← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 25

Sashe 3

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dadi ne ya ratsa zuciyar kuluwa saboda idan da
abinda take so to karatu ne ita dai a rayuwar ta
tana so ta ganta a makaranta tana daukar
darasi, maganar anty salma ce ta katse mata
tunanin ta, yaya ya fada min komai game da irin
rayuwar da kike yi a hannun iyatu da duk irin
tsangwamar da tayi miki, na rasa me yasa iyatu
bata da halin kwarai ta dauki duniya ta riketa
kamar ba zata barta ba, amma yanzu gashi ai
kin tafi kin barta sai muga wanda zata
takurawa, shiru kuluwa tayi aranta tace Allah
sarki babana yanzu kuma shine zai jure jarabar
iyatu tunda ni bana nan.

Misalin karfe 3 na yamma su kuluwa suka isa
garin kanon dabo tumbin giwa wanda masu iya
salon magana su kance ko da me kazo an fika,
kai tsaye unguwar sharada phase 2 suka wuce,
kuluwa zare ido tayi ta fara kalle kallen
abubuwan ban mamakin da suke cikin birnin
saboda ko motocin dake wucewa abin kallo ne
gashi dan adam kamar ba a mutuwa,
suna shiga unguwar kuluwa ta cika da mamaki
saboda ganin irin gine ginen dake girke a
unguwar kowanne gida ya hadu iya haduwa ga
shuke shuke ta ko ina.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�3�

Manyan gidaje ne iya ganinka saboda unguwa
ce ta masu hannu da shuni, kuma unguwar shiru
take babu hayaniya gata tsit kamar babu
mutane,
wani babban gida mai bene suka isa anan anty
salma tayi hon cikin dan kankanin lokaci wani
mai gadi yazo ya bude musu kofar gate din,
kutsa kan motar tayi ciki taje tayi packing dinta
a inda aka tanada, cikin gidan suka hara wanda
yake katoton gaske gashi yasha ginin zamani
sai kyalli yake, tana gama kuluwa na biye da ita
a baya har cikin wawakeken wani falo wanda ya
tsaru iya tsaruwa, kujera anty salma ta nuna
mata tace zauna ina zuwa, nan kuluwa ta zauna
in banda kalle kalle babu abinda take yi komai
na falon bakone a wurin ta shiyasa ta tsaya take
ta kallon fallon har anty salma ta fito ta kawo
mata abinci ta bata.

Abincin ta fara afkawa har ta koshi sannan ta
samu nutsuwa, kallonta anty salma tayi hawwa
kin san Ummi?

Girgiza kai tayi, Ummi yata ce
ita ma ba zaki fita a haife ba, tare zaku zauna a
gidan nan saboda dama ni ba anan nake da
zama ba, zuwa nake yi lokaci lokaci, yanzu ki
taso muje ku gaisa da kishiya ta kafin ummin
tazo.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�4�

Bin bayan anty salma tayi har zuwa wani
hadadden sashe mai mutukar kyau da tsaruwa
komai na ciki mai tsada ne,
wata farar mata kyakkyawa ta gani zaune a falo
tana ganinsu ta fara fara'a da alama suna
zaman lafiya da anty salman, zama kuluwa tayi
ta gaida ta ta amsa fuska a sake kamar dama
ta santa, maman ummi ga yar tawa wadda zasu
zauna da ummi dan Allah idan anga tayi ba
daidai ba a tsawatar mata, babu komai anty ai
shi da na kowa ne, tashi anty salma tayi tace to
zo mu tafi hawwa, binta kuluwa tayi suka fita
daga bangaren Maman Ummi suka koma nata
suna zuwa suka tarar da har Ummi ta dawo nan
kuluwa ta saki baki tana kallon ummi wadda
take yar gayu kamar yar India gata dai bata fita
a haife ba amma ta iya tsara gayu, zaunar su
anty salma tayi ta gabatar wa da kowacce yar
uwarta tare da dorawa ta hanyar cewa hawwa
zan samo miki teacher wanda zai rinka yi miki
lesson kafin ki fara zuwa makaranta murmushi
kuluwa tayi nagode anty salma Allah ya saka da
alkairi dama wlh ina son makaranta sosai, kiyi
hakuri hawwa zaki yi kinji, to anty na gode.

Kwana 2 da zuwan kuluwa ta dan goge tayi fes
saboda yanzu bata aikin wahala komai yi musu
ake yi sai dai kawai suci su sha su kwanta nan
fa kuluwa ta fara hada kiba saboda samun jin
dadin da take,
tuni anty salma ta nemo mata lesson teacher
wanda zai rinka koyar da ita turanci da sauran
subjects din da za tayi a makaranta, ita kuma
ummi kullum tana zuwa school safe da yamma
a halin yanzu tana ss2 zata shiga ss 3.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�5�

Lokaci ne yaci gaba da tafiya da dafarko
kuluwa ta dan fuskanci matsala wajen koyon
harshen turanci amma koda ta dage ta maida
hankali dandanan ta fara fuskanta kan Ummi
A'isha ta ankare tuni kuluwa ta zama baturiya
domin ita da ummi yanzu basa hausa komai
nasu da turanci suke yi, ganin haka yasa anty
salma zuwa tayi mata registration a wata
private school mai suna sharada standard boys
and girls school, ss 2 suka bata saboda tayi
girma ta wuce asata a junior section, sai dai ba
makarantar su daya da Ummi ba kowa tasa
daban ita ummi inda take zuwa da nisa ita
kuma kuluwa babu nisa domin acikin unguwar
ne.

