← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 25

Sashe 24

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kika rama ta wannan hanyar ai
kasheni zaki yi" murmushi kuluwa tayi "kajishi
kamar gaske" "wallahi dagaske nake, kinji kuwa
kwanakin nan da bakya nan kamar marar lafiya
haka nadawo dan har mom sai da ta gane nayi
missing dinki shine wai tace to idan wani abu
nake bukata na sanar mata sai tasa masu aiki
suyi min nikuma abunda nake bukata duk duniya
ke kadai ce zaki iya bani shi, Allah dagaske
nasha wahala da baki nan saboda kin
sangartani da yawa komai kece kike yimin
shiyasa nakasa sukuni", wani dadi taji ya
shigeta saboda jin kalmominsa, kallonsa tayi
"you lucky guy" "you too" yafada yana sinsinar
tafin hannunta yana rike da yan yatsunta sai
jujjuya su yake har suka shiga kano, dan
murmushi kuluwa tayi saboda ganin yanda duk
ya wani rikice ya rude kamar ta shekara bata
nan,"yau zansha jagwalgwalo kenan dan nasan
yau idan na shiga hannunka babu mai rabamu
sai Allah" haka ta fada acikin ranta, lokacin da
suka je gida kuwa dakinsa har dariya yabata
saboda kaura yayi daga dakinsa zuwa nata
lokacin da bata nan, duk kayansa da yasa ya
ciccire gasu nan baje akan gadonta, koda ta leka
kitchen ma abun ba acewa komai duk ya
babbata mata kayan kitchen saboda kitchen din
guda biyune daya wanda kukunsu yake amfani
dashi daya kuma nata ne na musamman, kayan
jikinta ta cire ta fito daga ita sai farar t shirt da
farin wando irin na yan ball dan kayan kwallon
junior ma tasa abayan rigar an rubuta junior,
kitchen ta shiga ta fara gyara kayanta da yayi
mata kaca kaca dasu tana ciki ya shigo ya
sameta daga shi sai gajeren wando "dan Allah
kizo kiji dani" kallonsa ta jiyo tayi, "haka ka bata
min gida?" "Eh na danyi girke girke ne da bakya
nan kuma wallahi duk ma food din bai ciyu ba
saboda babu dadi irin naki" juyawa tayi zata
fara wanke wanke dagata yayi ya sabeta ya
nufi dakinsa da ita dariya tafara "kabari nagama
aikin mana" "ai baki isaba ko zakiyi aiki sai kin
bani koko nasha" kan gadonsa ya kaita ya direta
nan suka shiga nunawa junansu yanda suka yi
rashin juna, kuluwa kam tasha jagwalgwalo a
hannun junior, kiss kuwa kamar zai cinyeta haka
ya rinka lasar ta.
*****************
Zamansu haka yayi ta tafiya lokacin har junior
ya fara service a b.u.k yana koyar da
organizational behavior ga yan public
administration department year 2/1, kullum tare
suke fita da kuluwa ya sauketa shima ya wuce
inda zai yi lecture damuwarta yanzu kwaya daya
ce ta rashin haihuwa amma baya da wannan
bata da damuwar komai domin tana jin dadin
zama da junior mutuka.

Yauma kamar kullum ta fito daga lecture ta
hango junior tsaye shida wata daliba tasha wata
doguwar riga da dan siririn mayafi, kyakkyawa
ce sosai kuma daga gani mahaifinta wanine,
daga nesa ta tsaya tana jiransa, kallonsa ta fara
yi sosai yana sanye cikin yellow din t shirt mai
dogon hannu da pink din wando sai yatsine
yatsinen fuska yake, "junior kenan, Allah ya
rabani da sharrin yanmatan jami'a" ta fada a
hankali, yana hangota ya taho inda take,"muje
gida ko jidda na" "eh" ta fada tare da yin gaba,
motarsa suka dosa suka shiga yaja suka tafi
kallonsa tayi "budurwa kayi ne?" Murmushi yayi
mata tareda kashe mata ido "kin fara gajiya
danine kike neman abokiyar zama?" "Junior
Allah serious ya kamata kayi aure tunda har
yanzu ni ban haihu ba kuma gashi su mom sun
kagu suka yaranka" hawaye ta fara "kayi aure ni
babu komai tunda nasan bana haihuwa ai
banida ikon kishi idan zakayi aure" hannunta ya
kamo ya sakale cikin nasa "jidda kin daina sona
ko?

