← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kara rushewa da kuka kuluwa tayi tace wlhi
sai Allah ya saka min mugaye kawai, sake
fitowa daga cikin motar junior yayi yace kai
bobo wlhi idan ba ka bar wannan village girl din
ba zan iya tafiya na barka ka tsaya sai wasting
din time dina kake a banza, tahowa bobo yayi
yana cewa double sorry my friend, juyawa
kuluwa tayi ta kama hanyar komawa tana tafe
tana kuka sai kace wata karamar yarinya, bobo
yana shiga motar Junior ya fusge ta aguje
kamar zai tashi sama yana driving yana bin
wakar omalele, dan kallonsa bobo yayi yarinyar
nan ta bani tausayi fa, sai kayi kuma junior
yafada lokacin da yake kara gudun motar,kai
tsaye unguwar jan bulo kubuga suka shiga dai
dai first gate suka karasa wani hamshakin gida
ginin dutse da dutse gida ne tangameme kuma
katoton gaske very massive, tun daga kofar
gidan ga wasu mopol nan da sojoji zaune suna
ganin mai shiga da mai fita, kan motar junior ya
kutsa cikin gidan,yana shiga yaje yayi packing
dinta acikin jerin gwanon yan uwanta, ya fito
shima bobo fitowa yayi yana cewa ya bahbah na
jira ka ne ko naje kawai?

Jeka kawai bobo i will
call you letter, ok sai na jika, cikin mai falon
gidan junior ya wuce yana tafe yana fito gamida
wakar oh my Darling i love you!

Da wannan
wakar ya karasa cikin falon wanda yake unguwa
guda mai karatu duk abinda ka sani na jin dadin
rayuwa to an tanade shi acikin wannan falon,
mom dinshi ya hango zaune tana waya da wata
fankaceciyar wayar ta tasha ado kamar bata
manyanta ba, wani dandatsetsen leshi ruwan
kwai tasa a jikin ta takafa dauri kunnenta da
wuyanta yasha gold mai girman gaske ga
zobuna data zubawa yan yatsunta da takalmi
hill a kafarta golden colour, inda take ya karasa
yana zuwa ya zauna kusa da ita gamida dora
kansa akan cinyar ta, kansa ta fara shafawa
kamar wani karamin yaro,muryar ta naji tana
cewa hajiya yabi ki siyo min setin gold dan
saudia guda daya amma ki hado da komai nasa
ajiki ina nufin tun daga kan dan kunnensa,
zobensa, awarwaron sa da sarkarsa amma bana
son mai araha kuma dan Allah ki zabo na
yanmata saboda wata girlfriend din junior ce za
tayi birthday shine zai bata a matsayin gift, ok
sai kin dawo, daidai lokacin ta kashe wayar ta
ajiye ta akusa da ita ta fara lailaya sumar kan
junior, junior whats happen?

Nothing mom, ok
har ka dawo daga wurin exercise din?

Mom na dawo amma zan kara yin wani now
now yana gama fadin haka ya tashi ya nufi wani
injin motsa jiki wanda ke girke acikin falon, hawa
yayi ya fara motsa jikinsa har na tsawon
mintuna 20 mom dinshi tana zaune tana
kallonsa har ya gama.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�7�

Sai da ya gama ya sauko daga kan gym din
kai tsaye dakinsa ya wuce, junior ba kayi
breakfast ba fa, zanyi mom kin san ban iya yin
break da sassafe sai nan da 11 yanzu bacci
nake ji saboda am too tired,to je ka huta maza
aje ayi bacci, murmushi yayi ya shige dakinsa
wanda yake kayace da kayan alatun more
rayuwa, toilet ya fara shiga yayi wanka ya fito
yazo ya kunna ac din dakin ya fada kan tafkeken
gadonsa wanda ya isa mutum 15 su kwanta ba
tare da takura ba domin gadon royal bed ne dan
gaske, remote ya dauka ya kamo tashar wakokin
turanci a tauraron dan adam ta cikin jibgegiyar
plasma tv din dake kafe a bangon dakin nasa,
kallo ya fara yi sama sama na wakokin da ake
sakawa marassa kyan gani domin wata wakar
ma mata ne tsirara suke rawa, yana cikin
kallonne bacci ya dauke shi nan ya bararraje ya
fara sharar baccinsa.

Ya dan jima yana bacci kafin ya tashi ya shiga
toilet yayi brush ya fito, falo ya nufa yana zuwa
yaga mom dinsa zaune ita da jawaheer da gudu
jawaheer ta taso tayi hugging dinsa tana sanye
da riga da skirt matsattsu, rungume ta yayi
tareda bata kiss a kumatu hy jawa yakike?

Yaushe kika zo?

Naje ai na ganka kana bacci, oh
yeah ya fada tareda sakalo hannunta cikin nasa
ya nufi wurin mom wadda ke zaune tana kallon
su sai faman murmushi take, hannun jawa cikin
na junior suka zauna kan kujera,bani labarin
boyfriend dinki, ya sunanshi, kafadar sa ta dan
doka, kasan ni ai ban fara soyayya ba amma kai
bani labarin girlfriend dinka, ni?

Ni ban da
budurwa amma ina da girlfriends da yawa more
than 100, dariya jawa tayi tace ai nasanka da
farin jinin yanmata sai alokacin mom tayi
magana ai junior kam girlfriends domin akwai
ma wadda zata yi birthday next week kinga har
gida tazo tayi inviting dinsa, dariya jawa ta fara
wa yaga na mamajo, duka junior ya kai mata ta
rike hannunsa ni dai ummi A'isha yau mamaki
ya gama cika ni, kallon junior mom tayi junior
baka yi breakfast bafa, mom ki barshi kawai na
yi lunch anjima, what?

