Sashe 16
Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Pls ki saki ranki nan da 3
weeks zaki ganni na dawo", "Allah ya kaimu",
daidai lokacin bobo ya shigo falon "ya baabah
zo mu tafi na kaika airport din kaga time yaja",
tashi junior yayi "ok bari na kira mom", dakin
mom ya nufa Jim kadan suka fito tare, daidai
lokacin shima dad ya shigo, "junior tafiyar ce?"
"Eh" dad, sakin mom yayi yaje ya rungume dad
dinsa "dad ayi min addu'a final exam zanyi",
'Allah yabaka sa'a junior we whish you gudluck
in your exams", "much tnx dad", kallon kuluwa
yayi wadda ta sunkuyar da kanta, bai karasa
inda take ba yace "jidda natafi,Allah ya kiyaye
hanya" inji kuluwa tafada muryar ta na rawa,
fita suka yi dukansu domin raka junior mota,
dawowa junior yayi "am hawwa i have forget to
tell you something, dan Allah idan zakije sch ki
rinka saka nikab kina rufe fuskarki kinji??"
"Naji" ta fada ba tare da ta kalleshi ba, juyawa
yayi ya fita, yana fita ta fashe da kuka, a haka
mom ta dawo ta sameta tanata kukan tafiyar
junior, kamata mom tayi suka shiga bedroom
dinta wanda haduwarsa tafi gaban kwatantawa,
akan gadonta ta zaunar da ita,
"kiyi hakuri hawwa kinji, ai ba jimawa zai yi ba,
kinga nima idan naga kina kukan nan hankalina
tashi zai yi, dan Allah kiyi shiru kinji", kukan ta
daina amma hawaye basu daina sintiri akan
kumatunta ba.
Fita mom tayi ta tafi sashen dad tabar kuluwa
kwance a dakinta, tajima tana kuka sannan tayi
shiru ta tashi ta fito, falon gaba dayansa kafe
yake da hotunan junior kala kala, wani ma tun
lokacin yana karami, wani yana pri sch, wani da
kayan kwallo wani da kananan kaya yasha dan
kunne da sarka, kai gasu nan dai birjik, dakinsa
na da ta leka, komai a shirye kamar yana ciki,
gefe gadonsa ga wani frame nan mai hoton jar
flower ajiki an rubuta I LOVE YOU JIDDA, frame
din ta dauka tana mamaki, ita jiddan ko wata
yake nufi saboda bakinta da nashi bai taba furta
mata kalmar so ba sai dai dazu taji dadin
kalamansa da yace ta rinka rufe fuskarta
wannan ya nuna mata kenan yana kishin wasu
mazan su kalle masa fuskarta, rungume frame
din tayi ajikinta tareda "furta love you too
junior!."
6�2�
Haka ta karaci zagaye zagayen ta agidan tana
kallon kayan kiriniyar junior wasu abubuwan ma
tun yana dan karami yayi amfani dasu amma
SANADIN GATA yasa an adana su suna nan har
yanzu, kayan wasan Sa kuwa ba acewa komai,
ga kekunansa da machine da motocinsa harda
dokinsa a daure duk nasa ne, lallai sai yau
kuluwa ta kara jinjina irin son da mom da dad
suke yiwa junior.
Ranar sai dare driver ya kaita gida, tana shiga
taji kunci ya rufeta, mai gadine ya biyota ciki
"gashi dazu abokin yallabai ya kawo wai abaki
inji oga", karba tayi ta nufi dakinta, wayar junior
ce kirar smart phone baka, kunna wayar tayi i
love you jidda shine welpaper din dake kan
screen din wayar, ajiye wayar tayi ta shiga
wanka ta fito ko rigar bacci bata saka ba ta
zizzira rigunan sanyi har guda hudu, ta
tukunkune acikin blanket, wasu hawaye ne suka
zubo akan kumatunta, sai yanzu taji hankalinta
ya sake tashi da rashin junior, "yau zanyi baccin
maraici tunda junior baya nan", fuskarta ta cusa
acikin pillow, tana ta son tayi bacci amma ta
kasa har asuba tayi.
