← Book details Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 25

Sashe 1

Sanadin Gata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ry 2017
aisha ummi at 04:09
SANADIN GATA 1-End
ONLINE HAUSA WRITERS
SANADIN GATA
Na
UMMI A'ISHA
JAN KUNNE-Duk wanda ya canja wannan
labarin ko sunan taurarin ciki ko na marubuciyar
Allah ya isa ban yafe ba.

Pg 1-10
~~Kanta dauke yake da farantin talla wanda aka
kasa mata dafaffen rogo da gyada kulli kulli, taci
damara sai kace wadda za tayi dambe tana tafe
tana rera wakar ta"iye nanaye ayye yaraye
nanaye carmama, ina tafiya ta jirgin goro zaya
kade ni, jirgin goro kar ka kadeni, jirgin goro zan
maka sako, sakon goro ko na turare in kaje kace
da uwata, in kaje kace da ubana jirgi yai bari,
jirgi yai bari da madaurin aurena, iye nanaye
ayye ya raye nanaye carmama, da inna da baba
an kawo kudin toshina cacas cas suna kirgawa,
sun ganni suna boyewa in kun so kubar boyewa,
auren fari sai na zaba sai na zabi wanda na ke
so koda soja ko dan sanda, koda kuku koda
boyi, koda jinjiri sha mama sai yaci tuwon
kwanona sai yasha ruwan kwanona sai na kai
ruwa sai nakai ruwa ban daki yai wanka, iye
nanaye ayye yaraye nanaye carma....kuluwa,
kuluwa kawo rogon, muryar wasu maza masu
sai da ruwa ne ya hana kuluwa karasa baitin
wakar da take rerawa, cikin sauri ta nufi wurin
da suke, tana zuwa ta sauke farantin da ke
kanta ta fara kukkulla musu kamar yadda suka
saba siya, nan da nan aka warwashe ta dauki
farantin ta cikin hanzari bayan ta kirga kudinta
ta hada Kansu naira dari biyu cif cif, sauri take
sosai dan tasan yanzu iyatu tana nan tana jiran
zuwanta.

Tafiya take gudu gudu sauri sauri kamar zata
bar garin har ta karasa gidan nasu wanda yake
ginin kasa ne wato jar kasa, ciki ta karasa can
ta hango iyatu kwance a tsakar dakin ta kamar
yadda ta saba a kullum.

Ta maza tayi ta tunkari
cikin dakin ta shiga bakinta dauke da sallama
agwasale iyatu ta amsa sallamar tata ta kara
gyara kwanciyarta kafin ta wurga mata harara,
tsugunnawa kuluwa tayi tace gashi iyatu na
sayar na dawo, baki iyatun ta taba sannan tace
miko min kudin na gani, mika mata kuluwa tayi
ta karba ta kirga kudi sun cika cif cif ko
kwandala bata bata ba, ungo wannan ki tashi ki
tafi kasuwa kije ki iyo cefanen tuwon dare da
zakiyi saura kuma ki tsaya a yawon da kika
saba ki ga yanda zan rugurguje ki a gidan nan,
yar masu da bakar zuciyar tsiya, tashi kuluwa
tayi ta fita daga cikin gidan ta nufi kasuwa inda
za ta iyo cefanen.

Wata azababbiyar yunwa take ji saboda rabonta
da taci abinci ta koshi har ta manta yunwa take
ji sosai, haka ta samu ta shiga kasuwar ta yi
cefanen ta nufo gida, akan hanyarta na dawowa
ne taci karo da mairo kawarta, kallon mairo tayi
cike da sha'awa saboda sanye take cikin
uniform din makarantar islamiya duk da cewa ita
ma mairon tana talle to amma ita tana zuwa
makarantar boko da islamiya sabanin ita da
babu abinda take yi sai talle, daga talle sai aike
sai aikin tsakar gida komai na gidan ita ke yinsa
ita iyatu bata da abin yi sai kwanciya sai ko
idan tayi wani abun na laifi ta jibgeta, cikeda
tausayawa mairo tace kuluwa daga ina haka?

Hmm mairo kenan ai kema kin san daga inda
nake domin daga talle sai aika sune ayyukana
ina son makarantar boko da arabi amma iyatu
ta hanani karfi da yaji, gashi iyatu bata tausaya
min ko kadan hatta baba bata daga masa kafa,
dafa kafadar ta mairo tayi kiyi hakuri kuluwa
kuma dan Allah kici gaba da hakuri da halayen
iyatu saboda wata rana sai labari komai na
duniya da kika ganshi mai wucewa ne, daga kai
kuluwa tayi idonta duk ya cicciko da kwalla
naira goma mairo ta mika mata gashi inji
shamsu yace idan na ganki na baki, karba tayi
tace nagode nagode mairo hakika shamsu ya
cika masoyi cikakke saboda komai runtsi yana
tare dani, murmushi mairo tayi hakane sai dai
Allah yasa soyayyar taku takai ga aure,
murmushi kuluwa tayi tare da juyawa ta fara
tafiya tana murmushi wa ya ganni nida shamsu
a matsayin ma'aurata?

Ni kaina nasan za a
zuba love ba dan kadan ba.

Gida ta tunkara tana shiga tun daga cikin soro
ta fara jiyo hargowar iyatu wannan shegiyar
yarinya tana kona min rai, wannan yarinyar kwai
marar albarka, tun da dadewa na aike ta amma
saboda bata ganina da mutunci shine taje tayi
zamanta to wlhi bara ta dawo yau mai rabani da
ita sai Allah, jikin kuluwa ne ya fara rawa
saboda jin kalaman iyatu saboda tasan bata iya
duka ba duk abinda ta samu kwada mata za
tayi, da makyarkyata ta shiga cikin gidan
bakinta yana rawa tayi sallama, ai iyatu na
ganinta ta fara ruwan bala'i sai yanzu kika
dawo?