Tunda kika ce haka nasan kin daina sona
kuma bakya kishina, haihuwa ai ta Allah ce
kuma da kiketa maganar su mom suna son
ganin yara na to kuma idan nine bana haihuwar
yaya zasu yi?" Da sauri takai hannunta ta rufe
masa baki cikin kuka tace "insha Allahu ma
kana haihuwa","kema kina haihuwa kawai Allah
ne bai kawo rabon ba, kuma wannan yarinyar ni
ba budurwa ta bace, saboda ko zan haihu to
nafi son na haihu dake" "Allah yasa" ta fada a
hankali,"amin" ya fada tareda tsotsar bakinta.

Ummi A'ishaSANADIN GATA!

Na
UMMI A'ISHA
8�5�

Duk da cewa junior yayi mata bayani amma
bata cire damuwa aranta ba haka take ta fama
da tunane tunane ganin haka yasa junior
daukarta suka je asibiti domin ganin likita bayan
likitan ya duba su ne ya sanar dasu dukkaninsu
lafiyarsu lau kuma zasu iya haihuwa a kowanne
lokaci sai a sannan hankalin kuluwa ya dan
kwanta ta rage damuwa.

Shirye shiryen bikin Ummi yar gidan Anty
Salma aka fara wanda za a gudanar watanni
biyu masu zuwa tun da bikin ya kusa kuluwa
take rokon junior kan yabarta taje gidan anty
Salma in yaso bayan biki sai ta dawo, kin yarda
yayi ganin ya hanata harda su kuka tayi, ana
saura kwana 5 bikin kungiyarsu ta kirashi kan
yaje Ghana zasu buga wani match shirye shiryen
tafiya ya fara wanda hakan ba karamin dadi
yayiwa kuluwa ba har sai da ya gane tana
murna zai tafi harararta yayi "wato murna kike
yi zan tafi ko?

"Ba murna fa nake yi ba" janta
yayi jikinsa yahada bakinsa da nata ya fara
tsotsa, kokarin rabata da kayan jikinta ya fara,
kyaleshi tayi ya gama jagwalgawalata son
ranshi kafin ya aika mata da sakonsa mai wuyar
fada.

A ranar da ya tafi itama ta tafi gidan anty
Salma nan suka hadu da Ummi aka fara tsare
tsaren yadda bikin zai gudana, anko kala biyar
anty salma ta dinka musu iri daya ita da Ummi,
tare sukaje akayi masu kunshi da gyaran gashi
har gyaran jiki duk tare aka yi musu nan kuluwa
ta zanzare ta fito kamar itace amaryar dan
alokacin babu wanda zai ganta ya zaci matar
aure ce kuma da yake itace akan komai tafito a
babbar kawar amarya sai su kansu abokan
angon suka zaci budurwa ce, kullum suna yin
waya da junior har lokacin da ya buga wasan
yake sanar mata da cewa yayi targade "gaskiya
junior ya kamata ka daina ball haka saboda kar
wata rana ka karye kuma" dariya yayi "kiyi mun
addu'a kedai kawai Allah ya dawo dani kisha
koko" murmushi kawai tayi, hidimar bikinsu suka
ci gaba dayi, kullum mom din junior itama tana
zuwa kayan gyaran amaryar da Anty Salma ta
hadowa Ummi kuwa da kuluwa suka shanye
tare, ranar alhamis akayi kamu, kai ranar idan
ba sani kayi ba kaga kuluwa cewa zakayi itace
amaryar tasha wani material orange riga da
skirt tayi dam acikin kayan tasa gwaggoro
orange ta dan yafa dan siririn dan kwalin
gwaggoron sai kaiwa da kawowa take tana
karbar bakinsu kawayen Ummi, mom tana daga
can tana hangota sai murmushi take yi tana
cewa "wannan yarinya da kokari take, ga ciki ga
kuma taki zama ta huta" saboda alokacin
kuluwa tayi wani fresh ga cika da tayi tako ina.