Washe gari ta shirya ta tafi makaranta yanzu
tana dan samun saukin damuwar rashin junior
saboda in taje sch tun 9 bata dawowa gida sai 4
da ta dawo kuma zata fara ayyukan gida ko ta
fara karanta lecture note dinta, sai dai har
yanzu ba tayi waya da junior ba tun tafiyarsa,
yau bayan ta dawo daga sch tanata aikinta a
kitchen kasancewar gidan babu kowa daga ita
sai yar shimi da dogon wando, wayar junior ce
tafara tsuwwa da sauri ta daga "hello junior",
"jidda yagida?" "Lfy lau ya papers?"
"Alhamdulillah kinjini shiru ko?
Wlh phone dina
na manta a taxi din dana hau sai yau aka kawo
min, ko mom ma ba muyi waya da ita ba",
"ayya to yakake"
"lfy lau, naga girki kike ko?
Me zaki dafa?"
"Ta ina ka ganni?"
" Ai video call ne duba ki gani", da sauri ta kalli
screen din wayar sai ga junior da gajeren wando
yana kwance akan katifa, "ashe kallona kake,
gaskiya ni ban shirya waya dakai ba sai kasa
riga", "ki bari anjima zan kiraki to", katse wayar
tayi cikeda farin ciki yau taji muryar junior kuma
harma ta ganshi, tun daga lokacin kusan kullum
sai sunyi waya da junior sunyi hira amma har
yau bai furta mata Kalmar so ba haka itama
bata furta masa ba, ko meye dalili?
Ummi
A'isha bata da masaniya.
[2/6, 6:13 PM] Ummi A'isha: SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
6�3�
Yanzu damuwar kuluwa kalilin ce shine na
rashin jin dumin junior domin yau ya kai kimanin
sati 2 da tafiya, bayan tafiyarsa taje sharada ta
wuni sau daya a gidan anty Salma sannan taje
gidan mom dinsa ma ta wuni.
Yau tun acikin Hall cikinta yake ciwo dan haka
lokacin data fito daga lecture masallacin mata
ta wuce taje ta kwanta, tana nan kwance
yanmata sai shigowa suke amma ita fuskarta da
nikab, masallacin cike yake da mata sai kace
kasuwa sai hayaniya ake, kowanne group da
hirar da suke, "hello teemah?
Eh, Allah?
Innanlillah, Allah ya saka miki wlhi, ai dan iska
ne zai iya, tab amma ya cuceki", wata budurwa
ce take furta wannan maganar lokacin da take
yin waya, tana kashe wayar ta fara masifa
"kuji wai junior yayi aure dan iska, waye junior?"
Suka tambaya, "wannan dan kwallon mana,
saurayin teemah nefa cousin dina gaba daya ta
gama sakankancewa shi zata aura kunji yayi
aure, bakuga yadda ya rinka daukarta ba lokacin
da suna soyayya, gashi sch daya suke lokacin
suna karatu a kasar Cyprus kullum suna tare da
yake itama yar harka ce har dakinsa take zuwa
ta kwana kafin a koreshi daga makarantar", "au
korarsa ma akayi?", "eh iskanci aka kamashi
sunayi shida wata malama a office dinta daga
nan aka koresu gaba daya shinefa ya koma
Ghana ya sake Neman admission a wata
makarantar to har lokacin basu rabu da teemah
ba daga Ghana yake hawa jirgi yatafi Cyprus
weekend wurin ta,kawai kuma sai yanzu wai taji
yayi aure, kunji dan iska", "wai da shi din waye
ubansa?"