Tuni kuluwa ta fara zuwa makaranta uniform
dinta riga da skirt ne maroon da hijab fari head
tied dinma fari ne tun farkon zuwan ta tasaba
da mutane tayi kawaye saboda yadda take da
farin jini sai dai kuma wani lokacin ta kan shiga
damuwa na rashin babanta a kusa da ita.

Yau
ma kamar kullum bayan sun gama breakfast
dinsu da ummi kuluwa ta tashi zata shiga
wanka, kallon ta ummi tayi hawwa yau ba zaki
school bane?

Zanje mana wanka kawai zanyi
saboda bana son naje ina tsami a rainani, um to
sai kin fito ni kam na tafi, uniform ummi tasa ta
dauki school bag dinta ta tafi ita kuma kuluwa
wanka ta shiga ta silla ta fito ta shirya tasha
turare tasa wankakken uniform dinta kuma
gogagge ta sabi school bag tayi hanyar
makaranta tasha safa fara da farin combos ga
school bag dinta baka,
daidai kwanar da zata sada ta da makarantar su
ta hango wata bakar mota hadaddiya mai black
din glasses kirar KIA Rio, in banda tashin sautin
music babu abinda kake ji yana fita daga cikin
motar kai kace speakers aka doddora ma motar,
motar tana zuwa saitin kuluwa ta shiga cikin
wani ruwa wanda ke kwance a tsakiyar hanyar
ya hadu da jar kasa yayi jawur, fatsalllll ruwan
ya fantsama ajikin kuluwa gaba daya farin
hijabinta ya wanke da ruwan kwatar ita kanta
fuskar ta sai da ruwan ya jikata, tsayawa
kuluwa tayi tana son ganin wanda yayi mata
wannan aikin, kamar motar ba zata tsaya ba sai
kuma taja ta tsaya a sannu aka bude bangaren
mai zaman banza wani dan kyakkyawan sauri
ya fito, baiwar Allah kiyi hakuri wlh muna sauri
ne ya fada yana kallonta, haba malam wannan
wanne irin abune kawai kuna driving without...

Rufe kofar motar yayi ya tako inda take kiyi
hakuri dan Allah tsaki kuluwa taja amma
gaskiya ba kusan mutuncin dan adam ba domin
kun cuceni sai da na gama shirina tsaf har na
kusa zuwa school zaku batani da kwata?

Hon
mai karfi aka matsa daga cikin motar da alama
wanda ke cikine ya gaji da jiran na wajen, hakuri
yaketa bata amma kuluwa ta rufe idonta taci
gaba da yaba masa magana, shi kuma na cikin
motar sai hon yake,yayi hon sunfi talatin ganin
na wajen yaki zuwa su tafi yasa shi bude kofar
motar a fusace ya fito, hmmm ni dai ummi
A'isha guy din yayi mugun tafiya da hankali na,
dogo ne dan madaidaici fatarsa chocolate colour
ce tamkar dan kasar Ethiopia yanada dogon
hanci gashi da manyan idanuwa kamar kwai
idonsa yake saboda round eyes gare shi, gashin
girarsa kamar na mace dan sunada yawa,
lebensa jajaye ne sosai ga dan madaidaicin
bakinsa, yana da dan saje a fuskarsa,kumatunsa
na dama kuma dauke yake da beautiful point, ya
tara suma him akansa kamar wanda za a kitsa,
kunnensa guda daya yasaka earring fari, haka
wuyansa ma yasa sarka fara yar sirirya, yana
sanye da bakar riga mai gajeren hannu da
shorts trouser iya gwiwar sa,
kamar wani wanda yaga kashi ya fara magana
kamar me yin rada, bobo meye haka?

Kazo mu
tafi kawai kana bata min lokaci, wanda aka kira
da suna bobo ne ya kalle shi sorry baka ga
abinda muka yi bane?

And so what?

Me zaka yi
mata?

Zaka wanke mata ne ko kuwa?

Ya fada
yana yiwa kuluwa kallon banza,ganin haka yasa
kuluwa fashewa da kuka, wlh ban yafe muku ba
mamugunta kawai yanzu idan naje makaranta a
haka dukana za ayi a wurin assembly sai dai na
koma gida, kiyi hakuri yanmata bobo ya fada ba
wani hakuri da zanyi wlh ban yafe muku ba,
shi dai classic guy dinnan na jikin motar
tsayawa yayi kawai yana kallon ta wannan
wacce irin shagwababbiyar yarinya ce?

Dan
kuka bashi da wuya kawai daga haka sai kuka?

Maganar bobo ce ta katse shi JUNIOR ka bata
hakuri tunda kaine ka bata ta, wannan ne kuma
bata isa ba junior ya fada yana komawa cikin
motarsa.

Masu karatu ku biyo ni dan jin waye junior.
[1/29, 10:19 PM] Ummi A'isha: 🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
2�6�
Chapter 3 · 0% Book details