← Book details Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Rushewar Rayuwa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙara wanka mata wani marin yayi yana haɗa mata da shuri sannan ya janye zanen dake jikinta ya kunce zariyar Wandonshi yana kusantota,ja da baya da dinga yi harya ƙure mata, haka kamar wani dabba ya kusanceta ta baya saida yayi mata fata_fata sannan ya ƙyaleta, yana kallonta ya ce "Sajeeda aka faɗa miki don wani abu ko dan tsafi ya saka na kawoki nan, abinda yasa na kawoki nan kawai don na dinga amfani dake,gashi harna samu ƴa dake wanda dama matata bata haihuwa sanadinki naga jinina" yana gama faɗa ya maida Wandonshi ya fice yana jan ƙofar ɗakin ya rufeta

Sosai Ammi ke kuka wai ita ce ƙaddara tazoma a haka,duk lokacin da Jogu ya kusanceta yakan fama mata raɗaɗin data daɗe dashi,duk lokacin data tuna ta haifi ƴa da Jogu ta ƙazamiyar hanya takan ƙara tsanarsa da kuma Nuraddeen, yanzu ma wane hali yarinyar take wace kalar rayuwa zata taso dukda tasan Jogu yana ma ƴar so na gaskiya bazai taɓa bari wani abu ya cutar da ita ba,shiyasa ya ɗauke ƴar daga wajenta bayan ta yayeta, ya kaita can ƙasar Turai ayi renonta, dukda ga ta tsatson data fito hakan bai hana Ammi ƙaunar ƴar ba,sosai take son ƴar da kuma tausayinta, a halin yanzun babu abinda take fata sama da mutuwa

*Ɓangare guda kuwa*

Tunda sassafe muka tashi nida Hameeda muka shirya girkin da zamu kai Asibiti, sanye nake da Atamfa ɗingi riga da siket waɗanda suka amshi jikina tsam sun fito dani caras,ga ɗaurin ɗan kwalin da Hameeda tayi man wanda daga tsakiya ta buɗe ta zubo man da dogon gashina, nayi kyau ba ƙarya sai zuba uban ƙamshi nake

a hankali nake tafiyar,tunda na ƙaraso Dada ta kafeni da idanu tana kallona can kuma saita taɓe baki tana galla Mani harara Murmushi kawai nai mata ina ƙara gaisheta da ƙyar ta amsa mani tana yatsina fuska, Hameeda ce ta kalleni ta ce "wai kinga kuwa yanda kikayi kyau kamar wata Aljana, wallahi ke koni nan idan na ganki tsaf zance ba Mutum ba ce dan tsabar kyanki"

Murmushi kawai nai mata ina shigewa Mota kusa da Dada sannan Hameeda ta shigo Driver yaja, Hameeda kuwa ta zage sai surutu take mana, Dada da haushi ya isheta ta sakarwa Hameeda dundu a baya tana faÉ—in "ke don Ubanki kiyiwa Mutane shiru ke kamar redio baki gajiya da surutu kin wani dage sai bama Aljana labari kike"

"Dada da bakina fa baki hanani yin surutu wallahi Dada ki rage hassada don nasan wannan fushin da kikeyi bai wuce ganin Raihana du tafi jikokinki ba,kuma kina baƙincikin ta raɓe mu ne don karta ci arziƙi shiyasa, ke nifa Hamma Nuraim zansa ya aureta ayiwa jikarki kishiya da ita" Hameeda ta faɗa don ta ƙule Dada

banza Dada tayi mata don tasan halin Hameeda halimsu É—aya da Abdurrahim shiyasa bata cika takura masu ba,

Da sallama ɗauke a bakunansu suka shiga zaune Nuraim yake Mommy nata fama dashi akan yasha koda tea ne amma ya ƙiya ga Nafisa zaune waje guda tana danna waya, jin Sallama yasaka Nuraim ɗago fuskarshi karaf idanunsu suka haɗe dana juna wanda ya saka zuciyoyinsu bugawa,da sauri ya janye idanunsa yana haɗe rai ya kauda fuskarsa,tunda Raihana ta shigo Nafisa take kallonta sosai gabanta ya faɗi ganin kyanta da kuma abubuwan data gani don duka wani sirrin tsafi na jikin Raihana tana ganinsa,tabbas idan ta ce zatai faɗa da Raihana a haka bazata kai labari ba, dole taje ta samo wasu ɗalasiman tsafin da zata fuskanceta..........✍️