Baka isa ba junior yanzu
zan yi maka dura kamar yadda muka saba, wai
mom har yanzu junior bai cin abinci sai kin dura
masa?

Ai haka yake jawa har yanzu, maza
dauko min flask din farfesun nan na dura masa
da sauri jawa ta mike zata tashi Junior ya
jawota ta fado jikinsa, riketa yayi wlh babu inda
zaki je yarinya.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�8�
~~~ Mom da kanta taje ta dauko abincin tazo
inda yake ta tashi jawa ita kuma ta zauna ai
tuni Junior ya bata fuska sai kace wani karamin
yaro dan yaye mom ki barni Allah anjima zan ci
da yawa, a'a my boy ka daure ka danci ko babu
yawa kaji, pls junior yawwa maza bude bakin,
naman ta yanko wanda yaji tumatur da albasa
da tafarnuwa dakyar junior ya bude dan karamin
bakinsa mom ta saka masa naman amma yana
hadiyewa yaji zuciyarsa na tashi saboda shi
baya son garlic kwata kwata, jin cikinsa yayi ya
fara murdawa abunku da shagwababbe tuni ya
fara langwabewa mom barshi haka my
stomach...

Mom karki kara min pls, cikin rudu
mom ta kalleshi junior menene?

Mom cikina
ciwo yake duk yadda aka yi ansa garlic ni kuma
bana sonta, a fusace mom ta danna inter come
kamar zata tsaga gidan dan kara, aguje
ma'aikatan gidan suka shigo cikin tsawa tace
ina kukun da yayi girkin nan?

Da sauri wani mai
green din Kaya yace hajiya bata nan taje gida ta
dawo, to yana dawowa ku turo min shi, juyowa
tayi ga junior ta rikeshi ta kwantar dashi a
jikinta tafara shafa bayansa tana jijjiga shi
kamar wani yaron goye, sannu Junior jawa ta
fada tare da matsowa kusa dashi, kamo hannun
jawa yayi yace zaki iya yin driving ki kai mu
country mall?

Zan iya mana me zaka yi acan?

Zanje ne naci abinci na siyo wasu abubuwan da
nake bukata, ok tashi muje, to kije dakina ki
dauko key din motar mana suna nan akan
bedside drawer dina duk wadda yayi miki ki
dauko, tashi jawa tayi ta nufi bedroom dinsa ita
kuma mom taci gaba da yi masa sannu tana
cewa junior zaka iya zuwa kuwa?

Ko dai na aika
a siyo maka, mom zan iya zuwa ai cikin nawa
ya daina ciwon zanje ne kawai na siyo
shawarma da dan fish gasasshe, to junior sai
kun dawo, tashi yayi lokacin da jawa ta fito
suka fita tare yana rike da hannunta domin shi
junior ba wani abu bane ya rike hannun mace ko
ya rungume ta harma yayi mata kiss duk
wannan is nothing a wurinshi dan har ya saba
duk lokacin da ya hadu da friends dinshi mata
to hugging da kissing din gaisuwar su, suna fita
wayar mom ta fara kara, a hankali ta daga tana
cewa hello dadyn junior, yes maman junior ya
kuke?

Lfy lau, ina junior?

Junior yanzu ya fita zaije country mall shida
jawa,
Yaci abinci kuwa?

Wlh dad junior yau baici komai ba,
Haba maman junior why ke ba zaki bashi ba
tunda kin san shi ba ci zai yi ba,
Am sorry dad junior wlh na fara bashi sai
cikinsa ya kama ciwo ashe abincin akwai garlic
aciki shi kuma kasan ba ya sonta,
What?

Yanzu yana ina?

Yaji relief har ya fita cin shawarma
Ok wanne kukun ne ya dafa abincin?

Ki tabbatar
kin sallame shi yabar gidan kafin na dawo,
To shikenan sai ka dawo, katse wayar yayi ya
ajiyeta cikin fushi domin a duniya ya tsani
abinda zai taba lafiyar junior, zai iya yi masa
komai a SANADIN GATAN da yake nuna masa.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
2�9�

Na
UMMI A'ISHA
Su junior suna fita county mall suka nufa shi da
jawa, ga wani kida da yake tashi tamkar a
cinema ko kuma wurin wani kwarya kwaryar
party suna tafe suna bin wakar har suka karasa,
parking din motar jawa tayi tareda fitowa,
hannun junior ta kama suka shiga ciki mutane
sai binsu da ido suke duk inda suka wulga idone
kawai yake binsu sai dai da yawa daga cikin
mutanen wurin kama tun daga ma'aikatan su
har masu siyayyar ba suyi mamaki ba
kasancewar sun San ko waye junior, kallonsa
jawa tayi junior what's all this eyes for?

What's
the meaning of this all looking??

Gaskiya yan
garin nan naku akwai gyara har yanzu baku
waye ba you are still villagers wlh, dan
murmushi junior yayi, that's why I hate 9ja
komai nasu abun kallo ne, yanzu dan na rikeki
meye abin kallo??

Tsaki jawa tayi forget about
them kawai, zagayawa suka ci gaba dayi har
suka tsini abinda suke so suka koma wurin shan
ice cream.
*************
A bangaren kuluwa kuwa tana komawa gida ta
kwanta taci gaba da kuka, kullum dama tana
kewar mahaifin ta, amma yau sai taji tafi
tunashi musamman wannan wulakancin da
gayen dazun yayi mata, kuka tayi sosai sannan
taji zuciyar ta ta dan nutsu yanzu ta danjita ta
dama dama, to amma shi wannan guy din waye
shi??
Chapter 4 · 0% Book details