallona da kayan motsa jikina acan, to kuma
ahaka zaka fita??

Dakinsa ya koma ya sako
dogon jeans yazo ya wuceta a falo ya tafi gidan
mom.
[1/31, 9:02 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
4�9�

Yana fita ta rakashi da murmushi oh junior
manya wai junior da mata, kuma matar ma ni,
tab!

Zansha aiki da shagwabar junior ga tsirfa
iri iri, ga shi shagwababbe komai mom komai
mom yanzu kuwa tunda babu mom ai nice zan
karbi aikin mom dolena, tashi tayi tashiga
dakinta sai yanzu ta ciro kayan da anty salma
ta kawo mata ganin junior ne mijin ya sata fara
amfani da kayan, tana sha aranta tana cewa
wannan shagwababben ma me zai iya, ai inajin
ko irin kukan nan da ake cewa anayi a first night
ni bazan yi ba saboda junior ai yarone karami ko
isa auren ma bai yi ba amma SANADIN GATA
yasa aka yi masa yanzu, kayan ta duddura
acikinta sannan ta tashi ta shiga kitchen, hmm
nidai ummi A'isha ban raina junior ba ehe.

Gidan mom junior ya shiga cikeda farin ciki yana
zuwa ya tarar da ita zaune akan dining taci
kwalliya sosai tana yin breakfast, good morning
mom ya fada yana murmushi, morning my boy,
karasawa inda mom take yayi yai mata kiss a
kumatu, mom bari naje filin kwallona nadawo,
ho junior ba za dai ka hakura da kwallo ba ko?

Murmushi yayi mom ko nadawo nan gidan ne
naga dad baya nan mun barki ke daya, a'a
junior ni ai haka yafi min dadi ganin kaima da
gidanka sai dai kazo min yawo, ya amaryar
taka?

Lfy lau mom,fita yayi zuwa filin kwallonsa
ya fara wasannin motsa jiki.

A bangaren kuluwa kuwa yau jinta take wasai
wasai, kitchen ta shiga ta soyawa junior dankali
da kwai kuma tayi masa miyar tunanin inda za
asamu koko tafara gashi rana tayi anya za
asamu koko kuwa?
Chapter 12 · 0% Book details