← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 25

Sashe 18

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da safe ya tashi idonsa jajur kamar
gauta, bai ci abin karyawar da aka kawo masa
ba, bayan sun gaisa da Baban kuluwa yace
masa "yau zai koma kano", "ai sai ku tafi tare
da hawwan tunda iyatun yanzu ta samu sauki",
"to baba", duk wadannan maganganun a cikin
kunnen kuluwa, daki ta shiga ta hada kayanta ta
fito yanzu duk a tsorace take da junior saboda
jin tsawar dayayi mata a daren jiya.
[2/8, 8:54 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�7�

Tana fitowa tsakar gida kawarta Mairo ta
shigo, bayan sun gaggaisa da su baban ta ne
suka kebe ita da mairon, "kuluwa ga wata
bagaruwar na kawo miki kiyi ta amfani da ita
kuma duk lokacin da kika gama period ki tafasa
ganyen magarya kiyi amfani dashi in dai kin riki
wannan wlh babu ruwanki da neman wasu
kayan matsi", "to Mairo nagode kinga yanzu ma
tafiya za muyi sai Allah ya kaimu wani lokacin
idan na dawo", "Allah ya kaiku lafiya kuluwa
amma wlh mijin naki kyakkyawa ne kamar ma
yafi ki kyau, ke bama kama bace wlhi ya fiki
kyau da aji", "to Mairo nagode da wannan cin
fuskar", dariya Mairo tayi "ai kin san abinda na
fada haka yake ba kage nayi ba", sallama suka
yi da Mairo ta tafi ita kuma kuluwa ta je tayiwa
iyatu sallama, har waje iyatu ta bisu tana
sanyawa kuluwa albarka tareda zubar da
hawayen nadamar abubuwan da tayi wa kuluwa
a baya.

Kuka kuluwa ta dan fara yi lokacin da ta shiga
motar, har bakin motar babanta yazo ya na
yiwa junior magana"Abdulrahman ayi ta hakuri
kaji, kasan mata sai da hakuri, dan Allah ayi
hakuri da juna", "ah baba babu komai kuma
insha Allah babu wata matsala, to Allah yayi
muku albarka" amin baba", motar ya tada ya
fita daga kauyen ya dau hanyar birni.

Tsit cikin motar yayi saboda yau ko dan music
din ma junior bai kunna ba sai fuskar shi da ya
daure kamar wanda aka aikowa da mutuwa,
wani irin kwarjini kuluwa taga yayi mata gashi
dai ko a haife ba da wasu shekaru masu yawa
ya fita ba saboda ita ahalin yanzu shekarunta
24 shi kuma tasan a yayi shekaru da yawa yayi
27 saboda junior yaro ne karami kawai SANADIN
GATA ne yasa su mom yi masa aure a shekarun
da yake yanzu, harare hararen da ta kula yana
ta yine ya sata kifa kanta cikin cinyoyin ta ta
yadda ma ba zata ci gaba da ganin muzaran da
yake yi ba,kamar wadda aka tsikara sai ta fara
kuka mai sauti, kyaleta yayi yana jinta tana kuka
ita kuma bakin cikin yaki kulata ya sata sake
daga murya, packing din motar yayi a gefen titi
tare da daka mata tsawa " ke ya isheki haka, ko
kiyi shiru ko kuma ki fice min acikin mota" jin
tsawar da yayi mata ya sata yin shiru cikin
mintocin da basu fi 2 ba, sai da yaga tayi shiru
sannan yaci gaba da driving din.