Nace sai yanzu kika dawo min?

Saboda
ke shashasha ce mai bakin hali shine kika je
kika yi zamanki ko?

Cikin in ina kuluwa tace wlh
iyatu babu a inda na tsaya, zaki fada min a inda
kika je kika zauna yanzu yanzun nan iyatu ta
fada tare da daukar wani faskare ta nufe ta tana
cewa kar ki kuskura ki gudu idan kika fita daga
gidan nan sai na lahanta ki, kuka kuluwa ta fara
yi ita kuwa iyatu ta nufeta gadan gadan, da
gudu mahifinta ya fito daga cikin turakar sa
yazo ya rike faskaren hannun iyatu yana cewa
haba tsahare me yasa kike haka ne?

Yarinyar
nan kina gallaza mata, kina cutar da ita ki kiyayi
ranar da sakayya za tazo wlh kiji tsoron Allah
tsahare domin yawancin yaron da ka cutar shine
yake zama wani abu a rayuwa,kuma irin su
Allah yake daukaka wa, rufe min baki tsohon
banza tsohon wofi, kai in banda ma hudubar
shaidan ta yaya zaka zauna kana yabon wannan
yarinyar har kana tunanin zata zama wata nan
gaba, to ai ba irin wadannan Allah yake
daukakawa ba saboda yarinyar nan ba yar arziki
bace yar tsiya ce kuma wlhi in dai ta iyo cikin
shege babu ruwa na sannan sai dai ta nemi
wani gidan amma ba dai wannan ba, in sha
Allahu hawwa'u ba zata yi cikin shege ba
saboda ni nasan irin tarbiyar da na bawa yata,
dakyau malam muhammadu, nace da kyau
Malam muhammdu lallai yayi maka kyau wato
saboda ban taba haihuwa ba shiyasa zaka yi
min gorin haihuwa?

Yayi maka dai dai babu
shakka kanka ya fito daga kuttu kuma ka samu
lafiya, nagode da ka daurewa yarka kugu tayi
min rashin kunya a gidan nan sannan kuma ka
nuna mata ban isa da ita ba dan bani ce na
haifeta ba,to wlhi sai na dau mataki a kanku, ba
dai da ni kake magana ba, yayi maka kyau,
juyowa ga kuluwa tayi ke kuma idan kin ga
dama kije ki dauko ruwa kizo ki dora abincin
idan kuma baki ga dama ba ki barshi shashasha
mai mugun yancin tsiya, bokiti kuluwa ta dauka
ta fita daga cikin gidan ta tafi tuka tukar dake
girke a filin gidan sarki, nan taje ta saka bokitin
ta akan layi ta koma gefe ta zauna ta fara
tunanin rayuwarta.

Ita kadai ce a wurin mahaifin ta, bayan ita bai
sake haihuwa ba, Allah ya karbi ran mahaifiyar
ta tun lokacin da ta haifeta domin a wurin
haihuwar ta ta rasa rayuwar ta, tun lokacin da
mahaifiyar ta ta rasu babanta ya auro iyatu
domin ta riketa amma sai abin ya canja salo
domin iyatu babu abinda take mata sai zalunci
sam ba ta kaunar ta ko kadan asalima duk
wanda ya nuna yana kaunar kuluwa to sai ta
dau karan tsana ta dora masa, ayanda mahaifin
ta ya bata labari mahaifiyar ta salaha ce
mutuniyar kirki mai son jama'a sam duniya bata
dame ta ba gata da rikon addini she is pious,
religious, gata kamila tunda ta samu cikin
kuluwa take fatan Allah yasa ta haifi yarinya
Mace domin ta rada mata suna hawwa'u amma
sai Allah bai yi zata zauna da yar tata ba.

Iya
babanta da iyatu kawai ta sani saboda bayan su
ba tasan dangin mahaifiyar ta ba balle na
mahaifin ta sai dai ako da yaushe mahaifin ta
yana bata labarin cewar yana da yan uwa guda
2 a birni daya mace daya namiji, namijin yayan
sa ne yayin da macen ita ce take binsa sunanta
Salma amma ita bata taba ganin yan uwan nasa
sun zo ba kuma yasha fada mata cewar yasan
iyatu ce tayi surkullen ta irin nasu na mata ta
raba shi da yan uwansa, wasu zafafan hawaye
ne suka zubo daga idanuwan ta suka gangaro
kan kumatunta saboda tausayin mahaifin ta da
taji ya mamaye ta a hakikanin gaskiya mutum
ne mai hakuri baya son fitina amma iyatu ta
sako shi gaba da masifa har kuka ta ke sashi
shiyasa itama taji iyatun ta fita daga ranta
saboda tsanar da take nuna mata ga mugun
bakin da take binta dashi kullum tsine mata take
tana yi mata fatan cikin shege ga zagin
mahaifiyar ta da take yawan yi alhalin ko zama
ba su yi ba tare tunda sai da mahaifiyar ta ta
rasu sannan aka auro iyatun.

Ummi A'isha©OHW
🔸SANADIN GATA🔸
Na
UMMI A'ISHA
Pg 11-20
~~Ganin layi yazo kanta ne ya sata katse
tunanin da ta keyi ta tafi bakin tuka tukar ta
tara bokitin ta,ta debi ruwan ta kama hanyar
gida tana zuwa ta tsinkayo iyatu tana ta kai
komo a tsakar gida sai yi take da bakinta me za
ayi da dan riko?
Chapter 1 · 0% Book details