A daure a dinga sharhi dan Allah

*Masu sharhi ina godiya*

*Mariyanbaba*

*Mmn minister*

*Gimbiyar oga*

ina godiya da sharhinku

Much love oll🥰❤️🙏

Wannan kenan

*Comment,share fisabilillah*

Waɗannan su ne ƙwarin guiwata

*By Riamcool Hasken Royal star🌟✨💫*

*08109554986*
[2/6, 5:51 PM] mariamsanee5060: *RUSHEWAR RAYUWA*

*Book 2*

*By Mariam sani Riamcool*

*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, fad'akarwa, ilimantarwa da kuma nishad'antarwa_*
_(R.S.W.A)Ruwa kad'ai ke maganin k'ishi_

*Alk'alaminmu 'yancinmu*

*_Ayi man afuwa da jina shiru_*

*Bismillahirrahmanirrahim*

*Page* 80&81

____________✍️ Wannan kallon da tayiwa Raihana ya tabbatar mata da Raihana ko wacece, shin anya ma koda ta ƙaro ɗalasiman tsafin zata iya fuskantar Raihana? saboda ganin hatsabiban ruhika da iko a tattare da ita, kallon Raihana ta ƙara yi a razane,karaf suka haɗa ido, kallonta nayi ina sakar mata wani shaiɗanin murmushi wanda ya saka ƴan hanjinta hautsinawa lokaci guda,tunda na shigo na ganta na fahimci ko ita ɗin wacece sosai naci alwashin ganin bayanta,

wani hatsabibain Murmushi na ƙara sakar mata wanda yake mata nuni akwai haɗuwar gwabza yaƙi a tsakanina da ita, sosai Nafisa cikinta ya hautsina ganin lallai ta ce su fafata da Raihana to lallai rayuwanta na cikin masifaffen haɗari, dan kar a fahimci wani abu ya saka nai saurin gaida ita ina zama kusa da Hamma Nuraim na masa ya jiki ya amsa man babu yabo ba fallasa, taɓe bakina nayi nima ina kauda kaina gefe, sosai muke fira nida Mommy har take tambayana ina mai gidan nawa, Murmushi kawai nayi mata na ce "Mommy jiya ai ya sawwaƙe mun" sosai Nuraim ya kasa kunne don yaji ƙarin zance

da mamaki Mommy ta kalleni tana faɗin kamar ya ya sawwaƙe miki ki faɗa yanda zan gane"

"Ina nufin yai man saki ukku,yanzun babu wasu kingin igiyoyi a tsakanin mu"

Sosai Nuraim yaji wani masifaffen daÉ—i ya ratsa zuciyarsa, nan take ya saki ran daya haÉ—e ya kalli Raihana yana faÉ—in "Alhamdulillahi da Allah ya rabaki da jalli jogan tshoho,ke karki wani damu nida kaina zan samar maki É—an sawalwalin saurayi kamar ni É—innan" ya faÉ—a da sigar zolaya, dariya muka saka dukkammu harda Mommy,don itama tayi farincikin dawowar Raihana wajenta,

Dada kam duk firar da suke ta kasa kunne tai ka saƙe tana ji taɓe baki tayi tana faɗin "yo dama Allah na tuba waye zai zauna da Aljana? ai ƙara ya saketa daya zauna da jarfa"

wani bala'in haushin tsohuwar naji yadda take ta shiga Al'amurrana, sauya idanuna nayi ya zuwa kalar na Maciji yadda ita kaɗai zata ga sauyawarsu,kallonta nayi tazo dalla mani harara karaf muka haɗa ido da ita sosai Dada ta firgita hantar cikinta ta kaɗa wani kalar zufa taji yana keto mata, ƙara zare mata idanuwana nayi yadda zata ƙara tsorata,cikin Dada ne ya murɗa alamar zawo, da gudu ta miƙe ta shige bayi tana gudawa, sosai cikin Dada ke ƙara hautsinawa, hawaye ta share tana faɗin "oh ni Saude yau bakina marar faɗin Alkhairi ya jawo man, gashi wajen tsinanniyar masifata na taɓo Aljana"

kowa mamaki yake yadda Dada ta rikice lokaci É—aya yake, Hameeda kam sai dariya take tana faÉ—in dama gudawar ajali take uban kowa ya huta da masifarta, nima dariya ta bani yadda ta zuba da gudu amma wannan kadan nai mata,