"Wannan dan siyasar ne mana na nan garin",
"ance ma ai matar junior din a sch dinnan take",
"yo kwana nawane ita dinma zai saketa ai da
zarar ya gama da ita zai yi waje da ita wlh
tunda ba isa auren yayi ba aka yi masa", "eh ai
SANADIN GATA ne yasa iyayen nashi yi masa
aure yanzu", "kuma kun san gayen akwai kudi
da kyau tunda dan kwallo ne duk wata biliyoyin
kudi government take tura mishi", "ni kuwa zan
so naga matar nan ta junior", "to ai ance ba shi
ya Aurota ba iyayen shine suka aura masa ita",
"lallai ashe auren gata aka yi masa", jin
maganganun sunyi yawa yasa kuluwa tashi ta
fita lokacin da zata fita taji wata na cewa "ai
ana zargin cewar ma junior din ba dan halak
bane", kuna taji zuciyar ta nayi mata, "wlh junior
dan halal ne" tafada acikin zuciyarta saboda duk
wanda yaga junior yaga dad dinsa to zai san
shine ya haife shi gashi dai ya dauko hasken
mom dinshi amma duk da haka yana kama da
dad dinsa ita kanta wani lokacin ma ganin
kamar junior da mahaifinta take, "kai Allah ya
kyauta meye amfanin haka yanzu?" Ita dai tasan
junior gagararre ne amma bata tsammaci abin
nasa yakai haka ba.
Waya tayiwa driver dinta yazo ya dauketa duk
da cewar bata gama lecture dinta ba amma dai
gara ta koma gida zai fi mata, yau taji duniyar
tayi mata zafi sosai, tana zuwa gida ta kwanta a
falo, haushin junior ta ji yana shigarta wato
dama har korarsa a kayi a sch?
Kalaman wata
dataji tana fada ne ya fado mata,"ai insha Allah
shima haka za ayiwa yayansa", "to kuma ai
"yayan junior "yaya nane tunda nice mahaifiyar
su, kai amma gaskiya junior ya bata wayonsa".
6�4�
Haka ta zauna cikin damuwa amma ba tayi
kuka ba sai dai idonta yayi tsananin ja, dakinta
ta koma ta kwanta duk jinta take kamar bata da
lafiya.
Washe gari da safe ta dauki waya ta kira
junior domin tana son zuwa asibiti ciwon ciki na
damunta, tanata ringing ba a dauka ba, can taji
mace ta dauka, da Sauri ta duba saboda video
call suke yi da junior tana dubawa taga wata
budurwa ce daga ita sai towel a dakin junior, da
Sauri ta katse wayar ta samu wuri ta zauna ta
ma rasa me zatayi, tana nan zaune junior ya
fara kiranta, kin dauka tayi har tayi karar ta
gama, text ya turo mata pls Jidda pick my call,
banza tayi dashi, "kenan duk abinda taji an fada
jiya akansa gaskiya ne?" Text ta tura masa
cewar zata tafi tabar gidansa idan ya sallami
karuwar tasa ya aiko mata da sakinta, tana
gama tura text din ta kashe wayarta ta fara
hada kayanta cikin babban akwati, lokacin da
junior yaga sakonta ba karamin tashi hankalinsa
yayi ba domin shi wlh bama ya gidan lokacin da
ta iyo wayar, kuluwa na gama hada kayanta ta
dauka ta fita ta sa driver ya kaita garinsu wato
kauyen ciyako.
Hankalin junior ba karamin tashi yayi ba gashi
babu halin ya taho gida saboda ya fara exam,
dole ya dan cire damuwar acikin ransa.
Ita kuwa kuluwa ko hawaye kasa zubarwa tayi
kuma tayi alqawarin ba zata sanar da kowa
wannan sirrin ba domin tsakaninsu ne ita da
junior dan haka idan ta tona asirinsa tamkar ta
tonawa kanta ne, shiyasa ma taga rashin
dacewar taje gidan anty salma da sunan yaji ko
kuma gidansu junior din domin dole sai an ji
dalilin zuwanta ita kuma bata son kowa yaji.