Motar shiru haka suka ci gaba da tafiya har
suka isa wudil sai a nanne taji ya dauki wayar
sa ya kira bobo " hello bobo, na kusa shigowa
fa, mu hadu kawai a gidan mom, nifa ban son
kana zuwa min gidana gaskiya, yes mu hadu
acan din, ok sai na shigo" ajiye wayar yayi
tareda jan tsaki da karfi sannan ya daki sitiyarin
motar.
[2/8, 9:05 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�8�

Da sauri ta dago kanta ta kalleshi ya ko juyo
ya galla mata wata harara, take taji yan hanjinta
sun juya, yau tsoron junior take ji sosai, "wayyo
Allah na, yau ko zai bani dumin ma ko kuma
shareni zai yi?" Ta fada acikin zuciyarta, "tab ai
yau kema kin san ragargaza ki zai yi da gaske
bada wasa ba, dan yau watakil sai ya rabaki da
budurcinki,gashi kuma kuruciya na damunsa kila
ta farat daya zai yi miki" wata zuciyar ta sake
bata amsa, "hmmm" ta saki ajiyar zuciya mai
karfi, har suka isa kano a tsorace take dashi ko
kwakkwaran motsi ta kasa yi, sai dai duk inda
suka dan tsaya ko a trapic jump haka sai taga
anata kallon junior ko ana nuna shi ana cewa
shine dan kwallon nan da haka har suka shiga
unguwar su wato shagari quarters.

Lokacin da suka shiga cikin gidan bayan yayi
packing ya juyo ya kalleta, "ni kika cewa na
sake ki ko?

To bazan sake kin ba kiyi duk
abinda za kiyi, inma zan sakeki sai bayan na
gama koya miki hankali tukunna stupid kawai",
take nadama ta shigi kuluwa jikinta yayi sanyi
sai ta fara kuka kuma, kallonta yayi aransa yace
"jita shagwababbiya kawai daga fadin haka har
ta fara kuka, na rasa me yasa take da saurin
kuka, daren yau akwai koke koke kenan, kiyi
kukan ki ki gama kafin kiyi mai dalili da daddare
dan yau duk kukanki sai nasha koko, nima jiya
har kukan kika sani", duk acikin ransa yayi
wadannan maganganun, bude kofar yayi ya fita
"yace in kin gadama ki fito min daga cikin mota
idan kuma baki gadama ba kina iya kwana
aciki".

Juyawa yayi ya wuce ciki, cikin kuka kuluwa ta
fito ta dauki jakar kayanta ta nufi cikin falon
gidan, dakinta ta shiga ta kwanta bayan ta
gama kukan da take yi.

Tana nan kwance junior
ya leko dakin nata, "kije ki gyara min dakina
kafin na dawo", tashi tayi tabi bayansa da kallo
ya sake kaya cikin brown din jeans da farar t
shirt mai gajeren hannu ajiki an rubuta
nectar,gashi yayi kyau sosai ya fito a junior
dinsa na asali mai tashen kyau da kuruciya,
kamshin da ya saba bar mata duk lokacin da ya
shigo dakin yau ma shi yatafi ya bari sai kace
aciki ya fesa turaren.

Tashi tayi ta nufi dakin nasa a karo na
farko,budewa tayi ta shiga, dakin ya hadu sosai
gashi yayi biyun nata a girma da fadi saboda an
shirya shi ya shiryu, komai na dakin ja ne tun
daga kan gadon ciki wanda yake katoton gaske
har bedsheet din da blanket da labulayen duk
red ne, gefe kuma an shirya wurin da yan
kananan kujeru jajaye guda uku an shirya su
kamar falo da wani dan center table a tsakiya,
dakin ta gyare tsaf ta fesa air freshener da
turaren tsinke, kallon gadon tayi, "oh akan
gadon nan za ayi yakin rabani da budurci na, ko
yau ko gobe,Allah yasa ba yau zai bani wannan
wahalar ba".
[2/8, 9:42 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�9�-7�0�

Bayan ta gama gyaran dakin ta wanke masa
toilet dinsa wanda shima yake a tsare kamar a
kasar turai, wani katon kwandon roba ta gani
wanda yake tara kananan kayansa masu datti
da kayan da yake ball dasu gasu nan sunfi
akirga da alama duk wanda ya cire baya
maimata su sai dai ya bude sabbi yasa.