Fitowa Dada tayi tana sharfe zufa kowa sannu yake mata "Dada mi kika ci haka ya hautsina maki ciki"Nuraim ya faɗa yana ƙunshe dariyarsa,

"Nura jaraba da masifa da kata'i duk sune naci" ta faɗa tana figar gyale don so take tabar ɗaki ko kaɗan bata son ƙara kallon Raihana, hanyar Toilet tayi wai fita zatayi duk ta ruɗe,saida tazo shiga taga ashe bayi ne "ke dan kut...... Nafisa taso ki maida ni gida" Dada ta faɗa tana ƙundumawa Nafisa ashariya

Kowa dariyarsa ya riƙe,Nafisa ta taso tana ƙara kallona don tasan abinda na aikata, mamakin shu'umancin Raihana take,jiki a sanyaye ta taso Dada ta figi hannunta da sauri suka bar ɗakin, Nafisa na aje Dada ta fita ta lalubo wata Number tana kira, ana ɗagawa ta ce "ku saki Abdurrahim bana son wani abu ya sameshi" tana gama faɗa ta datse kiran tana sakin wata nannauyar ajiyar zuciya Sabreen ta kira tana ɗagawa ta ce "Sabreen akwai fa matsala ina buƙatar temakonki sosai"

"haba Nafeesa ba ta'aziyya ba gaisuwa zaki ce akwai matsala" Sabreen ta faÉ—a cikin jin haushi

haƙuri Nafisa ta bata ta ce dan Allah komi take tazo cikin satin tana buƙatar temakonta,nan take yanke Nafisa ta janye dukkan wani shirinta da ƙullinta akan su Nuraim da ƴan uwansa don tana ganin hakan shine zaisa su rabu da Raihana (tab kina ruwa Nafisa Raihana fa bata yafiya)

Bayan kwana biyu sosai Nuraim ya warke ya samu sauƙi har an sallamo shi, zaune nake ina tunanin ta inda zani fara yaƙar azzalumai na kawo ƙarshen zalunci,takan wa zan fara,sosai nai zurfi cikin tunani,can kuma na tuna Abba, "shine wanda zan taimaka ya warke" na faɗa ina sakin murmushin jin daɗi

tsaye yake yana kallonta ya harɗe hannuwansa a ƙirji yana ta zuba murmushi shi kaɗai,
Sanye yake da T_shirt red wacce ta amshi fatar jikinsa sai wando jeans black, ga sumar kanshi da taci uban gyara sai ƙyalli take tana ƙamshi, sosai kayan jikinsa sukai masa kyau da ƙara haska Kyakkyawan fatar jikinsa, wani sassanyan ƙamshi ne ke fita ta jikinsa,a hankali ya tako ya zuwa bayanta hannu ya saka yana rufe mata Idanu ta baya

nayi nisa a cikin tunani naji an rufe man ido ga wani sassanyan ƙamshi dake tashi dariya nayi na ce "Hamma nafa ganeka baka san ni tawa baiwar ba har ta baya ina ganin mutane"na faɗa ina dariya

sakina yayi shima yana dariyar ya ce "kaji Æ´ar baiwar Mommy ki ce ke taki baiwar tana da yawa" ya faÉ—a yana dawowa kusa dani

Juya masa fararen idanuna nayi ina dariya na ce "eh mana kaÉ—an daga cikin baiwata kenan"

Yanda ta juya masa idanun sosai zuciyarsa ta wani tsinke yana dafe saitin Zuciyar

*Abba*

Sosai abin nashi yaƙi yin sauƙi kullum babu sauƙi,ga maganin ake amma yaƙi gaba yaƙi baya,kullum Sadeeq cikin damuwa da tashin hankali yake don gani yake koda wane lokaci zai iya rasa Abba wanda shi kaɗai ne ya rage masa a halin yanzun, gashi ji yake koda yaushe gabanshi na sake matsanancin faɗuwa,

Zaune yake yayi zugum kusa da Abba yana share hawayen days saba zubar dasu a koda yaushe
Chapter 9 · 0% Book details