Ranar ko waya ba suyi ba da junior saboda
shagulgula sun hau kanta, sai dare sannan ta
samu damar yin waya dashi.

Washe gari akayi
wuni aka daura aure, kuma a ranar za akai
amarya kuma za ayi dinner dan haka daga wurin
dinner din gidan amarya za a zarce, shirya
amarya kuluwa tayi sannan itama ta shirya
kanta cikin material red, gwaggoro red, takalmi
red mai mutukar tsini tasha sarka fashion
katuwa golden, kwalliya aka yiwa amarya itama
aka yimata, ko dan abun yafawa bata dauka ba
haka suka tarkata suka tafi wurin dinner din
kuluwa ce a gaban motar da amarya da ango
suke, suna zuwa ta fita tareda shiga cikin hall
din taje ta gyara high table, nan ango da amarya
suka shigo daga can ta hango mom amma
bataje wurin ba, shagali aka fara gudanarwa nan
kuluwa takasa zama tayi nan tayi nan gashi
komai za ayi ita abokan ango suke zuwa su
fadawa, khamis daya daga cikin abokan angon
ne yazo kusa da ita "um jidda dan Allah ga
wasu matan abokan mu can sunzo kije ku gaisa
tunda ita amaryar babu halin zuwa" " OK ina
zuwa" "harda kishiyarki aciki" wal tayi da ido
"nifa matar aure ce, wallahi ina da aure"
hannunta taji an kama tana juyowa taga junior
janta yayi take ta bishi babu musu, suna fita ya
fara balbala mata masifa "ke kin manta kinada
aure ne?

Oh saboda ana biki shine zaki ajiye
auren ko?

To wuce mu tafi gida" kuka tafara
"dan Allah kayi hakuri ka barni nakai Ummi
gidanta" "bazaki kaitan ba" jikinta ya matsa ya
matseta a jikin kofa, hannunsa ya tura cikin
rigarta ya chafko kayan wasansa ya fara
matsarsu dama tasan yadda ya jima baya nan
dinnan dole yau ta gane kurenta, yar kara ta
saki saboda jin yadda ya matsa da karfi "dan
Allah ka barni na koma ciki" shiru yayi mata
babu amsa, mom ce tafito ashe tare sukazo da
junior shine ma ya kaita saboda tun yamma ya
dawo amma bai fadawa kuluwa ba, dakyar mom
ta shawo kansa ya yarda ya barta saboda idan
ta tafi babu wanda zai yi maraba da bakin
Ummi, komawa ciki tayi shikuma ya koma cikin
mota ya zauna.

Sai karfe 11 aka tashi daga dinner din aka nufi
gidan amarya agurguje kuluwa tayiwa Ummi
huduba ta fito saboda junior yana jiranta, tunda
ta shiga motar yaji yawunsa ya tsinke, "wash
nagaji" tafada tana mika "ai kuwa yau dolenki ki
bani hakkina wallahi, babu ruwana da wata
gajiyarki" zaro ido tayi amma batace komai ba
har sukaje gida, suna zuwa ya dauketa cak yayi
bedroom da ita, suna shiga ya fara cilli da
gwaggoronta, da su sarkarta sai da duk ya
ciresu sannan yafara nuna mata zallar so.

Washe gari kasa tashi tayi dan gajiya, sai junior
ne yayi musu girki, sati biyu da gama bikin
Ummi kuluwa ta fara laulayi sosai, nan suka
fara murna ita da junior kafin wani lokaci har ya
sanar dasu mom zancen cikin nan fa aka fara
lissafin haihuwa gaba dayansu sun dauki burin
duniya sun dorashi akan wannan cikin na kuluwa
shi kuwa junior kullum bashida magana sai "me
zaki ci?
Chapter 24 · 0% Book details