Kayan ta kinkima ta shiga toilet din ta fara
wanke masa su, tunda ta fara bata tashi ba sai
da lokacin salla yayi, tana idarwa ta sake
dawowa taci gaba da yin wankin, wuni tayi tana
yi masa wankin kayansa har sai da ta wankesu
kaf lokacin har yamma tayi lukwi.

Agajiye taje
kan dining ta zubo abunci ta zauna taci ta
kwanta akan kujera a falo, yau jinta take agajiye
lis tayi mugun gajiya.

Bayan sallar isha ta shiga dakinta ta kwanta
bayan tayi wanka, yau ana surfa sanyi amma
tasan junior ba lallai ne yazo dakinta ba tunda
taga fushi yake yi da ita.

Karfe 8 junior ya shigo
gidan ganin irin aikin da kuluwa tasha ya sashi
niyyar kyaleta yau saboda ta aikatu mutuka,
"hmm yau zan barki ki huta saboda kin gaji dan
haka zan barki amma gobe sai kinyi bayani
acikin dakin nan", haka junior ya fada acikin
ransa, dakin kuluwa ya shiga tana kwance ta
lulluba, "tashi kiyi alwala kizo muyi salla",
bedsheet din taja ta rufe jikinta ta tashi saboda
bata son ya ganta a haka domin rigarta bata da
maraba da tsirara, fita yayi daga dakin ganin
tanata kunbiya kunbiya, sai da ya daidaici ta
gama sannan ya dawo dakin lokacin ta saka
dogon hijabi ta shimfida abin salla.

Salla ya jasu suka yi raka'a 2 suka idar,
kowannensu addu'a ya fara yi acikin
zuciyarsa,addu'ar kuluwa ta kare ne akan Allah
yasa junior ya zauna da ita har abada, shi ma
junior addu'arsa ta tafi ne akan Allah yasa ta so
ta kaunace shi kafin daga baya ya tashi ya
koma dakinsa yaje ya kudunduna acikin bargo,
sanyin yau jinsa yake yafi na ko wacce rana
gashi baya son zuwa jikin kuluwa yau dan ya
tabbatar ba zai iya yin hakuri ba muddin ya jita
a kusa dashi, gashi tasha aiki ta gaji wannan ne
ya sashi tausaya mata yaga gara ya kyaleta ta
huta in yaso gobe sai ayita ta kare.

Kasa bacci
yayi saboda sanyin da yaji yana faman ratsashi,
zaune ya tashi ya kudundune jikinsa wuri daya
yana ta faman rawar dari, jikinsa sai karkarwa
yake, shi dama ko agida in dai da sanyi ne to
mom bata hutawa da hidimar sa duk abinda
tasan zai bashi dumi to sai ta nemo masa.

Abangaren kuluwa kuwa yau ta gama tsurewa
da lamarin junior saboda ko lokacin da ya shigo
su kayi sallar nan jikinta ya gama bata cewar
junior bazai rabuda ita a daren yau ba, labarin
da Mairo ta bata lokacin da tana amarya ne ya
fara dawowa cikin kwakwalwar ta,"wlh kuluwa
idan mutum ya hadu da marar tausayi tsaf zai
raunata ka domin sai yayi maka fata fata, wani
ma saboda tsabar rashin tausayi yana ganin
kana fitar da jinin wahala amma ba zai barka ba
har sai ya gaji dan kansa sannan zai bari, ni
kinga duk ihun da nayi mutumin nan bai barni
ba har sai da ya cika burinsa" ajiyar zuciya
kuluwa tayi "hmm to ni ko ya zamu kare da
nawa gwanin?

May be nima sai yayi min fata
fatan".

Tunanin abin tai tayi acikin ranta har
bacci ya dauketa ga uban sanyin da take ji yana
ratsata.
Chapter 18 · 0% Book details